Advertisements
Chapter 15 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 36

42K to 45K   out of 106K words

din sannan ya fesa mata body spray kala uku. Don Allah baki ji
dadin jikinki ba yanzu ya tambayeta yana murmushi. Kanta a kasa tace naji...yace
good, lesson one duk dare sai kinyi wanka kafin ki kwanta kinji ko. A hankali tace
to. Wayarsa ya kunna yace to sai da safe ya fita ya bar mata fitilar.
Gado ta haye tayi addu'o'in kwanciya sai dai baccin yaki zuwa. Duk abinda Hamza
yayi mata tun shigowarsa ta rinka tunawa tana murmushi......
[9/26, 12:32 AM] #+234 803 244 1205#: AL'ADUN WASU #45

Batul Mamman(Mrs)#




Amma yarinyar nan bata da hankali. Rai a bace ya tashi ya zaki min haka? Don me
bakiyi shawara dani ba kika fadawa maigadi kamar zamansa kike yi? Ni gidana babu
aljanu. Dariya take kasa kasa, daga abin arziki sai kayi min fada. A take ta kwabe
fuska tana shirin yin kuka....sau biyu suka ci min abinci. Wannan wace sabuwar
rigimar ce kuma ya fada a zuci. Sannan ya dan rage murya ni kada kiyi min kuka.
Kamar yace yi kukan kuwa hawaye ya wanke mata fuska. Sai dai bai sani ba hawayen
dariyar da takeyi ne ta wayance kamar kuka take. Rannan sunci min kosai a kitchen
sannan a gabanka ma suka ci min tuwo. Subhanallah.....da gaske wai ta zata aljanu
ne? Muryarsa da kyar take fita yace ke banda jaraba meye na kirga kosai har kika
san anci miki. Kuma ya akayi kika san anci tuwonki a gabana? Zuhra na kukan karya
tace ka manta da suka ci tuwon har suka saki cokalin a kasa. Kawar da kansa yayi
gefe, ni banji ba bana son sharri. Da dankwalinta ta share idanunta tace kosan zai
kai goma wanda suka ci. Hamza bai san lokacin da yace kiji tsoron Allah uku ne zuwa
hudu kawai.

Ai kuwa Zuhra ta kyalkyale da dariya sosai. Duk yadda yaso dakewa fuskarsa sai ta
bawa mutum dariya. Har yayi hanyar fita ya fadawa maigadi kada a kira malam mai
ruqiya sai kawai ya gano tsokanarsa take yi. Ya rufe bakinsa da hannunsa da ya tuna
har adadin kosan da yaci ya fada mata. Yana juyowa suka hada ido Zuhra ta kwasa da
gudu tayi sama. Binta yayi wato kin mayar dani abokin wasanki ko. Nine aljani me
satar abinci.... bata jira ya iso ba ta shige daki ta rufo kofa. Duk yadda taso ta
kasa murda key din ta rufe saboda tsoro gashi yana turo kofar. Karfinsu ma ba daya
bane sai kawai ya tura kofar.

Hanyar toilet tayi yayi murmushi kina shiga zan rufeki a dakin nan sai kin kwana
biyu. Can gefen gado ta tafi babu wurin buya....gabanta na dukan uku uku taga ya
biyota. Sai kawai ta zauna a wurin ta boye fuskarta a cikin cinyoyinta. A hankali
ya tako yazo gabanta yana murmushi sannan shima ya zauna suna fuskantar juna. Zaman
nasu yayi kusa da yawa saboda wurin yayi musu kadan. Da wata irin murya mai dadi
yace dago kanki. Sake tura kan tayi cikin cinyoyinta zuciyarta na bugawa da karfi.
Bata ankara ba taji yasa hannu biyu ya daga kan nata. Babu inda baya rawa a
jikinta don tsoro...shi kuwa wani irin yanayi na daban ya tsinci kansa. Kukan gaske
yaga tana yi sai ya soma dariya har sai da tayi mamaki. Yayi ajiyar zuciya, kin iya
tsokana amma kina tsoron hukunci ko. Shiru tayi yau babu rashin kunya su kadai a
gida. Duk laifinki ne baki taba yimin tayin abinci ba, baki damu da inda mijinki
yake samun abinda zaici ba. Kunnenta yaji da kyau kuwa? Miji fa yace. Bata iya
kallonsa ba tace kai kace na rinka dafa na iya cikina. Kuma itama kafin ta tafi
tace kada nayi girki da kai. Hannunta ya kama suka tashi muje na hukunta ki. Sake
yin alamar kuka tayi yace kinga ni na dena yarda da kukan naki na karya.

Plates din ya dauka yace babu ruwa ne ko juice. Akwai ta amsa da mamakin me zaiyi.
Ki dauko ki hado da wani spoon din. Falonsa ya shige da abincin. Sai a lokacin tayi
ajiyar zuciya....wai amma ta tsorata. A tray ta dora jug cike da zobo mai sanyi da
cup da kuma spoon din da yace ta dauko. Samunsa tayi a falonsa yana zaune a kasa
yana cin abincin. Murmushin da tayi yayi masa kyau yace na dena satar abincin a
bayan idonki. Gabansa ya nuna mata zauna muci.

Dawa??? Ta kwalalo idanu tana kallonsa. Tashi yayi ya zaunar da ita. Punishment
dinki kenan na tsokanata kici abinci tare dani. Idan baki ci ba kuma nayi bakinki
zan dalle. Don Allah kayi....hannu ya daga mata. Kada ki bata bakinki ki bani
hakuri. Daga yau har Izzy ta dawo zaki rinka yin abinci dani. Tace to amma ni
bazanci da kai ba. Harara ya sakar mata. Don ma kin samu Hamza zaici abinci plate
daya dake...kuma wallahi bana son kazanta. Idan zakiyi na dare zan zo inspection
naga yadda kike girkin don nasan halinki.

Ba yadda ta iya dole ta zauna suka ci. Sai dai bata iya sakin jiki ba don da ta
diba zaice lomarta tayi girma ko kuma tayi kadan. Haka yayi ta mata har suka gama
ta kwashe komai ya wanke. Zobon kuwa bayan ya shanye cewa yayi ta hada masa
wani...zobo ma yana cikin abinba Izzy bata masa. Shima na masu karamin karfi ne.

Da daddare tuwon semovita yace tayi da duk miyar da ta ga dama. Su Hamza an sami
sake Izzy bata nan. Miyar kuka ta kada taji wake da nama. Bai iya boye mata
santinsa ba. Sai da ta gyara kitchen din tsaf ta tafi dakinta.

Wurin shadaya da rabi tana kallo aka dauke wuta. wayarta tayi saurin janyowa daga
jikin chaja sai taga ashe bata yi chajin ba. Chajar bata shiga jikin socket din da
kyau ba, ga wayar dama bata rikon chaji yanzu. A take ta fara jin tsoro ga zafi. Da
bin bango ta janyo bargo daga gadonta da pillow tayi shimfida a gefen kofa. Bata
son duhu ko kadan shiyasa take kwana da fitila a kunne ko ta kunna torch light din
wayarta.

Hamza na fesa bodyspray ya fito daga wanka aka dauke wuta. Wurin minti biyar baiji
maigadi ya tayar da inji ba sai ya sauka. Maigadi yayi yayi injin yaki karbar wuta
kuma akwai mai a ciki. Dama irin babban nan ne da yake daukar har AC da fridge.
Sunyi iya kokarinsu abu yaci tura Hamza ya kira mutumin dake masa gyara yace ko
zaizo da safe. Mutumin yace yana kauyensu yaje karbar kudin auren kanwarsa amma
jibi zai dawo. Hakan baiyiwa Hamza dadi ba ya yanke shawarar neman wani washegari
domin zafin gari sai ya hana mutum bacci. Dakinsa ya koma sai ya tuna da Zuhra yace
bari ya doba ko tayi bacci.

Tsoro yasa Zuhra ta dukunkune kanta cikin bargo duk zafin da akeyi. A hankali ya
bude kofar dakin gudun kada ya tasheta idan baccin take yi.

Dishi dishi take ganin inuwar mutum da yayi hanyar gadonta. A ranta tace shikenan
barawo ya fado dakinta. Tashi tayi da sauri zata gudu ko da bin bango ne taje dakin
Hamza taji anyi saurin rungumota ta baya. Sandarewa tayi a wurin don tsoro kamar ta
saki futsari, gumi ya rinka tsatstsafo mata. Hamza bai ankara ba yaji ta kai masa
naushi a ciki ta soma ihu...Wayyo Allah barawo. Duk da zafin cikin bakinta ya samu
ya toshe da hannunsa ai kuwa ta gantsara masa cizo iya karfinta.
[9/26, 8:58 AM] #+234 815 728 4163#: AL'ADUN WASU #47

Batul Mamman(Mrs)#
Zuhra na idar da sallar asuba ta sauka zuwa kitchen. A zafin nan da rashin wuta
tana tsoron kada naman cikin fridge din ya lalace. Fito dashi tayi tana wankewa
Hamza ya dawo daga masallaci ya sameta. To acici me kike yi a kitchen da asubar
fari. Muryarsa taji kamar hancinsa a toshe yake. Amma yau gabadaya kunyarsa take ji
da ladabin musamman ta gaisheshi. Sannan tace nama zan tafasa na soya kada ya
lalace saboda babu wuta. Ta sunkuyar da kanta, ya jiki naji kamar yau murar tafi ta
jiya. Hamza yace eh amma da sauki. Yaji dadin yadda har ta fuskanci bashi da lafiya
ta nuna damuwarta. Kallonta yake yadda take aiki ga hijab dan madaidaici a jikinta,
hakan bai hanashi tuno surarta da ya gani ba daren jiya duk da duhun dakin. Ji tayi
kamar ana kallonta ta dan juya suka hada ido. Murmushi kawai yayi mata ya tafi.

Flask ta dauko sabo na tea ta wanke sannan ta tafasa ruwan zafi da lipton, citta da
kaninfari. Ta soya kwai guda uku da albasa yar kadan saboda bata sani ba ko Hamza
na son kwai da albasa. A karamin plate ta zuba ta rufe shi da wani irinsa sannan ta
dora mug na shan tea da teaspoon a tray. Bread daya ta bawa maigadi ya siyo musu
jiya gashi bata da dankali ko doya. Duka bread din ta dora masa da kayan tea. Kasa
shiga falon nasa tayi tana tunanin ko tayi masa karambani ne.

Sai da ta gaji da tsayuwa sannan tayi sallama ta shiga. A kwance ta ganshi kan
doguwar kujera ya zurfafa a tunani. Ba komai ke damunsa ba kamar harkar office ga
mura tayi masa kamu sosai. Sallamarta ce ta tashe shi ya zauna. Batayi magana ba ta
ajiye masa tray din a gabansa sannan ta koma ta dauko flask din. Kallon kayan
yakeyi har ta dawo...ta ajiye flask din tana dan sosa kai tace uhmm dama nasa citta
da kaninfari a ruwan. Idan baka so sai na tafasa wani. Dago kansa yayi jikinsa duk
babu kwari sosai yace me yasa kika dafa da cittar? Naga kana mura ne zai bude maka
kirji. To nagode da kulawarki, taimaka ki hada min amma kada kisa sugar. Tausayi ya
bata sosai bata yi masa musu ba ta hada masa sannan ta fita ta koma kitchen.

Kazar dama daya ce tayi mata saura ta wanketa sosai ta hada da kayan kamshi da
jajjagen kayan miya tayi farfesu. Yana kan wuta ta wanke shinkafa ta baza a tray
sannan ta shiga yanka su cabbage, albasa, attaruhu, karas da koren wake. Harda
grating din tafarnuwa kadan. Duk bayan ta gama ta sake komawa falon ko ya gama cin
abincin. Ya gama amma fa bread din da rage bazata iya raba musu ita da maigadi ba
saboda dama ba wani babba bane. Duk yadda take jin yunwa da ta kwashe kayan kwai
biyu ta soya ta hadawa maigadi tea da bread din. Tace idan ya gama zai kai mata
nikan shinkafa. Talle maigadi yanzu duk gidan babu wanda yake ganin girmansa kamar
Zuhra yace to Hajiya nagode. Kitchen ta koma ta kashe farfesun sannan ta fara soya
sauran naman. Tana yi ta hada tea ta zauna a kan kujera tana sha don bazata iya cin
kwai zalla ba.

Bayan yaci abinci yasha magani jikinsa yayi dan kwari. Shiru babu motsin Zuhra sai
yaji babu dadi. Sama yazo hawa yaji alamun har yanzu tana kitchen. Tea ya hangota
tana sha shi kadai. Shiga yayi yana kallonta tea kadai kike sha ba bread? A'a na
cinye bread din ne. Yadda tayi magabar yasa bai yarda ba ya duba dustbin dinta ina
ledar. A zuciyarta tace kaji mutum da bin kwaf. Shiru tayi ba amsa yace bakya jina
ne? Na bawa maigadi....kin me? Dama bashi da yawa kika bani, kuma sauran kika bawa
maigadi to ke me zaki ci. Baki da Indomie ne? Murmushi kawai tayi ai yanzu zan dora
abincin rana bana jin yunwa ma. Mamakinta yake...yanzu kamar Zuhra tasan ta hakura
da abinda take so domin wani. Ji yayi ta sami wani gurbi a zuciyarsa. Hannunta ya
kama suka koma falo...meyasa baki fada min ba kika yi shiru zaki kwari kanki. Wasa
ta soma yi da yatsunta taki kallonsa..ai naga baka da lafiya kuma zan iya jira.
Lallai yau ya koyi darasi a wurin Zuhra...shi bai taba bata kudin siyan wani abu ba
yasan da kudinta ta sayi bread din kuma ta bashi. Kallon da yake mata yasa duk ta
kasa sakewa . Shi kuwa hannu yasa yana shafa gefen fuskarta har sai da tsigar
jikinta ta tashi. Nagode kinji, Allah Ya baki lada, kin nuna damuwa da rashin
lafiyata sannan kin iya hakura da abinci don wani yaji dadi. Amma daga yau ki rinka
fadamin duk abinda kike bukata, tace to cike da kunya sannan ya saketa ta koma
aikinta zuciyarta na bugawa da sauri. Sauran naman ta kwashe ta bawa maigadi nikan
shinkafar sannan taje tayi wanka. Har ta dauko foundation sai ta tuna da kwalliyar
da ya gyara mata ranar da suka fita. Irin yadda yayi mata haka tayi aka dauki
deodorant da body spray aka fesa. Sannan kayanta ma suka sha turare mai kamshi.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #48

Batul Mamman(Mrs)#




Hamza na falonsa ya gama waya da assistant director akan wasu ayyuka. Duk yayi musu
bayanin yadda yake so ayi aikin da alkawarin idan yaji sauki anjima zai shiga
office. Bayan ya gama Izzatu ya kira. Hira kadan suka yi ya gaisa da su Khalifa
tace masa tana son wucewa Abuja idan an gama bikin. Dad dinta ne zai tafi Japan
shine zata je yi masa sallama sai wata lahadin zata dawo. Ransa a bace yace Izzy ba
haka muka yi dake ba. I need you here, bama ni da lafiya. Izzy tace kayi hakuri
baby amma Dad zaiyi wata biyu kaga ya kamata naje muyi sallama. Idan yace bai
amince bama yasan sai taje ko tasa mamanta ta kira shi a waya. Abin mamakin ma
tsakaninsa da Allah rashin dawowar tata bai wani dameshi ba. Shi da baya iya nisa
da ita...yace to su Khalifa kinsan zasuyi missing school da yawa ko. Eh zasu taho
da Tala ranar lahadin amma da Nana zan tafi Abujan. Bye baby, love you. Dip ta
ajiye wayar, rike tasa wayar yayi a hannu yana mamakin Izzatu. Ko sau daya bata yi
masa sannu ba duk da muryarsa data canja ko bai fada ba za'a gane bashi da lafiya.
Har tunani yake yi wai dama haka take masa ko yanzu ne dai saboda bikin da suke yi.

Zuhra na saukowa aka kawo wuta. Tsabar murna yasa tayi ihu har sai da Hamza yaji.
Da sauri ya fito yaga abinda ya sameta sai yaga tana ta juyi a falo tana kiran
nepa, nepa.... baki ya rike yana kallon ikon Allah, sai kace wata karamar yarinya
sai tsalle take yi. Riga da skirt ta saka na yadi mai laushi. Dinkin ya kamata tsam
ta daura dankwalinta. Duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi masa kyau.
Gabadaya surar jikinta ta fito sai tuna masa daren jiya take. Sannu da aiki yar
kauye ya fada yana tsaye a bakin koma.

Da farko tsoro taji har zata gudu sai kuma ta tsaya ta fara neman wuyan hijab dinta
ta saka. Jira yayi ta saka din sannan ya karasa gabanta ya kama kasan hijabin.
Hannunta tasa tana neman kwacewa ya janyota gabadaya jikinsa. A take ta fara rawar
jiki tana cewa kayi hakuri na dena tsallen. Sosai ya rungumeta yana kallon fuskarta
ya cire mata hijab din cikin nutsuwa sannan ya saketa. Kirjinta ta fara kokarin
rufewa yace ke jiki ba jiki ba kiyi ta wani rufewa. Haushi taji ta dan tura baki
sai ta fara juyi a gabansa tace a hakan? Wallahi ina da jiki, kaga fa...dariyar da
yake mata yana cewa juya na gani da kyau yan mata yasa ta bar abinda take yi ta
soma kokarin kwatar hijab dinta. Hannunsa ya daga sama tace to na bar maka bari na
dauko wani. Baifi taku biyu tayi ba ya jawota jikinsa. Hannuwansa na gaban kirjinta
ya dan rage tsaho daidai da kunnenta...ki hakura da hijab din kinga akwai zafi.
Kuma naga ashe kina da jikin da zan kalla. Yana magana taji yasa hannunsa a
kafadarta yana mayar mata da hannuwan breziyarta da suka fito. Daga daren jiya zuwa
yau Hamza yasa Zuhra tsananin jin kunya. Yadda ya rufe mata jiki gabadaya ta baya
yasa ta kasa motsi. Zuciyarta ce kawai take bugawa da sauri. Tana wannan yanayin
har ya saketa bata sani ba. Ganinsa kawai tayi a gabanta yana murmushin da yanzu
take yawan gani tare dashi. Hada ido suka yi ta kawar da kanta, a hankali tace duk
kasa ni jin kunya. Sai ka rinka wayon taba min jiki. Kuma dai kasan babu kyau. Ya
daga gira kina matar tawa. Tace to ba sakina zaka yi ba. Tana fada ta wuce kitchen
ta barshi a tsaye. Maganar Zuhra tasa ya shiga damuwa sosai.

Dambun shinkafa ta hada mai rai da lafiya. Ta rinka yawo tsakanin falo da kitchen
har abincin ya dahu. Daya da yan mintuna ta gama ta mikawa maigadi. Shi kam yana
jindadin sauyin da ake samu na girki a gidan nan. Gashi harda ruwan sanyi tunda an
kawo wuta. Na Hamza ma ta hada masa komai a tray ta shiga falonsa ta ajiye sai dai
baya ciki. Yunwa take ji sosai domin yau tayi dauriya. Nata tayi niyar zuwa ta diba
a kitchen sai taga wata kofa ta bude ashe da toilet a wurin. Tashi tayi zata gudu
yace dawo ki zauna fita zanyi, da alama alwala yayi. Zan canja kaya naje office
zaman gidan ya isheni. Ba komai ke damunsa ba sai maganar Zuhra ta saki. Ya rasa
gane yana son zancen sakin nan yanzu ko kuwa. Da 'yar damuwa a fuskarta tace amma
baka da lafiya, ka hakura mana. Yana jindadin yadda take kulawa dashi yace bazan
dade ba in sha Allah. A gaban tray din ya tsuguna Me kika dafa mana ne...yar
kazama ta iya girki. Tray din ta dauka tunda ni kazama ce ka nemi wani a waje. Yi
hakuri ki kawo kinji, ai kinfi kowa tsafta a gidan nan. Bubbude flask din yayi yaga
dambun shinkafa tayi da farfesun kaza. A take yawunsa ya tsinke. Wai me yake
damunka ne Hamza da kaga abincin sai ka rude kamar wani mayunwaci. Kinsan abincin
da Hajiya tafi so kenan dambu ko wane iri ne. Zuhra tace da gaske? tare da dauke
flask din da ta zuba masa nasa. Bari naje na juye sauran ina ga zai kai cin mutum
uku idan aka hada. Tana magana tana neman fita daga falon. Hamza yace ke dawo
bangane me kike nufi ba? Ya daga kawo min abinci ko tasting banyi ba kin dauke.
Buga kafa tayi irin ya ma zai ki ganewa...yanzu fa kace min Hajiya na son dambu.
Zan hada da sauran sai ka kai mata. Bari nayi sauri ko taliya na dafa mana tunda
kaima fita zaka yi.

Tashi yayi da sauri ya kamo wuyan rigarta ta baya ya dawo da ita...haba yar kauye
daga magana sai ki dauke abincin. Ya dan yi mata kalar tausayi, nima ina son ci don
Allah ki ajiye. Zuhra ta dan harare shi to Hajiyan fa? Flask din ya soma ja itama
tana ja. Da taga yafi karfinta sai tace to bari na zuba maka kadan sai ka kai mata
sauran. Kaga duk duniya ga namiji bashi da abinda yakai mahaifiyarsa daraja. Kafin
na tafi in sha Allah idan kana so kullum duk abinda take ci ka fada min sai na dafa
mata. Ummana tace idan nayi aure

15 / 36