Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
A haka ya koma gida duk
yadda Izzatu taso ya saurareta ko abinci ya ci abu ya gagara.
Washegari da safe ya bawa Tala umarnin ta gyara dakin Zuhra kafin ya dawo. Da
murnarta tace an ganta ne?
Hamza yayi murmushi mai ciwo...a'a amma bana so ta dawo ta rasa wurin kwana. Yadda
yayi magana yasa Tala hawaye. Me yasa iyayensa suka ki sanar dashi inda matarsa
take. Sajensa duk yayi wani iri saboda rashin gyara wani gashin yafi wani tsaho.
Ruwan tea kawai yasha ya fita zuwa office din 'yan sanda da suka kirashi an tsinci
wata mata. Yaje ya tarar ba Zuhra bace kafin ya fito Alhaji ya kirashi yana masa
tuni gobe ne za'a kawo kudin Adabiyya da Hamida kuma za'a saka ranar aure. Shiru
yayi na dan lokaci sannan yace yanzu Alhaji ni baza'a yafe min zuwa ba? Duk su Kawu
basu isa ba sai nazo?
Alhaji yace kaine babba a gidan nan Yaya rashin zuwanka bazai nuna abu mai kyau ba.
Kuma ina maganar Zuhra ta kwana? Har yanzu baka ce komai ba.
Ina kan dubawa Alhaji yanzu ma ina police station.
Tausayin dan nasa yaji yace ka koma gida haka gobe kuzo kai da matarka. Na sami
labari ina tunanin an kusa ganinta. Bai jira amsar Hamza ba ya kashe wayar.
Cikin minti talatin Hamza ya iso gidan ya dami Alhaji sai ya fada masa labarin da
yaji. Alhaji yace ya bari sai gobe idan ya tabbatar amma yazo tare da Izzatu idan
an gama karbar kudin zasuyi magana.
***
Zuhra na daki tun shigowar Hamza tana kuka. A haka Mama ta shigo ta sameta sai tace
abu ne ya fada mata a ido.
Idanun Mama suka ciko da hawaye na tausayi. Wurin Alhaji taje tana rokonsa ya bar
Hamza yaga matarsa haka. Musamman Zuhra da take da ciki ga damuwa. Alhaji yace zuwa
gobe in sha Allah zasu ga juna. Mutumci yake son siya mata.
Hamza bai taba ganin dare mai nisa kamar na yau ba. Zuciyarsa ta gama bashi Alhaji
ya san inda matarsa take. Tunda ya koma gida ya fadawa Izzatu zasu je gidan za'a
kawo kudin auren kannensa. Baki ta turo tana mita. Tasan aiki kawai zasu sakata.
Tun karfe takwas Hamza yayi wanka ya kuma dami Izzatu sai da tayi. Batun office
dama tunda ya dawo bai waiwayesu ba. Suma sun masa uzuri saboda ya dade baya tare
da iyalinsa.
Tara na safe suka isa gidansu. Lokacin mutan gidan basu gama tashi daga bacci ba.
Ita dai Izzatu ranta ya gama baci amma yadda Hamza ya zama masifaffe tunda ya dawo
baiga Zuhra ba dole tayi hakuri.
Kowa ya fito sai yayi mamakin ganinsu. Adabiyya ta fadawa Zuhra yazo dadi ya isheta
saboda Mama ta fada mata yau zata koma gidanta. Duk wani shiri da ya kamata mace
tayi anyiwa Zuhra. Hatta salon taje an gyara mata gashinta ga lalle baki da ja irin
wanda Hamza yake so. Kana ganinta kaga amarya da dan karamin cikinta da yake fitowa
idan kaya suka kama ta.
Ana aikin soye soyen da za'a kaiwa baki idan sun zo Mama ta kira Zuhra kitchen ta
tambayeta ko zata iya girki. Zuhra tace eh saboda yanzu bata wannan tashin zuciyar.
Mama tayi murmushi to maza ki dafawa mijinki abinda kika san zai masa dadi zansa
ayi gadin kitchen har ki gama. Allah Yayi muku albarka. Murmushi kawai Zuhra tayi.
A yadda su Hamida suka ce mata Hamza ya rame sosai kwana uku kawai sai tayi masa
tuwon shinkafa da miyar taushe. Nutsuwa tayi tayi girkin yadda zaiyi dadi sosai. Ta
dai sha tsiya wurinsu Mariya amma yau ko a jikinta.
****
Hamza ya gaji da jan lokacin da Alhaji yake masa amma haka ya hakura don babu yadda
zaiyi. Izzatu duk aikin da akeyi tana zaune a wurinsa a falo. Su Hajiya kawai taje
ta gaisar a dakunansu ta sake komawa wurin mijinta.
Suna nan zaune har su Ibrahim suka zo sannan 'yan uwansu da suka kwana a gidan maza
suka fito zuwa falon Alhaji. A nan aka hadu da dangin mazan suka yi abinda ya
kawosu aka saka biki bayan sallah babba.
Da kyar Hamza ya iya bari suka gama tafiya ya matsa kusa da Alhaji.
Alh Nasiru yayi dariya babana ban sanka da zumudi ba. Yau ance a kusan a gidan nan
ka kwana.
Hamza dai babu amsa sai jiran bayanin da Alhaji yake dashi. Alhaji ya tura Nura ya
kirawo su Hajiya da Izzatu.
Hankalinta kwance tana tunanin kwanakin da aka bawa Hamza sun kare Alhaji zaisa ya
saketa.
Duk sun zauna harda su Ibrahim. Alhaji ya kalli Izzatu yace... Izzatu ina so ki
dubi girman Allah ki fada mana inda kika kai Zuhra. Daga ke sai ita ne a gidanku
saboda haka ko zata bar gidan na tabbatar akwai sa hannunki a ciki.
Izzatu ta firgita ta daga kai suka hada ido da Hamza. Shima kallonta yake yi ya
kasa gane dalilin Alhaji na yi mata wannan tambayar.
Idanun kowa a kanta suke tace ni fa bansan inda take ba. Tashi nayi da safe kawai
naga bata nan. Har nemanta naje yi banganta ba. Wallahi Baby ka da ka yarda da duk
abinda za'a fada maka sharri ake son kulla min. Ba tun yau ba nasan babu mai
kaunata a gidan nan. Hakuri kawai kuke yi....
Tsawar da Hamza ya daka mata ce tasa tayi saurin yin shiru. Izzy idan kina da
masaniya akan batan Zuhra ki fada min tun wuri. Sama da wata biyu Allah kadai Yasan
halin da take ciki.
Alhaji ya dubi iyalinsa yace ya isa haka Yaya. Kunga dai na bata dama ta wanke
kanta wurin mijinta sai ta zabi tayi karya. To ni nasan inda Zuhra take amma tunda
bazaki fadi gaskiya ba ku tashi ku tafi kawai.
Hamza duk ya gigice yace Izzy zan saba miki wallahi. Ki fadi abinda Alhaji ke
tambayarki. Me kika sani game da batan ta?
Izzatu ta dage bata san komai ba. Alhaji yace to ni na sami labari kin hada bako da
wasu sunzo har gida sun saceta ko ba haka bane Ibrahim? Ibrahim yace haka ne don
akwai shaidu. So suke ta fadi gaskiya da bakinta.
Tana jin haka ta fara zare ido saboda yadda taga Hamza yayo kanta... wallahi karya
ake min. Duk wanda ya fada karya yake yi. A airport kawai na barta a daren da ka
tafi na koma gida ni kadai.
A ransa Hamza yaji maganar....a sanyaye yace me kike nufi Izzy?
Ibrahim yace bari nayi maka bayani kamar yadda idanunmu suka gane mana. Hamza dai
har kuka yayi da yaji a irin halin da suka ga Zuhra a gaban sojoji. Shiyasa babu
wanda yayi yunkurin dakatar dashi a lokacin da ya kwadawa Izzatu mari har uku.
Zaiyi na hudun Alhaji ya hana shi. Hamza ya nunata da yatsa...nasan baki da hankali
wani lokacin amma bansan ke mahaukaciya bace sai yau. Yanzu da sun harbeta kina
tunanin zaki cigaba da rayuwa ne? Duk abinda kike yi ina kawar da kai sai da kika
kureni. Izzy har mahaifa kika cire da ciki da gangan na cigaba da zama dake. Me
kike so ne a rayuwarki?
Yana hawaye su Hajiya suna yi saboda jin irin abinda tayi. Alhaji yace nayi hakuri
da halinki Izzatu amma wannan karon zan nuna miki matsayina a wurin mijinki. Kai
Hamza yi mata saki daya....
Gaban Alhaji taje ta durkusa tana kuka tana rokonsa yayi hakuri. Fuskarsa a hade
yace ko baka ji bane?
Hamza yace na sakeki saki daya.
Alhaji yace nagode kara mata daya...
Wannan karon gabansu Hajiya ta koma tana kuka tana rokon su rufa mata asiri.
Bata bawa kowa tausayi ba duk da basu taba tsammanin haka daga Alhaji ba. Hamza ya
kara cewa na sakeki Izzatu.
Alhaji yace to saura igiya daya tsakaninku. Idan kina da hankali sai kiyi
tattalinta har karshen rayuwarki domin na bashi dama ranar da kika sake kwatanta
irin haka ya cika miki na ukun. Allah ne yayi Zuhra na da sauran kwana a yadda
sojoji ke harbi idan suna zargin mutum. Ki koma gidanki kiyi idda wannan kuma
umarni ne na addini ba nawa ba. Hamza ka fada mata idan ta kuskura taki zama a
gidan to sauran igiyar ma zaka karasata.
Kamar mutum mutumi haka Hamza ya zama ya maimaita abinda Alhaji yace. Zuciyarsa na
can tana saka masa abinda zai faru ba don Tala tayi tunani ba.
Kukan Izzatu duk ya cika falon Alhaji yace ko tana da sauran magana tayi saurin
girgiza kai. Kada yayi sanadin rabata da farincikin rayuwarta. Yace Nura tashi ka
kaita gida. Nura ya fara kunkuni, yaushe zai manta yadda yaga Zuhra babu ko
dankwali sojoji sun zagayeta da bindiga. Don babu yadda zaiyi ne suka fita tare
tana kuka.
Suna fita Alhaji yace Yaya ka mayar da matarka yanzun nan. Hamza ya dago jajayen
idanu yace Alhaji bazan iya ba. Da kanka kace na saketa.
Ni bani da burin rabata da 'ya'yanta. Ka mayar da ita amma kada ta sani sai tayi
wata uku a tunaninta idda take. Kila idan anyi sa'a ta canja hali a dan lokacin.
Nayi haka ne don tasan cewa ba'a wasa da ran dan Adam. Idan bazaka iya ba kuma zan
mayar da Zuhra ga iyayenta.
Ba shiri Hamza yace na mayar da ita. Mama don Allah ina Zuhran take?
Muryarta yaji daga bakin kofa tana sallama. Dama a tsaye Hamza yake tana shigowa
yayi saurin rungumeta ita kuma tana kokarin ture shi. Su Hajiya kowa sai kawar da
kai yake yi. Alhaji da yaso tarasu yayi musu nasiha yace kai Yaya ku bar wurin nan.
Sam Hamza bai ji ba ya fara neman bakin Zuhra.
Alhaji ya daga murya yace kai Hamza zan saba maka. Nace ku bar wurin nan. Wani
murmushi yayi ya juya ya kalli iyayensa. Sai a lokacin yaji kunya yaja hannun Zuhra
wadda take jin kamar ta nutse a kasa suka fita.
Mama ta kwashe da dariya. Alhaji ni bazan ce komai ba sai Allah Ya kara. Dama rabon
kaga rashin kunya yasa kaki bashi matarsa da wuri. Dariya suka soma yi harda Hajiya
sai suka kula da Ibrahim da ya rufe fuska da hula. Alhaji yace bana son gulma kaima
tashi ka tafi wurin matarka. Da gudu ya fice yana dariya.
****
Rasa dakin da zai shiga da ita yayi ya ja hannunta zuwa dakin Nura. Yana rufe kofar
ya juyo yana kallonta. Sai da ya juyata a gabansa yace Cutie babu inda yake miki
ciwo? Dariya take yi tace Ya Hamzana babu.
Ya rungumeta sosai yana suna ajiyar zuciya. Ya dago kai yana shafa bakinta...I miss
you Cutie. Kiyi hakuri don Allah ban kula dake yadda ya kamata ba. Duk abinda ya
faru laifina ne. Yakamata ace naga tafiyarku kafin na koma ciki.
Hawaye fal idonta tace duk ya wuce. Zai sake magana ta rufe masa baki da nata. Sun
jima a haka sannan yace Cutie duk kin canja kin kara kyau.
Hannunsa ta kama ta zira a karkashin rigarta. Ya ware ido sosai yana
kallonta...tauri fa nake ji Cutie. Sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta kasa
tana murmushi. Ya sa hannuwansa biyu ya dago kan nata....are you pregnant? Maimakon
ta bashi amsa sai kawai ta rungumeshi. A hankali tace wata hudu kenan. Sakinta yayi
ya durkusa a gabanta yana shafa cikin cike da kulawa...baby your daddy is back.
Yayi kissing cikin sannan ya tashi ya kura mata ido. I love you so much Fatima.
Tace nima haka..
Hamza yace ban karba ba.
Tayi dariya I love you Ya Hamza.
Wani kallo yake binta dashi ya kama hannunta muje ki dauko mayafinki mu tafi gida.
Tace har girki nayi maka kuma su Hajiya basu ce na tafi ba.
Kinga na baki minti goma ki dauko abinda zaki dauko mu tafi idan ba haka ba kuma na
maimaita irin abin dazu a gabansu. Fita tayi cikin farinciki ta dauko dan kwandon
da ta saka flask din abincin. Dakinsu Adabiyya ta shiga daukar mayafi su Jidda suka
fara tsokanarta. Mariya tace kinga wuce ki tafi Mama tace sun yafe sallamar wai
wadda kuka yi dazu ta wadatar. Zuhra taji kunya sosai ta fita suka rakata har bakin
mota suna ta shakiyanci. Ganin Hamza ya hade fuska yasa suka koma ciki. Shi kuma ya
tada mota sai gida.
[11/3, 6:36 PM] Angel Teema: AL'ADUN WASU #78
Batul Mamman(Mrs)#
Saida suka gama wanka sannan Hamza ya dauko Zuhra. Bai ajeta ko'ina ba sai kan gado
ya dauko vasseline dake kan dress mirror ya mikawa Zuhra gami da lakutar hancinta
yace Cutie sai ki qarasa aikinki. Murmushi tayi gami da rufe fuskarta da tafin
hannunta alamar kunya janyota yayi jikinsa sannan ya fara magana a kunnenta chan
qasa yace Cutie tunda bazaki qarasa aikinki ba bare naje Izzy ta min. Dagowa tayi
da sauri suka hada ido sannan ta dauki vasseline din dake gefensu ta shiga shafa
masa cikin shagwaba tace nifa ba haka nake nufi ba Yaya Hamza, yace to yayane Cutie
ya qarasa maganar cikin dariya. Zumburo baki tayi, kissing dinta yayi sannan yace
to kiyi haquri My Cutie.
Haka suka gama shiryawa cike da nishadi suka sakko qasa. Izzatu dake zaune a palo
ganin Zuhra na sakkowa tare da Hamza ta miqe da sauri ta nufi inda suke da murmushi
gami da rungumeshi tana fadin Baby ga abincinka yana jiranka a dinning, a hankali
ya saci kallon Zuhra data hade rai sannan ya ture Izzatu yana fadin bana son shirme
Izzy. Wait for Batul Mamman lol.
Da kuka Izzatu ta fito daga motar Nura. Maigadi ya biyota yana tambayar ko lafiya.
Bata bashi amsa ba sai kallon banza. Murya a sama tana kuka ta shige ciki. Nura dai
tsaki yayi ya ja motarsa.
Tala ma da yaran duka babu wanda ta kula ta wuce ta tafi dakinta. Wai ita Hamza
zaiyiwa saki har biyu? Lallai dan Adam ba'a ci masa laya. Irin soyayyar da suka yi
tun kafin suyi aure ta zauna tana tunawa. Bakincikinta ya karu ne saboda a ganinta
ba karamin kaskanci bane ace an saketa saboda wata Zuhra. Yarinyar da bata jin ko
brush din kirki ta iya lokacin da Hamza ya aureta. Rasa mafita tayi ta dauki waya
ta kira Raliya. Babu abinda ta ragewa mahaifiyar tata na dangane da abinda tayiwa
Zuhra zuwa halin da take ciki yanzu.
Raliya ma kukan ta soma yi tace Izzatu kinga abinda nake ta ji miki tsoro sai da ya
faru. Ban ga ranar bin al'adun wasu don ka burge wasu tsiraran mutane ba.
Kwalin tissue din da ta kusa kararwa daga shigarta daki ta kuma janyo wata ta goge
hawaye....Mum ya zaki ce ina bin al'adun wasu. Duk abinda muke yi da ai tare dashi
mukeyi. 'Yan wadanda nayi da baya so sosai kadan ne. Kuma naga shima dan zaman da
yayi a Canada ya isa ace ya waye da dabi'unsu. Ace mu kullum 'yan Nigeria babu wani
canji a rayuwarmu. Ni a ganina kawai gajiya yayi dani amma babu wasu al'adun wasu
da nake yi.
Ta yaro kyau take Raliya ta fada tana tuna irin sakacin da ya samo asali daga wurin
Alh Sunusi a fannin tarbiyar 'ya'yansu. Shine ya dage sai su barsu su sake bayan
sun bar kasarsu. Tun Raliya bata jindadin yadda 'ya'yansu ke sajewa da na turawa
ta fannin dabi'a har ta fara so musamman idan suka zo gida Nigeria suka shiga cikin
'yan uwa. Dan turancin da sukeyi da 'yar fitsara shi yake burge mutanenmu. Sai kaga
kowa na kokarin kyautata musu tamkar anga 'ya'yan wani shugaban kasa. Kuma irin
haka dama halinmu ne musamman Hausawa. Da 'yan uwanmu sun tafi kasar waje mun rinka
shela kenan sai kowa ya sani. Idan suka zo ganin gida kuwa ba'a magana. Kowa jiki
na rawa yana tasa bajintar.
Raliya tayi ajiyar zuciya....yanzu duk bazaki gane abinda nake nufi ba kila sai nan
gaba. Amma ina so ki sani namiji duk inda yake indai akwai sauran mutumci a tare
dashi to yana son a kyautatawa iyayensa. Sai kika yi rashin sa'a gidan Alh Nasiru
tsarin rayuwarki bai burgesu ba. A zatonki sonki ne basa yi shiyasa kuka yi ta
samun sabani da Hamza da farko har sonki ya rufe masa ido ya koma yana biye miki.
To kada ki manta dama tun da fari ga irin tarbiyar da ya tashi da ita yake hakuri
da irin taki tunda ke kinki canjawa don ki faranta masa. Sai Allah Ya kawo wadda
zata yi masa yadda yake so kafin yace yana so. Ai wallahi dole ra'ayinsa ya juya
can. Gashi ke kuma sai shirmenki ya karu ninki akan na baya.
Izzatu dai kuka take tana sauraron mahaifiyarta. Raliya tace kina jina kuwa? A
hankali tace eh.
Duk abinda kika yi masa kinga ai ya hakura musamman cire mahaifa. Amma yau da
yarinyar nan ta mutu wallahi banda saki uku nasan sai yasa an kulleki. Kinyi sake
tauraronki ya dishe a zuciyarsa. Abinda Larai take ta korafin zai iya faruwa kenan
duk muka banzatar da ita. Yanzu ki bari zan kira Ustaz dan gidan Kawu mai zare na
tambayeshi game da dalilin cewa sai kinyi idda a gidan. Kafin nan don Allah Izzatu
ki kama kanki kinji ko. Zan kiraki idan munyi magana.
Yau daya a rayuwarta da take ganin ta rasa abu mai matukar mahimmanci ta nutsu ta
saurari mahaifiyarta. Idan har akwai yadda zatayi ta sake mallakar Hamza to zata
yi. Abu daya ne bata yarda dashi ba saboda tashin turai da tayi shine bin malaman
tsibbu da bokaye. Kyankyaminsu take ji kuma gata da tsoron zuwa irin wuraren nan.
Ta taba kawa da ta kaita wai a basu maganin mallaka. Tunda taji ana zancen tayi
masa lemo da jinin al'adarta na ranar karshe a wata bata koma ba. Bokan na fada
tana amai ma.
****
Babu wata hira tsakanin Hamza da Zuhra a motar sai kallon juna da murmushi. Karshe
ma hannunta ya hada da giyar motar ya rike. Dukkaninsu farincikin da suke ciki
bazai misaltu ba.
Maigadi na bude gate da ya hangota kamar yayi tsalle don murna. Tabbas yasan inda
take a bakin Tala amma dole yayi kewarta. Abinci da kyautawar da take musu ai
bazasu manta ba.
Hatta jakar hannunta mika hannu yayi zai karba Hamza ya karbe yana dariya...Mal
Talle anya kayi farincikin ganina ranar da na dawo kuwa. Irin wannan murna haka?
Zuhra tayi murmushi kawai ta shige ta barsu. Maigadi yace Yallabai ka rike matarka
da kyau. Wallahi tana da kirki sosai.
Hamza yace nagode. Ga wannan gobe kaje gida kayi sati biyu....Kudi ne maigadi ya
karba da murna. Lallai an sami canji. A da Hamza don kansa baya barinsu zuwa ganin
gida sai sunyi ta roko amma yanzu ya san hakkin mutane sosai.
A cikin gidan ma tamkar an kawo wutar nepa bayan shekara daya haka suka yi ta
murna. Tala ta kwashi 'yan kayan da Zuhra ta sami daukowa ta kai sama. Su Khalifa
kuwa suka dane jikinta. Nana sarkin rigima tace Maama goyani..
Zuhra na durkusawa Hamza ya shigo yace ke rufa min asiri. Nana zo na goyaki kinji.
Maama da kayana a jikinta.
Nana ta sa kuka ita bayan Maama. Tun yana lallabata har ya soma fada. Zuhra ta dage
zaya iya goyata yace sam bai yarda ba.
Izzatu ce taji kukan ya isheta ta fito. Ganin Hamza yasa zata koma sai kuma ta kula
da Zuhra. Ba karamin kyau tayi