Advertisements
Chapter 33 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 36

96K to 99K   out of 106K words

ba idan aka hadata da Zuhran da ta sani da farko.
Kamar ta sauko tayi mata magana taji dalilin da yasa ta boya ta jawo mata saki. Sai
ta tuna da shawarar da Raliya ta bata ta koma dakinta tare da bugo kofa da karfi.

Da kyar Hamza ya lallaba Nana ta yadda ya goyata. Amma ta dage sai ya saka zani.
Zuhra dasu Junior suna ta yi musu dariya yace bazai saka ba. Zuhra ya kalla yace
zaki san ni kika yiwa dariya idan na kamaki. Tana jin haka ta haye sama tasan zata
sha aiki. Sai dai ga mamakinta dakin fes ta same shi. Komai a gyare, hatta zanin
gado Hamza ya dauko sabo Tala ta shimfida a kan gadon.
Tare dasu Junior ta tafi dakin suna ta bata labarin abubuwan da sukayi lokacin da
bata nan. Hamza ya shigo da Nana a hannu tun yana saka baki a hirar har ransa ya
soma baci. Yau da yake son kasancewa da Zuhra bayan lokacin da suka dauka basa tare
shine ta biyewa yara hira. Gajiya yayi ya fita dakinsa ya bude jakar kayan
tsarabar da bai sami damar budewa ba tunda ya dawo. Kayayakin da ya siyowa yaran ya
debo harda wasu riguna da ya siyowa Tala da maigadi. Bawa kowa nasa yayi sannan ya
basu nasu Tala. Harda kashedi idan kun kai musu kuje ku nunawa Mummy.

Yara an sami abinda ake so suka fita suna ta murna. Suna tafiya ya rufe kofar harda
murda mukulli. Zuhra ta dawo kusa dashi ta tsaya yana ta kallonta musamman dan
cikinta da ya tasa kadan. Hannuwanta ta sakala a wuyansa ta rungumeshi. Yace da
kinsan abinda kike so kenan kika biyewa yara kina hira kawai don ki ja min
aji....ya kama hannuwan nata ya cire...nima yanzu zan ja nawa sai ki bisu kuyi hira
ni bacci nake ji.

Zuhra tayi dariya ta sake rungumarsa. Haba Ya Hamza kaga suma nayi kewarsu ne
shiyasa. Dan zo kaji irin yadda nayi kewarka duk tafi ta kowa.

Matsawa ya kara yi naki din. An fada miki mata ne kadai suka iya yanga. Sai nan da
sati daya zamu fara kwana a daki daya ma. Kinga tafiyata.

Yana tafiya Zuhra ta sake binshi ta rungumeshi ta baya tana masa dariya....idan ka
fita abinda na kawo maka na murnar dawowarka zan fasa baka....yadda take magana
tana jan kowane harafi yasa shi saurin juyowa suna kallon juna. Kafin ya daga hannu
ya tabata an soma kiran sallar magriba.

Ya cije lebe Zuhra ta kwashe da dariya. Ai kaga yanzu sai kayi yanga da hujja. Ni
bari naje nayi alwala sai bayan sati idan mun hadu.

Hannunta ya rike suna bin kiran sallar har aka gama suka yi addua sannan yace yau
idan kika shigo hannuna Cutie...hmmmm sai na dawo dai. Love you.

Itama tace masa Love you too sannan ya fara shiga toilet dinta yayi alwala ya fito
ya tafi masallaci.

Da Zuhra ta idar da sallah kasa ta sauka wurinsu Tala. Abincin da tayiwa Hamza
bashi da yawan da zasu ci duka gidan shiyasa ta dora jallof din taliya. Ba jimawa
ta gama ta zubawa kowa. Tala sai kallonta take tana murmushi. Ba karamin kewa ta
barsu dashi ba. Bare da ta kula kamar Zuhran ciki gareta shikenan komai sai tace
kawo na karasa. Haka suka gama girkin ta koma dakinta tayi sallar Isha.

Bayan Ishar Hamza ya dawo. Yau fa anga Cutie bashi da wurin zama sai inda take.
Hijab din da tayi sallah ya samu tana ninkewa ya karba ya karasa mata sannan yace
ta zauna zasu yi magana.
Zancen abinda Izzatu tayi yayi mata sannan yace nasan kina sane da hukuncin da
Alhaji ya yanke na cewa na saketa ko?
Sunkuyar da kai Zuhra tayi bata ce komai ba sai hawaye dake barazanar saukowa daga
idonta. Sauran abubuwan da Izzatu tayi mata duk da bata ji dadi ba amma tana iya
danne bacin ranta ta hakura. Wannan karon kuwa idan har tace ta hakura babu komai
ita kanta tasan dole a jerata sahun farko a makaryata. Babu macen da zata fuskanci
abu makamancin wannan tace ta hakura lokaci daya.

Duk tunanin da Zuhra take yi Hamza na kallonta. Abu ne mai wuya ace Zuhra ta yafewa
Izzatu....sake matsowa yayi jikinta sosai yace..babu wanda zai iya kwatanta halin
da kika shiga sai wanda ya tsinci kansa a ciki. Abinda Izzy tayi miki ba abu bane
da zamu iya mantawa da wuri. Sai dai ina rokonki alfarma yadda kike kokarin kiyaye
dukkan abinda kika san ya sabawa shari'a ko zaman aure don Allah Cutie kada ki fara
shi saboda bacin rai, kinji.

Bata iya magana ba sai kai da ta gyada a hankali. Hawayen da take boyewa suka fara
sintiri a fuskarta lokacin da yace mata a gidan Izzatu zata yi Idda. Ga kishi ga
bakincinkin abinda ya faru. Hamza bai hanata kuka ba sai ma rungumarta da yayi. A
hankali ya sake magana saboda yasan ranta a bace yake... Cutie nasan abinda zan
fada yanzu zai kara bata miki rai sai dai ina son kada kiyi hukunci da son zuciya.
Kiyi tunani a matsayinki na musulma wadda take fatan itama idan tayi kuskure a yafe
mata. Rikon da tayi masa ya tabbatar masa tana jinsa.... Alhaji yasa na mayar da
Izzy bayan fitarta dazu saboda haka a matsayin matata take har yanzu duk da bata
san hakan ba. Na fada miki ne saboda kada kiga wani dalili yasa naje inda take tana
da hakki a kaina har yanzu. Zan bari sai tayi tunanin ta gama idda sannan na sanar
da ita. Hakan muna fata ya zama sanadiyar nutsuwarta. Batun girki kuma zata dafa
iya na cikinta banda su Nana.

Zancen Hamza har zuci ya daki Zuhra sai dai kuma tana da tabbacin son zuciya bazai
taba zama alkhairi gareta ba. Shi Izzatu tayi sai gashi ita da take raina kanta da
kanta ta mallaki zuciyar mutum kamar Hamza. Dago fuska tayi suka hada ido tayi
saurin rufe nata....Ya Hamza in sha Allahu bazan taba shiga tsakaninka da matarka
ba. Tare na ganku kuma nasan duk matsalolin nan saboda ni suke faruwa. Idan a da
ban fahimceta ba yanzu nasan ya mace take ji idan taga mijinta da wata. Allah Yasa
a samu abinda ake nema...ta mike tsaye tana jan hannunsa.... ka tashi muje muci
abinci sai ayi wanka a kwanta.

Dawo da ita yayi kan cinyarsa...dan fada min ya mace take ji idan taga mijinta da
wata.

Zuhra tace tabdi ai rai ne yake baci sosai. Nifa ranar da ta dawo da kyar nayi
bacci.

Hamza yayi dariya yace kina ta tunanin ko muna can muna....

Bakinsa ta toshe da hannunta ta tashi tana jin kunya. Kafin ya tashi ta fice daga
dakin.

****
Abin duniya ya ishi Izzatu sai juyi take akan gado ga wata uwar yunwa na cinta.
Bata son fita ta hadu da Zuhra ko Hamza. Da wane ido zasu kalli juna? Kila Zuhra ta
rinka mata dariya ma saboda yanzu an saketa. Tana wannan tunanin Raliya ta kirata.
Da sauri ta dauki wayar tana son jin jawabin Ustaz.

Raliya tace to ki saurare ni da kyau Izzatu. Idan kika bari wannan damar ta wuceki
babu ruwana. Ustaz yace ba karamin kokari suka yi ba suka ce kiyi idda a gidan.
Mutanenmu da yawa basu san cewa yana da kyau idan anyi saki daya ko biyu mace tayi
idda a gidanta ba. Hakan zai sa a wannan lokacin tayi kokarin jan hankalin mijinta
har ta mantar dashi dalilin sakin ya yafe mata ya dawo da ita . Sai ayi saki daya
ace na baki minti biyar ki kwashe kayanki.

Izzatu tace to Mum hakan dole ne ko mutum nada zabi?

Raliya tace mace na da zabi amma zaman shi yafi. Kinfi kowa sanin Hamza saboda
shekarun da kuka yi tare. Kinsan me kike yi ki janyo hankalinsa. Sai ki dage da
ladabi da biyayya. Girki ma ko bazaici ba kiyi maidadi kiyi masa tayi. Banda saurin
fushi kuma babu ruwanki da Zuhra. Idan kika yi ganganci da sauran igiyar nan zaki
yi kuka da idanunki don yanzu 'yan mata ma neman miji suke ido rufe bare bazawara
mara mahaifa.

Haba mana Mum ya zaki fadi haka? Izzatu ta fada kamar tayi kuka.

Ya bazan fada ba Izzatu. Ai mahaifar nan da kika cire wallahi ko yau ko gobe sai
kin cije yatsa. Naga har yau baki fara damuwa bane. Allah Ya kyauta .

Izzatu tace Amin ta tashi da kwarin gwiwa. Wanka tayi ta bata lokaci wurin gyara
jikinta sosai tayi kwalliya. Wata rigar bacci ta saka shara shara ta feshe jikinta
da turare ta fito ta sauka kasa.

Tala har bari tayi saboda shigar da Izzatu tayi. Tayi saurin rufe ido tana tunanin
yaushe Hajiyarsu zata dena irin wannan abubuwan. Ita bata taba ganinta da riga irin
wannan ba duk da ta saba yawo a gidan da kayan bacci amma masu mutumci ne.

Hayaniyar su Khalifa ta jiyo a falon Hamza tayi murmushi tasan yana ciki. Canja
tafiya tayi ta shiga falon.

Zuhra da Hamza ke cin tuwon da tayi masa da Nana wadda idonta idon tuwo. Junior da
Khalifa suna ta wasa da bindigar roba. Kamshin turarenta ne ya fara sanar dasu ta
iso.

Junior ya kalleta baki bude yace Mummy yau kuma baki saka kaya ba kika fito daga
daki?

Khalifa yace kai ta saka amma irin rigar da Malam yace idan mace ta saka ta fita
za'a sakata a wuta ne. Mummy wallahi babu kyau yawo a haka.

Zuhra dai kawar da kanta tayi gefe don tsiraicin yayi yawa. Hamza yasa su Khalifa
suka daukarwa Nana plate din tuwon yace su tafi wurin Tala. Suna fita ya juyo kan
Izzatu ransa a bace.

Yanzu don Allah Izzy baki ji kunyar saukowa haka 'ya'yan cikinki su ganki ba. Kila
Tala ma ta ganki ko?

Izzatu tayi murmushi...Babyna bansanka da zafin kishi ba. Kuma harda su Khalifa. Ni
yunwa nake ji me zamu ci ne?

Zuhra yake kallo ido ya cika da hawaye. Yasan dole taji babu dadi musamman da tasan
ya mayar da Izzatu. Uwa uba yadda ta kunyata kanta batare da ta damu ba.

Ya tashi ya tsaya a gabanta. Kinga Izzy ki bar wurin nan kafin ranki ya baci. Idan
har kina so mu shirya to wallahi kada ki sake fitowa da irin wannan kayan. Sai
kinyi kamar hankali ya shigeki sai ki fara wani shirmen. Meye amfanin yaro kamar
Khalifa yana fada miki babu kyau irin wannan dressing din.

Izzatu dai bata damu ba ko kadan. A ranta taji dadin yanayin da Zuhra ta shiga.
Dole ta dage ta karkato da hankalinsa ta dawo matsayin matarsa.
Karshen takaici Zuhra taji sai ta daure ta tashi ta kama hannun Hamza... Ya Hamza
muje nayi maka wanka kaga dare yana kara yi.

Daga shi har Izzatu baki suka bude don ko su kadai ne yasan tana jin kunyarsa.
Yadda suka yi yasa sauran kadan ta karaya sai ta daure tace...muje mana Ya Hamzana.

Bin bayanta yayi suka fita suka bar Izzatu a tsaye rai a bace. Ita bata ga laifin
shigarta ba. Tala dai mace ce 'yar uwarta sai kuma 'ya'yanta. To cikinsu waye bai
kamata yaganta a haka ba. Tabe baki tayi ta fita ta tafi kitchen ta dafa indomie
kwaya daya. Indai haka ake zaman iddar ai bazata dade ba komai zai daidaita.

Dakinsa ya ja Zuhra ya bude mata nata tsarabar. Kananan kaya ne da kayan bacci masu
kyau. Bakin nan nata ta turo shi gaba ita a dole tana fushi tace ni a dakina zan
kwana. Tana magana tana tattare kayan da ya bata.

Hamza yace ai baki isa ba sai kinyi min wankan nan. Da bakinki ki fadi abu kuma
yanzu ki canja.

Zuhra tace ka rufa min asiri Ya Hamza ai sai ace min mara kunya.

Daya bayan daya ya sauke kayan hannunta ya shafa cikinta....kinga karshen rashin
kunya kuma kin riga kinyi to me kuma ya rage.

Sosai taji kunyar maganarsa ta fara sunne kai a kirjinsa....ai kawai fada nayi amma
ba gaske bane.

Yace to ni da gaske na dauka bari ki gani...bata ankara ba ya dauketa yana cewa kin
kara nauyi fa yarinyar nan. Bai ajiyeya ko'ina ba sai cikin toilet ya rufe musu
kofa.
[11/3, 6:36 PM] Angel Teema: AL'ADUN WASU #78

Batul Mamman(Mrs)#




Saman ta bisu yau zata ga karyar soyayya. Sai tayi abinda zai hanasu kwanan
farinciki kamar yadda itama bazata yi ba. Dadi taji Hamza bai rufe kofar falon da
mukulli ba ta shiga da sanda. Tana zuwa kofar dakin ta jiyo dariyarsu shi da Zuhra.
Kunne ta saka jikin kofar har ta gane fadan waye zai fara shafawa dan uwansa mai
ake yi. Mutuwar tsaye tayi har wani daci take ji a bakinta saboda bakinciki. Bata
taba kawowa a ranta akwai ranar da Hamza zai kasance a cikin dakinsa da wata matar
ba ita kuma a waje a matsayin sakakkiya. Hawaye ne mai zafi ya fara sakko mata har
tayi nadamar labewa a bakin kofar. Hirar soyayya suke abinsu hankali kwance basu
san Izzatu na bakin kofar ba. Jikinta duk yayi sanyi ta fasa abinda tayi niyya ta
koma dakinta. Kwana tayi tana kuka don a yanzu ta tabbatar Zuhra ta gama da ita
indai ta maganar zuciyar Hamza ne, sai dai bazata bari ta rabata da yaranta ba
saboda su ma kirikiri suke nuna sunfi son Zuhran a kanta.

Da sassafe ta tashi ta hadawa su Khalifa breakfast. A wadace tayi abincin tunda
yanzu Zuhra ta bude musu ciki da shegen cin tsiya a ganinta. Ita dama saboda tana
gudar musu kiba ne take basu dan kadan. Kafin karfe takwas tayi musu wanka da kanta
duk da babu makaranta ta basu abinci sunci. Zama tayi a dakinsu ta biye musu suna
ta wasa. Sunji dadin hakan tunda basu saba ba. Kafin ta bar gidan sai tasa sun kara
sonta yadda bazasu yarda ta tafi ta barsu ba. Dole Hamza ya zaba ko ya mayar da ita
ko ya bata 'ya'yanta.

****
A gaggauce Zuhra ta tashi tayi wanka. Zata tafi dakinta Hamza ya bude ido ya ganta
tana yafa mayafi akan tawul din jikinta. Murmushi yayi na jin dadin ganinta...Ina
zaki je da sanyin safiyar nan? Ke da kika kusa wata uku baki ganni ba ki dawo yau a
nan zamu wuni...ya fada yana nuna mata kusa dashi akan gadon.

Itama murmshin tayi masa...Ya Hamza su kila su Nana sun tashi kaga har tara saura
basu ci komai ba.

Tala ta nan fa please Cutie ki dawo ki kwanta. Kinsan irin yadda nayi missing dinki
kuwa?

Kusa dashi ta koma ta zauna har ya fara murna tace...ka bari na je na hada abinci
ina gamawa namu anan zamu ci ma babu inda zan sake zuwa sai zan dora na rana.

Ba'a son ransa ta fita ba. Ganinta yake kamar wata sabuwar amarya. Tayi masa kyau
sosai ga dan cikinta da yake kalla yaji dadi.

Kofunan tea ta gani a falo da plates da sauran dankali da kwai a cikin wasu. Tala
ce ta fito zata kwashe ta tambaya ko ita ta bawa su Khalifa. Tala tace Izzatu ce
tayi girki itama da ta fito sun riga sun ci abinci. Ko kadan bata ji bacin rai ba
ta wuce nata kitchen din ta hada musu nasu abincin.

Ba jimawa ta koma ta samu har lokacin Hamza yana nan kan gado amma yana aiki da
laptop a gabansa. Yana ganin Zuhra ta shigo ya tura laptop din gefe...taho my Cute
baby nayi miki tausa nasan kin gaji. Nan da lokaci kadan zaki dena girkin nan bana
so ki wahalar min da baby.

Zuhra ta turo baki...ba tani kake yi ba sai baby din da baka sani ba. Nagode bari
na koma wurinsu Khalifa muyi hira.

Yi hakuri wasa nake miki. Ai babu dan da zaki haifa ya kai rabin matsayinki a
wurina. Ke ai daban kike da kowa.

Ta shafa cikinta...to kai kaji babanka yace baya sonka. Har ka bani tausayi, amma
babu komai ni ina sonka kaji.

Hamza ya bude baki yana kallon Zuhra tana ta surutu da ciki....haka kika zama kanwa
uwar hadi?...kansa ya kai daidai cikin yace kada ka bari ta hadamu. Mata rikicinsu
da yawa. Rigima zata min na dan yi mata dadin baki shine zata juya zancen ta hadamu
fada. Idan kuma ke mace ce to tun wuri kada ki koyi rigimar mamanki don bata jin
magana.

Haka suka zauna suna ta hirarsu ana soyayya. Zuhra bata sami saukowa ba sai karfe
daya lokacin Hamza ya gama shiryawa zai je masallaci daga nan ya wuce office.

Abinci suka samu su Khalifa na ci Izzatu tana bawa Nana a baki. Wani material ta
saka dinkin yayi mata kyau sosai tasha kwalliya. Tana ganin sun sauko muryoyinsu na
jiya taji suna mata yawo a kunne. Gaskiya labe masifa ne musamman idan miji da
kishiya aka yiwa, wata har ta mutu abinda taji bazai taba gogewa daga zuciyarta ba.
Shiyasa gara kawai mace ta nesanta kanta daga irin wannan dabi'ar.

Ba karamin dauriya tayi ba ta gaishe da Hamza wanda shima haushinsa take ji yanzu.
Amsa mata yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa. Zuhra ma tayi tata dauriyar tace
mata an tashi lafiya?

Da kyar Izzatu ta amsa. Riga da skirt ne na atampa a jikin Zuhra itama tayi
kwalliyarta. Rigar ta fito da dan cikin wanda idon Izzatu ya kai gareshi. A take
taji kamar an sara mata guduma a ka. Ciki kuma??? Gara ta fitar da rai da samun
Hamza.
Yana kallon yadda fuskarta ta canja da ta kula da cikin yayi murmushi. Irin wannan
lokacin yake jiye mata da tayi gangancin cire mahaifa. Rai a dan bace yace Izzy ina
son ganinki a falona.

Zuhra ta kawar da kai ganin Izzatu tana rangwada jiki ta bi bayansa. Zama tayi suka
suma hira da su Junior.

****
Ko zama Hamza baiyi ba yace har kin manta matsayinki a yanzu? A wane dalili zaki
yiwa yarana abinci? Iya abinda zaki ci nace ki dafa idan ba haka ba kuma idan Zuhra
tayi ta zuba miki.

Izzatu tace dama shine dalilin kiran? to gaskiya idan kayi min haka baka yi min
adalci ba. Dan zaman da zanyi a gidan nan takaitacce ne. A iya abinda yayi saura ka
bari na kara shakuwa da 'ya'yana.

Yayi murmushin takaici...yanzu da can baki gama shakuwa dasu ba. Na riga na fada
miki kiji da kanki kafin lokacin tafiyarki.

Ganin ya kafe yasa ta soma kuka. Tasan baya kaunar kukanta tana yi tana rokonsa ya
bari ita ta rinka yin abinci dasu har zuwa lokacin da zata tafi. Burinta ya amince
ta yadda zata ce idan suna ci suka ganshi su matsa masa shima sai yaci. Tasan yadda
yake son yaransa kila yaci din. Dagewa zata yi da dafa irin abincin da tasan yana
burgeshi. Ai duk sonsa da abincin gargajiya dole wata rana yaso na zamani wanda
tasan tafi Zuhra iyawa. Yadda take ta magiya da hawaye yasa Hamza amincewa amma da
sharadin ta rinka basu su koshi baya son wannan abincin kamar an roka.

Ta nuna masa farincikinta sosai harda rungumeshi. Yana kokarin tureta ta rike shi
kam. A hankali ta soma bashi hakuri tana rokonsa ya yafe mata. Ita ko bazai mayarda
ita ba yace ya yafe mata. Tana magana tana bin fuskarsa da kiss yana kawar da
kansa.

Izzy kada kisa na makara sallah naji na yafe please ki sakar min riga.

Kanta a sunkuye ta sake shi tana murmushi.
***

Lokacin da suka fito Zuhra tana kitchen. Izzatu baki

33 / 36