Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
ita, mugun kallon da Hamza ya watsa mata yasa tayi saurin zamewa kasa,
dama a darare ta zauna. Wasu yan siraran hawaye Izzatu ta soma yi tace Zuhra don
Allah ki yafeni. I played a cruel joke on you. Zuhra tace eyye...play kuma? Kawar
da kai Hamza yayi yayi dan murmushi. Yana ganin da kyar idan Zuhra ta fahimci
abinda Izzatu ta fada saboda yadda ta soma yaken karfi da yaji. Izzatu ta cigaba da
magana, nasan ban kyauta ba amma don Allah ki yafe min.
Babu komai Zuhra tace idanunta na cikowa da kwalla. Ta dai yafe amma bata jin zata
taba manta irin dariyar da Izzatu tayi mata a gaban mutane. Tashi ma tayi zata koma
nata dakin Izzatu ta dan taba Hamza, baka bata hakuri ba. Ni kuma??? A wani dalili?
Dan marairaicewa Izzatu tayi, shi kuma yana kallon Zuhra da ta tsare shi da ido.
Dena kallona ya fada yana harararta. Kanta ta sunkuyar dama tasan bazai bata
hakurin ba. Izzatu dai da fara'arta tace ni na baki hakuri a madadinsa. Kai Zuhra
ta gyada kawai, Izzatu tace to tunda kin hakura ina fata zaki amince ya SAKE ki. Ta
juya ga Hamza, daga shi har Zuhra kallon mamaki suke mata. Zuhra tace dama abinda
kike so kenan shine kika rinka yi min kirki dazu? Duk abin Izzatu sai da taji
kunya. Hannuwan Zuhra ta rike, nasan kema auren nan dole ake yi miki kamar yadda
aka yi mana. Ki amince ya sakeki ki koma gida ki auri miji daidai da ke wanda zai
so ki. Nasan idan da bakinki kika fadawa Alhaji ke kika nemi sakin bazai ga laifin
Sweetyna ba. Sai ta kalli Hamza ta kalli Zuhra duk tunani suke yi. Dan gyaran murya
Hamza yayi duka suka mayar da hankulansu gareshi. Idan kin amince da sakin bazan
sake ki yanzu ba sai nan da kamar wata shida ko shekara daya saboda Alhaji bazai
taba yarda ke kika nema ba. Izzatu ta bata fuska habaaaa Hamza, wata shida is too
long. Hankalinsa yana ga Zuhra yana karantar yanayinta saboda ta zurfafa a tunani.
Zaman gidan nan ba nata bane saboda babu mai kaunarta. Itama kuma ba son mijin take
ba, son kyautatawa iyayenta da nunawa Izzatu kurenta yasa tun farko ta amince. To
yanzu idan aka saketa yaya Baba da Umma zasu ji? Waye zai yarda ya aureta idan aka
ji aurenta ya mutu bayan wata shida. A sanyaye ta dago kanta suka hada ido da
Hamza, saurin kawar da kanta tayi kamar ba itace mai tsare mutane da ido ba. Na
yarda amma don Allah kada ku bata min suna idan anyi sakin saboda iyayena....hawaye
ne suka zubo mata tayi saurin rufe fuskarta da mayafinta ta fita. Tana jiyo ihun
murnar Izzatu ta sake danewa jikin Hamza.
Shima duk jikinsa yayi sanyi don baiyi tunanin zata amince da wuri haka ba. Dole ya
sami dalilin da zai fadawa iyayensu yadda baza'a ga laifin kowa cikinsu ba.
Izzatu yaji tana kokarin cire masa riga yasa hannu biyu ya rike abarsa. Meye haka?
Dazu kinzo kinyi hugging dina a gaban yarinya. To meye ta fada tana jan rigarsa. Ai
tasan abinda yafi haka ma munayi. Tana dariya tace Baby we need to celebrate bari
na samo mana juice mai sanyi da cups muyi toasting. Duk da wata shida is a long
time amma ba komai. Fita ta sake yi ta barshi yana tunani. Kamata yayi ya yi murna
da amincewar Zuhra sai dai a kasan zuciyarsa yasan abinda suke niyar yi bai kamata
ba.
Ba jimawa ta dawo da apple juice a wata roba mai kyau ta tsiyaya musu a glass cups.
Hamza zai kai nashi baki ta rike hannun, I said lets toast ta kashe masa ido. Tare
suka dan buga cups din suka yi yar kara. Izzatu tace TO FREEDOM.
[9/25, 3:53 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #37
Batul Mamman(Mrs)#
Kwanaki biyu a tsakani Zuhra na zaune a falo don yanzu Izzatu tace ta rinka zama
tana sakewa. Hatta su Khalifa tana bari su zauna da ita. Wurin karfe biyar na yamma
Hamza ya shigo maigadi ya biyo shi da ledoji. Kofar inda ya kamata ya zama kitchen
din Zuhra yace ya ajiye masa. Su Junior da Izzatu suna ta yi masa sannu da zuwa
Zuhra ta mayar da idanunta ga kallon tv. Ita yanzu da tasan matsayinta a gidan tana
ganin yi masa sannu da zuwa kamar shishshigi ne. Shima a nasa bangaren bai kulata
ba suka tafi dakinsa shi da Izzatu. Ba jimawa ya fito da shirt mara nauyi da dogon
wando, da gani wanka yayi.
Abinci ya zauna ci suna ta hira da Izzatu. Sai da ya gama ya tashi ya bude kitchen
din Zuhra sannan yace ke zo. Da farko tayi niyar sharewa sai Izzatu tace mata jeki
mana Zuhra kayan miya ya siyo miki. A hankali take tafiyar har sai da yaji haushi.
Ya nuna mata kayan da hannu alamun ta dauko. Wato kace na dauka da bakinka ne kake
ganin asara....Allah Ya sauwake ta fada a ranta. Dauka tayi gabadaya hudun ta
shigar dasu kitchen din. Kallon mamakin da yayi mata yasa ta tuna maganarsu dasu
Anas da suka ce mata maza basa son mata masu karfi. Sai kuma ta tunawa kanta ai
Hamza ba mijin da zasu so juna bane.
Kwalin gas cooker dinta ya farke ya sake fita. Bai dade ba ya shigo dauke da
karamar cylinder. Daga can gefe ya ajiyeta sannan ya hada mata gas din. Ya koma kan
fridge din shima dan madaidaici ya jona mata. Ita dai tana gefe tana binsa da ido.
Sai da ya gama tsaf yace ga kayan miya nan da nama sai ki saka a fridge kada su
lalace. Daga yau ki rinka dafa iya abincin da zaki ci. Idan akwai abinda babu a
cikin kayanki sai ki fada a siyo. Tsananin farinciki da taji yasa ta washe baki da
gaske kake don Allah....daure fuska yayi, na taba wasa dake ne? Nagode, nagode,
nagode ta rinka fada tana bude ledojin. Ji tayi yace kuma ki kula kada ki bata
wurin nan kinga tun asali ba kitchen bane. Ya nuna mata sink shi kadai zan iya sawa
idan kin tafi sai a cire amma bazan miki wani kitchen kabinet ba. Duk da haka ma
nagode ta fada cike da murna. Yau zata dafa abinci son ranta taci ta koshi. Hango
kanta take da kwano ba ma plate ba shake da abinci.
Wannan irin farinciki da take yi yasa shi jindadi. Ko ba komai yana ganin ya tsira
daga laifin tauye mata hakki a ganinsa. Zuhra tana susar kai tace uhmmm....yes ya
amsa don yasan akwai abinda take son fada. Dama...dama... gajiya yayi da inda
indarta yace dama me? Uhmm nace shi gas din ya zan rinka kunnawa? Au dama baki iya
kunnawa ba aka kawo ki dashi. Turo masa baki tayi to mu a gida ba da itace muke yi
ba ko risho. Ganin ya daga hannu tasan a bakinta zai sauke shi tayi saurin ja da
baya. Nufi na fa ban saba dashi ba amma cikin kayana akwai risho din sai na fito
dashi. Hannu ya daga yana nunata, ki fito da me? Wallahi kada kuskura ki kunna min
risho a wurin nan in ba so kike ki sake min sabon fenti ba. Kinji ko! Gyada kai ta
rinka yi kamar kadangaruwa da taji ya fara daga murya. Sai kuma yace matso ki
gani..kunnawa yayi sannan ya gwada ragewa da kashewa duk tana gani. Idan kin kasa
ki kira Tala ta nuna miki don naga alama kin fita kauyanci. Ni ba yar kauye bace ta
fada tana kara turo bakin nan nata. Biyota Hamza yayi zaiyi maganin rashin kunya
ta juya da gudu. A bakin kofa suka ga Izzatu tana dariya. Ai tunda naji kana daga
murya nasan kun fara fada shine nazo kallo. Ta kalli Zuhra bai dake ba ko...babu
wanda ya bata amsa ta cigaba da dariyarta ta kama hannun Hamza suka fita.
Tuwo Zuhra tayi niyar yi Izzatu tace kada tayi girki an riga anyi abincin dare da
ita. Har ranta bata ji dadi ba amma haka ta daure taci abincin.
Inuwa sakatare yana ta hada wasu files zai kaiwa Hamza saboda meeting din da zasu
yi sai gashi ya fito daga office dinsa rike da waya da makullin mota. Inuwa yace
ranka ya dade fita zaka yi ne? Akwai meeting fa biyu da rabi. Ba jimawa zanyi ba
Inuwa in sha Allah. Zanje banki ne tun friday kaga yau alhamis banji alert ba na
kudin da ka ciro. Inuwa yace to Allah Ya kiyaye adawo lafiya. Amma ranka ya dade
yaushe Oscar yace zai dawo ne muna bukatar sa hannunsa a wasu takardu. Hamza yace
nima duk na damu ko jikin mahaifiyar tasa ne sai dai ban same shi a waya ba. Bari
nayi sauri na dawo sai muyi maganar dai. Koda ya fita jikin Inuwa sakatare yayi
sanyi....Allah Yasa abinda zuciyarsa take kitsa masa ba gaskiya bane.
Manyan architects yau da kanka a office dina. Manaja ke magana yana tashi tsaye
suka gaisa da Hamza. Kowa fuskarsa dauke da murmushi suka tambayi juna iyali.
Manaja yace sai kuma naji kayi aure ba labari. Kai Hamza ya dan sosa yana tunanin
yadda zance ke yawo a gari..kayi hakuri abin ne yazo a gaggauce. Babu komai Allah
Ya sanya alkhairi. Yanzu dai how can I help you? Tashi Hamza yayi kada ka damu
shigowa nayi mu gaisa na riga na sanar dasu a costumer care alert ne bana ji tun
last friday. Kuma har a atm da na cire kudi still banji ba. Manaja yayi dariya ai
dole ka damu ku masu harka da manyan kudi. Suna magana text ya shigowa Hamza. Yayi
murmushi dadina da bankin nan saurin gyara abu. Gashi har alerts din sun shigo.
Yanayin fuskarsa ne ya soma canjawa a take. Manaja ya naga alert na an cire ten
million har sau biyu a ranar friday din? Manaja ma dena murmushi yayi ai sau biyun
ne Architect. Ka turo sakatare dinka sannan ga mamakina ka turo wani Mr..Mr....mtsw
na manta sunan amma dai na kira nayi confirming a wurinka kafin a sakar masa kudin.
Jiri ne ya soma dibar Hamza daga tsaye yayi saurin dafa tebur din manaja ya zauna.
Da kyar ya iya cewa Mr Oscar? Eh shi kuwa manajan ya amsa. Ka tuna na kira na
tambayeka kace eh kaine ka turo shi. Tabbas manaja ya kira amma a lokacin Izzatu ke
faman daga murya tana masifa sai ya saki Zuhra baiji abinda manajan yace ba ya amsa
masa. Wato shiyasa Oscar yace mamansa ba lafiya ya tafi garinsu gashi an kusa sati
babu mai samunsa a waya. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlufni khairan minha.
[9/25, 3:53 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #38
Batul Mamman(Mrs)#
A rikice manaja ya fara tambayar Hamza ko sunyi kuskure ne. Numfashin Hamza da kyar
yake fita ya dago idanunsa da suka yi nauyi lokaci guda yace babu abinda kayi
manaja. Matsalar daga bangarena ne. Sau biyu yana yunkurin tashi amma kafafunsa sun
kasa daukarsa. Manajan sai bashi baki yake yana rokonsa ya zauna har zuciyarsa ta
daidaita amma sam yaki zama. Ko da ya shiga mota rasa wurin zuwa yayi. Gidansa zai
tafi ko office zai koma. Yafi rabin awa a motar kafin ya tayar ya dauki hanya.
Lokacin da ya shiga gidan babu kowa sai Kande mai aikinsu. Da fara'arta ta tare shi
tana masa sannu da zuwa. Jikinsa duk a sanyaye yake yace ina mutan gidan ne naji
shiru. Nura yana daki su Adabiyya kuma sun tafi makatanta. Hajiya da Mama kuma
sunje unguwa. To din ma da kyar ya iya fada sai ya tashi ya tafi dakin Hajiya. Babu
abinda yake a lokacin kamar yaga mahaifiyasa. Yaji dadi a bude ta barshi kamar
tasan zai zo. Gadonta ya nufa ya kwanta abinda ya dade baiyi ba. Yana rufe ido sai
wasu zafafan hawaye suka sauko masa. Ji yake kamar komai nashi ya tsaya cak. Cheque
din da Mr Oscar ya dauka hade da sauran da suke office dinsa idan an hada miliyan
arbain kenan zai hada ya bawa su Mr Peter ya kawo karshen contract dinsu. A dalilin
hada wannan kudin gabadaya maaikatansa suka amince da karban rabin albashinsu a
wannan watan don kawai su tseratar da kamfanin. Yanzu gashi miliyan goma ta tafi a
kudin bai san ta ina zai samu su ba. Ginin gidansa yaci kudi ba na wasa ba. Idan
kuma ya tattara kudaden account dinsa tare da sayar da filayensa zai iya biyan
kudin to amma rike iyalinsa zai zama da matsala domin kuwa akalla kafin kudin
ayyukan da yake su fito zai dan dauki lokaci. Yana wannan tunanin bacci ya dauke
shi.
Hajiya ta kira Mama ko sun taho daukarta daga tata unguwar Mama tace tun dazu nake
kiranki ban samu ba. Gamu a garejin makanike ban je inda zani ba. Amma na fasa ana
gamawa zamu biyo. Hajiya tace babu komai bari na bi adaidaita sahu kaina ke ciwo.
To ki kira Nura mana yazo ya dauke ki. Hajiya tace babu komai shima yau da mura ya
tashi. Sai kun dawo ni zan wuce gida. Tana gama wayar suka yi sallama da kawarta da
taje dubawa ta fita ta hau adaidaita sahu.
Gabanta yayi mummunan faduwa ganin mutum a kwance a kan gadonta. Alhaji yana Kumo
kuma ko shine da wuya ya kwanta a dakinta. Nura kuma sai da ta leka dakinsa ta
dubashi sannan ta taho nata. Babu inda baya rawa a jikinta ta ja kafa ta je gefen
gadon inda zata ga fuskar mai baccin. Sai da ta dan ja baya saboda wanda bata taba
tsammani ba ta gani. A tsorace tace Yaya....shima kansa ke masifar ciwo ya bude
idanunsa da kyar. Hawaye ne bushe a fuskarshi Hajiya ta matsa ta taba shi. Bakinta
har rawa yake saboda tsoron abinda zai ce tace Yaya me ya faru? Tashi yayi ya gyara
rigarsa da ta yamutse sannan ya mayar da hularsa. Yana dan murmushi yace Hajiya
babu komai. Zuwa nayi mu gaisa duk bakwa gidan. Bari na koma office sai anjima.
Hannunsa ta rike. Itama hawayen take yi....haba Yaya duk duniya idan akwai wanda
zaka boyewa damuwarka kasan banda ni ko. Bar ganin ban fiye shiga harkarka ba duk
yanayin da ka shiga nakan gane na farinciki ne ko akasinsa. Dawowa yayi yasa mata
kuka kamar karamin yaro. Kai bakace Hamza bane dan shekara talatin da takwas mijin
Izzatu da Zuhra. Akan kujera ta zauna tana rike da hannunsa ya zauna a gabanta.
Kansa ta dora akan cinyarta yayi kukansa mai isarsa. Rabonsa da yi mata irin kukan
nan tun ranar da zai tafi Canada. Duk ranar da yayi irinsa to ba karamar damuwa
yake ciki ba. Babu wanda yasan yana yi sai ita mahaifiyarsa. Cike da tausayawa
irin ta uwa ta rinka shafa kansa har yayi shiru. Ko da ya dago kansa murmushi ne a
fuskarsa yace Hajiya na dade banyi miki kuka ba ko. Yau ma sha'awarsa nayi shine na
taso daga office. Bari na koma ana jirana meeting karfe biyu da rabi. Lokacin biyu
saura kwata. Tunaninsa bai wuce yadda ya mori kudinsa ba lokacin da yake dasu shi
kadai. Sai da matsala ta tashi zaizo ya tayarwa da mahaifiyarsa rai. Ya santa bata
da magana sosai, ba lallai ko Alhaji ta fadawa amma zata shiga damuwa. Hajiya tace
tunda baka son fada min damuwarka zan tayaka addua kamar kullum. Allah Ya kawo
sauki cikin dukkan al'amuranka. Ka yawaita ambaton Allah hakan yana yaye damuwa da
bacin rai, sannan kayi kokarin sauke hakkin wadanda ke kanka Allah Yayi maka
albarka. Wani hawayen ne ya sauko masa yayi saurin gogewa. Amin Hajiya nagode. Tana
kallo ya fita ta shiga toilet tayi alwala. Tasan da kansa zaizo ya fada mata
matsalar amma abinda yafi dacewa yanzu tayi zata masa. Addua ta dukufa yi masa
sannan ta saka dukkan kannensa da iyalansu.
Waya yayiwa Inuwa meeting sai gobe baya jindadin jikinsa. Tunani ne fal a
zuciyarsa. Sai yanzu yake tunawa cewa Allah SWT Ya na jarabtar bayinsa ta hanyoyi
da dama. A irin rayuwar sakaci da addini da yayi ai dole watarana ya fuskanci irin
wannan. Sai yanzu ya sake nadamar abubuwan da yayi a baya da wanda yake kanyi yanzu
wato sake da hakkokin matarsa don a zahiri suna damunsa. Sonta kawai baya yi. Zaiyi
kokarin kyautata alakarsa da Mahaliccinsa da sauran mutane. Itama Zuhra zaiyi
kokari ya sake da ita zuwa lokacin da zai saketa. Tunda basa son juna rabuwar ce
zata fi. ta yadda bazai cigaba da daukan hakkinta ba. Zai bari sai komai ya lafa
masa a wurin aiki sai ya sanar da Alhaji zai saketa saboda gudun kada Allah Ya
kamashi. A lokaci daya duk sai ya zama abin tausayi.
[9/25, 3:54 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #39
Batul Mamman(Mrs)#
Karo na biyar kenan da Zuhra ke dandana ruwan miyarta. Yawunta duk ya tsinke saboda
yadda kamshin daddawa ke tashi. Nana na biye da ita a kitchen din har ta gama.
Tuwon shinkafa tayi malmala biyar yadda zai isheta taci da rana, da daddare sannan
ta sami na dumame da safe. Plate ta dauko mai dan fadi da zurfi ta saka malmalar da
tafi kowacce girma da miyar kukarta duk a hade. Manshanu kadan ta zuba ta goya Nana
a bayanta ba zani ta dauki plate din da hannu biyu ta tafi falo. Tana tafiya tana
cewa Nana rike wuyana sosai fa. Ita kuwa Nana sai murna take tace toh.
Sai da ta shimfida tabarma kusa ta dinning table sannan ta zauna cin tuwo. Loma
take kaiwa kamar za'a kwace. Tana ci tana bawa Nana a baki. Sun kusa cin rabi
Izzatu ta sauko...idanunta kan Zuhra tana bawa yarta tuwo a baki. Har da nan
gudunta tayi saurin zuwa inda suke ta dauke Nana tana ta warin kuka da daddawa.
Zuhra ya zaki bata abincinki ke da aka ce ki dafa naki ke kadai? Ni ban saba bata
abinci da hannu ba kuma bama tuwo sosai saboda yayi mata nauyi. Bata nuna jin
haushi ba tace kiyi hakuri ban sani ba. Ganin Izzatu tayi hanyar kitchen yasa Nana
ihu tana cewa Mummy sauketa, sauketa abinci. Izzatu tace naji yunwa kike ji bari na
wanke miki baki na zuba miki couscous. Bata ankara ba Nana ta galla mata cizo a
kafada. Ba shiri ta sauketa tana sosa wurin. Ita kuwa da gudu ta koma gaban kwanon
Zuhra. Hannu biyu tasa tana ci bata jira Zuhra ta bata ba. Sake komawa Izzatu tayi
zata dauketa sai taji muryar Hamza yana sallama.
Yana shigowa Zuhra ta kai wata shirgegiyar loma bakinta. Ido suka hada ai kuwa ta
kware saboda kunya. Ji yayi nauyin zuciyarsa ya ragu saboda yadda yaga tana cin
tuwon cike da nishadi. Izzatu tace sweety kaga rigimar Nana wai sai taci abincin
Zuhra. To ki kyaleta mana ya fada tare da wucewa sama. Ita kanta Zuhra tayi mamakin
amsarsa. Bayansa Izzatu tabi tana masa sannu da zuwa.
Zuhra ji tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin da taga Hamza. Da gani yana cikin
damuwa Allah Yasa ba wani laifin tayi masa ba. Plate din tuwo kuwa sai da suka sude
shi tas ita da yarta Nana sannan aka tashi aka wanke hannu.
Bayan yayi wanka Izzatu ke tambayarsa ya