Advertisements
Chapter 19 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 36

54K to 57K   out of 106K words

kai yana shafa
gashinta da yake ta sheki...da gaske ni kika yiwa kwalliya? Me yasa?
Fuskarta ta dago tare da ware idanunta hawaye na fita ta gefe amma murmushi take
yi. So nake na nuna maka nagode da ka zama yayana kake kulawa dani yanzu. Ya Hamza
bazan taba mantawa da kirkinka ba a rayuwata. Allah ne Ya hadamu don ka zama yayana
ka canja min rayuwa. Sai kuma ta dan harare shi...amma kaga nan, ta nuna lips
dinta. Bazasu manta da yadda suka sha dalli a wurinka ba. Kai Ya Hamza ka iya cin
zali ko sannu baka taba yi min ba. Komai Zuhra tayi burgeshi take yi, yayi dariya
yanzu yanzu kike yabo na kin koma korafi. Turo lips din ta kara yi.... gasu ka basu
hakuri sai na janye korafin. Yace naki, lokacin ba tsiwa kike min ba. Wani hawayen
yaga ta soma yace oh Cutie baki san wasa bane..to rufe idonki na baki hakuri.

Ba musu Zuhra ta rufe ido tana murmushin jindadi zai bata hakuri. Abinda bata taba
tsammani ba yayi mata. Da farko ji tayi kamar ya dan shafasu da dan yatsansa har
tsigar jikinta ta tashi sai dai kafin ta gudu ya hade bakinsu wuri daya. Kissing
dinta yake sosai ta kasa koda kwakkwaran motsi saboda yanayin da ta tsinci kanta.
Hamza bai barta ba sai da suka kusa minti biyar a haka yana bin har wuyanta da duk
fuskarta yana kissing. Kiran sallar Magriba ne yasa ya kyaleta ba don yaso ba. Kasa
kallonsa tayi harda rufe fuska da hannuwanta. Ya Hamza duk kasa ni jin kunya, ni
daga yau ko kallonka bazan iya ba. Murmushi yayi mai nuni da tsantsar jindadi da
kaunarsa gareta sannan ya sauke mata hannun da ta rufe fuska. Gira ya daga mata
kinga kujerar nan ya kamata ki bata mahimmanci a rayuwarki. Kanta a sunkuye tace
meyasa? Idanunsa a kanta yace saboda a kanta Ya Hamza ya fara kissing din Cutie
kuma yasan taji dadi.

Tsananin kunyar da taji yasa ta tashi da gudu ta bar falon. Dariya yayi shima ya
tashi yaje yayi alwala ya tafi masallaci.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU # 57

Batul Mamman(Mrs)#




Tare ta hada musu abinci bayan isha ta kai falonsa. Dariya yayi yace har kin gaji
da wasan buyan ne? To karaso sai ki bani a baki. Dan harararsa tayi Allah Ya Hamza
zan tashi. Haka kawai ina zaman zamana kasa duk minti daya sai nayi tunaninka sai
naji kamar na tona kasa na shige. Hannunta Hamza ya kama yana mata wani kallo kasa
kasa, Cutie da gaske kina tunani na? Tell me, me kika fi tunawa. Sunkuyar da kanta
tayi kasa tana wasa da yatsun hannunta. Yace nifa bana son gulma, yarinya taji dadi
kina so kina kaiwa kasuwa. Bari muci abinci ni yunwa nake ji sai mu koma kujerar
tamu ko. Naga kamar karatun yayi miki dadi.

Karshen kunya dai Zuhra ta gama ji ko kanta ta kasa dagawa. Shi kuwa Hamza yana
sane yake ta tsokanarta, dariya ma yake mata. Kasa cin abincin tayi ta tashi zata
fita. Yace ina kuma zaki? dawo kinji, na dena tsokanarki. A kunyace tace kayana zan
kwashe daga dakinka tunda gobe su Khalifa zasu dawo. Damuwa karara ya gani a
fuskarta, yasan ba dawowar su Khalifa kawai take son cewa ba. Har inda take tsaye
yaje ya riko hannunta suka dawo suka zauna. Cutie kina tunanin idan Izzy ta dawo
zan tashi daga Ya Hamzanki? Daga kan da zata yi kawai sai kuka ya kwace mata. Dama
ga ciwon mara da ya fara matsa mata sannan ga shagwaba. Kuka take sosai Hamza yana
ta aikin rarrashi. Da kyar ya samu tayi shiru ya dan ja hancinta. Cutie baki da
dama, daga magana sai kuka. Tace to irin yadda kake yi min da zaka cigaba idan ta
dawo? Hamza yayi murmushi ganin cewa Zuhra ta damu dashi. Kada kisa komai a ranki
na damuwa. Idan ta dawo zan raba muku kwana saboda bamu gama lessons dinmu ba, ya
fada yana murmushi. Ranar girkinki zaki yi abinci dani kuma zaki kwana a dakina. Ya
danyi dariya nasan kwanciya kusa dani ne bakya son denawa shine harda kuka. Yarinya
ta soma sabawa da jin dumin maigida a kusa da ita. Ji tayi kamar ta nutse a kasa
don kunya kawai sai ta soma salati, ni kada kayi min sharri bayan kaine da ka
ganni sai ka rinka wayon taba ni. Yace karewar tabaki yau da kaina zanyi miki
wanka. Jin haka yasa ta tashi da gudu ta barshi shi kadai.

Wurin su Hamida ta koma suna ta hira suna bata labarin samarinsu Haidar da Yasir.
Zuhra tace kuce mun kusa shan biki. Haka suka cigaba da hira cikin nishadi hankalin
Zuhra a kwance Izzatu bazata dawo da wuri ba. Saboda yadda take fargabar dawowar
Izzatun har mafarki tayi wai ta dawo Hamza ya koma yadda yake da.
Mararta ce ta soma murdawa sosai hirar ta soma gagararta. Adabiyya ce ta kula da
yadda take rike ciki tace Anti Zuhra tun dazu na kula kamar baki da lafiya. Tace
marata ce take ciwo bari naje na kwanta. Bayan ta hau sama Hamida tace ikon Allah
naji ance da anyi aure ake dena ciwon nan kinga har yanzu bata dena ba. Adabiyya ta
kai mata duka to uwar tsurku. Amma seriously naji wasu sunce idan mace bata dena
bayan aure ba tana haihuwar fari take denawa.

Wanka Zuhra tayi da ruwa mai zafi sosai sannan ta fito ta shirya cikin kayan bacci
riga da dogon wando na cotton. Yanzu dai bata sake da kamshi bare kuma ana period
dole duk mace ta kula sosai da kanta. Gado ta hau tana juyi saboda ciwon ya fara
yawa. Duk wata a gida haka take fama ranar su Umma basa samun baccin kirki.

Har shabiyu saura Hamza na aiki Adabiyya ta leka tace masa sai da safe saboda an
dauke wuta. Yace yau anyi abin kai baku jira nazo na tasheku ba. Ina Antin taku?
Hamida ce ta bashi amsa, Yaya ta tafi daki tun dazu bata da lafiya. Kashe laptop
din yayi ya taso meyasa babu wanda ya fada min a cikinku. Suna soma hawa sama
maigadi ya tayar da inji. Hamza ya rufe ko'ina ya wuce dakinsa.

A kan gadon ya hangota ta nade wuri guda yayi zaton bacci take yi ya je yayi wanka.
Yana cikin saka kaya yaga sai juye juye take tsakanin bangaren hagu da dama tana
rike da ciki. Rigar ya fasa sakawa ya zo ya dafa bayanta. Cutie me ya sameki? Baki
da lafiya kuma shine baki fada min ba. Cikinta ta nuna masa tana kokarin tashi
zaune. Shi kuma ya taimaka mata ta tashi yace murdawa cikin yake yi? Ko toilet zaki
je bari na taimaka miki. Baza'a rasa flagyl ko imodium ba a cikin first aid box.
Takaici ya kama Zuhra me yake nufi da cewa cikinta ya murda, wato a tunaninsa......
kai amma ya cuceta da zaiyi wannan tunanin. Yana kokarin dagata muje na kaiki
toilet ta dage ta doke hannunsa harda zumbura baki tace ni ba ciwon shiga toilet
nake yi ba. Hamza yace oh kina fama da ciwo kina tsiwa. To me ya same ki? A hankali
tace marata ce take ciwo. Yace sai kice min period pain ne, ko muje asibiti? A'a
zuwa safiya zai dena ta amsa da 'yar kunya. Gyara mata kwanciya yayi sannan shima
ya kwanta a kusa da ita yana mata sannu. Kusan minti shabiyar ciwon ya lafa daga
baya ya dawo sosai. Hamza ya rasa me zaiyi mata taji dadi hawaye take yi kawai abin
tausayi. Ko kula da cewa babu riga a jikinsa ma bata yi ba ciwo ya isheta kuma tace
ita babu maganin da take sha har ya dena.

Ruwa ta bukaci sha ya tafi ya debo mata a dispencer din falonsa. Tana gama sha tace
Ya Hamza...yes Cutie me kike so? Tace zaka shafa min bayana. Tausayinta ne ya
kamashi ta kwanta ruf da ciki ya rinka shafa mata bayan a hankali. Kamar zata yi
bacci amma kwanciyar taki dadi ta sake juyawa. Ya Hamza...dan kwanciya yayi ya
rankwafo kusa da ita. Yace ina jinki Cutie na, me kike so? A dan kunyace tace zaka
shafa min cikina? Umma tana yi min a gida ina jin dadi. Ji yake kamar ciwon ya dawo
jikinsa ta dena hawayen da take yi. Hannunsa ya dora akan cikin ya soma shafa mata
a hankali. Da ta gaji sake kwanciya tayi ta tura pillow kasan cikinta. Shi dai
Hamza duk abinda tace haka yake mata. Daga baya ya dage sai sun je asibiti tace a'a
zata warke zuwa safiya. Ba su suka yi bacci ba sai wurin hudu. Ta riga shi yi ma ya
gyara mata kwanciya a jikinsa shima yayi.

Ana asuba ya farka ya tafi masallaci. Da ya dawo ya kwankwasawa su Adabiyya kofa ya
sanar dasu su hada breakfast harda maigadi Zuhra bata jindadi. Doguwar rigarsa
kawai ya cire ya dawo ya kwanta. Cikin 'yan mintuna bacci mai nauyi ya dauke shi.
Ba su farka ba sai shabiyu saura. Zuhra ce ta fara tashi ta ganta kwance a jikinsa
kamar wata mage. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #58

Batul Mamman(Mrs)#
Kallo ta kare masa yana bacci. Tasan jiya ba wani baccin kirki ya samu ba shiyasa
ta fita daga dakin a hankali ta rufe masa kofa. Wata mahaukaciyar yunwa take ji
kamar anyi mata sata a ciki. A gaggauce tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na
atampa ta sauka kasa. Banda breakfast hatta abincin rana su Hamida sun kusa gamawa.
Shinkafa da miya suka yi, Adabiyya na gyara salad Zuhra ta shiga kitchen din suka
yi mata sannu. Tace kuyi hakuri yau na barku da aiki. Adabiyya tace haba dai aiki,
ai tun jiya na kula baki da lafiya sosai. Da asuba kuma Yaya yace baki dade da
samun bacci ba. A kitchen din ta zauna cin abinci suna hira.

Har karfe daya babu motsin Hamza tace bari ta duba shi kada ya makara zuwa
masallaci. Tana bude kofar dakin ya fito daga toilet da karamin tawul a hannunsa ya
daura wani a kugunsa. Juya masa baya tayi tana bashi hakuri. Har inda take tsaye ya
karasa ya rufe mata kanta da karamin tawul din. A bayanta ya tsaya ya rungumeta. Ko
motsin kirki ta kasa, yayi kasa da kansa ya sauke akan kafadarta. Cutie ya jiki? Ta
runtse ido tace da sauki Alhamdulillah. Rikon da yayi mata ne yasa ta tuna yadda ta
rinka makale masa cikin dare. Dan murmushi kawai take yi tana jira ya saketa ta
gudu. A hankali ya juyo da ita muje ki shafa min mai yana daga cikin lessons dinmu.
Alamar kuka yaga tayi ta kasa daga ido ta kalle shi. Ya Hamza kayi hakuri banda
shafa mai. Yadda nake jin kunyarka hannuna rawa zai rinka yi fa. Shiyasa nake so ki
koya har ki saba ya fada yana jan hannunta. Idan baki shafa min ba kinsan dai
zunubi za'a rubuta miki ni babu ruwana. Tawul din da ya dora mata taja ta sake rufe
fuskarta sannan ta mika hannu bani man....yana jindadin kasancewa tare da Zuhra.
Kamar gaske tasa hannu a cikin man sai yaga ta lakato shi da yawa kamar mai shirin
wasan mai. Saurin yin baya yayi...Cutie me zakiyi da wannan man? Sai da tayi dariya
sannan tace shafa maka zanyi. Haba ke kuwa, wannan ai man da zan shafa a wata biyu
ne kika lakata. Dan kadan ta rage tace to wannan yayi? Yace kinga jeki kiyi wani
abin kafin na shirya. Idan kika shafa min wannan man ai ko Takitse bazata gaya min
narkewa ba. Dama haka take so ta cire tawul din ta ajiye sai ta rufe idonta wai
kada ta ganshi ba kaya ta mika hannu ni dai sai na shafa maka ko a fuska ne saboda
kada ladan ya wuce ni. Da gaske take matsowa kusa dashi yana yin baya yana bata
hakuri. Kamar zugata yake kara yi tana ta binsa suna zagaye dakin tana dariya. Da
ya gaji yace idan baki fita daga dakin nan ba Cutie zan daukeki muje mu sake yin
wanka. Bata jira ya maimaita maganar ba ta fita tana dariya. Shima dariyar yayi ya
soma shiryawa.

Karfe uku da kwata suka ji horn din mota alamun su Khalifa sun dawo. Murna a wurin
Zuhra tamkar 'ya'yan cikinta ne. Yadda take son babansu haka suka shiga ranta su
ma. Dreban kamfaninsa ne ya daukosu, yana tsayar da motar suka fito suna ta ihu
suna kiran Daddy. Su biyu suka shigo a guje suka rungume shi tare da yi masa kiss a
goshi shima yana yi musu. Junior ya rugo wurin Zuhra da ta fito daga kitchen da
sauri. Dama tukin tuwo yasa bata fito da wuri ba. Kankameta yayi yace I miss you.
Duk rashin turancinta tasan ma'anar wannan kalmar shiyasa taji dadi sosai. Bakinta
kamar gonar auduga tace I miss you too Junior. Khalifa ya soma rigima Daddy kaji
Zuhra bata yi missing dina ba. Kuma ni har nafi Junior missing dinki. Har sweet na
rage miki fa. Zuhra tace yi hakuri kai babba ne shiyasa na fara fadawa kaninka.
Hamza duk kunya ta isheshi da Khalifa yace mata Zuhra. Basu taba tunanin gyara musu
ba da suke fada a da. Da dan borin kunya yace kada na sake jin kun kirata Zuhra.
Junior yace to me zamu fada? Adabiyya ce ta bashi amsa, ku rinka kiranta Maama.
Khalifa ya wani rungumeta don ace yafi sonta yace Maama I miss you. Tace nima haka
tana dariya. Zuciyar Hamza kamar an masa albishir maidadi ganin yadda yaransa suke
son Zuhra.

Tala ce ta shigo da Nana a hannunta tana jan jakar kayansu. Har wani tsalle ta soma
yi da ta hango Hamza. Ajiyeta Tala tayi da dan gudunta ta taho zata rungume Hamza
sai ta kula da Zuhra mai bata abinci. Kwana tayi ta barshi da hannu a bude ta tafi
wurin Zuhra ta rike mata kafa. Fuskar nan babu alamun wasa tace zanci tuwo. Hamza
ya soma salati ana dariya. Yanzu duk gidanmu ki rasa wanda zaki gada sai Hamida mai
cikin zani da babarki Zuhra. Hamida tace haba Yaya don Allah a gaban yara kake
fadan wannan sunan. Adabiyya da Zuhra sai dariya suke yi. Hamza yace gashi nan ta
gado ki a cin abinci da kiba. Ji yadda take gudu duk jikinta na juyawa kamar wata
'yar shekara hudu. Zuhra ta dauki Nana tace kai dai kawai kaji haushi 'yata tafi
sona shine kake hucewa a kanmu. Tala ta gaishe su sannan ta wuce ciki da kayan.

Ana la'asar Hamza ya fito zai tafi masallaci su Junior suna ta wasa a falo. Zuhra
tace Junior, Khalifa Daddy zai tafi masallaci fa. Khalifa yace mun gani Daddy bye
bye. Cigaba da wasan suka yi Zuhra tace kuzo muje kuyi alwala kada ya tafi ya
barku. Maza a masallaci ake so su rinka sallolinsu. Junior yace Zuhra sai kuma ya
rike baki... au Maama yau sallah babba ce ko sallah karama da zamu je masallaci?
Allah Yasa su Hamida sun tafi yin alwala da kunyar da Hamza zaiji sai tafi wannan.
Shi yasan bai taba damuwa da nunawa yaransa zuwa masallaci ba sai lokacin Idi.
Zuhra ta kalle shi bari muyi sauri suyi alwala sai ku tafi. Ai dolensa ma ya jirasu
tunda kanwar bayansa ce take fada masa abinda ya kamata. Yaran kuwa sai murna suka
shirya suka bi babansu.

Tala ce ta gama ware kayansu ta shiga kitchen din Izzatu zata dora abinci. Hamza na
falon yaji motsin kwanuka ya tura Khalifa ya kirawota. Me kike yi a kitchen? Sai da
ta durkusa daga gefe sannan tace abinci zan dora. Yace abinci wane iri? Tana dan
susar kai tace Maman Khalifa tace idan mun dawo na rinka yi muku girki kai da
yaran. Ransa a bace yace kada ma ki soma. A wane dalilin zaki yi mana girki bayan
Zuhra na nan? Kema idan ta dafa zata baki so kada ki yi wani girki indai ba ta nemi
ki tayata ba. Kuma ki rinka yi mata wanke wanke da sauran ayyuka idan ta bukata.
Tala bata iya boye mamakin fuskarta ba. Hamza yace ko akwai wani abu ne? Tayi
saurin mikewa a'a.

Dayake Hamza yace ana magariba zasu je mayar dasu Hamida gida shiyasa Zuhra tayi
girki da wuri. Tuwon shinkafa tayi da miyar agushi. Tala ta shigo kitchen din yana
ta kamshi tana tambayarta ko akwai abinda zata tayata Zuhra tace babu komai. Bata
manta kashedin da Izzatu tayi mata ba akan Tala. Khalifa ya shigo yace Tala ina
sabon takalmi na zan nunawa Maama. Zuhra tace Khalifa kaga Tala babba ce ku rinka
ce mata Anti Tala ko. Yace dama Mummy ce tace maiaiki ce ita ba sai mun ce Anti ba.
Zuhra tace idan kana fada har aljanna zaka shiga. Da murnarsa yace bari na fadawa
Junior ya fita. Tala tace nagode sosai saboda taji dadin yadda Zuhra ta darajata.
Murmushi tayi ta dauki abincin maigadi zata mika masa Tala ta karba tace bari na
kai masa.

Tana zuwa inda yake zaune kan benci yace yau kun kusa saka min hawan jini. Tala
tace saboda me? Ya gyara zama, wato ina ganin motarku gabana ya fadi nace Hajiyar
ta dawo zamu koma gidan jiya..yunwa salamu alaikum. Tala tayi dariya sannan tace ai
ni gidan mamaki ya bani. Dan bani labari meya faru bayan tafiyarmu. Maigadi ya bata
labarin yadda Zuhra ke kyautata masa ga abinci a wadace. Tala ta bude flask dinsa
taga tuwon yadda zaici ya koshi. Nan ta bashi labarin yadda suka yi da Izzatu kafin
ta taho. Maigadi yace bar marowaciya....sai ya rufe baki kada wani yaji. Ai ki
kyaleta kawai ni nan kullum addua nake yiwa Hajiya amarya Allah Ya kawo kazantar
daki. Tala tace amin amin ai yanzu yallabai yayi aure. Wai har Anti tace su Khalifa
su kirani.

Gabadayansu suka shirya suka mayar dasu Hamida gida. Yaran sai murna sunga
kakanninsu. Zuhra ta tafi gaisawa da Hajiya a dakinta ta bar Hamza a dakin Mama.
Hamida ta dauko kudi ta nunawa Maman tace kinga Yaya ya bamu dubu bibbiyu ita kuma
Anti Zuhra ta bamu kayan kwalliya. Mama tace Allah Ya saka da alkhairi Yaya
mungode. Mamaki ne ya kamashi domin kuwa bashi ya bawa Zuhra kudin ba. Bayan fitar
Hamida kasa shiru yayi ya fadawa Mama. Mama tayi murmushi tace Yaya Allah ne Ya
hadaka da yarinyar nan domin ta tayaka gyara dukkan abinda ka bata. Har abada
tsakaninmu da ita sai addua da fatan alkhairi. Abinda take yi maka shi ake bukata
daga duk matar kwarai mai neman rahmar Allah. Cike da farinciki Hamza yake kara jin
son amaryarsa. Mama tace idan Izzatu ta dawo sai kayi kokari ku zauna kayi mata
nasiha. Idan da tarbiyar gidansu a halayyarta harda sakaci irin naka. Baka taba
kokarin hanata ba a da sai ma biye mata da kake yi. Yanzu sai sauke nauyin dake
kanka na yiwa iyalinka tarbiya irin ta addini.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [10/4, 12:59 PM] #+234 806 970 6638#: AL'ADUN
WASU #59

Batul Mamman(Mrs)#




A gajiye Izzatu ta isa gidan iyayenta a cikin garin Abuja. Bayan ta sallami mai
motar da tayi shata tun daga Kaduna maigadinsu ya biyota ciki da jakar kayanta.

Raliya

19 / 36