Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
mata yau kin janyo mun makara sallar asuba.
Tashi tayi tana ninke abin sallah, babu ruwana ko yanzu ma ai na rigaka tashi.
Gadon ta tafi zata gyara Hamza ya haye ya zauna a tsakiya yace ni bacci bai isheni
ba kizo mu kwanta. Zuhra tace kitchen zani kaga muna da baki. Kinga zo kiyi
kwanciyarki ya fada yana mika mata hannu. Indai wadannan yaran ne sai su kai
shadaya suna bacci. Zuhra tace to maigadi fa. Tashi Hamza yayi ya zagaya ta
bayanta, bata ankara ba taji ya dagata cak ya sauketa a taskiyar gadon. Tsoro taji
ta kankame shi ya kwanto a jikinta yana kallon yadda ta runtse idanunta. Sonta yake
ji yana shigarsa ko ta ina. Idan da wani ne ya fada masa zai so ta bazai taba yarda
ba. Kamar mai rada yace Cutie ba'a son yiwa miji musu. Mu danyi bacci kadan sai ki
tashi. A jikinsa ya kwantar da ita tasa hannuwanta duk biyu ta rufe fuska.
Matsananciyar kunyarsa take ji fiye da ta da. Kanta na kirjinsa ya sake sassauta
murya. In cire miki hijab din kisha iska? Maimakon ta bashi amsa kama jikinta tayi
kam. Bai sake magana ba sai bayanta da yake shafawa a hankali.
Har bacci ya soma daukarsa ita kuwa ta zata shima idonsa biyu tace Ya Hamza akan
maganar da mukayi jiya akwai shawarar da nake son baka amma don Allah idan hakan
laifi ne kayi hakuri. Ina jinki yace cikin muryar bacci. Ta tashi zaune, kayi
hakuri bansan ka soma bacci ba. Bude ido yayi yana kallonta, babu komai ina jinki.
Komai nata kishiyar na Izzatu ne.
A nutse ta soma magana kamar ba ita ba. "Nasan duk wadanda suka san abinda ke
faruwa da kai sun baka shawara kila ma irin wadda zan baka ko wadda tafi ta.
Lokacin da tsautsayi ya ritsa da Baba a wurin aikinsu mun sha wahala. Sanda yake da
duka hannuwansa munfi wadata da rufin asiri. Da aka yanke hannun yana jinya a gida
ga kudin magani da sauran abubuwa na yau da gobe ya kasance an koro ni daga
makaranta. Ba don Malam babansu Hajara ba abinci ma sai ya gagare mu wata rana duk
da a haka Baba ya fishi rufin asiri. Wata rana Umma tace naje makota na sanar dasu
zata fara wainar flawa. Ranar baka ga kukan da nayi ba." Hawayen ta soma Hamza ya
sa yatsansa ya share mata. Ta cigaba da magana "bakincikina mun talauce har abin ya
kaimu ga sayar da wainar flawa. Ina kuka na sanar da Umma bazani ba, ta soma fada
nace so take kawayena suyi min dariya. Sai ta zaunar dani ta dena fada tace min.
Zuhra aure ba abin wasa bane. Aljannar mace kuma tana karkashin kafar mijinta.
Ma'ana samun aljannarta na tattare da yardar mijinta. Lokacin da babanki yake da
lafiya ya wadata mu Alhamdulillah. Yanzu kuma lalura ta same shi 'yan uwa da abokan
arziki duk sunyi mana kokari amma dole mu yiwa kanmu. Idan miji ya shiga matsala
mace ana so tayi iya kokarinta da yin abinda bai sabawa shari'ah ba wurin kyautata
rayuwarsu. Idan har bata da hali kuma sai ta taya shi da addua dare da rana har
Allah Ya kawo musu sauki. Kada ki taba daukar maganar masu cewa idan mace ta
taimaki mijinta wata rana zai saka mata da tsiya. Dama don Allah kika yi saboda
haka ki nemi lada a wurinSa. Tun daga ranar na koyi tattali da adana abu saboda na
ragewa Baba kashe kudi. Idan ya siyo min turare ko sabulu na rinka janjaninsa har
kazanta ta dan kamani. Amma dai yanzu na dena ko " tayi maganar da murmushi sannan
ta dago kanta suka hada ido da Hamza." Kasan me yasa na baka labarin nan?" Yace
"sai kin fada". Zuhra ta gyara zama." Ni a shawarar da zan baka Ya Hamza kafin
komai ya daidaita ka rage kashe kudi. Misali tunda nazo gidannan tun karfe shida na
yamma ake kunna inji har tara na safe. Wani lokacin da rana ma sai an kunna duk
yadda abubuwa suke tsada yanzu. Kuma na kula ranar alhamis a waje kake siyo abinci.
Gashi yawancin safiya kullum za'a soyawa su Khalifa kwai kowa bibbiyu. Suci rabi su
bar rabi ya shiga shara." Ta dan daga hannu " ba cewa nayi a takurasu ba amma a
rage irin wannan. A koya musu yau su sami yadda suke so gobe su hakura saboda halin
rayuwa. Injin ma a barshi sai kamar tara ko goma na dare a kunna. Da duk abubuwan
da kasan basu da mahimmanci sai a barsu."
Tunda Zuhra ta fara magana Hamza yake kallonta. Kallo irin na tsabar soyayya da
mutuntawa. Yarinya ce Zuhra sosai a kanshi da Izzatu amma duk yadda suke ganin
shirmenta ta san abinda take yi. Matsalar gabansa bata dame shi ba kamar yadda yake
son gina soyayyarsa a zuciyar amaryarsa.
Zuhra duk ta tsargu da kallon da yake mata tace Ya Hamza na shiga abinda bai kamata
ba ko? Nasan duk aikin Maman Khalifa ne. Dama kawai nayi ne don nima na sami ladan
da mata ke samu a gidan aure. Kaga bansan lokacin da zan sake aure ba idan muka
rabu. Tayi masa murmushinta mai kyau...shiyasa nake son samun lada a iya zaman da
zamuyi.
Kasa magana yayi sai mamakinta kawai. Dan taba shi tayi saboda yadda ya kasa dena
kallonta. Ba tare da ya dauke idonsa daga kanta ba ya dorata kan cinyarsa tare da
rungumeta sosai a jikinsa. Sannan yace nagode sosai Fatima, Allah Yayi miki
albarka. Abinda na fada miki jiya babu wanda ya sani sai ke sai mutane kadan a
office dinmu saboda haka ki rike min sirrina. Kuma na baki dama ki fada min duk
abinda kika ga ya dace na gyara ni Hamza nayi miki alqawari zan gyara. So yake yace
mata yana sonta amma baya son tsorata ta don yasan tana tsoron halin Izzy. A
hankali zai bi da ita har sai yasa taji irin yadda yake ji game da ita a tasa
zuciyar.
Ba jimawa ta fito daga dakin ta sauka kasa. Adabiyya da Hamida ta gani sun share
ko'ina sun dafa tea. Abinda za'a ci ne basu sani ba. Kunyarsu ta kamata ta soma
'yan kame kame. Yau makara nayi wallahi. Kuyi hakuri....da yake su Jidda sun kawo
mata dankali tace rbari a soya dankali. Hamida tace gaskiya Anti dankali akwai bata
lokaci kawai muci indomie. Tace to Adabiyya ta dafa musu harda ita, zata soyawa Ya
Hamza shi kadai.
[10/2, 9:57 AM] #+234 803 220 0468#: AL'ADUN WASU #55
Batul Mamman(Mrs)#
Zuhra na hada kayan wanki a dakinta Hamza ya shigo yace su shirya yaji jiya suna
zancen zuwa salon ita da su Adabiyya. Taji dadin hakan sosai dama a dalilin bata
son auren taki yarda a saka mata relaxer a kanta wai kada ya rinka hanata zuwa
tunda yace kuntata mata zai yi a gidansa. Dubu ashirin ya bata ita da su Hamida
kowa yayi abinda yake so. Zuhra ta bude baki, wannan kudin yayi yawa har ka manta
zancen da muka yi dazu? Ban manta ba baki nayi ki rike a hannunki koda bukata zata
zo miki. Tayi ta masa godiya duk da a ganinta kudin sunyi yawa. Shabiyu saura suka
fita tare ya sauke su yace zai je unguwa idan sun kusa gamawa su kira shi. Zuhra
tace ai babu nisa sosai muna tafe muna hira ma sai mu koma. Su Adabiyya dake bayan
motar yacewa su fita su jirata a ciki. Suna tafe suna waige da yiwa yayan nasu
dariya har suka shige. Ya mayar da hankalinsa gareta. Akwai abinda kike so na taho
miki dashi ne? Ta girgiza kai Allah Yasa kaje lafiya ka dawo lafiya. Allah Ya bada
abinda ake nema. Ya nuna mata jindadinsa da adduarta yace nagode sai na dawo. Da ta
fito wata mata ta gani ga baby a hannunta ga jaka da zanin goyo duk kayan sun mata
yawa. Da sauri ta karasa ta tare mata jakar da ke shirin faduwa. Matar tayi
murmushi kai amma nagode miki. Sai da na zo nan hannun jakar ya tsinke ga Muhsina
ta min kuka. Zuhra ta karbi yarinyar matar ta hade bakin jakarta da zanin goyon
suka shiga tare. Har su Adabiyya sun kama mata layi da yake weekend ne wurin ya
cika. Wuri daya Zuhra da matar suka zauna tana ta yiwa yarinyar wasa ita kuma tana
dariya. Matar tace ni sunana Sa'adatu ke fa? Zuhra ta fada mata sunanta tace ina
son baby dinnan. Sa'adatu tayi dariya ai naga alama kema tana sonki don kyuya take
yiwa mutane amma gashi tana miki dariya. Suna hira matar tace ita har lalle zata
yi. Hamida ta taso daga inda Adabiyya ke tayata tsifa Anti don Allah kema kiyi
lallen wallahi Yaya yana so. Duk sallah baya fashin bamu kudin lalle ko Adabiyya.
Adabiyya tace ce eh.
A wani daki ake yin lallen Zuhra tabi bayan Sa'adatu ta shiga. Ai kuwa mutum daya
suka tarar ana tsara mata ado sosai. Sa'adatu tace ni dai kada kiga ina ta kallonki
wallahi kamar na taba ganinki a wani gida. Zuhra tace kila mun hadu, a wace unguwa
ne? Sa'adatu ta soma bata labarin wasu da suka tare a unguwarsu ana walima aka yiwa
wata April fool. Wallahi sai kuke dan yimin kama da yarinyar duk da ba kare mata
kallo nayi ba. Murmushi Zuhra tayi sannan tace nice yarinyar. Sa'adatu ta bude baki
don Allah da gaske? Ana ta rade radin mijin matar ya auri yarinyar. Don Allah ke
ce? Zuhra tayi ajiyar zuciya. Nice, har an kusa wata biyu da auren. Sa'adatu tace
lallai Zuhra rayuwarki ishara ce ga wawayen mata. Duk yawancin matan unguwar nan da
Izzatun nan ta gayyata walimar tarewarsu sai da suka zageta ranar da abin ya faru.
Yadda kika san kanwata aka yiwa wulakancin nan, har maigidana na bawa labarin
abinda ya faru. Mai lallen ce ta fita karo leda Sa'adatu ta matso kusa da Zuhra. Ko
baki fada ba nasan aurenku da mijin Izzatu bazai zama na jindadi kamar na kowa ba
duba da irin abinda ya faru da farko. Amma zan baki shawara ki rike mijinki sosai
yadda har abada idan Izzatu ko mai hali irin nata tayi niyyar daukan al'adun wasu
zata sake tunani. Kinga yau muka fara haduwa amma haka kawai naji ina sonki da
alkhairi. Zuhra dai sai murmushi take yi. Auren da yake da lokacin karewa wane rike
miji zata yi?... Sa'adatu tace kina son mijin naki? Kanta ta sunkuyar kasa kawai
tana murmushi. Ai an gama wannan murmushin naki ya isheni amsa. To kalleni da kyau
bari na koya miki karatun saye zuciyar mijin matar da bata san inda ke mata ciwo
ba. Ina ma da Ummu Sudais muka zo wurin nan. Don baki ga yadda tafi kowa jin haushi
ba ranar. Kada kiga kamar cin fuska amma ko ba'a fada ba wayewarki da ta Izzatu ba
daya ba. A irin haka tayi miki wayo har hakan ta faru. Abu na farko da nake so dake
shine daga yau mijinki ya ga kin canza masa gabadaya. Canji irin wanda zaisa ko
fita yayi yana tunanin Zuhra a gida. Ki rike TSAFTA sosai domin ita ce abu na
farko da kowane miji yake nema daga matarsa. Duk kyaunki da iya kwalliya idan baki
da tsafta ko jiki na wari miji bazai so kusantarki ba. A hankali kuma zaki fice
masa a rai ya fara neman wata. Na biyu ki iya KWALLIYA irin ta zamani amma fa ba
mai yawa da za'a kasa ganeki ba saboda tsabar fuska tasha fenti. Na uku
SHAGWABA,Zuhra ba sai na bata lokaci ba a nan. Duk mijin da zaki mayar da kanki
yarinya a gabansa dole ya soki. TATTALI DA ADANI yana da kyau ga dukkan matar aure.
Babu namijin da zai so ya auri matar da take da almubazzaranci. GIRMAMA IYAYE da
son 'yan uwan miji shima yana karawa mace daraja a idon mijinta. IYA ABINCI wannan
kowa yasan shine jigon dorewar zaman lafiya a gidan aure. KULAWA, maza nason mace
ta kula dasu tamkar yara kamar yadda muma muke son hakan. Ki rage kunya domin ba'a
son don kinyi aure ki ajiyeta gabadaya, ki nunawa mijinki so da kauna ta sigar da
zai manta da yadda ya auroki ya rike ki da zuciya daya. Ke kike aurensa saboda haka
kinsan bukatunsa, idan baki sani ba kisa ido sosai ki nemi soyayyar mijinki da
gaskiya. Abu na karshe kuma mafi mahimmanci shine ki rike ALLAH SWT DA MANZONSA
SAW, idan kika yi haka to in sha Allahu komai zai zo miki da sauki. Mu 'yan unguwar
nan duk 'yan bayanki ne wallahi. Abinda duk ya shige miki duhu zan baki numberta
sai mu rinka zumunci.
Zuhra tsaf ta nade shawarwarin Sa'adatu tayi mata godiya sosai. A ranta ta kudurce
in Allah Ya yarda zata yi iya kokarinta taga cewa Hamza bai saketa ba domin tsakani
da Allah tasan tana sonsa. Karshe ma sai kafin a fara lallen tace ita gyaran jiki
zata fara yi tunda suna yi. Bayan an gama aka yi mata lalle da retouching. Idan
kaga Zuhra sai ka zata ba ita bace jiki sai sheki yake don ma na rana daya tayi.
Hamza sai waya yake Adabiyya na dauka tace ba'a gama ba har sai da ransa ya baci
yace wane irin abu suke yi a wurin. Sai karfe biyar Zuhra ta kira shi lokacin ya
dade da komawa gida. Yaso yi mata mita sai dai tana zuwa gaban motar ta daga masa
hannuwanta tana dariya.. Ya Hamza lallena yayi kyau? Fasa fadan yayi saboda yayi
kyau din. Baki da ja aka yi mata tamkar wata amarya. Hamza na son mace tayi lalle
amma Izzatu tace kauyanci ne shiyasa bata sake yi ba tun na aure.
Wai ya labarin Izzatu a Kaduna???
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #56
Batul Mamman(Mrs)#
Izzatu na tsaye akan Tala ta gama hada kayan su Khalifa suna ta shiri washegari
zasu koma Kano. Tuno babban dalilin da zai kaita Abuja tayi tace kinga Tala ki hada
harda kayan Nana ku tafi tare. Ga wannan wayar zan rinka kiranki akai-akai kina
sanar dani abinda ke faruwa a gidan. Nasan babyna bazai kula wannan yarinyar ba
amma dai ki sa ido kafin na dawo. Ki rinka yi masa girki saboda nasan ya wahala a
siyan abinci kwanakin da bana nan. Tala tace to Maman Khalifa. Izzatu tace ba to ba
aiki zaki min. Idan kika ga zata shige masa ki hanata ni na baki wannan damar
sannan ki kular min da yara bana son suna cin kazantar da take kira abinci. Sosai
ta karantawa Tala dukkan abinda take so tayi mata idan ta koma. Daga nan suka
shirya aka tafi kai amarya. Sai da suka kaita akayi sallar magariba suka shirya aka
tafi dinner wadda ango ya shirya.
Ko wanka Zuhra bata yi ba da suka koma gida sai da tayi sauce din hanta wanda yaji
albasa da kayan lambu sannan ta dafa farar shinkafa. Harkar girki duk aikin Anti
Faiza ne shiyasa take son yi mata siyayya mai kyau idan zata je gidanta. Hamida da
Adabiyya sun tayata suka hada komai sannan aka fara layin wanka. Zuhra kayanta ta
dauka ta fita ta tafi dakin Hamza. Yana falonsa yana aiki shiyasa ta shiga kai
tsaye.
Bata dade da shiga toilet din ba ta fito zuciyarta babu dadi. Tasan yau da kyar
zata sami bacci tunda abin yazo. Matsanancin ciwon mara yake saka mata. Dama kwana
biyu kenan tana jin alama. Dakinta ta koma ta dauko pad sannan ta dawo ta shiga
wanka. Lallenta ya kara yin fes dashi. Harda humra ta dauko a dakinta tabi duk
jikinta ta shafa musamman cinyoyinta. Sannan ta fesa turaren jiki kala daban daban.
Dogon skirt ta saka baki mara fadi don ya kama mata jiki sannan tasa wata jar top
itama ta kamata sannan hannunta dan iya kafada kawai ya rufe. Sake fesa turare tayi
sannan tabi gashin nan da yasha gyara tayi styling dinsa. Ta taje shi baya ta zubo
da wani ya rufe mata rabin fuska. Juyi ta rinka yi gaban madubi tana yiwa kanta
dariyar yadda zata je gaban Hamza a haka. Kwalliyarta ta dan gyara wadda tayi
alkawarin mayar da hankali ta kara koya sannan ta fito daga dakin.
Kamar abin kirki har ta fara saukowa ta koma daki neman mayafi. Ai da kunya taje
gaban Ya Hamza a haka. Tana shiga dakin su Adabiyya suka fara yaba kyan da tayi.
Karfafa zuciyarta tayi ta bi bayansu suka sauka.
Sai da ta dan tsaya a kofar falon tana tunanin da tadda zata shiga a haka. Daga
baya dai ta tuna yanzu dama ce ta samu da zata yi kokarin samun soyayyar Hamza idan
ba haka ba nan da 'yan watanni sunanta bazawara. Muryarta a can kasa tayi sallama
sannan ta shiga ciki. Hamza na zaune a kan wata kujera irin mai juyawar nan a gaban
wani table daga karshen falon yana aiki a computer. Bayansa take iya gani shima ba
tare da ya juyo ba yace ni yau munyi fada Cutie. Duk sai shareni kike yi tunda muka
dawo sai yanzu zaki zo. A hankali take tafiya tana gwada yadda taga mata masu ji da
gayu suna tafiya. Ta hadu dasu kala kala a salon yau. Cikin nutsuwa ta karasa kusa
da shi kamshinta mai dadi ya sanar masa da isowarta. A daidai bayan kujerar ta
tsaya tace Ya Hamza bazaka juyo kaga kwalliyata ba? Murmushi yayi amma yaki juyowa.
Ni lessons din da na koya miki bamu zo kan jan aji ba amma har kin koya. To nima
nawa zanyi miki bazan juyo ba. Turo baki tayi ta soma shagwaba....Allah sai ka
gani. Ji yayi tasa iya karfinta tana kokarin juyo kujerar. Ko da ta juyo dashi da
kyar sai taga ya runtse ido. Duk kiyi ki gama bazan kalleki ba yau. Murmushi tayi
sannan ta matso da fuskarta kusa da tashi har yana jin numfashinta. Ya Hamza don
Allah ka bude idonka ka gani. Irin kwalliyar da zanyi ce idan na sake aure.
Bukatarta ta biya domin tana rufe baki ya bude idanunsa suka sauka a kanta. Ya
tsani ta rinka zancen idan sun rabu balle kuma idan tana cewa ga abinda zata a
gidan sabon mijinta. Mikewa tayi ta soma juya jikinta a gabansa. So da kaunar Zuhra
ke kara karfi a zuciyarsa. Kallonta yake kamar ba ita ya aura ba saboda yadda tayi
masa kyau. Da ya kula tana jindadin kallon nasa amsa take jira sai ya dan tabe
baki....to,kin so kiyi kyau amma dai da saura. Muryarta kamar zata yi kuka tace da
saura fa kace? Hamza yayi murmushi eh mana. Da akan wannan 'yar kwalliyar kika zo
zaki dameni.
Ba karamin mamaki yayi ba da yaga ta soma hawaye da gaske tana buga kafa. Baka ga
yadda na dade ina yin kwalliyar nan ba shine zaka ce banyi kyau ba. Hankalinsa ya
tashi ganin tana kuka yace wasa fa nake miki. Hannunta ya ja ya zaunar da ita a kan
cinyarsa a kujerar yace haba Cutie ke kin fiye rigima. Meye abin kuka don na dan
tsokaneki. Zuhra ta wani shige jikinsa duk ta kunyar da take ji...to ni ba yau
saboda kai nayi kwalliyar ba amma baka ce nayi kyau ba. Hannu ya