Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
ya fara yi da ita hanyar toilet ta soma kokarin zillewa.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #63
Batul Mamman(Mrs)#
A kofa toilet ya ajiyeta ya fara juyata a gabansa yana karewa kayan jikinta kallo.
Kokarin rufe jikinta ta soma yi yace wai ni ta ina kika saka rigar nan? Duk na duba
na rasa maballi ko zip. Ajiyar zuciya tayi mai karfi tana murna da bai gani ba. A
tsorace take da Ya Hamza. Janyota yayi jikinsa ya zagayeta da hannuwansa. Daga
gefen kafadarta ta dama taji ya kama zip din wanda yake boye a jikin riga ya soma
sauke mata shi kasa. Duk yadda tayi ta gudu abu ya gagara. Jiki na rawa tace Ya
Hamza don Allah banda wanka. Yace kin manta sunnah ne? A'a amma akwai wasu dayawa.
Idan nayi wankan da kaina duk abinda kake so zanyi maka. Wani murmushi yayi mata
wanda shi kadai yasan ma'anarsa yace to amaryata. Zan jiraki a daki. Sai da ya
manna mata kiss a goshi sannan ya tafi.
Sai yanzu take jin tsoron Ya Hamza kuma. Wanka zatayi kawai tayi kwanciyarta. Ta
dade tana kalkale jiki ta fito aka bata lokaci a gaban mudubi ana ta shafe shafe.
Turaruka ta saka masu kamshi sosai da daukar hankali sannan ta daura zani ta tayar
da sallar isha da bata yi ba. Tana idarwa ta cire hijab ta fara neman rigar da zata
saka. Daga ita sai daurin kirji Hamza ya turo kofar.
Cikinta har kullewa yaso yi don kaduwar da tayi. Yana lura da yadda ta kidime ya
matso daf da ita. Zuhra idanu kamar su fado kasa don tsoro tace dama riga zan saka
na fito. Yace Cutie ba na hanaki daurin kirji ba. Da sauri tace yanzu zan kwance
nasa kayan bacci. Don Allah ka tafi zan zo. Bai kulata ba sai ma hugging dinta da
yayi yana murmushi. Kamshi kike yi maidadi Cutie. Ita dai kasa magana tayi jin
yadda yake shafa kanta. A hankali ya saketa ya bude inda kayan baccinta suke. Wata
riga ya dauko ruwan madara wadda da alama sabuwa ce ya warwareta. Bazata wuce mata
gwiwa ba amma tamkar net haka take tasha ado sosai. Tana kallo ya karasa gaban
mirror ya fesheta da turaruka sannan ya ajiye a kan gado. Wani irin kallo yake bin
Zuhra dashi yace saka hijab muyi sallah.
Idan baka kalli bakinta ba bazaka ji yadda tace nayi sallah ba can a kasan makoshi.
Yace wannan nafila ce da zamuyi kafin mu kwanta. Abin sallah ya shimfida a gaban
nata ya jasu sallah raka'a biyu. Bayan sun idar ya dade yana musu addua sannan yayi
mata alama da hannu. Dan matsawa tayi kusa dashi ya dora hannunsa a kanta ya
karanto addu'a kamar yadda yazo a sunnah.
Rigar da ya ajiye ya dauko sannan ya kama hannunta ya kashe fitila suka tafi
dakinsa. Kamar wani sabon mutum haka take ganinsa. Sonsa ne yake karuwa a zuciyarta
amma ta kasa sakin jiki. Sai da ya kaita har bakin gado sannan ya kama hijab din ya
cire mata. Duk abinda yake yi idanunsa a kanta yana yi mata murmushi. Rigar
hannunsa ya saka mata sannan a hankali ya zare zanin ta kasa. Bin jikinta yiya da
kallo ita kuwa kamar walkiya don sauri ta haye gado ta kudundune jikinta. Dariya
yake yi yana kallonta ke da kika ce zaki min duk abinda nake so, ai ban fara ba ma.
Zuhra ta turo baki cikin shagwaba Ya Hamza haka ake soyayyar,ka sa sai kunyarka
nake ji. Sai da ya kashe fitila ya zauna kusa da ita yace wannan sunansa sharar
fage yanzu za'a fara karatun sosai. Tana ji ya kwantar da ita rub da ciki, tashi
take sonyi domin bata san abinda zaiyi mata ba. Ga mamakinta hannuwansa yasa a
bayanta ya fara yi mata tausa tun daga kafada har karshen bayanta. Nasan kin gaji
sosai just relax ki huta. Yau karatun bazaiyi nisa ba naga duk kin tsorata. A
hankali ta saki jikinta tana dan murmushi. Bata taba kawowa a ranta rana irin
wannan zata taba zuwa tsakaninsu ba. Ya kusa minti goma yana yi mata tausa yaji
tayi shiru. Cutie, ya kira sunanta a hankali. Itama a hankalin tace Ya Hamza. Gyara
mata kwanciya yayi ya dora kansa a kirjinta tare da kankameta a jikinsa. Tace Ya
Hamza kunyarka nake ji sosai. Hannuwansu ya hada wuri daya yace zan rage miki ita a
hankali ne Cutie. Yanzu bacci nake so kiyi saboda kin yini kina aiki. Kansa ta
shafa a hankali tace a haka zanyi baccin da kanka a kirjina kamar wani baby? Dagowa
yayi duk da duhun dakin ya saita fuskarsa da tata. Cutie na fada miki miji tamkar
baby ake son matarsa ta rinka bashi kulawa. Gyada kanta tayi tace to sai da safe.
Yace babu goodnight kiss? Rufe ido tayi ita kam yau Ya Hamza ya hanata sakewa.
Idonta a rufe taji lips dinsa akan nata. A hankali yasa ta saki jikinta har suka
dade a haka. Daga baya ya kwantar da ita a jikinsa a kunnenta yace love you Cutie,
yanzu da nasan wace ce ke bana fata Allah Ya kawo abinda zai raba mu . Kanta na
kirjinsa tace love you too Ya Hamza tana mai jindadin abinda ya fada .
A haka bacci maidadi ya daukesu. Hamza yana tunanin ranar da zai mayar da ita
cikakkiyar amarya. A hankali yake so ta gama sakin jiki dashi sannan su gina
soyayyarsu cikin aminci.
Ita ta fara tashi da asuba Hamza na rike da ita kamar zai mayar da ita ciki.
Murmushi tayi cike da farincikin Allah Ya amsa adduarta Ya daidaita tsakaninta da
mijinta. Kwantawa ta sakeyi kusa dashi ta kama gashinta ta soma zirawa a cikin
kunnensa. Sau biyu yana kawo hannu idonsa a rufe sai tayi saurin matsawa. A na ukun
janyota yayi ta fado jikinsa. Ya dan bude idanu, Cutie tsokana ko? Dariya tayi ka
tashi asuba tayi. Ya sake rufe ido ba fa haka ake tashin miji daga bacci ba. Ina
koya miki karatu kin kasa....bakinta ta hada da nasa tayi kissing yaji wani abu na
masa yawo a jiki. Kafin ya ankara ta tashi ta fice daga dakin da gudu. Shi kam ya
dace da mata ya fada a ransa sannan ya tafi yayi alwala.
Yana dawowa daga masallaci suka hadu da ita tana saukowa zata kitchen. Kada ma ki
karasa saukowa ya fada yana hawa benen. Ta dan bata fuska Ya Hamza ina da aiki da
yawa fa. Ya kwaikwayi muryarta Cutie baki da aikin da ya wuce nawa, ni kuma bacci
nake so mu koma. Daukarta yayi tana dariya ya koma da ita. Tala dake makale a bakin
bene basu ganta ba tace Allah Yasa Hajiya Izzatu sai badi zata dawo gidan nan.
*****
Karfe takwas na safe jirgin su Izzatu ya sauka a filin jirgi na Mal Aminu Kano. Ta
kira wayar Hamza yafi sau ashirin bai sani ba. Wayar tana falonsa tun dare yasa ta
a chaji. Ranta a bace domin tayi zaton zai zo tararta a airport din. Gajiya tayi ta
nemi taxi ta daukota har gida.
Koda maigadi ya bude mata kofa sai da jinin nasa ya dan haura. Shikenan zasu dena
jindadi yadda suka saba. Tala ma tsoro ne ya bayyana a fuskarta da suka hada ido da
ita. Ta wayance tana tambayarta lafiya ta dawo da sassafe? Izzatu tace Babyna bai
fada miki kiyi min girki ba zan dawo yau da safe? Anyway ki kai min jakata daki
tana bakin kofa. Tana magana tana hawa sama. Tala tace yau mun shiga uku.....
Dakinta ta fara zuwa tayi wanka aka sha turare da kwalliya sannan tasa wata doguwar
riga iya gwiwa. Surprising din Hamza zata yi. Tasan kila makara yayi shiyasa baije
daukanta a airport ba.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #64
Batul Mamman(Mrs)#
Tunda Hamza ya kai Zuhra daki akan gado ya ajiyeta ya soma bubbuga hannu, wai
yarinyar nan haka kike da nauyi dama. Zuhra ta turo baki ni bani da nauyi. Yadda
bakinta yayi ya bashi sha'awa ya zauna kusa da ita yasa dan yatsansa yana shafa
bakin. Ina son dan bakin nan naki na rashin kunya Cutie mai nauyin buhun shinkafa
biyu. Zuhra ta hade fuska kamar zata yi kuka ta sauke kafafunta daga kan gadon. Ni
dakina zan tafi, dama dauko ni kayi don ka tsokaneni. Kuma yau da daurin kirji zan
wuni a gidan nan. Yayi murmushi Allah Ya baki sa'a da yin daurin kirjin nan. Idan
suka koma suka kwanta kamar na wata tsohuwa aure zan kara yi. Zuhra tace suwaye
zasu kwanta? Abinda kike daurewa da zani mana ko na nuna miki su? Sunkunyar da
kanta tayi tana murmushi don ta gane abinda yake nufi. Shima murmushi yayi ya tashi
ya cire rigarsa saboda tun asuba yasa ake kashe inji yanzu. Garin sai yayi zafi
kamar za'ayi ruwa dama wasu garuruwan na kusa da Kano sun fara samun ruwa. Tana ji
tana gani ya kwance mata zanin da ta daura akan 'yar rigar jikinta tare da cire
mata mayafi. Yace to mu kwanta da gaske bacci nake ji. Jiyan nan....sai yayi shiru
yana gyara kwanciya a kusa da ita.
Ya Hamza me ya faru jiyan?
Babu komai Cutie kawai dai ki shirya yau ba irin jiya bane.
Danyi min bayani meye bambancin jiya da kuma yau da kace na shirya.
Bai bata amsa ba sai kallo da yake binta dashi. Zuhra tayi masa kyau sosai ga rigar
jikinta.....
Kula tayi da abinda yake kallo taji kunya. Rufe jikinta tayi tana cewa Ya Hamza zan
dena zuwa dakinka indai haka zaka rinka kallo na. Yace to na dena amma dan cire
bargon kinga ai babu laifi idan na kalli matata. Dariya tayi ta sake kankame
jikinta. Tashi yayi ya koma can inda kafafunta suke ya daga bargon ya turo kansa.
Dariya Zuhra takeyi tana cewa yayi hakuri.
Bakiga komai ba yarinya ya fada lokacin da ya fito da kansa a daidai kirjinta da
yake dukan uku uku. Runtse idonta tayi saboda yadda take jin kunyarsa. Gabadaya ya
danneta sannan ya zubawa fuskarta idanu. A hankali ya fara kissing ko'ina a fuskar
har ya kai bakinta. Jira kawai take yayi mata abinda ta fara sabawa dashi sai taji
ya tsaya tana jin saukar numfashinsa a fuskarta. Cutie kice kin yafe min duk abinda
nayi miki a baya. Ido a rufe tace Ya Hamza na yafe nima ka yafe min. Ya sake matso
da fuskarsa, kin yafe har da na kusa cutar kaina nace zanyiwa Inuwa tayinki? Hakan
ya bata dariya ta bude ido a hankali. Har shi na yafe Ya Hamza.
Ya lumshe ido to tabbatar min da hakan.
Bata san a inda ta sami kwarin gwiwar daga hannuwanta ta sauko da fuskarsa sosai ta
hada bakinta da nasa. Shiru bata kara komai akan hakan ba yace naga alama karatun
nan bai gama shiga kanki ba. Kinga yadda ake yi.....daga nan ya fara nuna mata
sabon salon da bata san akwai shi ba.
******
Da wata irin tafiyar jan hankali Izzatu ta shigo falon Hamza. Da tayi niyar kiran
sunansa sai ta fasa kada ta bata surprise dinta. A hankali ta bude kofar dakin ko
bacci yake yi kada ya tashi sai ta kwanta a kusa dashi. Labulen ta daga ta dan tura
kai......tamkar wadda taga wani mugun dodo haka tayi saurin sakin labulen ta koma
da baya a hankali. Dakinta ta tafi kai tsaye ta wuce bandaki ta wanke fuskarta da
sabulu. Ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana mayar da numfashi a wahale. Lallai
Izzatu, yau da abinda kika gani gaske ne kila sai kin shiga coma. Shine abinda ta
fada a zuciyarta sannan ta sake sabuwar kwalliya ta fita. Tasan ba wani abu bane
dama ance abinda kafi so ko kafi tsana wani lokacin sai kaga yana maka gizo. In ba
haka ba me zaisa taga hannuwan mace sun rungume mijinta Hamza suna kissing juna
irin haka.
*******
Zuhra ke kokawa da Hamza ya dage sai ta cire rigarta tasha iska. Kamar tayi kuka
tace Ya Hamza, bama Yaya ba, Baba Hamza kayi hakuri mana. Yace ni gaskiya Inna
Fatima bazan hakura ba. A haka kike son nan da wata taran na kaiki asibiti haihuwa.
Yana jan rigarta itama tana ja suna ta dariya.
*****
Sake komawa dakin nasa Izzatu tayi sai dai wannan karon tun daga falon take jin
dariyar Hamza da wata mace. Zuciyarta ce tayi wani mugun bugu kamar zata ballo
kirjinta. A fusace ta banka kofar dakin ta ga wace karuwar Hamza ya kawo gidansa.
Karar kofar ya mayar da hankalin Hamza da Zuhra kofar dakin. Izzatu ce ta shigo
tamkar wata zakanya idanunta sun kankance babu abinda ake gani sai tsantsan bacin
rai.
Shima Hamzan a fusace ya tashi da ya ganta. Shaf ya manta tace yau zata dawo amma
duk da haka hakan bai zama dalilin da zata shigo masa daki babu sallama ba. Ita
kuwa Zuhra bargo taja ta suturta jikinta saboda rigarta ba mai kauri bace. Cikin
masifa Izzatu tace Hamza me zan gani haka? Karuwa har cikin gidan aure, har kan
matrimonial bed(gadon aure)din mu. Daurw fuska yayi shima yana fadan...Izzy a wane
dalili zaki shigo min daki babu sallama.
Heyyyy! aa'a! maza har abada bakwa rabo da abin mamaki. Na kamaka da karuwar kace
zaka min wa'azin sallama. To ban karba ba sai ka kama wata hanyar borin kunyar ba
wannan ba.
Kallonta ta mayar ga Zuhra ta daka mata tsawa ke kuma tsohuwar 'yar bariki wallahi
ni da kike gani bani da mutumci akan mijina. Sai kinyi nadamar hada jiki dashi.
Zaki sakko daga kan gadon nan ko sai nazo na babballaki?
A gigice Zuhra tayi yunkurin sauka daga gadon tana lullube da bargo hakan ya jawo
ta bige gwiwarta da gefen gadon, tana tashi ta soma dingisa kafa. Hamza yayi saurin
tareta, Cutie koma kiyi zamanki let me handle this issue. Ya nuna kofa Izzy wuce
muje dakinki we need to talk.
Ko sauraronsa bata yi ba ta taho gaban gadon ta kwaye bargon da Zuhra ke ta rufe
jikinta dashi. Idonta cike da hawaye tace Hamza buduwar ka samo shiyasa naga har
wani jan kafa take yi. Zuhra ta rasa inda zata saka kanta saboda wannan tozarci da
Izzatu tayi mata. Bayan Hamza taje ta tsaya saboda tasan ko kadan bai kamata Izzatu
ta ganta da wannan shigar ba. Gadon Izzatu ta rinka dubawa Hamza yana mata fada ko
daga kai bata yi ba. Ka barni na duba shaidar cin amanar da kayi min da wannan 'yar
isakar da take son nuna min ita budurwa ce. Hamza yace Izzy idan baki nutsu kin
fita daga dakin nan ba wallahi zaki ga baccin rai.
Jajayen idanunta ta dago tana kallonsa, bacin rai har ya wuce wannan munafukar
karuwar da ka dauko daga bakin titi. Hannu ta kai zata janyo Zuhra dake zubar da
hawaye a bayan Hamza ya rike hannun tare da zagba mata mari. Shima nasa idon bacin
rai yasa sunyi ja yace kada ki sake kira min mata karuwa wallahi.
Izzatu ta dafe kunci ni ka mara Hamza??? To na fada din karuwa matsiyaci....wani
wawan marin ya bata wanda yafi na farko. I am warning you Izzy ki kiyaye bakinki.
Zuhra matata ce ba karuwa ba. Magana Izzatu taso yi sai dai kalmarsa ta karshe tasa
ta hadiye maganar tare da kukan da take yi.
Kunnenta ta dan buga sannan tace me kace Hamza, Zuhra matarka ce? Wannan karuwar ce
Zuhra? Ta fada tana nuna ta.
Hamza yace idan ba ita ba ina da wata matar ne bayan ke? Haka kawai kin shigo kina
ta bala'i kamar wata mahaukaciya. Ki fice daga dakin nan kafin na saba miki.
Sai a lokacin Izzatu ta karewa Zuhra kallo. Ko da wasa bata ganeta ba da farko
saboda ba haka tasan Zuhra ba. Jikinta a sanyaye tayi zaman 'yan bori akan gadon.
Ta dago kai a hankali tana kallon Zuhra dake labe a bayan Hamza. Tsakanina da kai
Hamza bazan taba yafe maka ba. Ni Izzatu Sunusi zaka yiwa irin wannan cin fuskar?
Ka kasheni kuma bazan yafe maka ba. Har gara ace sophisticated
prostitute( hadaddiyar karuwa) ka dauko sai nasan cewa gazawa nayi shiyasa ka nemi
wadda ta fini amma ZUHRA, HAMZA KWANA DA ZUHRA yana nufin mummunan kaskanci gareni
a matsayin mace.
Maganar Izzy ta batawa Hamza rai sosai yace kinga for the last time ki fita daga
dakin nan. Kina iya daukan tarayyata da Zuhra duk abinda yazo ranki amma ki sani
matata ce ta sunnah wadda all thanks to your stupidity na aureta, kuma nake
alfahari da auren. Now GET OUT.
Cikin sanyin jiki Izzatu ta tashi jiri na dibarta ta kalli Zuhra da gabanta ke
faduwa. Nayi miki alkawarin barin gidan nan kamar yadda nayi sanadin shigowarki
cikinsa. Sai kinyi dana sanin cin amanata kika kawo kanka ga mijina. Nasan ba
laifinsa bane Hamza baya iya dadewa babu mace shine kika yi amfani da wannan kika
bashi kanki. Bakiyi nasara ba Zuhra sai kin koma inda kika fito domin ni ban
daukeki a matsayin mace ba ma.
Hannun Izzatu Hamza ya kama zai fitar da ita ta doke hannun, kada kayi tunanin zan
sake bari ka tabani bayan ka taba waccan kazantar. Fita tayi daga dakin babu ko
digon hawaye a idonta. Bakin cikin da take ji yafi karfin kuka.
Hamza ya juyo ga Zuhra ya rungumeta, sai a lokacin ta soma kuka da sauti. Bayanta
yake shafawa kiyi hakuri Cutie. Duk laifina ne da sakaci har ya janyo haka. In sha
Allah Izzatu sai ta koyi mutuntaki a matsayin matata. I love you so much. Rabon
Zuhra da ganin wulakanci tun ranar da aka mata April fool. Tayi kusan minti goma
tana kuka Hamza na aikin rarrashi. Daga baya ta sake shi ta nemi zaninta ta daura.
Hannunta ya riko Cutie ina zaki kuma. Muryarta a dashe tace dakina. Zama yayi ya
dorata a cinyarsa. Ki zauna anan kema kinsan bazan iya barinki ki fita a haka ba.
Tashi nayi miki wanka....murmushi tayi ta dora kanta a kafadarsa ni bazan yarda
kayi min wanka ba. Shima murmushi yayi zaki zo da kanki ne kuma lokacin nima yanga
zanyi miki. Rungumeta yayi a jikinsa yana ji tana ajiyar zuciya. A hankali ta tashi
bari naje nayi wanka. Ya dan ja hancinta please Cutie na kada kisa komai a ranki
kinji ko. Komai zai daidaita in sha Allah zanyiwa Izzy magana. Murmushin yake kawai
Zuhra tayi ta fita.
Tana zuwa falo Hamza ya tashi shima wankan yake shirin yi ya jiyo ihunta da salati.
A guje ya fito ya ganta a tsaye jiki na bari. Ya Hamza kaga jini.....jini ne digo
digo a falon har bakin kofa. Da hanzari suka bi jinin har kofar dakin Izzatu. A
kulle Hamza yaji kofar ya soma bugawa yana kiranta amma shiru. Duk ya rude ga Zuhra
tana kuka. Sai da ya gaji da bugun ga kofar da karfin tsiya ya tuna yana da spare
key. Daukowa yaje yayi ya bude kofar dakin nata. Kwance suka tarar da ita a sume ga
jini yana bin kafarta.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #65
Batul Mamman(Mrs)#
Gabadayansu ba karamin tashin hankali suka shiga ba. Da sauri Hamza ya koma dakinsa
ya dauko wata doguwar riga ya sakata gaba a baya ya dauko Izzatu. Zuhra ma hijab ta
burma ta bi bayanshi