Advertisements
Chapter 8 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 36

21K to 24K   out of 106K words

WASU 🗿
24

Batul Mamman(Mrs)💖




Wurin goma da rabi na safe kukan Nana ya tashi Izzatu daga bacci. Tana bude ido ta
kalli agogo. Da sauri ta sauko daga kan gadon ta dauki Nana da ke kawo karar Junior
ta tafi dakin Hamza. Abin mamaki a rufe taji dakin. Ta tsaya tana bugawa Khalifa
yace Daddy ya fita. Ranta ne ya baci. Tunda suka yi aure ranaku kadan ne suka taba
kwana daki daban shima sai da dalili mai karfi. Amma akan abinda bai kai ya kawo ba
shine jiya yaki tashinta daga bacci ta koma dakinsa kuma yau harda kulle kofar
daki. Kwafa tayi zai dawo ya sameta ne. Bayan tayi wanka ta sauko kasa. Tala ta
gyara gidan tas kamar ba'ayi taro a cikinsa ba. Hatta su Khalifa duk tayi musu
wanka. Da yake asabar ce babu makaranta. Sabon dakin wasansu suka tafi suna ta
tsalle tsalle. Tala ce ta rugu da gudu ta kawowa Izzatu wayarta da ke ringing a
daki. Bakuwar number ta gani ta dauka suka gaisa. Da jin gaisuwar kasan bata san da
wa take magana ba. Mama tace Haj Kaltume ce daga gidan Alh Nasiru uban mijinki.
Izzatu ta dan ji kunya tace yi hakuri Mama bangane ba. Mama tace ah ai babu komai
idan kina da lokaci kizo nan gida Alhaji ya bayar da sako. Kafin Izzatu ta amsa
Mama ta kashe wayarta.

Duk da babu mutane sosai a office din saboda weekend ne amma can Hamza yaje. Tunani
ne yayi masa yawa bai iya yin baccin kirki ba. Shawara daya ya yanke zai basu ribar
kamar yadda suka bukata sannan zaiyi kokarin hada kudin da suka bashi ya biyasu.
Yana wannan tunanin Izzatu ta kira shi tana sanar dashi kiran Mama. Yace taje shima
zai je anjima kadan. Har zai ajiye wayar yaji tace sweetyna kayi hakuri da duk
abinda nayi ba daidai ba. Sai yaji ta bashi tausayi. Basa iya dogon fushi da
junansu. Babu komai Izzy, love you. Tace love you more.

Dakin Mama ta wuce kai tsaye tunda ita ta kirata. Hamida tana gyaran wardrobe din
Mama taji sallamar Izzatu. Wata sabon gani. Anti Izzatu dama kina nan, yaushe
rabonki da gidan nan? Izzatu ta dan sunkuyar da kai. Ita kanta tasan tafi wata
biyar rabonta da gidan iyayen mijinta. Ko da Mama ta karye kunya da tunanin basa
sonta ya hanata zuwa. Kuma Hamza baice taje ba. Mama ta fito daga toilet tace
Hamida bana son rashin kunya ko sa'arki ce da zaki zauna ki titsiyeta. Tashi ki
fita magana zamuyi. Ki kawo mata dan abinda zata ci. Izzatu ta sami wuri ta zauna
tace ki barshi a koshe nake. Hamida ta tabe baki tayi gaba.

Mama ta dubeta, gabadaya Izzatu ta fice mata a rai. Mun sami labarin abinda kuka
yiwa yar mutane jiya a gaban jama'a. Izzatu na jin haka tasan kila fada za'ayi mata
tace Mama don Allah kuyi hakuri. Itama yarinyar zan kirata na bata hakuri. Maybe
bata ji haushi ba saboda bata yi kama da mai daukar abu serious ba. Mama tace ga
mahaukaciya ko, dole kice bata daukar abu serious. To sakamakon abinda kuka yi jiya
Alhaji yaje neman aurenta wurin iyayenta. Izzatu ta zaro ido harda dafe kirji.
Yanzu Alhaji Zuhra zai aura? Karamar yarinya ce fa da kadan zata girmi Hamida. Ikon
Allah ai da Nura ya nemarwa aurenta. Mama ta tsaya kawai tana kallon Izzatu ranta
na kara baci. Ba shi zai aureta ba mijinki ya nemawa aurenta kamar yadda kika fada
mata. What? Tashi Izzatu tayi a gigice... Mama don Allah da gaske kike? Hajiya ce
da ta shigo dakin a lokacin tace da kuna yar wasa ne da ita. Kan kace meye wannan
Izzatu sai kuka. Ta durkusa gaban Hajiya don Allah ku bawa Alhaji hakuri wallahi
bazan iya zama da kishiya ba. Bazan iya sharing mijina ba. Daga Mama har Hajiya
kallonta suke yi tana kuka wiwi. Mama tace don baki da kunya Izzatu mu kike gayawa
bazaki iya sharing miji ba. In sha Allah aure kamar anyi an gama. Tana kuka tace
dama kirana kuka yi kuyi min wulakanci.

KE IZZATU MEYE HAKA. Ta yi saurin juyawa wurin Hamza daya shigo dakin shima.
Rungume shi tayi tana kuka. Kaji abinda suke cewa wai Zuhra za'a aura maka. Duk
kunya ta kamashi yana kokarin tureta tana dada kankame shi. Ya daka mata tsawa sake
ni mana... iyayen nawa kike cewa suna miki wulakanci? Ba kin iya kiranta ki fada
mata Hamza na sonta ba. To zan aureta kinga bukatarki sai ta biya. Idanu sharbe da
hawaye tace ni kake fadawa haka Hamza....sai kawai ta fice.

Mama tayi murmushi sannan ta nuna masa kofa bita kada tayi wani wurin. Ya yi hanyar
kofar Hajiya tace Alhaji yace na fada maka lallai kaje gidansu Zuhra yau ku
daidaita. Tsayawa yayi kamar gunki yana kallon yadda su Hajiya ke nishadi saboda
za'a kakaba masa auren da baya so. Bai ankara ba yaji tashin motar Izzatu. Da sauri
yabi bayanta. Hajiya tace an dai ji jiki. Wallahi Alhaji yayi min daidai. Su Mama
za'ayi surika, Allah Ya tabbatar da alkhairi. Mama tace Amin Hajiya tana fadada
murmushinta.
[9/25, 3:42 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿23

Batul Mamman(Mrs)💖




Yaron da ya rakasu gidan har soro ya shiga dasu sannan ya karasa ciki ya fadawa
Baba yayi baki har su uku. Dama a shirye yake shi da baban su Anti Faiza ne a
tsakar gidan suna jiran zuwan suriki. Basu san wainar da ake toyawa ba. Baba yayi
wa yaron godiya yace da Umma ta dauko juice din nan da ya tanada domin bakon.
Manyan kwalin happy hour ne guda biyu sai ruwan roba babba daya. Akan tray ta jera
da cups hudu ya mika hannu zai karba babansu Anti Faiza da ake kira Malam yace haba
Baban yara bari na dauka.

Tabarmi biyu Baba ya dauko suka shigo soron. Da yake akwai wuta yana ganin bakin
yadan ji faduwar gaba. Irin wadannan mutanen da gani masu arziki ne. Anya sa'anin
auren Zuhra ne kuwa. Ibrahim yayi sauran karban tabarmin ya shimfida musu. Suka
zazzauna suna gaisawa. Alh Nasiru ya sake dasu sosai suna ta barkwanci kamar sun
dade da sanin juna. Idon Hamza kyar akan dungulmin hannun Baba. A ransa tunani yake
Allah Yasa ba kuturu bane. Kodayake ya gama tsara yadda zaiyi ya gujewa auren nan.
Alh Nasiru ne ya fara magana. Alhamdulillah tun kafin muyi abinda ya kawo mu kunyi
mana tarba mai kyau. Wannan yasa naji dadi nasan yaron nan baiyi zaben tumun dare
ba. Malam yace in sha Allahu. Ai Zuhra yarinya ce mai ladabi duk layin nan ko ince
unguwar nan babu wanda bai san gidan Mal Bashir ba. Baban yara ake kiransa saboda
dan kowa nasa ne. Bakin gwargwado kuma yayiwa tasa yar tarbiya. Alh Nasiru yace
haka ake son duk uba nagari. Ni sunana Alh Nasiru Hamza amma anfi sani na da
Maifata saboda sana'ar sayar da fata nake yi sannan yayi musu bayanin asalinsa. Ya
nuna Hamza da Ibrahim duk ya gabatar dasu. Sai ya nuna Hamza shine mai neman auren
Zuhra. Baba ya sake kallonsa yace nagodewa Allah. Dana Allah Yasa kai abokin rayuwa
ne na kwarai ga Zuhra. Ita kadai Allah Ya bani kullum adduata ta sami miji nagari.
Tun farkon lokacin da ka fara turo mata sako a waya babu abinda ta boye min. Ni
kuma a lokacin na yaba da tarbiyarka nake ta addua. Allah Yasa ayi a saa. Kowa yace
Amin. Baba yayi musu bayanin matsayin karatunta da sana'ar da take yi yanzu. Alh
Nasiru yace duk babu komai. Zai sanar da yan uwansu na Kumo nan da sati biyu idan
ya amince sai a kawo kudin aure ayi maganar sa rana don baya son a dauki lokaci.
Hamza dai sai yake yakeyi zuciyarsa na zafi. Ya rasa ta ina zai fara kokarin
tattaro rayuwarsa da ke neman rugujewa lokaci guda. Suna mota Alh Nasiru yace yanzu
da bamu zo ba ai alhakin yarinyar nan kila har jikoki sai ya bika Yaya.

Zuhra na dawowa Baba ya sanar da ita Hamza da mahaifinsa sun zo. A zahiri ta nuna
musu farincikinta amma a tsorace take da abin. Gashi baban Hamza ya roketa ta rufa
masa asiri kada ta fada a gida. Anti Faiza ma tace ko Hajara kada ta fadawa. Haka
ta shiga daki ta kwanta tana jin iyayenta suna tattaunawa akan bikinta.

Hamza bai sami komawa gida ba sai kusan shadayan dare. Dakin Izzatu ya shiga ya
sameta a kwance tana bacci. Hmmm kina jindadinki ya fada kafin ya koma nasa dakin.
Yunwa yake ji sosai don rabonsa da abinci tun safe amma baya sha'awar komai.
Kitchen din kasa ya sauka ya tarar da kulolin abinci kala kala ga wasu ko budesu
ba'ayi ba. Kitchen din tsamin abinci kawai yake yi. Duk da cewa ba'a gama taron ba
ya watse amma anyi almubazzarancin abinci. Tea ya hada ya koma daki. Tunanin sa na
farko yadda zai biya turawan nan kudinsu gaba daya ya fasa hadin gwiwar dasu.
Kudaden kamfanin yanzu da yawa an fara ayyukan ginin dake gabansu. Daya a Jigawa ne
dayan kuma a Abuja. Kowanne sai sunyi rabin aiki za'a biyasu gashi duk zasu ci kudi
sosai. Nasa kudin kuma ya kashewa gidansa don komai sabo ne a gidan. A gefe daya
kuma ga zancen auren yarinyar nan. Gashi iyayensa duk fushi suke yi dashi. Ji yayi
kansa yana sarawa saboda tunanin da yayi masa yawa ya tashi ya dauro alwala yana ta
nafilfili da adduar samun sauki akan dukkan matsalarsa. Mama ce zai iya fadawa
matsalarsa ta bashi shawara to itama yanzu basa dasawa kamar da. Izzatu kuma
damuwarta akan abinda ya shafeta ce kawai.
[9/25, 3:45 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿25

Batul Mamman(Mrs)💖




Gidan kanwar Mamanta inda suka yi masauki Izzatu ta tafi. Ko rufe motar bata yi ba
ta shiga cikin gidan tana ta rusa kuka. Ana ta tambayarta abinda ya faru taki bada
amsa. Sai da kanwar Maman tasu tayi mata tsawa sannan tana shesshekar kuka tace
Alhaji ne yace Hamza sai ya auri yarinyar da nayiwa April fool jiya. Anti Larai
kanwar Raliya tace kai amma Allah Ya sakawa Alh Nasiru da alheri. Ni dama kinsan
duk wannan shirmen naki ba zuwa nake yi ba saboda na rasa wace irin rayuwa kuke yi
ke da mijinki. Tun jiya da aka bani labarin abinda kika yi raina ke kuna. Ta mayar
da kallonta ga Raliya...Wallahi duk laifinku ne Yaya Raliya. Rayuwar turai ai ba
hauka bane. Yara kusan shekara tara da dawowarku kasar nan amma sunki yarda su yar
da al'adun da ba nasu ba. Yanzu wa gari ya waya. Raliya ta sunkuyar da kanta kasa.
Tasan tabbas gaskiya kanwarta take fada. Ta kalli Izzatu da take ta kuka...sai ki
rungumi kaddara tunda ke kika jawowa kanki. Ni bazan shiga zancen nan ba kuma
daddynku ma zan fada masa babu ruwansa. Allah Ya baku zaman lafiya. Izzatu tace
haba Mum haka ma zaki ce. Raliya tace to ai tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke
duka. Daki Zeenatu ta Izzatu tana rarrashi. Kinga Izzatu kiyi hakuri yayi auren nan
tunda dama yan gidansu basa kaunarki. Idan kika nuna bakya son auren suna iya sawa
ya rabu dake. The way I see it wannan yarinyar bazata kai ko'ina a gidan ba zai
saketa. Da haka tayi ta rarrashin Izzatu har ta hakura ta dauki wayar Hamza da yake
ta kiranta ta fada masa inda take sannan ta kusa dawowa gida.

Bayan ta koma ne suka yanke shawarar yaje gidan su Zuhra kamar yadda Alhaji ya
bukata. Maganar auren tasa fushin da yake da Izzatu akan matsalar kamfaninsa ta
ragu.

Wani light blue din yadi ya saka da aka yiwa dinki mai kyau amma simple style ba
ado da yawa. Yasa hula mai ruwan madara da light blue. Yayi kyau sosai don ma bai
fiye sa manyan kaya ba. Ya sha turare sannan Izzatu ta daura masa links a hannun
rigar da agogo. Yana saka takalmi tace cikin shagwaba ni gaskiya kayi kyau da yawa
kamar kada ka fita. Murmushi yayi mata. Kada ki damu bazan dade ba.
Da tambaya ya iso gidan domin zuwan su na dare ga ransa a bace ko kallon hanya
baiyi ba. Yaro ya tura yayi masa sallama da Zuhra. Yaron na tafiya yabi bayansa ya
tsaya a soron inda suka zauna da Baba.

Yaron na sallama Zuhra ta amsa. Ita kadai ce a gidan Umma ana la'asar suka tafi kai
garar Hajara. Baba ma ya fita tun safe bai dawo ba. Tana gaban murhu zata fara tuka
tuwo. Da murmushinta tace Isuhu daga ina haka? Isuhu yace wani mutum ne a waje wai
Hamza yace kizo. Wallahi baki ga yadda ya hadu ba Zuhra, motarsa ma abin kallo ce.
Ga wani kamshi dan ubansu yana fitarwa. Tunda Isuhu ya fara magana gabanta ya fadi.
Ba yadda za'ayi ta yarda da auren nan. Rokonsa kawai zata yi su fadawa iyayensu
basa son auren. Ina ita ina wannan mutumim, ita tsoronsa take ji. Isuhu ta kalla
kace masa ina zuwa tuwo zan tuka na kwashe. Babu kowa ne a gidan. Duk maganar da
sukeyi Hamza na jinsu. Bashi da niyar dadewa a gidan saboda haka dan aiken nasa na
fitowa naira hamsin ya bashi shi kuma yayi sallama ya dan shiga daga cikin tsakar
gidan.

Zuhra bata gama tantance sallamar waye ba taga mutum ya soma shigowa. Gashi ta zuba
garin alkama ta fara tuka tuwon. Da sauri ta fara cewa kai dakata kada ka shigo
mana. Wani tsohon zani ne a jikinta da koriyar t-shirt sai dankwalin zanin da ta
daure kanta tamau dashi. Hamza bai kula ta ba ya shigo har tsakiyar tsakar gidan
tana ta kokawa da dankwalinta tana son bude shi ta rufe jikinta. Wani irin kallo ya
bita dashi mai wuyar fassara. Kinga yi aikinki ni ba zama nazo yi ba. Magana nake
so muyi ina sauri ne. Fuskarta a turbune tace don kana sauri ko sallamarka ban amsa
ba ka fado mana cikin gida. Kuma ko lullubi babu a jikina. Dan karamin tsaki yayi,
kwantar da hankalinki baki da abinda zai daga min hankali don na ganki ba mayafi.
Maganar ta bata haushi sai ta danne tace ina wuni? Kafin ya amsa ta cigaba da tuka
tuwonta.

Kallo ya bita dashi yadda take zaune gaban murhu zafin baya damunta. Bazaki bani
wurin zama ba? Ko juyowa bata yi ba tace na dauka ba zama kazo yi ba. Can gefe ya
sake matsawa saboda wutar ta fara hayaki. Ita kanta Zuhran yana damunta ta fara
hawaye da majina. Tasa gefen dankwalinta ta goge fuskar ta cigaba da aiki. Da kyar
ya hadiyi yawu saboda gabadaya kyankyaminta ne ya kamashi. Gara yayi abinda ya kawo
shi ya fita kafin zuciyarsa ta fara tashi.

Ji tayi yace Ke,wai baki da saurayi ne?....ta murguda baki duk da ta juya masa baya
ni ba sunana ke ba. Kuma ina ruwanka da samarina. What ever taji ya fada da
turanci. A ranta tace ban yafe ba idan ka zagen. Alhaji yace yana so na zo wurinki
atleast sau uku kafin a kawo kudi. Za'a tambayeki kafin ranar idan kin amince da
auren, ina so kice ba kya sona. Mun gama magana da Izzatu tace kina da saukin kai
zaki amince. Izzatu da ya fada ya kara bata haushi. Ko kadan bata son sake jin
sunan matar. Kinga ni bana sonki kuma idan kika aureni wahala zaki sha. A tsarina
mace daya ta isheni. Tunda bana jin kina da saurayi akwai sakatare na Inuwa zanyi
mishi tayinki. Idan ya amince kinga shikenan. Ko ba komai na taimaka miki. Kuma
nayi alkawarin yi miki kayan daki idan kin tashi aure.

Murmushi kawai Zuhra keyi ta gama tuka tuwon ta rufe tukunyar sannan ta gyara
wutar. Wato mutumin nan ya raina mata hankali. Shi iyayensa su yabe shi ita kuma
ace bata da kunya. Wai har cewa yake zaiyiwa wani tayinta. Ko na sati ne sai ta
aure shi ta bata masa rai daga shi har masoyiyar tasa Izzatu. Da wannan shawarar ta
dago kanta amma bata hada ido dashi ba. Tace shikenan abinda ya kawoka? Hamza yace
eh ko kudi kike so zan iya biya kice ba kya sona kinji. Wannan karon tamkar mai
magiya yake magana. hanyar dan karamin falonsu ta kama. Zanyi tunani a kan
maganar, ka gaida gida. Shigewa tayi ta barshi nan a tsaye yana mamakin wai itama
ta iya jan aji. Ya kada kansa ya fice daga gidan. [9/25, 3:45 PM] #+234 803 040
6305#: AL'ADUN WASU#26

Batul Mamman(Mrs)#
Washegari Hamza ya koma gidansu Zuhra. Soro ta fito ta same shi. Yau zama yayi yana
lissafa mata irin mawuyacin halin da zata iya shiga muddin ta yarda aka yi auren.
Kanta a kasa har ya gama bayaninsa ya juya ya tafi. A waje ya hadu da Baba yana
dawowa gida. Yara ne sunfi goma suke biye dashi yana rarraba musu alawa. Hakan ya
bawa Hamza sha'awa. Karasawa yayi suka gaisa da Baba cikin ladabi sannan ya tafi.
Yau dai ya karewa hannun Baba kallo ya kula yankewa aka yi ba kuturta bace ta cinye
yatsun.

Saboda matsalar office dinsa sai bayan kwana biyu ya sake komawa. Umma tasa tayi
kwalliya irin wadda ta saba yi tana ta yabon kyan tilon yarta. Zuhra tace don ma
banyi wanka ba Umma ai da sai nafi haka kyau. Umma tace to sakarai sai kin fada da
karfi yaji yasan cewa ke kazama ce ko. Bata rai tayi haba Umma ki dena ce min
kazama. Baba yace na kile. Ai fa naga alama, to wuce ki tafi kin barshi yana
jiranki.

Tabarma ta dauka ta fita soron. Kamshin turarensa ya cika wurin. Yau suit ce a
jikinsa ruwan toka. Zuhra ta gaishe shi ta sami wuri ta zauna don baya zama akan
tabarmar. To yau nayi zuwa uku ina fata kina rike da dukkan abinda nake fada miki.
Ya dan jima yana magana sannan ya lura ba saurarensa take ba. Shi ta kurawa
ido....ke, keee, KE lafiyarki? Bata dawo hayyacinta ba sai da ya dan tafa
hannuwansa a gaban fuskarta. Ajiyar zuciya tayi sannan tace yanzu don Allah kana
iya numfashi? Ni bansan haka ake saka abinnan a zahiri ba sai yau. Waige ya fara yi
don bai gane kan zancen ba. Tace neck tayil dinka nake nufi. Naga ya shake maka
wuya kamar mai shirin rataye kansa. Yanayin maganarta yasa shi yin murmushi.
Necktie ake cewa sannan bai shake ni ba. Amma dai baka sakewa ko? Dauri irin wannan
akwai ganganci a cikinsa. Dole Izzatu tace yarinyar nan tana da shirme. Yace ni zan
tafi ina tunanin jibi Alhaji zai zo. Ki kiyaye abinda na fada miki. Har ya juya sai
ya dawo...by the way nayiwa Inuwa maganarki sai dai mun makara. An kusa kai kudin
aurensa. Zuhra tace babu komai. Nagode.....yadda yaga kamar ta nutsu yasa ya
kwantar da hankalinsa. Dubu goma ya dauko yan dari dari sababbi ya mika mata. Ga
wannan ki rike. Nagode ta sake cewa sai kawai ta nade tabarmarta ta shige ciki.
Mayar da kudinsa yayi aljihu yana mamaki da bata karba ba.

Bayan Isha Baba ya kira Zuhra da Umma. Wani katon littafi ya dauko mai hotunan
kayan daki irinsu gado, kujeru da kitchen cabinet masu tsada. Kunsan aikina ba wai
ina yin kayan daki na masu kudi bane sosai. To amma

8 / 36