Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
booth ta saka sannan ta
dawo gaba ta zauna. Sai da ta zauna sannan ta gaishe da Izzatu. Sanyin AC yasa ta
wani lumshe ido don har ta fara gumi. Izzatu ta ce gidan Faiza zaki je ko? Kai
Zuhra ta daga don ji takeyi kamar tayi bacci. Ba karamin dadi take ji ba yadda
sanyi ke busowa ta gaban motar. Ko da suka tsaya tace da mun saba dake cewa zanyi
ki sake kunna min sanyin nan ko da na minti daya ne. Izzatu sai dariya tace ai mun
saba idan kina so sai na kunna miki amma idan zaki bini gidana. Da sauri Zuhra ta
bude kofa, wa ya aikeni naje na hadu da mijinki. Rufa min asiri.
Tare suka shiga gidan tana jan jakar kayan Izzatu na binta a baya. Anti Faiza tayi
mata godiyar taimakon Zuhra da tayi. Izzatu tace ai ba komai. Kanwar taki ce akwai
ban dariya. Ta dauko wayarta daga jaka, dan bani number dinki sai mu rinka gaisawa.
Anti Faiza tayi saurin rike hannun Zuhra da take kokarin duba numbarta a cikin
wayarta don bata haddace numbar ba. Tana dan yake tace rabu da lamarin Zuhra
damunki zata rinka yi da flashing. Zuhra ta zumburo baki haba Anti Faiza nima fa
yanzu ba zaman banza nake ba. Da sana'a ta, dan kudin gaisawa dai ina dashi. Izzatu
tana dariya tana kallon kayan da Anti Faiza ke dubawa. Daya ta dauka ta bude daga
cikin ledarta tace amma sakar nan tayi kyau. A ina kuka siya? Zuhra tayi caraf tace
ni nayi. Da gaske Izzatu ta tambaya. Anti Faiza tace eh sanaarta kenan. Izzatu na
jin haka tace lallai sai ta karbi numbar Zuhra. Kizo muje gidana ki gwada su Nana
sai kiyi musu. Zuhra tana ta zumudi ta bada number sannan ta amince zata je gidan
Izzatu tunda ta tabbatar mijinta baya gida.
Cikin daki Anti Faiza ta kira Zuhra. Naga kina ta rawar kai akan matar nan. Tunda
nake da ita bata taba zuwa gidana ba sai kwanakin baya da suka kusa bige ki a mota.
Daga ranar ban kara ganinta ba sai yau duk a dalilinki. Don Allah ki kama kanki
nima ba wani sabawa mukayi ba. Aikin kayan flawa take bani tana biyana. Kuma
kodayaushe ni nake zuwa gidanta. Zuhra tace to ko dai na fasa zuwa kawai. Nace ta
kawo yaran nan. Anti Faiza tace ba haka nake nufi ba. Kije amma ki kula kinji ko.
A hanyarsu ta zuwa gidan Izzatu tana ta yiwa Zuhra tambayoyi ita kuma ta dena yar
fara'ar da take yi saboda maganar Anti Faiza. Izzatu duk ta damu don ita tsakani da
Allah shirmen Zuhra na burgeta. Tace ko dai nayi miki wani Zuhra? Eh to ba wai wani
abu kika yi ba, Anti Faiza ce tace na kama kaina a gabanki itama bata saba dake
sosai ba. Izzatu tace kuma a sirri ta fada miki ko? Zuhra tace eh....au tayi saurin
rufe baki. Kuma wai sai na fada miki. Kai amma banji dadi ba. Izzatu tace bazan
taba nuna mata kin fada ba. It's going to be a secret. Zuhra tace uhmmm tana dan
murmushi. Turancin yayi tsauri kuma gashi kamar na yan TV ba'a ganewa sosai.
Shiyasa tayi shiru kawai.
Gida ne mai kyau suka shiga sai dai ga kaya a kwaleye ko ta ina. A falon ma babu
kujeru sai carpet kawai. Zuhra tana ta kalle kalle tace tashi kuke ko tarewa?
Izzatu tace tashi zamuyi. Babyna ya gama gininsa. Zuhra ta rufe fuska da hijab tana
dariya. Wai baby....Izzatu tace shine kike min dariya to ya kike kiran naki
saurayin? Zuhra tace bani dashi amma ko na samu ni ban iya irin wannan abin ba.
Kunya zanji wallahi. Izzatu tayi dariya sannan ta tashi ta kirawo yaranta daga
dakinsu. Zuhra kallonsu kawai tayi tace ta gane yadda zata yi sakar. Suna tafiya
tace 'ya'yanki kyawawa kema kyakkyawa. Ke kam kinji dadinki. Ga gidanku ma mai
kyau. Yanzu idan kuka tashi wanda zaku koma ya kai girman wannan? Izzatu tace yafi
wannan ma. Hira sosai suka yi har Zuhra ta fahimci Izzatu tana da kirki. Har
kyautar turare tayi mata da zata tafi.
Bayan ta koma gida ne take bawa su Umma labarin Izzatu da kyautar da tayi mata.
Sunji dadi amma anyi mata fadan karbar turaren.
A nata bangaren Izzatu ta bawa yayarta Zeenatu labarin Zuhra ta waya suna ta
dariya. Zeenatu tace irinsu idan kika yi fooling dinsu bazasu gane da wuri ba.
Izzatu tace kwarai kuwa. Ita da akayi sirri da ita shine ta fada min. Ina jin APRIL
FOOL din shekarar nan da ita zanyi. Zeenatu tace ke da mijinki ya kafa miki doka.
Mtsw rabo dashi wannan ai ba harkar kudi bace bazai damu ba. Ke ni har dashi ma zan
hada ta fada tana dariya. Dama nace zan rama hanani party da yayi. Zeenatu tace
zamu zo Kanon da su Mummy cikin next month kafin na koma Alaska.
[9/25, 3:36 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿18
Batul Mamman(Mrs)💖
Bayan kwana biyu Izzatu ta gama tsara yadda zata bullowa Zuhra. Murmushi keta tayi
don ta tabbatar ba karamin shan dariya zasuyi ba.
Hamza ya dawo gida a gajiye 'yan kwanakin nan baya samun hutu sosai. Wani aiki ne
ya sasu gaba, ga shirin tashi sunayi. Duk abin ya rincabe masa. Yana kwance necktie
dinsa Izzatu ta shigo dakin ta rungume shi ta baya. Sannu da zuwa my darling.
Murmushi yayi mata..kema sannu Izzy. Duk na barku da aiki ko. Ba komai, how was
your day? Alhamdulillah ya bata amsa. Amma ina jin yunwa sosai. Me kika dafa mana
yau? Ban fahimceka ba, ka manta yau thursday. Ga yara sun dawo daga school kowa
yunwa muna ta jiranka. Naso kiranka na tuna maka a kawo na rana sai nayi bakuwa.
Tun kafin ta gama magana ya rufe idanunsa saboda ransa da ya baci. Ba rashin girkin
ne ya dame shi ba kamar yunwar yaran. A hankali ya kalleta Izzy ina ganin lokacin
canja wannan tsarin yayi. Ga 'ya'ya Allah Ya bamu. Ki duba irin ayyukan da suke
gabana kinsan dole na manta. Kuma su yaran ba kya jin tausayinsu ne. Ko indomie sai
ki dafa musu. Ta harare shi wasa ma kake yi Hamza. Duk tsarin da muka yiwa
rayuwarmu tun kafin aure yanzu a hankali kake soke komai. Don kawai kaga ina
hakuri. Tana magana sai kuka ya kwace mata. Kada ka bari soyayyarmu ta ja baya
saboda sabon ra'ayinka. Ni ba wannan Hamzan na aura ba. Wanda na aura ya damu da
farincikina. Tausayi ta bashi ya rungumeta yana bata hakuri. A hankali yake magana.
Izzy ya kamata mu fuskanci rayuwa a yadda take. Na daukar miki alqawura da dama ba
tare da dogon tunani ba. Ba kullum ne zamu sami abinda muke so ba. Kinga saboda
bana son tsegumi da kaina nake siyo mana abinci duk alhamis. Yau na gaji ga ayyuka.
Ki daure ki rinka girkin ni kuma duk lokacin da nake da time sai na siyo a waje mu
ci. Ta dago fuska sharbe da hawaye to naji amma sai ka amince ranar da zamu tare
zamu danyi walima mutane su tayamu murna. Izzy na dauka mun rufe irin wadannan
abubuwan. Tace walima nace ba party ba. Ko kida bazamu kunna ba I promise. To ba
komai amma har yaushe zaki shirya wata walima. Tace ka bari sai nan da kwana tara
mu koma. Jumaa ta sama kenan, mu sami albarkar Jumaa. Yayi dariya to naji amma
please kafin nayi wanka abinci....tana tafiya tace Jumaa 1st April tayi kwafa.
Su Zuhra ana ta shirye shiryen bikin Hajara zama ya gagare su. Kullum sai sun fita.
Sune kasuwa ko wurin mai dinki. Ana saura kwana biyu kamu ta dawo daga raka Hajara
saloon din unguwarsu taji Baba da Umma suna magana a tsakar gida. Allah Yasa
Hajaran ta wuce gida. Baba ne yake cewa...ina farinciki da auren Hajara amma
lamarin Zuhra na damuna. Duk samarin da ke zuwa sai kiga babu na aure. Bana son
tayi ta zama a gida tunda ba karatu take yi ba. Umma tace haka ne, kuma abin ba zai
dameta ba yanzu sai taga an kai Hajara dakinta. Amma da kake damuwa yarinyar nan ko
shekara ashirin da daya bata cika ba. Baba yace to ai dai ta kusa. Shekaranjiya da
naje Ajingi baki ji fadan da Inna tayi ba wai mun sa yarinya a gaba munki yi mata
aure. Yaya Sabiu kuma sai cewa yayi ko Garzali ne na wajensa a hada su tunda shima
yaki karatun. Zuhra tana daga soro ta dafe kirji....Yaya Garzali kuma? Allah Ya
kiyaye. Mutum mai shegen ji da kai kamar wani mai mulki. Baba taji yace duk da ba
kudi gareni ba bana fatan yarinyar nan ta auri mara ilimi irinta. Ba mai kudi nake
jira ba amma ina mata fatan samun rufin asiri a rayuwarta. Umma tace Allah Yayi
mana zabi nagari. Idan ta dawo sai kayi mata maganar Garzalin tunda a gaban Inna
akayi ya kamata ta sani.
Hawaye ne suka saukowa Zuhra ba tare da ta sani ba. Allah Sarki Baba da Umma. Sai
yanzu take jin inama ta dan mayar da hankali a makaranta. Wayarta ta zaro daga yar
jakarta ta bude sakonnin da yau kwana uku kenan kullum sai anyi mata safe da dare.
Ta rasa ko waye yake mata wadannan sakonnin soyayya. Lokaci yayi da zata dena
sharewa kila alkhairin da Baba ke jira ne ya tunkaro ta. Ta goge fuska ta shiga
ciki.
Jikin Umma ta fada tace wash Allah nagaji sosai. Umma ta ture ta to dagani kada ki
karasa kashin tsufa. Zuhra ta tashi ta koma kusa da Baba. Tana dan daga gira tace
in kwanta a jikinka Baban yara? Rankwashi ya kawo mata ta goce...yarinyar nan kin
gama rainani. Wayarta ta mika masa Baba sirri nazo muyi. Umma tace ai sai dai idan
na fita amma babu inda zani ayi a gabana. Shi kuma Baba yana murmushi yace to ko
daki zamu shiga. Dariya kawai tayi ta bashi wayarta ta nuna masa sakonnin text da
ake yi mata. Baba ya karanta yafi sau uku uku murmushinsa na fadada yace waye
wannan? Zuhra tace nima ban san shi ba. Amma kaga a sakon karshe yace yana jiran
amincewata ne ya gabatar da kansa wurinka. Da izininka zai fara zuwa. Duk dadi ya
kama Baba sai murna yake. Umma tace kuyi min bayani mana. Baba yace saurayi muka
yi. Umma tace kai Baban Zuhra akan yar nan ka iya rufe ido ka manta kai babanta ne.
Yace to da 'yar wani kike so nayi. Kinga Zuhra ki tura masa da amsa mai
dadi...banda shirme kinji ko sannan kice kin amince ya gabatar da kansa. Tunda yace
yana aiki a wani kamfani ai kinga ko ba komai da dan iliminsa ko da na sakandare
ne.
Karfe tara na dare text ya sake shigowa wayar Zuhra.
** Kewarki ta dameni, ki amince na nuna miki soyayyata gareki**
Wani juyi Zuhra ta rinka yi cike da tsananin jindadi. A yan kwanakin nan ta tsinci
kanta da jiran text duk safiya da dare. Reply ta tura kamar yadda Baba ya bata
shawara
** Na amince**
Har Izzatu ta kwanta taji shigowar text. Hamza ya kai hannu zai dauki wayarsa tayi
saurin dauka. Yace ni da wayata zaki min kwace? Tayi murmushi ta bude ta karanta.
Dadi ne ya kamata. Hamza yace text din waye ne kike murmushi. Kamar yadda ta saba
saurin gogewa tayi tace kyale tallan MTN ne.
[9/25, 3:37 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿19
Batul Mamman(Mrs)💖
Su Zuhra an fara biki. Sunyi kamu ranar laraba a wani fili nan cikin layinsu. Yan
makarantarsu da yawa sun zo bikin. Wata cikinsu mai suna Ikilima ce tayiwa amarya
kwalliya. Zuhra tana daura dankwalin ankonta Ikilima tace don Allah ki bari nayi
miki kwalliya. Wannan fuskar taki duk kin bata ta. Tissue tasa ta goge fuskar Zuhra
sannan tayi mata kwalliya. Nan kawayensu suka rinka cewa tayi kyau sosai.
Washegari da babu abinda zasu yi amma an dan taru a gidansu Hajara. Yan mata kuma
suna gidansu Zuhra. Tana zaune ana yi mata kitso wayarta tayi kara. Ta daga taga
sunan Izzatu. Hankalinta ya dan tashi bata gama mata sakar yaranta ba. Hakuri ta
soma bata tana daga wayar.
Izzatu tace ba komai ai nasan kuna bikin kanwar Faiza. Ni magana daban na bugo
muyi.
Zuhra tace to ina ji.
Izzatu tayi yar dariya, dama ranar da kika zo gidana kina fita kanina ya shigo kila
ma kin ganshi.
Zuhra ta dan yi tunani kai babu kowa a hanyar.
Izzatu tayi saurin gyara zancen kada Zuhra ta gane. Cewa yayi ya ganki don yana
shigowa tambayata yayi ko kina da aure. Nace a'a. Shine ya dame ni har na bashi
numbarki. Ina tsammani ya kiraki ko yayi text.
Daga daya bangaren Zuhra taji wata murya mai dadi ana cewa haba Izzatu na fada miki
ban fara yi mata waya ba sai naga babanta. Zuciyarta har wani saurin bugawa tayi,
ba dai mai yi mata text dinnan bane.
Izzatu ta katse mata tunani yace sai gobe zai zo gidanku magana da babanki bayan
magariba. To a ranar zamu tashi shine za'ayi walima a sabon gidan. Don Allah kizo
in nuna miki shi. Ni a ganina gara ku fara haduwa kafin maganar taje ga iyaye. Kuma
sunansa Hamza don yace bai fada miki ba ko.
Lallai da gaske Izzatu take don jiya yayi mata text yace zai zo ranar Jumaa. A take
taji tana jin kunyar Izzatu. Ashe ma dan gayu ne indai kanin Izzatu ne. Ji tayi
ance Zuhra zaki iya zuwa din ko ma hadu a gida? Farinciki fal zuciyarta ta rike
wayar tana murmushi. Wai ita ce saurayi ke mata magana irin haka. A hankali tace
zanzo in sha Allah. Daga nan ta ajiye wayar.
Izzatu ta kalli kaninta Walid tace gobe akwai show a gidan nan. Walid yace amma sis
sai naji ba dadi kuma. Dungure masa kai tayi...to kill joy idan ka ga dama kada ma
kazo. Ya gyara face cap dinsa da ta karkace wai da yaya kike daukar wayar Hamza ne
bai sani ba? An gaya maka ni din ta wasa ce? Baya amfani da wayar sosai sai nace ya
bani aronta don kada Zuhra tayi text ko waya yana office.
Bayan an watse ne ta sanar da Umma yadda suka yi da su Izzatu. Umma tace ba komai
amma idan kinje kada ki dade saboda lanchin din Hajara. Ku ne iyayen biki. Haba ai
bazan dade ba Umma. Don tana ta rokona ne ma. Umma tace ba komai ki yi sauri dai.
Daga nan fita tayi taje ta sanar da aminiyarta Hajara. Amma fa ban fadawa Umma zamu
hadu dashi ba. Hajara tayi mata dundu tana dariya tace yarinya ta fara sanin
soyayya. Tana dawowa gida ta tarar da Umma tana wanke wata farar shaddar Baba mai
kyau. Zuhra tace gobe zashi daurin aure ne? Umma tace ba kince yaron nan Hamza zai
zo gaishe shi ba, ai gara a ganshi da kwarjininsa shima. Wani dadi Zuhra taji tace
to kawo na karasa wankin. Umma tace bari dauraya ta rage min.
Biyun dare ta wuce sannan aka kawo wuta. Zuhra ta tashi tana magagin bacci dama
jiran wutar take yi. Da sanda ta lallaba ta dauko kayan Baba daga shanya tazo ta
goge masa. Itama cikin kayanta na bikin Hajara ta sake gogewa. Daya zata je gidan
Izzatu walimar tarewa, dayan kuma sai da yamma idan Hamza yazo.
Rigunan sanyin da ta karasa sakawa ta saka a leda ta gama shirinta tsaf. Shigen
gyaran girar da kawarta tayi mata a kamun Hajara ta kokarta tayi. Sai dai tata tayi
girma da baki da yawa. Leben nan yasha janbaki purple don ance mata shi ake yayi
yanzu. Tayi daurin dankwalinta sannan ta kawo katon mayafi ta dora a kai. Umma ta
yaba da kwalliyar tace idan kin kai mata kayan kada ki karbi kudi tunda kinga inda
rabo kaninta zaki aura. Zuhra tayi dan murmushi tace to Umma. Ko daga nesa ka
hangota za ka san tana cikin nishadi. A haka ta je gidan anti Faiza don tare zasu
tafi. Anti Faiza tace naga alama dai Izzatu na ji dake. To dai muyi sauri kinga
akwai sauran shiri a gabanmu. Ni ba don aikin meatpie dinta ba ai ba inda zani. Sai
dai ta bani fiye da kudin aikin shiyasa na karba. Dreba Izzatu ta turo ya dauki su
Zuhra saboda kulolin da Anti Faiza ta zuba meatpie har uku ne.
Hamza ya gama magana da lauyansa an gama komai a takardun tsohon gidansa. Da
daddare in Allah Ya yarda zai kaiwa Alhaji a bawa kaninsa Nura. Idan yaso in ya
tashi aure sai a kara gyara gidan. Ya dan shafi kansa yasan yau iyayensa zasuyi
farinciki da abinda yayi musamman Mama. Sakonnin email dinsa ya bude yana karantawa
don yau bazai koma gida da wuri ba sai sun gama walimarsu. A firgice ya tashi yana
kiran Inuwa sakatare. Inuwa ya shigo da sauri yana tambayar ko lafiya. Hamza ya
nuna masa wani sako da aka turo daga Mr Peter wakilin turawan da suka hada gwiwa
dashi. Gumi ke keto masa ko ta ina yace Inuwa mutanen nan sunsha kwaya ne da zasu
ce wai suna yi min tuni akan basu ribar da muka samu a watannin nan shida gaba
daya. Ya ture takardun tebur dinsa. Ni ban fahimce su ba kwata kwata ina aka taba
kasuwanci haka.. Inuwa yace ranka ya dade ka manta a contract din ance ribar wata
shidan farko tasu ce. Daga nan kuma sai ku rinka raba ribar kai da su. Hamza ya
daka tsawa inji uban wa??? Inuwa ya zabura ya matsa gefe.
Wata tsawar ya sake yi jeka ka dauko min copy din contract din. Inuwa jiki na bari
ya bude wata drawer a cikin office din Hamza ya dauko masa. Karantawa yake yana
maimaitawa. Ya dago idanunsa da suka yi ja yace Inuwa garin yaya nasa hannu a
takardar nan? Inuwa ya tausayawa ogansa yace ranar da Junior ya karye ne. Nima
bayan ka fita na sake karantawa shiyasa na turo maka da text a daren. Hamza yayi
saurin dago kai. Text kuma? Eh text na sake maka bayanin contract din ko zaa gyara
tun kafin abin yayi nisa. Kuma ka tabbatar min ka karanta. Don kace Hajiya ta sanar
da kai na bugu waya ma. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Izzatu kin kasheni shine
abinda Hamza ya iya fada a hankali.
[9/25, 3:40 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿20
Batul Mamman(Mrs)💖
Lokacin da suka isa gidan cike yake da mutane tamkar ana biki. 'Yan gidansu Izzatu
har da mamanta duk sun zo. Ga kawayenta da makota da wadanda ma ba'a sansu ba 'yan
cin ta tsotse. Kannen Hamza kuwa Mariya ce kadai taje sai Ummahani matar Ibrahim.
Su Hamida suna Kumo ita da Adabiyya da Nura.
Gidan ya tsaru sosai kana gani kaga gidan babban architect. Sama da kasan ko'ina
mutane hawa sukeyi ana kallon yadda aka kashewa gidan kudi. Zuhra sai rakube rakube
take yi ita tazo gidan surukai. Anti Faiza tana mata dariya don Hajara ta tsegunta
mata zancen kanin Izzatu.
Izzatu na ganinsu sai murna tasa aka shigo da meatpie din aka hada shi cikin kayan
rabo. Zuhra ta mika mata kayan sanyi tace bari na dauki miki