Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
aiki. A hankali yake magana yace
Alhamdulillah. Tana zaune akan kujera tana masa kallon tuhuma tace Hamza ko ka
fara sonta ne? Bangane ba shima a zaunen yake don baya jin zai iya cin abinci.
Banda damuwar da yake ciki hannun Zuhra yake hangowa miya na binsa ta gefe tana kai
lomar tuwo. Yarinyar ta fiye kazanta. Izzatu ta dan sha kunu Zuhra nake nufi.
Lokacin da ka shigo ita ka fara kallo kuma ka danyi murmushi. Izzatu kenan,yanzu
baki bani komai nasa a baki ba kike tuhumata. To idan naso ta laifi ne? Matata ce
fa. Sosai ta daure fuska bana so, Hamza bana son irin wannan wasan. Nan da wata
shida zata koma gidan iyayenta mu cigaba da zamanmu yadda muka saba. Daga nan sai
kuma ta soma murmushi baka ga yadda take cin abinci ba dazu. Baka ce dan bakin nan
tana zai dauki abinda take tura masa ba. Idan ka fita yau pizza zaka siyo mana Baby
a matsayin dinner. Ko sau daya bata damu da rashin walwalarsa ba. Hmmm kina bani
mamaki Izzy...me kuma nayi Babyna? Murmushi take masa tana kashe ido. Fada mata ma
bata lokaci ne don karshenta ta fadi abinda zai kara bata masa rai. Babu komai bari
na dan kwanta kaina na ciwo. Tashi tayi to bari na kawo maka magani. Amma kafin nan
ga wannan....ta dauko cards har kala hudu na biki. Ni duk matsalar Zuhra yasa na
manta next week za'a fara bikin Mardiya cousin dina ta kaduna. Yar Uncle Jibril
kanin Dad dinmu. Wai matar da miji ya fadawa yana ciwon kai kenan. Ga naka na
daurin aure, ni a son raina ranar saturday na tafi kadunan saboda muna da shirye
shirye a gabanmu. Kasan dani suka dogara tunda na zauna a Canada suna son ayi abin
da tsari sosai. Kije Allah Ya kiyaye hanya ya fada a takaice....bargo yaja ya rufa
har kansa. Bashi da kwarin yi mata fada ko fada mata abinda ya kamata. Sai da ta
gama yi masa lissafin kudin da take bukata sannan ta dauko masa magani da ruwa.
Sai la'asar ya tashi jikinsa ya danyi kwari sannan kan ya dena ciwo. Masallacin
kusa da gidansa yaje yayi sallah ya dawo yaci abinci. Yana gama cin abincin ya
dauki key din mota....Izzy ni zan fita ki fadawa yarinyar nan kada tayi abincin
dare zan taho muku da pizza din in sha Allah. Duk maganar a sanyaye yake yinta,
wani salihanci yake ji tunda Oscar ya dibga masa sata. Tace harda Zuhra kuma? Ba
kayi mata siyayyar kayan abinci ba. Yace nasan nayi amma as long as tana gidan nan
zanyi kokarin sauke nauyinta. Tabe baki Izzatu tayi to shikenan sai ka dawo. Har
bakin mota ta rakashi ya tafi gidansu. Nan ya zauna suka sha hira da kannensa kamar
bashi ba. Hajiya taji dadin ganin ya sake ba kamar dazu ba.
[9/25, 3:54 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #40
Batul Mamman(Mrs)#
Takwas da rabi a gida tayi masa ya shigo da ledar pizza har hudu manya. Ya riga ya
kudurce a ransa daga yau siyayyar abincin alhamis ta kare sai lokaci lokaci kuma.
Itama Izzatu zai bata kudi taje bikin ta dawo sannan ya sanar da ita halin da yake
ciki tunda bata tambaya da kanta ba. Ita da yara suna ta murna da ya dawo ta karba
ta rarraba. Yanka biyu ta sakawa Zuhra a plate Hamza yace ta kara mata daya saboda
big size ce. Tala ta kirawo ta kaiwa Zuhra daki saboda tun bayan magriba bata sauko
ba. Tala ta fito daga kitchen hannunta duk kumfa tana gogewa da tsumma. Hamza ya
mika hannu bari na kai mata saman zani. Plate din ta mika masa tana tambayarsa a
ina zai ci tasa yace ta kai masa falonsa yau baya son hayaniya.
Zuhra na kwance akan doguwar kujerarta tana kallon wani film din Hausa na marigayi
Rabilu Musa dan ibro tana ta dariya. Tun daga bakin kofar dakin Hamza yake jin
dariyarta. Yarinyar nan bata da kamun kai ya fada a ransa. Ji yadda take dariya
kamar ba mace ba. Sallama yayi ta tashi da gudu ta dora hijab a jikinta. Plate din
kawai ya mika mata zai fita sai yaji tace ina wuni? Tunawa tayi dazu tana cin tuwo
bata gaishe shi ba. Jiya kuwa dama basu hadu ba. Da ya juyo ya amsa sai yaga plate
din take karewa kallo. Ta dan kalle shi....shi kuma wannan menene? Pizza ce, baki
taba ganinta bane? Tace eh, Allah Yasa da dadi dai. Sai da yayi murmushi sannan
yace ci ki ji mana. Yanka daya ta dauko gashi da girma ta dan lankwasa shi biyu ta
tura a baki ta gutsiri rabi. Sai da Hamza yasa hannu a bakinsa don mamaki....tabdi!
Ke bakinki zai iya yagewa idan kina katuwar loma haka. Dan gayun nan na mata ma
baki iya ba. Wani irin dandano taji da bata taba ji ba. Abin dai bazata iya
kwatantashi ba. Bata san lokacin da ta furzar da na cikin bakinta ba, wanda bai
sauka a ko'ina ba sai kafar Hamza.
Wayyo Allah, Wayyo Allah, Wayyo Allah shine abinda yake ta nanatawa ya dage kafar
tare da kawar da kansa gefe. Idan ya kalli kafarsa yasan dole ne yayi amai. Kamar
yayi kuka saboda da takaici. Yana girgiza kai yace ke kuwa me nayi miki zaki tofa
min abin baki. A tsorace ta dago kai zata bashi hakuri. Sauran ya gani a gefen
bakinta da habarta. Dan danne fushin da yake yi ne ya gagara ya daka mata
tsawa....Goge bakinki mana. Da hijab dinta tayi saurin gogewa sannan ta sake cewa
kayi hakuri, shi kuwa sake hade fuska yayi yana ta yatsina hanci....kai so
disgusting yace yana rike hanci.
Irin kallon bangane ba tayi masa sannan tace SO kuma? Ni yaushe kaji nace so? Ba
cewa nayi ina sonka ba hakuri nake baka. A wane dalilin zan ce ina sonka? Mamaki ta
bashi ya rasa daga ina taji kalmar. Sai daga baya ya tuna yace SO DISGUSTING.
Dariya sosai abin ya bashi, yace anya kin taba shiga aji kuwa? Sosai ma kuwa, har
SS3 na kai a sakandire. Tana magana ta durkusa zata goge masa na kafar tasa da
hannunta. Saurin jan kafar yayi tare da yin tsaki...kazama da hannu kuma zaki goge,
ni bani tissue. Eyye me kace? Ya sake maimaimatawa. Dan murmushi tayi na ta gane
zancen. Toli fefa kake nufi, wallahi bani da ita. Jin kafarsa yake kamar ya yanke
ta yace to dauko min ta toilet dinki da sauri. Ya dan kalli kafar....Oh God I hate
this.
Gani yayi bata tafi ba ya dan daga murya nace ki dauko ta toilet kin tsaya kina
kallona. Baya ta dan sake matsawa na fada maka babu. Iko sai Allah, yanzu ko a
toilet babu? To da me kike amfani. Dariya ya bata ji wata irin tambaya.... tace da
tawul mana, ni bansan ana goge jiki da toli fefa ba. Jin bata fahimce shi ba ya
kara bashi haushi. Ni ba cewa nayi a goge jiki ba. Shiru yayi saboda kunyar abinda
zai fada. Da kyar yace kafin kiyi tsarki nake nufi. Kanta ta dan juyar a kunyace
tace tsarki da toli fefa kuma kamar wata arniya.
Yarinyar nan duka take so...kwafa yayi sannan yace ke a kazantarki idan kin gama
abinda kike a toilet hannu kike sawa? Shi kam Izzatu ta cuce shi da tayi sanadin
auren nan. Gaskiya ke kazama ce ta karshe ya fada yana toshe hanci. Hanyar toilet
dinta yabi zai wanke kafarsa sai wata zuciyar ta hanashi. Karshenta yaga wani kayan
kazantar. Da jan kafa ya fita daga dakin ya tafi nasa. Ya shiga toilet ya sakarwa
kafar ruwa. Sai da yaga babu komai a kafar sannan yayi wanka ya fito.
Ita kuma Zuhra gyara wurin da abin pizzar ya bata tayi ta sauka da sauran a plate.
Izzatu ta kaiwa suna cin nasu dasu Khalifa tace bazan iya cin wannan abin ba.
Izzatu tayi dariya dama shi ya dage sai ya baki. Tana karba ta bude plate din da ta
saka masa nasa ta kara da sauran biyun na Zuhra. Tana kallo Zuhra ta wuce kitchen
dinta ta dumama tuwo ta haye sama zata ci.
A bakin bene suka hadu yace mhmmm haka kika iya, ki cika kwano da tuwo. Bata amsa
ba ta bashi wuri ya sauka. Izzatu ta biyoshi falonsa da nasa abincin. Biyun saman
wanda aka yi da naman kaza ya cinye yace ya koshi. Izzatu tace kuma kai na ajiyewa
mai beef(naman saniya) din don nasan shi kafi so. Ruwa ya dauka a cup yana sha tace
ashe rabonka ne mai chicken din da Zuhra ta dawo dashi wai bata.......kwarewa yayi
sosai tun kafin ta gama maganar ya soma kakarin amai. Idanunsa har ja suka yi
saboda wahala yace yanzu Izzy ragowar yarinyar nan kika bani. Tace to meye ai bata
ci ba, hannu tasa tana shafa masa baya. Sannu kaji my darling shiyasa ba'a son
magana idan an cin abinci.
[9/25, 3:54 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #41
Batul Mamman(Mrs)#
Washegari meeting din gaggawa ya kira da dukkan maaikatansa. A nan yake sanar dasu
abinda Mr Oscar yayi. Inuwa sakatare yace shi yayi mamaki da ya ganshi a banki amma
tunda manaja yace da yardar Hamza aka saki kudin shiyasa bai tayar da zancen ba.
Maaikatan suka tambayi Hamza garin yaya haka ta faru yace matsalace ta taso daga
gida a lokacin. Yana kujerar tsakaya a conference room din yadda kowa zai iya
ganinshi a katon zagayayyen table dinsu yace kada ku damu in sha Allah bazan bari
kwazonku ya tashi a banza ba. Sauran cheques din ya nuna musu Allah Yasa na rarraba
da guda daya ne Oscar ya dauka ba karamar matsala zamu shiga ba. In Allah Ya yarda
zan san yadda nayi na fito da wata miliyan goman da zamu hada musu. Next zuwan Mr
Peter kasar nan zamu hada musu kudinsu. Ayyukan gabanmu kuma kunga manyan projects
ne. Ina rokon kuwa dage ayi ingantaccen aiki. Sannan ina neman afuwarku na
kasancewata shugaba mai sakaci da aiki. Muryoyi ne suka rinka tashi suna fada masa
babu komai. Wani yace yallabai irin haka shine yake sa bawa ya kara jajicewa da
imani. Ba karamin dadi yaji ba da yadda suka yi masa uzuri. Bayan sun gama
tattaunawa addua suka yi aka rufe taron. Shima sai ya sake samun kwarin gwiwa tare
da yiwa kansa alkawarin bazai sake basu kunya ba.
Kafin ya koma Izzatu ta gama hada duk kayan da zata bukata na tafiyar. Idan ta tafi
sai lahadi ta sama zata dawo. Sannan ta sanar da Zuhra zatayi tafiya. Tala ma ta
hada nata kayan dana yara.
Suna zaune a falo daga Zuhra sai Izzatu tace idan mun tafi basai kinyi girki da
Sweetyna ba. Zai rinka siyan abincinsa, da zaki yarda ma kawai ki tafi gidanku ki
kwana biyu kafin na dawo. Zuhra tace a ranta lallai Izzatun nan ma, daga aure sai
tafiya gida a kwana? Wannan ai sai mutane su gane lallai auren babu lafiya. Izzatu
tace kinyi shiru ko ba kya son zuwa gida. Nasan dole zaki fi jindadi da sakewa a
nan to amma....Zuhra taji haushin maganar tace ba haka bane, su Baba zasu yi
tunanin ko akwai matsala. Kinga idan akayi sakin laifinsa zasu gani. Izzatu tayi
dan tunani eh haka ne fa. To ki zauna amma ko da wasa kada ki shiga harkarsa nasan
shima bazai shiga taki ba don ba sonki yake ba. Murmushi Zuhra tayi tana jin yadda
Izzatu ke fada mata bakaken maganganu.
Dubu dari Hamza ya bawa Izzatu kafin su kwanta. Tayi murna amma fuskarta ta nuna ba
haka taso ba. Yana daga kwance yace ya akayi ne? Juya kudin take yi a hannu babu
komai, nayi tunanin zaka karamin ne saboda yara. Ga Tala zan tafi da ita don ta
kula dasu. Tashi yayi zaune ba shiri, da Tala zaki tafi amma baki fada min ba?
Tunaninsa bai wuce zaman da zaiyi da Zuhra shi kadai ba na kwana takwas. Izzatu
tace da bakinka kace ko unguwa zani na dade na rinka tafiya da ita. To zan sami
karin kudin? No, yace tare da sake kwanciya. Bani dasu. Idan kin dawo akwai maganar
da nake so muyi. Ta tashi ta saka kudin a jaka. Indai ba Zuhra ka fara so ba ko
meye babu damuwa. Hamza ya girgiza kansa kawai ya kwanta, halin Izzatu sai ita.
Wato gara duk abinda zai faru ya faru akan ta zauna da kishiya.
Washegari da wuri suka shirya kafin goma duk kayansu suna mota. Suna gama breakfast
dreban da yake kai su Khalifa makaranta ya iso. Tare zasu tafi ya dawo a motar haya
ya barwa Izzatu motar. Idan sun tashi dawowa ya koma ya dauko su. Har bakin mota
Zuhra ta rako su. Hamza ya rungume 'ya'yansa sannan suka wani manne da juna shi da
Izzatu ana kiss a gaban mutane. Kunya duk ta ishe Zuhra. Ita kuwa Tala dama ta saba
gani. Nan suka tsaya har motar ta fita maigadi ya rufe gate.
Ajiyar zuciya Zuhra tayi tana tausayawa kanta yadda zata zauna ita kadai a gidan.
Kasancewar Hamza ba tafiya zaiyi ba bai dameta ba tunda ba harkar juna suke shiga
ba. Ciki ta koma zata tafi dakinta Hamza ya shigo yace ki shirya bayan azahar zamu
fita. A sanyaye ta dan juyo gida zaka mayar dani? Na fada mata zan zauna a nan
saboda kada a zargi wani abu a gida. Hamza yace Izzatu tace ki koma gida ne? Wai
ita zai nunawa bai sani ba. Tace eh jiya ta fada min. Dan guntun tsaki yayi. Izzy
ta fiye rigima itama. Ki shirya zamu je ki gaisa dasu Baba sannan muje gidanmu.
Wani tsalle tayi da yasa ya matsa gefe kada ta bige shi. Alhamdulillah ta fada ta
haye sama cike da murna. Wani lokacin sai ya ganta kamar mai hankali, idan abin ya
motsa kuma ba kanta. Daga murya yayi yace idan na dawo daga masallaci baki shirya
ba an fasa. A hankali tace zaka sha mamaki.
Ai kuwa yasha mamakin domin yana dawowa daga masallacin ya ganta zaune kwam a falo
ta gama shirinta. Tuna masa tayi da ranar da ya fara ganinta har ya kusa bigeta da
mota. Duk zafin da ake a gari fuskarta sai kyallin foundation take. Tabi girarta da
pink din jagira ta gyarata, da yake kayan jikinta akwai green sosai har mayafin
haka ta saka green din eyeshadow. Sai yan labbanta da ta zanawa bakin lining sannan
ta saka jan janbaki da ya fito sosai. Abin bai bashi dariya ba ma, wannan wace
irin kwalliya ce. Mtswwww
Da taji yayi tsaki ga wani kallo da yake binta dashi sai jikinta yayi sanyi. Shi
dama bai ma gama shiri ba don jallabiyace a jikinsa. Muje yace da ita yana shirin
hawa bene. A tsorace tace ina???? Sama ya nuna mata da hannu. Kawai gani yayi ta
durkusa gwiwoyi a kasa idanunta sun ciko da hawaye don Allah kada mu fasa zuwa. Don
Allah ka kaini naga Ummana da Babana. Yayi yar dariya au gorin iyaye zaki min?
Girgiza kai tayi da sauri a'a Ummanmu da Babanmu nake nufi. Yace to naji tashi
muje yana murmushi. Da gaske sama taga zai hau sai ta dan ja baya. Hannunta kawai
ya kama ya ja ta suka hau saman tana ta tirjewa. Wani abu yaji ya soki zuciyarsa da
ya kama mata hannu.
[9/25, 3:55 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #43
Batul Mamman(Mrs)#
Har suka isa gidan babu wanda yayi magana a motar. Ficewarsa ma yayi daga motar ya
shiga gidan ya barta. Kwafa tayi sannan ta fito da ledarta a hannu. Hanyar da yabi
itama ta bi. Sai ta ganshi a bakin kofa yana tsaye...kinji yadda naji dazu da kika
fita baki jirani ba. Bude baki tayi....lahhh wai haushi kaji. Sai kuma yaji haushin
kansa meye zai biye mata harda ramawa. Gyaran murya yayu shi a dole a bawa. Shige
muje ya nuna mata hanya.
Dakin Mama suka fara zuwa bata ciki. A hanyarsu ta zuwa dakin Hajiya suka hadu da
Adabiyya. Wani ihu ta saki tare da kankame Zuhra. Oyoyo Anti Zuhra....Hamida naji
ita ma ta fito daga dakinsu suna ta ihun murna Zuhra na murmushi. Hamza yace
lallai yaran nan. Kirikiri kun nuna min bakwa son uwar 'ya'yana. Hamida tace to
Yaya ai itama ba sonmu take ba. Tana fada ta shige daki da gudu don tasan muguntar
dallin bakin da yake mata. Adabiyya ta gaishe shi sannan taja hannun Zuhra suka
tafi kitchen.
Hajiya na dora ruwan tuwo suna hira da Mama. Adabiyya na shiga Hajiya tace wato don
kada kuyi aiki kunce zakuyi karatun jarabawa sai gashi kun cika mana gida da ihu.
Adabiyya tana dariya ta turo Zuhra da ke makale jikin kofa kinga bakuwar da muka
yi. Mama ta taso itama tana mata sannu da zuwa. Kasa Zuhra tayi duk ta gaishesu.
Ina Yayan naku Mama ta tambayi Adabiyya. Yana wajen dakinku. Fita Mama tayi tace
Adabiyya kaita dakinku zata fi sakewa ki kai mata abinci.
Idon Zuhra na kan Hajiya tana bare albasa zata hada ruwan miya. Gabanta ta karasa
a kunyace tace Hajiya kawo na yanka miki. Itama Hajiyan ta rasa dalilin da yasa
taji kunyar Zuhra kamar yanzu Yaya ya fara aure. Barshi kuje daki da Adabiyya idan
na gama zanzo mu sake gaisawa. Adabiyya ta gama hada cup da lemo a tray tace zo
muje Antinmu. Zuhra ta mika hannu don Allah Hajiya ki kawo na tayaki. Me zaki dafa
nayi miki? Na iya girki fa. Hajiya tayi murmushi tana kallon Zuhra. Mayafinta ta
cire ta jefa saman kofar kitchen din. Adabiyya tace don Allah kizo muje idan kika
sha ruwa sai mu dawo. Ki tayani zama a nan kawai muyi girki. Ta karbi albasar
Hajiya kije ki huta. Sosai Hajiya taji dadi sai dai kuma girkin saboda Alhaji da
zai dawo daga Kumo yau take yi. Amma yadda Zuhra ta langabe mata kai yasa ta hakura
ta fada mata tuwon semovita zata yi da miyar danyar kubewa wadda tuni Hamida ta
gurza. Tana fita Adabiyya tace gaskiya ina taya Yaya murna yanzu yayi aure. Zuhra
bata ce komai ba sai dariya tace ta bata roba zata yi rude. Sai ga Hamida da
littafi a hannu tace ayi hirar da ita. Sunso sa mata hannu tace ita dai su tayata
zama. Komai ta nema zasu nuna mata haka tayi tuwonta wanda ya tuku sosai yayi
kauri. A leda ta kulle sannan ta bar ruwan miyar wajen awa daya yana dahuwa wutar
kasa kasa yadda Umma ke yi. Hamida tace ita kamshi ya dameta a kada miyar yau tuwo
zata ci ba indomie ba. Suna ta barkwancinsu har ta gama hada miyar kitchen din yana
ta kamshi.
Mama da Hamza suna daki suna hira. Da suka gama yace zai fita sai bayan sallar isha
zai dawo. Dakin Hajiya taje tace mu leka yarinyar nan ko? Hajiya tace tana kitchen
da yan uwanta wai ita zata yi tuwon. Farincikin Mama bazai misaltu ba tace Hajiya
kinga ikon Allah ko. Kina ganin Zuhra kinsan yarinya ce mai tarbiya. Hajiyan ma
murmushi take, sai wani koda surika kike a gabana ko kunya babu. Bari nawa dan Nura
yayi aure kisha mamaki. Haka suka sha hirarsu gwanin sha'awa har