Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
a ciki ka dena ce min ke kamar
wata...yan lips din nata ya kama da yatsunsa biyu. Taji zafi ta fara kokarin cire
hannun nasa. Idan kika ki tsayawa tsinkesu zanyi sai naga na tsiwar . Idanunta duk
sun firfito sai hawaye sharrr.
Sai lokacin ya kare mata kallo. Ba wani tsahon kirki gareta kuma tana da jiki
madaidaici. Kalar fatarta bata da haske sosai amma kuma ba baka zaa kirata ba.
Akwaita da idanuwa masu kyau ga hancinta da baki duk yan madaidaita. Banda rashin
iya kwalliya da itama zata shiga jerin matan da basu da muni. Hijabin jikinta ya
kalla duk yasha hawaye da majina. Sai lokacin yaji kyankyami ya sakar mata lebe. Ta
karkace baki ta sake cewa Allah zai saka min. Kan gadon ta haye zata zagaye shi ta
gudu. Yasa hannu ya fizgota ta saki kara. Da karfi ya manna ta da bango ta runtse
idanunta tana jira ya sake kama leben. Dalli taji masu zafi guda uku ta sake cewa
Allah Ya....wani ya kara mata da yafi sauran zafi. Nan da nan ta soma kuka mai
sauti. Irin kukan da idan ta fara a gida har makota sai sun leko an bata hakuri
take denawa.
Hamza huci kawai yake don bacin rai. Me zaisa Alhaji ya hadashi aure da wannan mara
kunyar yarinyar. Gashi ta kafeshi da idanu kamar wani sa'anta. Yi min shiru ya fada
da karfi. Tsaf ta hadiye kukanta. Ina so kisan cewa ba'a min rashin kunya. Sannan
kika kara cewa Allah Ya isa sai na dirje miki baki. Kina jina? A hankali ta gyada
kanta domin taji zafi a bakin da ya dalle. Good ya fada, me yasa baki fada min za'a
kawo gara ba? Kuma a ina kika sami abinda zaki bawa bakin? A hankali tace Anti
Faiza ce ta kawo. Ga gidan yunwa ko, shine abinda za'a bawa baki ma sai kin roka
don ki jawo min magana ace bana kula dake. Hannu tasa ta rufe bakinta sannan tace
nima bansan zasu zo ba sai jiya. Kuma ban ganka ba bare na fada maka. Ni duk abinda
kuke yi min banji haushi ba sai....sai me ya tambaya da yaga ta kasa karasa
maganar. Ba komai ta sunkuyar da kai. Zare mata ido yayi bazaki fada ba sai na kara
dalle bakin. To ba kaine jiya kace zaka aiko min da abinci ba amma naji shiru. Da
daddare ma kuka barni na kwana da yunwa. Wani iri yaji a jikinsa...kika kwana da
yunwa??? Nufinki ba'a kawo miki abinci ba. Zaka ce baka sani bane.....auuuu, tayi
saurin rufe kanta da hijab kada ya sake mata wani abin. Ga mamakinta shiru taji
tana dago kai har ya bude kofa sai ya juyo. Da sauri ta sake rufe bakinta. Key din
kitchen din ya jefo mata gashi nan zansa a hada miki gas cooker. Bai kula ba yayi
tafiyarsa. Key kuwa a goshinta ya sameta ta soma tsalle tana ihu. Allah Ya isa ta
fada a hankali.
Kasa ya sauka ya sami Izzatu tana kallo. Tana ganinsa ta taso Baby....hannuwanta ya
ture da take shirin taba shi. A wane dalili ne jiya baki bawa yarinyar nan abinci
ba? Wani irin kallo ta masa Why do you care? Saboda matata ce hakkinta ne na ciyar
da ita. Matarka fa kace Hamza? Har Zuhra takai matsayin da zata hada kai dani.
Wallahi sai ka saketa a yau....wayarsa ce ta soma ringing. Yana dubawa yaga manajan
bankin da ya tura Inuwa ne ya karbo kudi a cigaba da aikin ginin da suke yi. Izzatu
sai fada take yana daga mata hannu tayi shiru taki.
Mr Oscar ya gama tsorata tunda manajan yace bari ya kira Alh Hamza ya tabbatar ko
shi ya aiko shi. Ya gama hango kansa a matsayin korarre daga aiki kila ma a rufe
shi. Bayan sun gaisa manaja yace Alhaji dama na kira ne domin confirming ko kai
kayi authorizing cheque na 10 million. Gefe Hamza ya dan matsa amma Izzatu har nan
ta biyo ita wallahi ko ita ko Zuhra. Daidai sanda manaja yace ka turo Mr Oscar
Hamza baiji ba amma tunda yasan ya turo Inuwa sakatare sai yace eh ya ajiye wayar.
Ya juyo ransa ya gama baci Izzatu ki shiga hankalinki dani wallahi. For God's sake
ya kike so nayi da rayuwata ne. Daga ke har yarinyar da kika yi sanadiyar zuwanta
gidan nan bakwa gabana. Duk kin birkita min lissafi lokaci guda. Da kamfanin zanji
ko masifarki? Come on get out of my way ya tureta ya fice don ya kusa makara
masallaci.
Mamaki ya kama Mr Oscar lokacin da manaja ya bada order a bashi kudin. A tsorace ya
karba jiki na rawa yana ta tunanin kada ace ya dawo dasu. A daidai bakin gate suka
hadu da Inuwa sakatare. Cikin Mr Oscar ya murda sosai ji yake kamar ya saki zawo
don firgici. Inuwa yace Oscar kaima ashe kana banking a nan. Nima sauri nake kada
su tashi kasan yau Friday Oga ya aiko ni. Kai kawai Oscar ya gyada yayi gaba yana
kankame jakar kudin.
Inuwa bai kawo komai ba ya shiga bankin. Shima wurin manaja aka kaishi saboda yawan
kudin. Manaja yace kuma kaga yanzu wani maaikacin kamfaninku ya karbi the same
amout na 10 million. Hala babban project ne a gabanku. Inuwa sakatare yace Oscar ma
kudin kamfani ya karba? Manaja yace eh har da Oganku nayi confirming. Inuwa yayi
mamaki dai amma sai ya karbi kudin ya tafi. A iya saninsa shi kadai Oga yake aika
banki.
[9/25, 3:52 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #33
Batul Mamman(Mrs)#
Washegari Jumaa tun bakwai da rabi Hamza ya fita zuwa site din da suke wani gini.
Dama a daren Izzatu ta kai masa karar Zuhra wai tayi mata rashin kunya. Da safe ta
sake tuna masa yace idan ya dawo zaiyi maganin abin. Yau bakin shayi da bread aka
kaiwa Zuhra a matsayin breakfast. Bata nuna damuwa ko kadan a fuskarta ba da Tala
ta kai mata. Tasan Izzatu na neman suyi fada ne ita kuwa bazata biye mata ba. Bayan
ta gama sha ta dauki kofin ta sauka kasa.
Junior ne ya tareta a kofar kitchen din...Zuhra meyasa kika dena cin abinci tare
damu? Shafa kansa tayi babu komai nafi son zama a daki ne. Hannunta ya rike to nima
zan rinka zama a dakinki. Khalifa ya taho da sauri ayi hirar dashi suka hada ido da
Izzatu. Ba shiri ya koma dakinsu don yasan ma'anar wannan kallon. Tsawa ta dakawa
Junior tace ya bar wurin. Ya buga kafa a kasa ni Mummy ki kyale ni Zuhra is my new
fiyend(friend). Karasowa tayi gabansu ta kalli yadda suka rike hannu. A sakar min
hannun yaro ko. Zuhra ta durkusa a gaban Junior. Kaga tunda Mummy tace ka tafi to
ka zama yaron kirki kaji. Watarana har goyaka zanyi,amma yanzu idan kana rashin
kunya babu ruwana da kai. Murmushi yayi wanda ya kara fito da kammaninsa da Hamza.
Pyomis(promise) ya fada yana tsalle. Dariya kawai tayi don bata gane abinda yake
nufi ba. Ga mamakinta dage yayi ya mata kiss a goshi tunda durkushe take a gabansa.
Izzatu ta fizgo shi tana fada. Muje nayi maka brush, ji yadda ka taba wannan
kazantar da bakinka. Ta gallawa Zuhra harara, ita kuwa bata tanka mata ba har suka
shige ciki. Mamaki take yadda dan karamin yaro ya iya iskanci a cewarta. Kiss ai
sai marasa kunya.....
Bata bar wurin ba Anti Faiza tayi sallama. Da sauri ta tarota ganinta da kaya niki
niki. Kwalayen juice ne guda hudu, ruwa guda biyu da cake da biskit duk na kwali.
Sai da suka gama hawa dasu Anti Faiza ta sake fita ta dauko wata katuwar kula da
taimakon mai adaidaitan da ya kawota. Zuhra tace Anti Faiza wannan kayan fa? Bari
na sallami mutumin nan ina zuwa.
A falo ta jirata ta dawo. Sai da suka gaisa Anti Faiza tace kudin da na karba a
wurinki dashi na siya. Kinga anjima zaa kawo gara sai ki bawa baki. Sauran ki ajiye
kiyi amfani dasu. Ta nuna kular can kuma meatpie ne da spring rolls shima sai a
basu. Da kuka Zuhra ta rungume Anti Faiza tana godiya.
Hayaniya Izzatu ta soma ji ta fito falon. Mata ta gani wadanda bata sani ba
zazzaune suna ta hira. Ana yan ciye ciye, yan uwan su Zuhra ne da wasu makotansu
harda Maman su Anti Faiza. Basu jima ba sai ga su Mama , Mariya, Jidda da Ummahani
matar Ibrahim. Cike da kunya Zuhra ta gaishe su. Mama tace duk kannenki ne kike
durkusa musu. Tashi abinki kinji matar Yaya. Kunya sosai take ji yadda Mama ke
janta a jiki kamar wata yarta. Su Umma sunyi matukar kokari kayan garar da suka
hadawa Zuhra. Mama ta basu tukwici suka fara shirin tafiya saboda kada a rufe
tituna tunda Jumaa ce. Izzatu komawa tayi daki ba tare da ta sauko sun gaisa ba ta
dauki waya ta kira Hamza.
Shi da accountant din kamfaninsa ne suke ta lissafin kudi. Duk yadda zaiyi su hada
kudin nan kokari yake yi. Sau uku ta kira baya dauka saboda abinda yake yi. A na
hudun ne ya dauka Izzy what is it? Honey ni bansan abinda akeyi ba a gidan nan amma
ga su Mama da wasu matan da ban taba gani ba a cikin gidan nan. Kamar wata walima
suke yi ko me oho. Ana ta ciye ciye dai a falon. Table din gabansa ya buga rai a
bace. Ya rasa wani irin abu ke faruwa dashi. Wane irin taro ake yi a gidansa wanda
bashi da masaniya a kai. Tunda Izzatu tace harda Mama gara ya kira yaji ko meye.
Yayi ta trying din number dinta ba'a dauka. Suna can tasa ana ta shigo da kayan
garar cikin falo. Ta tambayi Zuhra tace key din inda akace shine kitchen dinta baya
wurinta.
Jin shiru da yayi yasa ya hada kayansa yace da accountant din zaije gida ya dawo.
Yana fita Mr Oscar ya fara hada takardun da yazo dasu wurin. Cheques ya gani har
hudu na miliyan goma goma da Hamza yasa hannu. A take zuciyarsa ta soma rawa.
Kamfanin nan na Hamza nema yake ya durkushe duk su rasa aiki. Gara ya taimaki kansa
kawai. Guda daya ya dauka ya fita. Shima rufe nasa office din yayi sai banki.
Hamza na zuwa gida ya tarar saura Anti Faiza dasu Mama. Duk sauran matan sun watse.
Izzatu na ganin shigowarsa ta taga ta fito daga dakinta. Sai a lokacin ta gaishe
da Mama. Ko kallonta bata yi ba ta cigaba da tambayar Hamza ya aiki. Baya jindadin
yadda iyayensa basa shiri da Izzatu. Tace Mariya ya yara? Itama bata kulata ba. Ai
nan Hamza ya soma fada akan me zata share matarsa. Jidda tace Yaya munfi awa daya a
gidan nan bata fito ta gaishe da Mama ba sai yanzu. Kallon Maman yayi tace kaga ina
key din kitchen din Zuhra a bude a zuba kayan nan a ciki. Sai a lokacin idanunsa
suka kai kan kayan. Kamar ya tambayi ko na meye sai ya fasa yace yana daki bari na
dauko. Mama tace yi zamanka mu danyi hira yanzu zan tafi. Zuhra jeki ki
dauko....dibi dibi ta soma yi don bata san inda zata duba ba. Izzatu ta sha kunu ,
shi kuma ya dan wayance ki duba bedside drawer ta bangaren dama.
A sanyaye ta hau saman. Ita da sau daya ta shiga falonsa ma bata gane inda yake
nufi ba. Su Nana ne suka fito daga daki sai murna anga Grams. Shiru Zuhra bata dawo
ba yayi dan murmushi Mama bari na bita.
A falon ta tsaya kasa shiga dakin. Bata ankara ba taji ya shigo ya rufe kofar har
sai da gabanta ya fadi. Hannunta ya ja cikin dakin ya matse shi iya karfinsa. A
tsawace yace what the hell is happening a gidan nan? Jikinta a take ya soma bari ga
hannu ya matse mata. Idanunta suka ciko da hawaye, ya sake yi mata tsawa nace me
ake yi a gidan nan? Kayan garata aka kawo. Tana fada hawayen ya soma digowa. Ransa
ya gama baci, kin fada min za'a kawo gara??? Tayi saurin girgiza kai. Snacks da
nagani anci a falon daga ina aka samo su? Shiru tayi saboda yadda hannunta ke zugi.
Baki da baki ne? Nan ma bata yi magana ba. Sakinta yayi ya dauko key din sannan ya
nuna mata toilet maza kije ki wanke wannan hawayen munafurcin. Da gudu gudu ta
tafi. Koda ta fito yana jiranta suka sauka tare.
Mama tana murmushi tace daga dauko key sai ka shanya mu Yaya. Zuhra yake kallo abu
ne ya shigar mata ido na tsaya wanke mata. Kowa sai sannu yake mata ana tambayarta
ko ya fita. Budar bakinta kawai sai ta soma kuka. Mama ta tashi da sauri tana
tambayarta me aka yi mata. Shima Hamzan tambayar da yake mata kenan a dan tsorace.
Tana kukan tace idon ke zafi....Mama ta rungumeta Yaya kace yar tawa sarauniyar
shagwaba ce. To sannu kinji Fadimatu ki dena kuka. Idan bai fita ba sai kuje
asibiti Yaya. Kai kawai ya daga yana kallon Zuhra cike da tsoron kada ta fadi
abinda yayi mata.
Sai da aka shigar da komai kitchen din har Mama na fadan garin yaya ba'a fara aikin
gyara wurin ba yace sai weekend mai aikin zai zo. Tare da Anti Faiza suka tafi suka
ajiyeta a hanya. Zuciyar Mama tana mata wasi wasin dalilin kukan Zuhra. Bata sani
ba ko idonta ne amma kamar ta rame ma.
[9/25, 3:52 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU # 35
Batul Mamman(Mrs)#
Fadan da Hamza yayiwa Izzatu yasa ta kuka sosai bayan fitarsa. Kwana biyu a tsakani
yana share lamarinta. Ranar monday ran kowa a bace suka rabu saboda sun kwana da
fushi da juna. Ta dage sai ya saki Zuhra idan yana son zaman lafiya. Takaicinsa
shine kamar bata san mahaifinsa yayi masa katanga da sakin Zuhran ba. Ita ba
ruwanta ko Alhaji zaiyi fushi dashi ita dai bukatarta ta biya. Ko kulata baiyi ba
ya fice abinsa. Saboda bacin rai wata jaka ta dauko tana kuka tana watsa kayanta a
ciki. Sai da ta gama ta kira mahaifiyarta tana sanar da ita zata taho gida. Idan
babu jirgi zata yi shatar mota. Da kyar Raliya ta samu Izzatu ta fada mata abinda
ya faru. Tsaki Raliya tayi...ni bansan baki da hankali ba sai yau Izzatu. Yanzu
sati daya da zuwan yarinyar har kin karaya? Duk ke kika jawowa kanki ai. Muryarta
har ta dashe don kuka tace what do I do Mum? Bazan iya zama da wata mace a gidan
nan a matsayin kishiya ba. Raliya tace calm down. Yanzu abinda nake so dake shine
ki bude kunnuwanki kiji abinda zan fada miki...........
A site din ginin Hamza ya hadu da Inuwa sakatare yace Inuwa hala baka sami zuwa
bankin bane ranar Jumaa banji alert ba. Ikon Allah kuma naje ranka ya dade har ma
na hadu da Oscar. Sakon yana cikin motata bari naje na dauko. Hamza ya dakatar
dashi. Ka bari sai mun koma office.
Zuhra tayi mamakin abincinta na rana yau. Duk da bashi da yawa sosai amma yafi
abinda aka saba zuba mata. Da laasar ma Izzatu har shiga dakinta tayi tace mata
zata je unguwa. A darare Zuhra tace Allah Ya kiyaye hanya. Bayan ta tafi Zuhra ta
tashi taje inda Izzatu ta tsaya zuwa bakin kofa ta karanta Ayatul Kursiyy ta tofa a
ko'ina. Irin wannan makircin na kishiyoyi ai mun saba jin labarinsa ta fada a fili
tana dan dube dube ko an barbada mata wani abin. Kin gama yi min masifa yau kice
min zaki fita kamar nice dan gatan mijin nan naki. Ga mamakinta da Izzatu ta dawo
tare da yaranta suka sake zuwa dakin Zuhra tace ta dawo. Da dan murmushinta na
tsoro tace sannu da zuwa. Zuciyarta ta gama bata akwai abinda ke shirin faruwa ko
zai faru.
Ranar Hamza bai sami dawowa gida ba sai wajen tara na dare. Gidansu ya biya Mama
take tambayarsa yaushe zai kawo amarya. Dammm yaji a zuciyarsa, yanzu jira ake ya
dauko wannan kazamar a mota. Cewa yayi weekend in Allah Ya yarda zai kawota. To ka
biya da ita taga nata iyayen inji Hajiya.
Lokacin da ya shiga gida falon tsit. Yasan su Khalifa sunyi bacci saboda makaranta.
Dinning table ya kalla yaga an jere shi da kwanuka kamar ana jiran baki. Ko bi ta
kai baiyi ba ya haye sama ya shige daki. Abinda ya kwana biyu bai gani bane Izzatu
ta gyare dakin tas sai kamshi ko ta ina. Murmushi yayi yasan tana neman shiri
kenan. Jakarsa da takalma ya ajiye yana cire safa ta fito daga toilet dinsa sanye
da wata rigar bacci mai matukar kyau. Binta yayi da ido har ta karaso gabansa. Ba
karamin kyau tayi ba tasha kwalliya. Safar ta karasa cire masa sannan ta rage masa
kayan jikinsa. Bata ce komai ba shima baiyi magana ba. Toilet ta kaishi ta taimaka
masa yayi wanka. Abinda ta dade bata yi ba tun kafin tayiwa Zuhra April fool. Sai
da ta gama shirya shi suka je kasa ta bashi abinci da kanta. Da ta tabbatar ya
koshi sai suka koma dakinsa durkusawa tayi a gabansa gwiwoyinta a kasa ta soma
kuka. My sweetbaby nasan na bata maka rai da yawa a iya zaman da muka yi amma ina
rokonka don Allah ka yafe min. Hannuwanta ya kama zai tayar da ita zaune taki
tashi. Bazan tashi ba sai ka fada da bakinka ka yafe min. Na janyo maka auren da mu
duka bamu shirya masa ba sannan itama yarinyar na dauki alhakinta. Kukanta har
ransa yake ji. Tayar da ita tsaye yayi ya rungumeta yana rarrashi. Komai ya wuce
Izzy tunda kin gane kuskurenki. Kissing dinta ya soma saboda shi kanshi ba karamin
missing dinta yayi na. Wani dadi taji yana ratsata ta biye masa. Sun jima a haka
kafin tace Hamza dear ina zuwa. Sai da tayi da gaske ya saketa ta fita.
Dakin Zuhra taje, lokacin Zuhra tana waya da Hajara suna ta hira kamar bata da wata
damuwa. Ganin Izzatu a bakin kofa yasa tayi saurin sallama da Hajara. Da fara'arta
kamar Izzatun da ta fara sani tace kizo zamuyi magana a dakin Hamza. I hope ban
takura miki ba? Zuhra kallonta take da mamaki ga wata irin riga da ta saka. A ranta
tace wasu matan dai basu da kamun kai. Yanzu meye na shigo min daki tsirara.
Mayafinta ta dauko ta yafa tabi bayanta. Suna zuwa Izzatu bata daukeshi komai ba ta
fada jikin Hamza wanda yake sanye da wandon bacci kawai. Dorawa yayi daga inda suka
tsaya. Zuhra tayi saurin runtse ido ta juya baya tace wayyo na shiga uku
iskan......
Hamza na ganinta yayi saurin ture Izzatu tare da yi mata tsawa. Idan kika kuskura
kika ce iskanci sai na dalle miki baki. Kina hauka ne zaki shigo mana daki babu
sallama. Izzatu ta sake rike shi ni na kirawota baby. Rigarsa ya dauka ya saka gaba
a baya saboda kunyar da yaji Zuhra ta ganshi a haka. Sabon raini zai shigo kenan.
[9/25, 3:53 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #36
Batul Mamman(Mrs)#
Bakin kofar Izzatu taje ta riko hannun Zuhra suka shigo cikin dakin. A gefen gado
ta zaunar da