Advertisements
Chapter 10 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 36

27K to 30K   out of 106K words

ba. Ita kanta tasan tayi abinda zaa jinjina mata.

A baya ta rinka binsa har suka sauko. Izzatu ta kai karshe wurin bacin rai, sai
kawai ta danne. Kujera ta samu kusa da yaran ta zauna tare da yin sallama. Khalifa
ne kawai ya amsa. Ya kalli Mamansa.
"Mummy wannan ma mai aiki ce?"

Hamza ya ce masa yayi shiru kawai yaci abinci. Zuhra tana sane bata ji ya gyara
masa yace ita ba mai aiki bace ko da bai kirata matarsa ba.

Izzatu ko daga kai batayi ba bare ta bashi amsa. Itama Zuhra taki kallonta. Yadda
take jin haushin Izzatu ko kallo bata isheta ba. A dalilinta tazo gidan nan da bata
da wata kima a idon mazauna cikinsa. Muryar Hamza ce ta katse mata tunani.
"Wai ba kya gaishe da mutane ne?"

Ta dago fuska suka hada ido. "Na gaisheka a daki"

Da kansa yayi mata alamar bata gaishe da Izzatu ba. Amma lallai ya rainata da yawa.
Su basu ce 'ya'yansu su gaisheta ba sai ita zata gaishe da matarsa. Kamar bazata yi
ba sai kuma tace "ina kwana"
Maimakon ta amsa sai kawai ta tashi ta koma dakinta. Hamza ya bi bayanta. Yaran ma
suka gama suka tashi. Suna tafiya Zuhra ta janyo flask ta bubbude sannan ta debi
abinda zata ci ta hada tea. Sai da taci ta koshi sannan ta tashi daga dinning area
din ta koma wurin yaran inda suke zaune suna kallo. Tambayarsu sunayensu tayi suka
bata amsa. Junior yace "ke kuma ya sunanki?".

Murmushi tayi "sunana Zuhra". Khalifa yace "nice name, will you be my friend?"

Ido ta dan zaro "tohhh kun iya turanci tun yanzu..." da haka suka rinka hira da ita
tana jansu da wasa. Hatta Nana mai kyuya ta yarda da Zuhra.

Hamza ya dauko laptop zai fara aiki sai kuma ya rufe. "Izzy kirawo yarinyar nan, I
need to talk to both of you"

Wani irin kallo tayi masa. " sweety nice zani dakin Zuhra? Allah Ya kiyaye. Kuma ai
bai kamata ta shigo mana bedroom ba. As far as am concerned ni ban dauketa matarka
ba."

"Gashi kuma na biya sadaki" yadda yayi maganar tasan har yanzu yana ganin laifinta
a matsayin wadda ta jawo masa auren.

Tana fitowa ta jiyo muryar Junior yana cewa Zuhra ta yi masa tatsuniya. Daga saman
ta leka ta kirawo Khalifa. Shi ta fadawa ya rako Zuhra dakin daddysu yana jiranta.

Rike da hannun Khalifa suka shiga dakin. Wata irin niima taji. Ita nata dakin sai
zafi. Falo ne a farko sannan kofar dakin daga ciki. Wurin ya tsaru sosai ta tsaya
tana kallo. Izzatu tace da Khalifa yaje wurinsu Junior.

Babu wadda ta kula yar uwarta har Hamza ya fito. Kusa da Izzatu ya zauna. Ita Zuhra
kasa ta zauna kan kafet saboda gudun kada ace tayi laifi. Gyara zamansa yayi
fuskarsa ta nuna alamun ba wasa. Sannan ya soma magana

"Kamar yadda kuka sani dukkaninku matana ne duk da cewa circumstances behind auren
kowacce is different......

Zuhra anzo wurin...gabadaya jumlar karshe bata fahimta ba.

.....bana son tashin hankali a gidan nan. Izzy kece babba ina so kija girmanki. Ke
kuma ya juya ga Zuhra ki bata girmanta. Tun farko na gargadeki akan auren nan kika
ki ji. So duk abinda kika gani sai kiyi hakuri. Sannan a yanzu baki da kitchen don
sai an gyara miki daki a kasa. For now idan Izzy tayi girki zata baki. Saboda haka
babu zancen rabon kwana sai an gama kitchen din." Ya kallesu duk su biyu. "Ko akwai
mai magana?"

Izzatu tana ta kumbure kumbure tace " ka fada mata ta fita harkar yarana".

Bai ce mata komai ba yace da Zuhra tana iya tafiya. Tunda ya soma magana bata daga
kai ba. Yayi tsammanin zata nuna bacin rai amma sai yaga tayi shiru. Kanta a kasa
ta fita daga dakin ta koma nata. Tana rufe kofar ta suma kuka duk yadda taso
daurewa ta kasa....ba son Hamza take ba amma babu macen da zata so a nuna mata ita
ba komai bace a gaban kishiya.
[9/25, 3:50 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #31

Batul Mamman(Mrs)#
Sai karfe uku da rabi Tala ta kwankwasa mata kofa. Ko da ta bude abinci ne a plate
an rufe da wani sai ruwa roba daya mai sanyi da cup. Godiya tayi mata ta karba.
Gara a rinka kawo mata don ita bata jin zata iya jurar zama tare da mutanen da basa
kaunarta su ci abinci.

Dama tuni ta soma jin yunwa. Tana budewa taliya ce da miya sai coleslaw a gefe.
Kare masa kallo tayi tana mamaki. Abin kuma harda rowar abinci? Abincin dan kukut a
plate kamar zaa bawa Khalifa. Tas ta cinye ta sha ruwa rabin robar. In ba haka tayi
ba tasan bazata koshi ba.

Hamza tun bayan azahar suka fita da wani abokinsa. Gidansu Zuhra suka je yi musu
ban gajiya. Su Umma sunji dadi sosai. Har ta cire kunyarta ta tambayeshi ya Zuhra
ta kwana. Murmushi yayi sannan yace mata lafiya kalau. Tana gaishe su. Da zasu tafi
Baba ya bawa Hamza wayar Zuhra. A jakar Hajara ta manta ta daren jiya. Juya wayar
ya rinka yi, banda tsufa ta dade da fita yayi.

Da daddare ma har daki aka biyota da abincin. Macaroni ce da vegetable soup. Sai
dai Zuhra ta tsani macaroni. Duk yunwar da take ji dole ta hakura. Gudun kada aga
kwadayinta ma ko naman dake cikin miyar bata ci ba ta dauki tray din ta sauka kasa
dashi. Tana tafiya Hamza da Izzatu dake zaune a dinning table na binta da ido. Bata
ko tanka musu ba ta wuce ta ajiye abincin a kitchen. Ta fito kenan Tala ta biyota
da sauri.
"Naga baki ci abincin ba"

Dan murmushi tayi "na koshi ne".

Tana wucewa idonta ya kai kan nasu abincin. Shinkafa suke ci, wato ita suka hada da
macaroni. Hamza na lura da irin kallon da take musu har ta wuce.

Wurin karfe goma da rabi Zuhra tana zaune tunani duk ya isheta gashi ta manta
wayarta a gida. Ga uwa uba yunwa. Turo kofar taji anyi tayi saurin tashi zaune ta
saka hijab. Daga ita sai daurin kirji saboda zafi ya dameta.

Kafin ta rufe jikinta ya kula da daurin kirjin. Ba karamin tsanar sa yayi ba. Bai
tsaya jan zance da ita ba yace..
" kina jindadin cin abincin ke kadai ko zaki rinka ci tare damu?"

Tasan har ransa ba so yake taci dasu din ba." Zanci ni kadai"

"Fine, sai ki rinka fada da wuri idan bazaki ci ba saboda a dena wasting. An kawo
miki kin mayar batare da kin taba ba".

Idan kika yi shiru zaki kwari kanki shine abinda zuciyarta ke raya mata. Ta dan
rage murya "bana cin macaroni ne"

"Macaroni kuma? Mtsw ke bana son karya."

Turo baki tayi "ni ba karya nake ba. Abinda aka kawo min kenan."

Dafa kansa yayi yadda yake idan yana cikin damuwa." Me yasa bakiyi magana ba.
Anyway nasan shinkafar bata kare ba idan kina so kije ki ci."

Tana kallo ya karaso cikin dakin ya kunna wani abu. Da yake tana setin AC din tuni
ta fara jin iska. Yana gani tayi murmushi. Sannan tace.
"Don Allah ina ka kunna? Jiya zafi ya isheni na zata da sankarau zan tashi da safe"

Ta kusa sashi dariya sai ya gimtse. Idan ya sakar mata fuska zata yi tunanin ta
sami karbuwa ne. Remote din AC din ya nuna mata sannan ya miko mata wayarta da
chaja a cikin leda. Murna tayi sosai tayi masa godiya.

Sai da ya kama hannun kofar ta sake magana tana sosa keya.
"uhmmm"

Ya tsaya yana kallonta
"yes" ganin taki magana.

"Dama, dama famfon bandakin ne naga kamar sun lalace."

"Kin lalata su dai" ya fada yana shiga ciki. Ya duba duka komai lafiya kalau. Ya
fito "wai ni abokin wasanki ne? Babu famfon da ya lalace"

Bata ce komai ba tayi saurin shiga. Hannu ta tara a famfon sink da baho duk ruwa ya
fito da kansa. Sai da ya tsorata ta duk da ta gani jiya. " ka gani ko, yau tun
sallar asuba da shaya nake yin alwala."

Wannan karon murmushi yayi. Sannan yayi mata bayanin yadda kan famfon yake. Tun
kafin ya fita ta rinka bi tana tara hannu ruwa na zuba. Dariya take yi don abin ya
burgeta. Yace to kada ki karar mana da ruwan gidan. Kunya taji tayi saurin cire
hannunta ta fito. Shi kuwa tuni ya fice ya tafi nasa dakin.
[9/25, 3:51 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #32

Batul Mamman(Mrs)#




Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Hamza. Kullum safe, rana da dare duk zaa
kawo mata abincin marowata kamar yadda take kiransa. A kullum zata yi waya da
iyayenta. Idan bata kira ba zasu kira ta. Idan aka tambayeta Hamza tace yana nan
kalau. Bata taba tunanin fadin komai ba domin Anti Faiza tace zaman gidan miji yana
bukatar sirri. Ko Hajara ta hanata ta sanarwa komai na dangane da gidan aurenta.
Hamza dai yasan ana bata abinci saboda haka bai taba damuwa da sanin yawansa ba.
Idan ta fito sauka da kwanunkan abinci suka hadu da Izzatu zata gaisheta a ciki
ciki. Itama da kyar take amsawa. Don Hamza yayi mata fadan baya son gaba ne da ko
kallon Zuhra bazata yi ba. Shi kuwa matsalar kamfaninsa tasa shi a gaba, bashi da
lokacin gidansa sosai.

Ranar alhamis da safe Tala ta kawo mata abinci kamar kullum. Tea ne a dan karamin
cup irin mai saucer dinnan wanda kurba biyar zuwa shida zai kare. A plate din kuma
sliced bread ne guda uku. Wani irin kallo Zuhra ta yiwa abincin. Ta dauki bread
daya taji shi a bushe da tauri. Murmushin yake tayi... Tala yau kuma bushasshen
brodi kike kawo min. Tala ta dawo ta dan durkusa gabanta amarya ai wannan tos ne.
Tala zata yi sa'ar Izzatu ko ta girmeta da kadan. To...to me? Zuhra ta fada tana
yamutsa fuska. Tala tace tos. A tosta ake sakawa sai kiga ya fito ta sama kamar an
jeho shi. Har dan bota na shafa miki don kiji dadinsa. Zuhra ta gyada kai, naga
alama. To nagode.

Bayan fitar Tala tayi ta juya bread din a hannunta. Tunda tazo gidan breakfast
dinta na farko ne kawai ta taba koshi. Kullum sai dai rage hanya, gashi bata taba
ganin alamar za'a fara aikin nata kitchen din ba. Ba yadda ta iya a dole ta fara
cin bread din. Kana ganin fuskarta kamar mai shan madaci. Ko rabi bata ci ba ta
shanye tea din. Ta sake kai bread din bakinta Hamza yayi sallama ya shigo batare da
ya jira ta amsa ba. Zaune take da tray a gabanta kanta babu dankwali. Doguwar riga
ce a jikinta ta wani material. Dinkin dai yayi kyau sai dai wadda tasa kayan ce sai
a hankali. Sunkuyar da kanta tayi kasa tace ina kwana?
Bai amsa ba yana daura agogo a hanunsa ya dubi plate din gabanta. Ashe ma zaki iya
ci. Dama naga toasted bread aka yi nayi tunanin baki saba ci ba a baki wani
abincin. Zuhra tayi sauri ta tofar da na bakinta akan tray din. Wallahi bana iya
ci, hakan ma dauriya ce kawai.

Hamza ji yayi kamar ya amayar da abinda yaci. Wannan wace irin kazanta ce ta gama
jika bread a bakinta ta dawo dashi. Fuskarsa na kallon gefe yace naga saura biyu da
rabi ki cinye. Tashi tsaye tayi tana karkade hannuwanta...wallahi dama uku ne. Dan
murmushi yayi...haka Izzatu take bata son ayi abinci da yawa, a cewarta zasu yi
kiba suyi loosing shape. Farkon aurensu har rama ya rinka yi. Daga baya sai yake
siyan biskit da cake a ajiye a office. Kyalesu zaiyi, kila idan Zuhra ta dan horo
zata nemi komawa gidan iyayenta. Sai ya saketa cikin sauki. Ba tare da ya kalleta
ba yace zansa a kawo miki wani abincin. Da ya juya zai tafi yaji tace adawo lafiya,
Allah Ya kiyaye, Ya bada sa'a, Ya tsare kuma Ya kare dukkan sharri. Adduar tayi
masa dadi yace Amin a hankali. Wannan adduar kullum Umma sai tayiwa Baba idan zai
fita wurin sana'arsa.

Tunda ya fita bata ga alamun abinci ba sai uku saura aka kawo na rana. Cikin
kankanin lokaci ta tayar da abincin. Ta fito daga toilet kenan Tala ta shigo tace
amarya kinyi baki. Shikenan anzo wurin.....kullum addua take yi kada tayi baki
saboda bata san me zata basu ba, yau gashi wasu sun zo. Tunani ta soma yi lokaci
guda idea ta zo mata. Kanta ta rike da hannu biyu ta rufe ido. Tala kaina ciwo yake
min sosai kamar zai tsage. Tala tayi saurin karasawa ta riketa har bakin gadonta.
Sannu amarya ko na karbo miki magani wurin Anti Izzatu? A'a Zuhra tayi saurin
dakatar da ita. Nima ina da shi. Kice su hawo nan bazan iya saukowa ba. Tala duk
tausayin Zuhra ya kamata tace ba komai amarya. Kafin ta fita Zuhra tace ki dan
taimaka musu da ruwan sha don Allah.

Tana fita Zuhra ta gyara kwanciya. Bata san ko su waye ba amma dai tasan gidan
amare ana son a bawa baki dan abin kusa da baka. Ita kuma bata da komai, idan za'a
bata ma karba zata yi.

Ba jimawa yan uwansu na Ajingi suka shigo. Kirikiri Zuhra taki tashi tana ta
langabewa ita mara lafiya. Da muguwar rawa gwamma kin tashi. Anti Faiza ce ta rako
su. Suna ta mata tsiya ko har an fara laulayi ne na kwana biyar. Ita dai sai
murmushi take yi a dole taji kunya. Tala ta kawo musu ruwa harda lemo a jug da
kofona. Basu dade ba suka ce gobe zasu koma Ajingi. Tayi musu godiya ta rakasu har
kofar daki. Sai da suka sauka kasa Anti Faiza ta dawo da sauri take tambayarta yaya
zaman nata. Kuka Zuhra tasa mata ta sanar da ita ko abincin kirki ba'a bata. Anti
Faiza tace kiyi hakuri gobe za'a kawo gararki. Akwai kudi ne a wurinki? Zuhra ta
share hawayenta tace eh Baba ya bani. Duka ta debo ta bata Anti Faiza ta dauki dubu
goma a ciki ta bata sauran. Zanje kasuwa gobe kafin azo kawo garar zan zo in sha
Allah. Ta dafa kafadarta...ki kara hakuri kuma kada ki bari Izzatu ta san ba kya
jindadin zaman. Daga ita har mijin nata so suke kiyi abinda zai sakeki. Kuma In sha
Allah kinzo kenan, yadda iyayensa suka yi miki kokari kema ki dage nemawar kanki
wurin zama a zuciyarsa. Zuhra ta tura baki ni me zanyi dashi Anti? Ai kawai idan ya
gaji ya sakeni. Anti Faiza toshe mata baki tayi. To banza na sake jin zancen saki
sai na fasa miki baki. Biskit ta dauko guda biyu a jakarta ta bawa Zuhra sannan ta
sauka kasa suka tafi.

Fitarsu ke da wuya Izzatu ta shigo tare da Tala. Zuhra tana kwance akan kujera ta
gansu. Tashi tayi zaune tace lafiya cike da tsiwa. Fuskar Izzatu a daure tace ke
kika ce Tala ta bawa bakinki ruwa da juice a jug dina? Zuhra ta kalli Tala tayi
tsuru tsuru. Kiyi hakuri na zata mijinmu ne ya saya shiyasa nace ta taimaka ta
kawo. Izzatu ta soma fada rai a bace...mijinmu fa kika ce? Yanzu Zuhra don baki da
kunya sai ki hada baki da inlaws dina ki auri mijina kawai don kinga ina sakar miki
fuska. To Tala mai aikina ce ni kadai kuma kada ki sake taba min kaya. Ignorant
fool yadda kika zo haka zaki fita ki bar min gida. Zuhra tayi yar dariya ko na
kwana daya ne Izzatu kin taba zama da kishiya a tarihin rayuwarki. Izzatu ta tsaya
tana kallon Zuhra..dama bata da kunya? Kwafa tayi sannan ta fita tare da buga kofar
da karfi. Tala ta dauki tray din Zuhra na bata hakuri tace babu komai. Ita sai
mamakin wannan aure na ubangidanta take da yadda suke wulakanta amaryar. Zuhra tayi
murmushi ko ba komai yau ta dan gasawa Izzatu magana taji dadi.

Daren ranar ba'ayi girki ba ana jiran Hamza ya kawo abinci daga tantalizers. Da
yake bai fito office da wuri ba abincinsu ya kare sai snacks ya siyo. Yana wanka
Izzatu ta rabawa kowa banda Zuhra. Shima burger yaci ya kwanta a zatonsa an aikawa
Zuhra nata. Tala tana son tambayar na amarya tana tsoro don ba karamin fada Izzatu
tayi mata ba.
Har shadaya da rabi babu abinci babu dalilinsa. Dole Zuhra ta karasa sauran biskit
din da Anti Faiza ta bata ta shiga toilet ta sha ruwa sannan ta kwanta ciki na
kukan yunwa.
[9/25, 3:52 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #34

Batul Mamman(Mrs)#




Kafin Hamza ya dawo daga raka su Mama mota tayi saurin shigowa ta hayewarta sama
tana murza hannunta wanda ya matse mata harda hawayenta. Tala tana kwashe trays din
da aka yi amfani dasu Izzatu ta tsaya mata a ka. Nace Tala ko kin gaji da aikin ne?
Ido ta zaro a'a Hajiya wani abin ne ya faru? harara Izzatu ta jefa mata. Jiya banyi
miki magana akan yiwa bakin yarinyar nan amfani da kayana bane? Tala tace Allah
Sarki ai naga harda maman Alhaji shiyasa na dauko musu. Kiyi hakuri. Izzatu tace ba
mamansa bace kishiyarta ce. Kuma na karshe kenan da zaki taba min kaya da sunan
karrama bakinta. Wallahi ranar zaki koma kauyenku. Daga nan ta juya ta koma kan
kujera ta zauna tana huci. Yadda Mama da su Mariya suka ki amsa gaisuwarta ke
damunta. Kwafa tayi inma suna rawar kafa ne sun koma bayan amarya zata bar gidan ne
da wuri. Su basu san wasa bane ko abubuwan nishadi da har zasu ji haushin abinda
tayiwa Zuhra asa mijinta aurenta. Tana ta karkada kafa tana mita a ranta Hamza ya
shigo yayi hanyar sama. Da bibbiyu yake tsallake steps din. Murmushin mugunta tayi
Allah Yasa daga nan ya saketa kowa ya huta.

Zuhra na tsaye gefen kujera tana hawayen yadda hannunta ke zafi tace kuma Allah Ya
isa na....dawa kike taji Hamza ya fada yana shigowa dakin. Duk da ta tsorata cike
da tsiwa fuska duk hawaye da majina harda murguda baki tace da wanda ya tsargu.
Baki Hamza ya saki lallai yarinyar nan bata da kunya. Shi saboda yadda yaki jinin
raini shiyasa baya shiga sabgar autarsu Hamida. Itama tsiwa ce da ita....

Ke, dani kike? Share shi tayi ta cigaba da matsa hannu. Tsawa ya daka mata ke ba
kya jina ne. Nace ni kike yiwa Allah Ya isa? Waige ta soma yi hagu da dama ita a
dole bata san da wa yake ba. Ransa ya kara baci yayi kanta. Da gudu ta kara shigewa
cikin dakin sai da ta kai jikin bango. Kafa yasa ya buga kofar da karfi daidai da
bugawar zuciyarta. Sai rarraba idanu take. Wani irin kallo yake mata kafin ya sake
cewa wai kina ji ina tambayarki kin kasa bani amsa saboda ki nuna min ban isa ba.
Tsoro kam ta gama ji amma ta rantse bazata yi shiru ba tace au dama dani kake?
Maganar ta sake sosa masa rai ya biyota har inda take tsaye jikinta ya soma rawa.
Tana cigaba da hawaye tace to ai ke naji kace ni kuma da aka haifeni Baba saniya da
rago ya yanka ya rada min suna Fatima. Dayake sunan Innarsa ne da kuma Ummana shine
ake kirana Zuhra. Ta turo baki sai ka zabi daya

10 / 36