Advertisements
Chapter 24 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 36

69K to 72K   out of 106K words

Yarinyar da ko certificate din shaidar tayi secondary school bata dashi,ga
kazanta ga rashin wayewa. Ikon Allah kenan, kada ka taba raina bawa domin baka san
abinda Allah yayi masa na arziki ba. Arziki kuwa ko da ba na kudi bane. Hawayen da
Hamza yake yi ya karyar mata da zuciya ta soma kuka. Haka suka rungume juna na
tsawon lokaci. Daga baya Hamza yace ta tashi su koma asibiti tace a'a yaje kasuwa
ba'a rasa masu bude shago ranar lahadi ya sayar. Ita kuma zata kara yin saka zuwa
la'asar ko bai dawo ba zata yi girki ta tafi asibitin da kanta. Sai da ya kwashe
kusan minti biyar yana kissing dinta sannan ya fita. Bai san da yaya zai gode mata
ba. Tunda ya shiga mota har ya isa kasuwar ALHAMDULILLAH yake ta nanatawa saboda
godiya ga Allah da Ya azurta shi da mace tagari a lokacin da rayuwarsa take tsaka
da rushewa.

A dalilin mugun tashin da dollar tayi wanda muke ta addu'a Allah Ya yafe mana Ya
kawo mana sassauci sai da Hamza ya sami dubu dari uku da tamanin da hudu a matsayin
kudin sarka, dankunne da zobe. A haka ma don mutanen sun kula kamar a matse yake da
ya sayar.

A hanyarsa ta tsallaka titi ya koma motarsa yaga wata tsohuwa tukuf itama ta rasa
yadda zatayi ta tsallaka. Da a lokacin da yake Hamzansa ne mijin Izzatu ita kadai
baya jin zai iya yadda hannunsa ya taba matar. Amma yanzu ya koyi darasin zaman
duniya. Hannun matar ya riko tana tafiya da kyar har ya tsallakar da ita titi.
Godiya ta rinka yi masa tare da addua. Harda dan kukanta tace ba don kai ba sai
nayi kusan minti shabiyar ina kokarin tsallaka titin nan. Magani na karbowa dana
yana fama da lalurar asma. Ta dauki wata leda da magani ta nuna masa. Hamza ya
tausaya mata yace baki da wasu yaran ko jikoki da zasu je miki? Tayi murmushi, shi
kadai ne dani. Bayan shekaru shabakwai sai yanzu matarsa take da tsohon ciki. Idan
abin ya tashi ita take zuwa amma yanzu bazata iya doguwar tafiya ba. Yana ganin
kansa a wani yanayi ga wadanda suka fishi. Kudin aljihunsa ya shafa ya sa hannu ya
kirga dubu goma ya bawa matar. Hannu na rawa ta karba tana ta kuka...Allah Ya
albarkaci rayuwarka data iyalinka, Allah Ya rabaka da masifun zamani, Allah Ya baka
arziki na halali daga inda baka taba tsammani ba. Yaro nagode, nagode. Hamza na
tsaye har ta shiga adaidaita sahu sannan shima ya tafi zuciyarsa kamar an cire masa
wani nauyi. Hakika sadaka maganin masifa ce kuma waraka daga bacin rai.

Asibitin ya koma ya tarar Izzatu ta farfado. Raliya ya kira a waya ya sanar da ita
halin da Izzatu ke ciki. Cikin kidima tace gobe zata taho in sha Allah. Tana ajiye
wayar ta kira kanwarta Larai ta fada mata asibitin da suke.

Tsananin bacin rai da kishi yasa Izzatu kuka tunda ta farfado. Yanayin da taga
Zuhra da Hamzanta shi kadai yake mata yawo a ka tunda ta bude ido. Su Mama kuwa sai
tausayinta suke yi a nasu tunanin bakincikin bari da cire mata mahaifa da akayi
take yi. Cike da tausayi Hamza yake mata sannu amma ko kallonsa taki yi. Su Mama
sai suka dauke kai kamar basu kula da abinda suke yi ba. Adabiyya tace Yaya ina
Anti Zuhra? Yace zata taho girki yasa bamu fito tare ba.

Basu dade ba kuwa sai gata da kwandon abinci. Bata tashi daga kan sakarta ba sai da
tayi mai yawa ta yadda abin da ya rage mata saura kadan. Itama ko kallo bata ishe
Izzatu ba duk da halin ciwon da take ciki. Sauran 'yan uwan Hamza suma duk sun zo.
Zuhra ma ta kira Baba ta fada masa Izzatu na asibiti yace zasu zo washegari tare da
Umma.

Anti Larai kanwar Raliya tazo tare suka karasa yinin sai dai ta baro maigidanta
babu lafiya saboda haka bazata iya kwana a asibitin ba. Dole aka yanke shawarar
Adabiyya da Zuhra su kwana da Izzatu. Ranta inyayi dubu ya baci amma ko tashi
bazata iya yi ba shiyasa dole ta hakura. Shabiyu saura na dare su Zuhra suka fita
suka bashi wuri ya dan zauna wurinta. Sai lallabata yake tana kuka ita bazata zauna
da wadda tayi sanadiyar zubar mata da ciki ba. Da kyar ya lallabata yace gobe shi
zai kwana. Haka suka rabu ranta a bace. Itama Zuhra yayi mata sallama sannan ya
tafi gida.

********
Wasu matasa ne su uku duk da bakaken kaya harda abin rufe fuska suka shigo cikin
kauyen da gudu da cikon na hudun a kafadar wanda yafi sauran girma. A kofar wani
katon family house suka ajiye na kafadar wanda yake ta zubar da jini sakamakon
harbinsa da aka yi a cinya suka gudu. Da yake tsakar dare ne babu wanda ya kula
dasu. Sai can wasu maza biyu suka zo wucewa a buge suka ga mutum a kwance a kasa.
Da har zasu gudu sai daya ya haska shi da touchlight, da sauri ya karaso giyar da
yasha ta fara barinsa yace sa dayan kazo mu taimaka masa Felix ne kanin Mr Oscar
miloniya.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [10/10, 1:59 PM] #+234 809 156 9113#: AL'ADUN
WASU #66

Batul Mamman(Mrs)#
Daga Zuhran har Adabiyyan babu wanda Izzatu take son gani. Har gara Adabiyya tunda
ita kanwar Hamza ce. Haka suka kwana jugum jugum ba abin suyi hira ba a junansu
tace sun dame ta. Sau biyu Zuhra na fita kiran nurse a canjawa Izzatu drip idan ya
kare. Ko baccin kirki bata samu ba amma banda sakon harara da tsaki babu abinda
Izzatu ke aika mata. Wurin karfe bakwai Nura ya kawo Hamida da abinci yace Hajiya
tace ya tafi da Adabiyya gida itama Zuhra ya kaita gida.

Zuhra suka fara kaiwa. A falo ta hadu da su Khalifa duk suka rungumeta suna murnar
ganinta. Khalifa yace wai Mummy bata da lafiya tana asibiti? Zuhra tace kuyi mata
addua Allah Ya bata lafiya. Daddy ya tashi ne? Tala tace bai dade da fita ba kika
shigo. Hanyar dakinta ta nufa tayi wanka Nana ta soma yi mata rigima wai sai ta
goyata gata akwai jiki. Haka Zuhra ta sabata a baya ta hau sama. Kafin ta fito daga
wanka ma Nanan tayi bacci, gefenta ta kwanta itama ko mai bata shafa ba, bata dade
ba bacci ya dauketa.

Sai shabiyu da rabi ta farka bata ga Nana ba, tasan kila tashi tayi ta sauka kasa.
A gaggauce tayi alwala ta shirya ta sauko. Allah Yasa Tala ta riga tayi girki sai
taci ta dauki na asibiti. Kafin ta fita Hamza ya kirata yace ta jira zaizo gida sai
su tafi tare.

Kamar ance Izzatu ta kalli kofa tana juyawa ta hada ido da Hamza da Zuhra. Wani
karin takaicin ya isheta dama dakin daga su Mama sai Umman Zuhra. Tare suka zo da
Baba shi ya tafi ya barta da Maman su Hajara. Zuhra murna an ga Umma sai washe baki
take yi. Bayan ta gaishe da kowa kusa da ita ta zauna kamar zata shige ciki. Mama
ta rinka tsokanarsu wai itama a bata sirrin shagwabar nan. Umma dai har kunya taji
ita kuwa Zuhra ko a jikinta.

Kamar jiya yau ma Zuhra tayiwa Izzatu sannu kin amsawa tayi tana wani yamutsa
fuska. Suna haka Raliya da Larai suka shigo. Ganin mamanta nan da nan Izzatu ta
soma kuka. Tausayinta suka rinka yi ana ganin kamar duk saboda ciwo ne ga rashin
mahaifa.

Haka su Zuhra suka zauna ana ta zuwa dubiya. Anti Faiza ma tazo tare dasu Mariya
don sun zama kawaye. Ana sallar Isha su Hajiya zasu tafi Hamza yace Zuhra ta bisu
Nura ya ajiyeta a gida. Babu musu ta tashi suka yi sallama da Raliya wadda ba kamar
'yarta ba ita tana dan sakar mata fuska suka tafi.

Sai shabiyu saura Hamza ya dawo ya shiga dakin Zuhra. Bacci ya gansu suna yi ita da
su Junior ga TV a kunne. Murmushi yayi cikin jindadin yadda take kula da komai da
ya shafe shi ya kashe TV din ya rufe musu kofa. Da safe bayan su Khalifa sun tafi
makaranta Zuhra ta koma ta dan kwanta. Kafin ta tashi Hamza ya tafi office daga can
ya wuce asibiti. Yau saka ta zauna tayi sai da ya rage gabadaya saura biyar sannan
ta tashi tayi jallof din couscous wadda tasha hanta da kayan lambu. Bata dade ba ta
gama ta sake yin wanka.

********
Izzatu ke kuka tana fada ita dole sai Hamza ya saki Zuhra idan ba haka ba aurensu
yazo karshe. Babu kowa a dakin daga shi sai Raliya da ta kwana a wurinta.
Dukkanninsu sai rarrashinta sukeyi suna bata hakuri amma ta rufe ido tace bazata
taba zama da Zuhra ba. Idan wata matar yake so ta amince yaje ya auri 'yar boko
irinta amma bazata yi kishi da kazama kamar Zuhra ba. Duk da cewa maganganunta nayi
masa zafi saboda ko kadan baya son abinda zai taba mutumcin Zuhra amma saboda
tausayin yanayin da Izzatun ke ciki yasa yake bata hakuri. Idan ta warke dole asan
me ake ciki don bazai dauki wannan wulakancin ba.

Suna haka wayarsa tayi ringing. Yana ganin Cutie yayi murmushi ya dauka. Can
kasakasa take magana tace Ya Hamza kana asibiti ko?

Ina nan, ya akayi?
Garin sauri na fito na manta jakata gashi mun kusa isowa asibitin. Ka fito ka bawa
mai adaidaita sahu kudinsa kada ya tara min jama'a.

Sai da yayi dariya sannan yace bazan zo ba, zan bari ya dan saita min bakin nan
naki mai tsiwa.

A shagwabe tace to shikenan zan ce ya saita shi irin yadda kake yi dinnan.....

Ke, wallahi kada ki soma ina bakin gate din asibitin.

Dariya tayi ...da ka koma kawai Ya Hamza ko na rabin minti sai.....

Cutie bana son irin wannan maganar please. Na janye da nace ya saita miki baki. Ni
kadai zan saita kayana.

Sun dauki mintuna suna hira har suka karaso baki gate din ya biya mutumin ya
tayata daukar kwandon abincin.

Suna tafe suna hira abin sha'awa yace yau zaki san ni kika tsokana. Gwalo Zuhra
tayi masa ai dai kai ka fara meye laifina don na taya ka? A haka suka iso kofar
dakin. Hamza zai bude kofar kenan ya jiyo abinda Raliya ke fada wanda yayi matukar
razana shi.

Yanzu ke Izzatu har kina da bakin cewa Hamza ya saki matarsa? Me tayi miki da zaki
tsaneta haka.

Mum kinfi kowa sanin ni bazan iya sharing mijina da kowa ba talkless of kazama irin
wannan yarinyar.

Raliya tayi tsaki....ni bansan baki da hankali ba sai yanzu. Izzatu mahaifa aka
cire miki fa. Kina tsammanin idan ya saki Zuhra bazai auri wata ta cigaba da haifar
masa 'ya'ya bane?

Muryar Izzatu suka ji tana kuka tace wallahi Mum idan ya dage sai ya zauna da
yarinyar nan to zai ga tashin hankali. Sai na hana shi nutsuwa balle ya sami
lokacin soyayya da ita.

Bakinciki fal zuciyar Raliya saboda yadda Izzatu bata jin magana tace idan kika
kuskura kika daga masa hankali nayi miki alkawarin sai na fada masa ke da kanki
kika sha magani kika zubar da ciki. Kuma har asibiti kika je domin a cire miki
mahaifa. Kin zauna mutane sai tausayinki suke ji basu san bukatarki bace ta biya.
Izzatu ina jiye miki tsoro idan Hamza ya sakeki fa babu wanda zaiso ya auri macen
da bazata haihu ba.

Hannu Izzatu tasa a kan bakinta alamun Raliya tayi shiru. Sai dai aikin gama ya
gama domin Hamza da Zuhra sunji komai.

Cike da bacin rai Hamza ya sake kama hannun kofar zai bude Zuhra tayi saurin rike
masa hannu saboda yadda taga fuskarsa gabadaya ta canja kamar bashi ba, jikinsa
rawa yake sosai. Hannun nasa ya fizge daga rikon da tayi masa ya shiga cikin
dakin.

A take Izzatu da Raliya nasu idanun suka firfito waje saboda tsabar kidimewa.
[10/10, 1:59 PM] #+234 809 156 9113#: AL'ADUN WASU #67

Batul Mamman(Mrs)#
Yadda Hamza ya shiga dakin tamkar wani zaki. Zuhra ta biyo bayansa ta rabe a gefen
kofa, bakinta a rufe da hannunta daya saboda zafin da lebenta yake sakamakon fizgar
da Hamza yayiwa hannunsa ya bigeta.

Kokarin tashi daga kan gadon Izzatu take yi domin yanayin Hamza ya bata tsoro.
Murmushi yake mata wanda gara ace duka ya rufe ta dashi saboda duk wanda yaga
yanayinsa dole ya tsorata. Sai da yaje kusa da gadon yace koma kiyi zamanki ranki
ya dade. Nazo inyi miki godiya ne saboda irin abubuwan da kike yi min. Abu daya ya
rage ki karasa ladanki shine ki kasheni ki huta.

Raliya tace Hamza don Allah kayi hakuri ka tsaya muyi magana kada zancen nan ya
fita.

Wani shekeke ya kalleta abinda bai taba yi mata ba. Kinga ki dauki 'yarki ku koma
gida idan an sallameta. Ke haihuwa ce kika gaji da ita. Ni kuwa da kika ganni
ganinki ne gabadaya bana son yi. Ba don kina gadon asibiti bane babu abinda zai
hana na nayi miki abinda zaisa a kawoki asibitin.

Raliya ta hada hannuwanta biyu tana hawaye Hamza kayi hakuri kada ka saketa. Izzatu
bata san meye rayuwa ba shiyasa take wannan haukan.

Indai zata yi haihuwa uku amma ta kasa sanin meye rayuwa to ina ganin har abada
bazata taba sani ba. Ya bata amsa rai a bace.

Izzatu dai sai kuka take yi. Duk haukanta tasan Hamza yana son haihuwa bazai taba
goyon bayanta a cire ciki ba balle mahaifa gabadaya. A hankali tace Sweetbaby am
sorry. Bana son nayi ta haihuwa ka dena ganin kyau na har ka fara tunanin sake
aure.

Mamakin kansa yake yi da yadda ya iya zama da Izzatu duk tsawon shekarun nan. A
kokarin kyautata mata ya rinka kuntatawa iyaye da 'yan uwansa. Kansa har wani irin
ciwo yake masa, fadan ma ya kasa yi yadda ya kamata. Izzatu ta cigaba da magana,
Baby a da indai nayi maka laifi fada kawai kake yi min. Amma yanzu duk ka canza
saboda yarinyar nan da ko kadan bata waye ba. Har me ka gani a jikinta wanda bani
dashi, me ya sami soyayyar da muke yiwa juna?

Ai ta tabo wa kanta masifa tunda tasa Zuhra a ciki. Itama Raliya shiru tayi saboda
irin fadan da Hamza yake yi yana gaggayawa Izzatu magana. Ke har kin isa ki hada
kanki da Zuhra? To bari na fada miki wallahi ban taba son wata mace kamar yadda
nake sonta ba, ciki kuwa harda ke Izzy. Zuhra tayi min abinda mata dayawa bazasu
iya yiwa mazansu ba a lokacin da kike yawon gidan biki. Wannan yarinyar da kika
raina ita ake kira matar rufin asiri. Kuma wallahi da ace wannan cikin da kika cire
shine na farko bazaki kara komawa gidana ba daga nan sai kwasar kayanki.

Hamza ni kake fadawa haka akan wannan yarinyar? To wallahi ko saki uku kayi min
babu inda zani. Ni da kai mutu ka raba. Kuma zubewar cikin ba laifinka bane? Eyye
nace ba laifinka bane??? Ai an tsayar da jinin tun a Abuja amma don wulakanci nazo
na ganka da yarinyar nan a kan gado kana romancing dinta....ko kunyar Raliya bata
ji ba take fadan wannan magana. Zuhra ta rasa me yake mata dadi.

Shima Hamza ya manta da Raliyar a wurin yace shi kawai kika gani? Baki kula ko riga
babu a jikina ba. Ki karasa bawa duniya labarin abinda kika gani a dakin mijinki
sakamakon shigar masa daki da kika yi babu sallama.

Raliya da Zuhra sai kallon kallo. Yau masoyan tamkar su cinye junansu don bacin
rai. Sai da suka gaji don kansu Hamza ya finciko hannun Zuhra suka fita. Sauri yake
kamar ya tashi sama. A motar ma babu wanda yace kala haka yaja suka tafi gida.
Nana tana ta yi masa gwaranci ko kallonta baiyi ba ya haye sama. Yau ran Hamza ya
baci fiye da yadda yaji lokacin da aka yi masa sata. Izzatu taci amanar soyayyar da
yake mata. Duk abinda take yi yana kawar da kai, wannan karon ta kure hakurinsa.

Tsoron binsa daki Zuhra tayi saboda yadda taga ya fusata. Lebenta ba kasa da ya
bige har dan kumbura yayi sannan wurin yayi ja sosai alamun jini ya taru. Rufawa
kanta asiri tayi ta dauki Al'Qurani ta shige wurin sakarta. Ta dade tana karatu
tare da addu'ar nemawa mijinta sauki daga kuncin da ya shiga.

********
Mama Agnes na tsaye akan autanta Felix tana ta zubar da hawaye. Irin matan nan ne
masu tsananin riko da addini ko takalmi bata sawa. Kwance yake akan gadon asibiti
ga yayyensa maza biyu da mace daya sai 'yan sanda biyu.

Dansanda daya yace a iya binciken da muka yi da kuma abinda abokan nasa da muka
kama suka sanar damu sata suka je yi akan high way lokacin wasu 'yan uwanmu suna
patrol shine aka harbe shi. Mama Agnes tace officer idan ya warke zaku tafi dashi
ne? Yace kwarai kuwa tunda an samu bullet din ya fita. Share hawayenta tayi tace
shikenan, ku zama shaida ta fada tana kallon sauran 'ya'yanta. Ko mutuwa nayi kada
ku bari Felix yazo kan gawata. Na yafe shi daga cikin 'ya'yana kuma na tsinewa
ranar da nayi cikinsa da ranar da na haifeshi. Cikinku idan akwai wanda yasan yayi
sata to ya mayar da hakki ga maishi domin daga nan zanje Church ne. Zamuyi addua ga
duk wani barawo a garin nan yayi mutuwar wulakanci da kaskanci. Duk cikin zuri'armu
babu abinda muka fi kyama kamar sata.

Felix na jin maganar da babarsa keyi ya soma kuka yana bata hakuri. Tace idan ma
hukuncin kisa aka yi maka to kasani sarai gawarka bazata sami bikin burial ba. Zamu
binneka tare da sauran masu abin ku yar kauyen nan..barayi 'yan uwanka.

Mama Agnes na gama magana ta fice ko waige babu. Kauyensu Mr Oscar gara mutum
yayiwa yarinya fyade akan yayi sata. Sata tafi kowane laifi girma a wajensu. Dayake
Mr Oscar ya yarda sosai da adduar Church dinsu shiyasa ya tsorata da abinda mamansa
ta fada. Kudin Hamza wanda har ya fara gini dashi su suka fado masa.

******
Bacci ne mai nauyi ya dauke Hamza sai karfe bakwai da rabi ya farka. Salati ya
rinka yi da mamakin dadewarsa a kwance. Da sauri ya fada bandaki yayi alwala yazo
ya gabatar da sallar magriba, kafin ya idar yaji ana isha a masallaci dole itama
yayita a gida.

Har lokacin zuciyarsa babu dadi sosai shiyasa shima ya zaune karatun Qur'ani. Ya
dade yana addu'o'i tare da istigfar saboda neman sauki a wurin Allah. Haka yayi ta
zama a daki har shadaya da rabi babu motsin Zuhra. Murmushi yayi da ya tuna
karshenta tana can tana fushi saboda shareta da yayi.

Dakinta ya fara dubawa babu kowa a ciki. Da ya sauka kasa ma tsit yaji sai karar
injin saka. Da saurinsa ya bude kofar dakin da take sakar ya ganta tana yi.

Zuhra na jin ya bude kofar gabanta ya fadi. Kusa da ita yaje ya zauna yana kokarin
cire hannunta daga jikin wani karfe da take turawa. Kin saki tayi sannan ta
sunkuyar da kanta kasa. Ka kyale ni yanzu zan gama ita ce ta karshe. Kin sakin
hannun nata yayi ya cire shi sannan ya kira sunanta cikin sanyin murya
Cutie....kamar wadda aka kunawa famfo sai kawai ta

24 / 36