Advertisements
Chapter 34 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   34 / 36

99K to 102K   out of 106K words

har kunne ganin Hamza ya nufi
hanyar kitchen din.

Durkushe ya sameta zata dauko tukunya ya karasa ya dauko mata. Zan tafi Cutie ina
jin bazan dawo da wuri ba saboda na tara ayyuka da yawa.

Adawo lafiya kawai tace amma taki kallonsa.

Murmushi yayi don yasan fushi take yi. Mata iyayen rigima ya fada a zuci. Hannu
yasa ya dago fuskarta har ta fara kuka...kishin ne ya motsa ko kallona bazaki yi
ba. Ko kina so na kasa yin aikin ne yau?

Dago idon da tayi ta ga kayan bacin rai. Goshinsa da kumatu har da gefen bakinsa
duk ga shatin janbakin Izzatu don tasan dai ba ita tayi ba. Sannan wuyan rigarsa da
kafada ma duk akwai. Wani kukan ta fashe dashi Hamza ya rasa ya zaiyi da ita.

Izzatu dake bakin kofa tayi kwafa tana dariya kasa kasa tace... Yarinya an fada
miki zama da kishiya kamar cin tuwo ne. Sake lekawa tayi fa taji shiru idonta ya
sauka akan Hamza da Zuhra kamar zasu shige cikin juna. Rungume suke da juna bakinsu
wuri guda.
Da sauri ta bar wurin zuciya na dukan uku uku. Wannan Zuhran ko mayya sai haka.
Minti daya tana kuka cikin dan lokaci har ta manta.

Ajiyar zuciya Zuhra tayi da ta hango Izzatu na barin wurin. Tana cikin kuka ta
hango inuwarta shine ta rungume Hamza. Ko ba'a fada ba tasan abinda ya faru anyi ne
da gayya shiyasa ta biyo bayansa taga yadda zasu kare.

Shi kuwa Hamza bai san me ake yiwa ba yace ashe abinda kike so kenan kika tada min
hankali. Ohhh yarinyar nan kinfi karfina...ya fada yana rike baki.

Dariya kawai tayi masa tace adawo lafiya amma ka fara zuwa ka canja kayan nan kuma
ka goge fuskarka.

Yace kayan ne bakya so?

Zuhra tace eh ka canja su wannan sunyi wani jirwaye daga wuyan.

Bai fahimceta ba amma dai don a zauna lafiya ya koma sama ya cire kayan. Mamaki ne
karara a fuskarsa da yaga janbakin Izzatu. Da sauri ya tafi gaban mudubi yaga na
fuskar ma. Allah Sarki Zuhra dole tayi kuka. Shi har kunya yaji ma da ya sakko ko
kitchen din bai koma ba ya fita.

A haka suka yi wata daya har da kwanaki. Duk yadda Izzatu zata bi ta janyo hankalin
Hamza tana yi. Waya da text idan ya fita ko yana daki shi da Zuhra kala kala. Abin
yana batawa Zuhra rai amma dai tunda tasan da aurensu sannan kuma ba shari'a ake
takewa ba dole take sawa zuciyarta hakuri.

Wata alhamis da safe Hamza ya gama shirin fita wurin aiki ya duba turarensa ya
kare. Shi kuma yafi son fesa akalla biyu a lokaci daya. Tunawa yayi da wani da ya
siyo a tafiyar da yayi ya dauko ya fesa. Yana gama fesawa Zuhra ta shigo dakin ko
magana bata yi masa ba ta ruga toilet tana ta amai. Bayanta yabi yaje ya na shafa
mata baya har ta gama sannan ya bata ruwa ta dauraye bakinta.

Suna fitowa dakin ya rungumota jikinsa ta sake shakar kamshin turaren ta zame
jikinta ta kuma komawa yin wani aman. Sai da tayi haka sau hudu yana ta yi mata
sannu.

Muryarta can kasa tace zata koma dakinta tana jin warin turarensa ne bata so.

Hamza yace wari kuma Cutie? Turare ai baya wari. Ko dai kinci wani abin ne yaki
zama.

Hancinta ta toshe ta ce fita daga dakin.

Shi dai abin ya bashi mamaki ya bita daki. Yana shiga ta soma amai a inda take
zaune.

Ko tabata baiyi ba ya koma dakinsa ya cire kayan. Hatta vest sai da ya cire ya saka
wasu ya fito. A zaune ya sameta a kasa tana ta kakari ga hawaye. Shi kam yana
jinjina ranar da zata shiga labour room. Dagata yayi ya kaita toilet ya gyara mata
jiki sannan ya dawo dakin ya gyara. Jikinta duk babu kwari ya kwantar da ita akan
gado...bari na turo Tala ta zauna min dake. Bazan dade ba in Allah Ya yarda. Kinsan
na fada miki minista zai turo ayi inspecting kamfaninmu kafinsu bamu aiki. Kuma ina
sa ran yau za'a biya kudin aikin ginin da muka gama. Da zarar mun kammala zan dawo
kinji.

Kai kawai ta gyada masa sannan tayi masa adduar fatan alkhairi.

Ya dan ja hancinta...wannan baby din zai gamu dani ne. Baki ga tsadar turaren nan
ba designer ne amma shine ya saki amai.

Maganarsa ta bata dariya yaji dadin ganin ta dan sake ya sauka ya turo mata Tala.

Da ya dan sami lokaci sai ya kirata a waya. Daga baya yaji shiru yasan kila tayi
bacci ne. Bata tashi ba sai wurin biyu da kwata cikinta a rarake. Tala ta kirawo ta
roketa ta soya mata fanke sannan taje tayi sallah.

Kafin a kawo fanken su Khalifa sun dawo daga makaranta. Sai da suka je dakinta suka
gaisheta sannan suka wuce wurin Izzatu suka ci abinci. Hamza ne ya kafa dokar idan
sun dawo su gaishe da kowa. Izzatu dai tace so yake lallai sai yaga ana irin zaman
da Hajiya da Mama suke yi. Ita kuwa tasan shisshigi ne kawai zai sa kishiyoyi su
mayarda juna 'yan uwa. Wannan munafurcin ba da ita ba.

Tala ta gama soyar fanken ta kaiwa Zuhra. Junior ta ce ta turo mata shine masoyin
fanke. Da murnarsa ya zo ta zuba masa a wani plate tace yaje suci tare da su
Khalifa. Kasa ya sauka yana kiransu. Ya dauki daya zai sa a baki Izzatu ta fizge
tare da dauke plate din tana masa fadan ita bata son kwadayi. Jiya ma ta soya masa
fanken nan kuma yanzu ba ta fada musu abincinta kawai zasu rinka ci ba.

Junior yana ji yana gani Izzatu ta juye fanken a shara tace idan ya koma dakin
Zuhra sai ta zane shi sannan tayi tafiyarta daki.

Har ya manta da batun fanke suna wasan goyo da Khalifa yace bari yaje yasha ruwa.
Kwandon sharan kitchen din ya kula dashi ya duba fanken suna ciki. Ukun sama ya
dauko ya karkade sannan ya boye a cikin rigarsa yayi gaba.

Tala ta shigo kitchen din Izzatu da tsintsiya da abin kwasar shara a hannu. Wata
sharar ta zuba ta dauki kwandon ta fita waje. Wurin maigadi taje tace ya zubar da
sharar a drum din waje saboda aikin store din Izzatu tayi. Leda ce a hannunta baka
ta rufe hannunta sannan ta dauko kwandon. Maigadi yace wannan rufe hannu kamar kin
dauko guba.

Tala tace ai gubar ce, motsi Hajiya taji a store tasa na fesa fiya fiya tana tunani
ko bera ne. Sharata ta uku kenan bamu ga komai ba. Gara ayi waje da sharar kasan
f[truncated by WhatsApp] AL'ADUN WASU #79

Batul Mamman(Mrs)#




Tun uku da ashirin Tala ta gama shirya Khalifa zasu tafi islamiyya amma shiru basu
ga Junior ba. Tayi kiran da neman har ta gaji. Ga Khalifa ya soma rigima shi ta
fara raka shi idan taga Junior ta kawo shi daban saboda kada malaminsu yayi masa
bulalar makara.

Sama ne bata duba ba ta hau lokacin ana sallar la'asar ta shiga dakin Zuhra. Sallah
ta tarar tana yi ta dan jira har ta idar sannan ta tambayeta ko Junior ya shigo.
Zuhra tace ai tunda na bashi fanke bai dawo ba. Bari na duba falon Daddyn su ko can
ya tafi.

Hanyar kasan tabi ita kuma Tala ta shiga dakin Izzatu. Itama fitowarta kenan daga
toilet tayi alwala. Da Tala ta fadi me ya kawota tace ki duba falon Daddy dinsu ni
sallah zanyi.

Har karkashin table din da Hamza ke aiki Zuhra ta duba babu alamun Junior. Abu
kamar wasa suka fita har bayan gidan. Gashi maigadi yayi ta rantsuwa baiga
fitowarsa ba.
Izzatu ma ta fito daga dakinta don taji a inda aka ga Junior ta tarar har lokacin
nemansa akeyi. Hankalinsu duk ya tashi sai kiransa suke yi shiru.

A gigice ta dauki waya ta kira Hamza lokacin yana tare da wasu baki bai sami damar
daukan wayar ba. Shi a tunaninsa ma irin wayar da take masa ne yanzu kullum ta
tambayeshi aiki. Murmushi yayi da yaga ita ke kiran da niyar idan bakin sun tafi
zai kirata.

A can gidan kuma daga Izzatu har Zuhra kuka suke yi. Tala sai basu hakuri take yi.
Khalifa ne ya dami Izzatu akan ta barshi ya cire uniform dinsa tunda ya makara da
yawa. Idan aka kaishi yanzu malam zai zane shi. Ko kula shi bata yi ba suka fara
shirin fita waje nemansa. Sake tambayarta yayi ta daka masa tsawa...jeka ni kada ka
dame ni.

Da 'yar murnarsa ya shiga dakinsu. Ba'a dade ba ya fito da gudu su Izzatu har sun
kai bakin gate yace ga Junior a cikin drawar kayansu.

Da sauri suka dawo ciki Izzatu ta gama kulewa tana tunanin irin dukan da zata yi
masa saboda yadda ya tayar musu da hankali. Zuhra kanta har ciwo yake saboda kukan
da tayi gashi dama jikinta babu kwari. Wayar chaja ta ga Izzatu ta ciro tasan sarai
Junior zata daka tabi bayanta da sauri.

Suna shiga dakin ta fara bata hakuri Izzatu ta janyo hannun Junior da yake kwance
cikin kaya kamar me bacci tace...tashi wato har bacci kake yi duk ka tayar min da
hankali.

Maimakon ya bude ido sai taga ya biyota gabadaya ya fadi a kasa. Tsorata tayi sai
ta dan dake tace Junior tashi mana.

Shiru ko motsi baya yi. Zuhra ce ta fara kula da yawon da ya fara fitowa daga
bakinsa sakamakon motsa shi da aka yi ta durkusa a gabansa ta fara shafa fuskarsa
tace ....Junior bude idonka.

Sai a lokacin Izzatu ta kula da yawun ta kwala ihu...Junior bude idonka don Allah.
Yawun meye wannan?

Daga ita har Zuhran a gigice suke ta girgiza shi ko zai bude ido amma abu ya
faskara.

Tashi tsaye Izzatu tayi ta daga shi tana kuka sai fanke ya fado daga hannunsa na
dama. Ta bi shi da ido har ya fadi sannan ta tura hannu a bakinsa sai ga wani
gutsiren fanken ta ciro. Ajiye Junior tayi ta cakumi wuyan Zuhra idanunta a
birkice.

Yanzu don kina da ciki Zuhra sai ki kashe min da? Har me nayi miki haka da zaki
huce akan innocent yara na? Sai da na kwace fanken nan na zuba a shara shine kika
sake bashi wani saboda mugun nufinki.

Zuhra sai kokarin cire hannun Izzatu take yi ta kasa sai da Tala ta shiga
tsakaninsu. Da kyar ta iya raba hannun Izzatu da wuyan rigar Zuhra.

Kasa magana tayi saboda yanayin da Junior yake ciki ga muguwar shakar da aka yi
mata tana ta tari ido na fidda hawaye. Suna kallo Izzatu ta kwance dankwalin kanta
ta goya Junior sannan ta fizge mayafin jikin Tala tayi hanyar waje tana kuka. Kafin
ta fita tace...idan yaron nan ya mutu Zuhra dayanmu zata bi bayansa.

Zuhra ta kalli Tala hankalinta yayi matukar tashi tace Tala wane irin plate kika
dauko na zuba musu a ciki? Nima naci kuma babu abinda ya sameni. Ya Allah Kasa
Junior ya tashi...tana magana tana kuka ta hau sama ta dauko wayarta. Itama dai
Hamza bai dauka ba sai kawai ta dauko jaka ta sakko.

Tala da maigadi ta gani sunyi jugum a waje sai Khalifa a gefensu. Zuhra tasan mota
Izzatu ta fita ta nema don babu wata motar a gidan tace da Tala ina Nana take?

Tana dakin Hajiya tana bacci.

Dama bukatarta ace bata ci fanken ba. Tana jin haka ta fita tayi sa'ar hango Izzatu
na shiga taxi. Adaidaita sahu ta samu tace yabi bayan taxi din gabansu. Suna tafiya
tana ta kokarin kiran Hamza wayar taki shiga saboda a wannan lokacin Izzatu ma
kiransa take yi shiyasa duk basu samu ba. Taxi din na tsayawa a bakin gate din wani
asibitin kudi inda Izzatu ta taba kwanciya su Zuhra ma suka tsaya. Da gudu suka
shiga asibitin Zuhra ta manta da tata rashin lafiyar. Emergency suka nufa nan da
nan nurses biyu suka karbi Junior aka kirawo likita suka shige dashi aka bar Izzatu
da Zuhra suna ta kai kawo kowacce da irin abinda zuciyarta take saka mata. Tsananan
tashin hankali yasa Izzatu bata kula Zuhra ba. Jira take taji a wane hali Junior
yake.

Suna nan tsaye Hamza ya kira wayar Izzatu. Da kuka ta dauka...Hamza matarka ta
kashe min da.

Yanayin muryarta ya tabbatar masa ba wasa take yi ba yace...ban fahimceki ba Izzy.
Tun dazu naga kuna ta kirana. Me ya faru? Waye ba lafiya?

Muryarta a dashe don kuka tace poison Zuhra tasa a fanke ta bawa Junior. Muna
asibiti yanzu.

Dama ya riga ya shiga mota a rude ya tayar ya fita bayan ta fada masa wane asibitin
suka je.

*****
Sai bayan kusan awa daya likitan ya fito tare da nurses din. Fuskarsa kadai zaka
kalla kasan cewa akwai matsala. Fitowarsu tayi daidai da shigowar Hamza. Duk kan
likitan suka yi suna tambayarsa halin da Junior yake ciki.

Office dinsa ya kirasu sannan yace...a gaskiya mata da yawa kuna sakaci da maganin
kwari. Sai ku rinka ajiye shi a inda yara zasu gani su dauka su ci.

Hamza da gumi ya gama wanke shi yace doctor ka fada min abinda ya sami yaron nan.

Likita yace to a iya bincikenmu Sunusi ya ci maganin kwari ne possibly piya piya.
Wanda yaci babu yawa sosai sai dai an bari tayi masa illa sosai a hanjinsa. Yanzu
munyi stabilizing condition dinsa amma zuwa jibi idan babu cigaba ina ganin sai
munyi masa aiki an yanke wurin da ya baci a jikin hanjin.

Kafafun Izzatu nema suke su kasa daukarta don fargaba. Zuhra tasa bakin mayafinta
ta toshe baki tana kuka. Hamzan ma dai idanunsa sunyi jazur ya dubi likitan...ni
dai idan har kasan yana bukatar aikin nan kawai kayi masa doctor ba sai am jira
kwana biyu ba.

Izzatu suka gani ta durkusa akan gwiwoyinta tana kuka...ka rufa min asiri likita ka
ceci rayuwar Junior.

Dr Ghali yace kuyi hakuri ba haka kawai zamuyi aiki ba sai bukatarsa ta tashi. Idan
jikinsa ya karbi medication din da ake masa muna fata ba sai anyi masa aikin ba.
Yana kare magana ya tashi suma suka bi bayansa suka fita.

Ran Hamza a bace yace su biyo shi waje. Kallon da yake musu yasa Zuhra kara tsorata
kada ya yarda ita ta bawa Junior guba....ina saurarenku ku fada min abinda ya faru.

Izzatu ce ta soma magana ta sanar dashi yadda suka yi da Junior da fanke. Itama
Zuhra ta fadi abinda ta sani. Kansa ya daure Izzatu ta dage Zuhra ke neman kashe
mata da. Kuka Izzatu take yi sosai tana tararrabin abinda zai faru. Hamza ya
rungumeta yana bata hakuri. A wannan yanayin Zuhra ta koma ciki zuciyarta babu
dadi. Tabbas fanke ne a bakin Junior kuma ita ma shi taci. To a ina ya sami maganin
kwari shine tambayar da take yiwa kanta.

Bata dade da shiga dakin ba su Hamza suka shigo sai ga Tala goye da Nana ta riko
hannun Khalifa. Hankalinta ne ya kasa kwanciya ta biyo bayansu.

Dakin babu mai magana sai sautin kuka har aka kira magariba. Jikinsu duk babu kwari
suka yi sallar. Junior bai farka ba sai da aka yi isha. Lokacin har su Alhaji sun
zo. Umma da Baba ma duk suna asibitin. Su Raliya ma sunyi alkawarin bin jirgi da
sassafe su taho Kano.

A hankali Junior ya bude idanunsa. Yini daya duk ya fada sai haske da yayi fayau.
Da kyar ya iya motsa bakinsa yace ruwa.

Ibrahim yace bari na tambayi likitan ko za'a iya bashi kada muyi garaje. Bayan
fitarsa Junior ya soma kukan cikinsa na ciwo. Hamza ya dora kan Junior a cinyarsa
yace bari Uncle Ibrahim ya kirawo likita sai ya duba maka cikin.

Izzatu ta kama hannunsa na hagu wanda babu allurar karin ruwa ta rike gam tana
fitar da hawaye mai zafi. Bakin Junior har tsagewa yayi yace Mummy kice kin yafe
min.

Maganarsa tasa dakin yayi tsit kowa na tausayinsa. Izzatu tace yi shiru babyn Mummy
ka dena magana kaga baka da lafiya.

Zuhra ta taso ta tsaya a gefen gadon Izzatu ta galla mata harara. Junior yace ni
dai kice kin yafe. Maama tace babu kyau mutum ya dauki abinda ba'a bashi ba. Kin
karbi fanken da ta bani kin zuba a dustbin dinki shine naje na dauka naci gashi
yanzu cikina yana ciwo. Kin yafe min Mummy?

Wani salati Tala ta soma yi da karfi tana kuka. Hajiya a cikin kwandon sharar
kitchen dinki na zuba sharar store da kika ce na saka piya piya dazu.

Dakin ya kaure da salati Izzatu kuwa kasa ta zauna tana kuka mai sauti. Ji take
kamar zuciyarta zata faso mata kirji. Zuhra ta durkusa a gabanta tana kokarin
dagata tace...Zuhra na kashe Junior ko? Da na sani na barshi yaci fanken.

Zuhra na kuka tace baki kashe shi ba tsautsayi ne.

Izzatu ta ki tashi duk da haka...barni kawai gara na mutu da naga mutuwar dan
cikina. Ni ba kara haihuwa zanyi ba idan duk suka mutu wa zan kalla inji dadi.

Tausayinta ne ya kama su Hajiya suka taimaka mata ta tashi tsaye. Duk abinda ake yi
Hamza bai kula su ba. Hankalinsa yana kan Junior da idanunsa suke ta kafewa.

Ibrahim ne ya shigo da likita aka sa kowa ya fita. Sun dan dauki lokaci kafin
likitan ya fito yace yayi masa allurai su barshi yayi bacci. Haka kowa ya tafi jiki
a mace ya rage Hamza da matansa don su Hajiya sun tafi dasu Tala.

Daga kai Hamza yayi zai musu maganar tafiya gida saboda dare yayi sosai ya gansu
kowacce tana kuka. Nasiha da ban hakuri ya kirkiro duk da yadda yake ji a ransa
yayi ta basu baki sannan yace bari ya kai Zuhra gida ya dawo. Da farko kin yadda
tayi ta tafi sai da yayi da gaske. Haka suka tafi babu mai cewa komai. A falo ta
zauna yaje ya daukowa Izzatu da Junior kaya yace mata zai koma can amma zai sa a
dawo dasu Tala.

A hankali tace to Allah Ya kiyaye hanya. yace amin.

Daren ranar babu wanda ya iya yin bacci. Da asuba Zuhra ta tashi ta dafa ruwan zafi
ta soya dankali. Karfe bakwai Hamza ya shigo jikinta har rawa yake tace ya jikin
Junior yace da sauki.

Wanka kawai yayi suka koma asibitin.

A gaban gadon ta zauna tana kallon yadda lokaci guda Junior ya fita daga
hayyacinsa.

Kafin shabiyun rana ranar Juma'a dakin ya cika da mutane harda Raliya wadda Izzatu
na ganinta ta fada jikinta tana kuka.

Tana rarrashinta Junior ya farka. Zuhra ya gani a tsaye a gefensa yayi dan
murmushi....Maama a aljanna akwai fanken da baya sa ciwon ciki ko?

Zuhra ta share hawaye tace sosai ma kuwa. Ai duk abinda ka sani na dadi akwai a
aljanna.

Yace Allah Yasa mu shiga jirgin aljanna tunda Mummy tace ta hakura naci abinda ta
hanani.

Maganganun Junior banda karyar musu da zuciya babu abinda suke yi. Daga masu kuka
da sauti sai masu share kwalla.

Izzatu ta kasa kukan ma. Ji take ina ma ciwon ya dawo jikinta akan taga danta a
wannan yanayin.

Hamza yana can wurin likita suna tattaunawa akan aikin da za'ayiwa Junior a daren
ranar saboda yadda yake jin jiki babu amfani a jira sai washegari. Tare suka taho
da likitan zai sake duba shi suka shiga dakin.

Izzatu ke kallon Junior tana tambayarsa ko akwai abinda yake so. Sai yayi wani irin
tari sannan yace Maama ki goyani irin yadda

34 / 36