Advertisements
Chapter 9 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 36

24K to 27K   out of 106K words

na sami wani ya bani aron
littafinsa nake son kwaikwayon duk wanda kika zaba zanyi kokari na kwatanta miki
irinsa uwata. Atine gashi ki tayata zabe. Hawaye ne mai zafi ya saukowa Zuhra.
Tabbas iyaye sun cancanci dukkan girmamawa daga 'ya'yansu. Allah Ka sakawa iyayenmu
da alkhairi. Baba ne ya fara gani yace meye haka uwata ta kaina? Da yake Umma ma
akwai rauni sai kawai suka hadu suna kuka maimakon ta rarrasheta. Baba ma dai ta
maza yayi ya fara musu fadan su dena yi masa kuka. Burina Zuhra tayi aure ta sami
mai kula da ita. Sai da shekaru suka zo mana muka haifeki dole nayi murna idan na
sami wanda zai tayani kula da Fatima kyauta daga Allah. Zuhra fadawa tayi jikin
Baba tana kuka. Ni bazanyi aure ba. Saurin tashe mata baki yayi...kul na sake jin
irin haka. Aure ai shine rufin asirin kowa. Zaki yi aure cikin gidan mutumci kuma
in Allah Ya yarda zaki kawo min jikoki su zo in basu labarin tabara irin ta
babarsu. dariya ta rinka yi. Daga baya suka zabi gado da kujeru ita da Umma.

Sai da ta kwanta ne a kan dan gadonta maganar Hamza ta rinka dawo mata. Tabbas da
niyarta ta aureshi ta kuntata masa. Don duk zancen da yake mata jinsa kawai take
yi. Sun dauketa wata gaula daga shi har matar tasa. To amma maganar Baba ta tsaya
mata a rai. Duk shirmenta tana kaunar iyayenta kuma bata son bata musu suna. In
Allah Ya yarda bazata wasta musu kasa a ido ba. Idan har baayi auren ba sai dai
idan Hamza da bakinsa yace baya so.
[9/25, 3:46 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #27

Batul Mamman(Mrs)#




Bayan kwana biyu Umma ta sanar da Zuhra yau iyayen Hamza zasu zo. Mamansu Hajara ta
shigo tayata aiki. Kaji hudu suka soya, Anti Faiza sarkin flour tayi musu cake,
meatpie da doughnut. Zuhra ta wanke tsakar gidansu tas dama irin fasassun tiles
dinnan ne. Nan da nan wurin ya hau sheki. Bayan ta gama aikin ta hau magiyar a
barta taje gidan Hajara. Tunda akayi biki Baba ya kafa mata dokar sai tayi sati
baya son yawon gulma. Anti Faiza tace ke da zasu ji ta bakinki ai bai kamata ki
fita ba. Kannen Umma biyu suma suna ta zolayarta da matar kanin Baba.

Sai bayan la'asar suka watse aka bar Maman Hajara da Umma. Baba ya shigo tare da
Malam yace su bakin zasu shigo. Kaninsa da yake aikin masinja ma yazo tunda Alh
Nasiru yace indai ta amince to a lokacin zasu bada kudi asa rana. Su Umma daki suka
koma bayan an jerawa baki kayan motsa baki. Sai da suka gama barkwancinsu sannan
Alh Nasiru ya bukaci ganin Zuhra domin yaji amsarta. Dan karamin falonsu ya shiga
tare da Baba. Kanta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana mai yabon halayenta. Sannan
ya tambayeta domin baya son matsa mata ta auri wanda bata so. Murmushi kawai tayi
ta sake sunkuyar da kai. Ganin haka ya mike suka koma tsakar gida. Ya dubi sauran
jamaar wurin. Shirun budurwa alama ce ta amincewarta saboda haka idan duk kun
amince ina so asa rana nan da sati hudu. Kowa yayi naam da hakan harda Baba. A take
suka bada kudin aure dubu dari aka yi addua taro ya watse.

Ranar murna a wurin Baba da Umma ba'a cewa komai. Kudin da aka bayar Baba yace zai
ajiye mata zuwa lokacin biki. Kinga ko mijinki bai yarda ki cigaba da saka ba kina
da dan abin hannunki. Sannan ku shirya karshen sati zamu je Ajingi. Nan Zuhra ta
hau murna zata je wurin Inna.

Yinin ranar Hamza suna ta meeting da maaikatansa akan yadda zasu samu su karasa
biyan kudin da turawan ke binsu kamfanin ya dawo mallakin Hamza shi kadai. Ya sanar
dasu dole su zage damtse ayi aiki sosai domin su fitar da kudin kafin watanni
shidan da aka basu su cika. Suna fitowa gidansu ya tafi saboda amsa kiran Alhaji.
Yasan zancen bazai wuce Zuhra taki amincewa ba ayi masa fadan bai yi abinda ya dace
wurin jan raayinta ba.

Mama bata gida lokacin da yaje sun fita da Nura. Da Hajiya suka gaisa kafin ya
karasa wurin Alhaji. Fuskarsa a sake ya amsa gaisuwar Hamza sannan yace ya kamata
ka fara shiri tunda sati hudu kawai aka sa rana. Idan baka son hadasu gida daya sai
ka gyara mata tsohon gidanka. A dan daburce Hamza yace wa zan gyarawa? Alh Nasiru
yayi murmushi amaryarka mana. Yadda gabansa ya fadi bai san lokacin da yace
amincewa tayi??? Alhaji yace ba haka kaso ba ko. Ai nasani Babana. To sai ka dau
hakuri yarinya tana neman albarkar iyaye. Hamza yace Alhaji nima ina nema. Don
Allah a janye zancen nan. Ko Nura ka aurawa ita. Dariya Alhaji yayi shi kuwa Hamza
kamar yayi kuka yace yarinya ce karama. Ya za'ayi na zauna da ita? Alhaji ya gyara
zamansa. Kaga ba jan zance nake so muyi ba. Aure ne sai an daura in sha Allah. Ni
ban dora maka nauyin komai ba sai sadaki. Tunda na fika son ayi auren na dauke maka
duk wata hidima da zata taso. Rasa bakin magana yayi yana kallon mahaifinsa. Mama
ce ta shigo tare da Nura da su Hamida suna rike da wasu jakunkuna masu kyau. Seti
ne guda shida, tace Alhaji kaga wadanda muka samu. Sai ta kalli Hamza, a'a kaga
babban dana angon Zuhra. Ta tura masa daya daga cikin jakankunan. Kaga wannan sunyi
kyau? Yanayin fuskarsa bazai fasaltu ba yace Mama harda ke? Nice ma kan gaba ta
bashi amsa. Uhm Alhaji gobe da safe zamu je da su Jidda kasuwar, kasan hada lefe
akwai cin lokaci. Yana shan furarsa yace Allah Ya kaimu. Share Hamza suka yi tamkar
baya wurin. Tunaninsa daya yadda zai fadawa Izzatu plan dinsu bai karbu ba.
[9/25, 3:47 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #28

Batul Mamman(Mrs)#




Abinda yaji tsoro ne ya faru. Izzatu tayi kuka har ta gaji. Rokon Hamza take yi ya
rufa mata asiri kada yayi auren. Tun yana rarrashinta har ransa ya baci da tace duk
gidansu babu mai kaunarta. A hasale yake kallonta ke har kina da bakin cewa ba'a
sonki Izzy? You caused everything. Lokaci guda kin lalata farincikin gidan nan.
Ganin ya soma fada yasa ta rungumeshi. Am sorry baby. Na yarda kayi auren amma
bayan lokaci kadan sai mu nemi dalilin da zaisa ka saketa. Jinta kawai yayi. Shi da
Alhaji ya kafa masa sharadin indai ba da dalilin da ya sabawa shariah ba bai yarda
ya saki Zuhra ba.

A bangaren su Zuhra kuwa shirye shirye ya kankama. Makota da abokan arziki kowa
yana son gwada bajintarsa wurin bikin tilon yar baban yara. Gudunmawar kudi suka
rinka bawa Mal Bashir sai da ya tashi da dubu dari biyu da talatin. Shi kanshi ba
karamin mamakin wannan karramawa ta mutanen unguwarsu yayi ba. Anas da Sani ma ba'a
barsu a baya ba domin kuwa gas cooker karami suka kawo. Baba yayi murna da godiya
sosai. Haka Umma ta rinka shiga gida gida tana godiya itama.

Zuhra taje gidan Hajara a nan suke nasu tsarin bikin duk da ba damunta yayi ba don
tasan wahala zata sha kawai. Hajara tace wato Zuhra da gaske kike da kika ce idan
kika tashi aure sai munyi mamaki. Gashi zaki auri dan gayu dan boko. Wallahi ki
dage sosai tunda yana da mata. Zuhra tayi dariya wace irin dagewa kuma. Ai kawai
indai zasu bani abinci naci na koshi to suje can su karata. Sahabi da yake daki ya
fito ba shiri. Amma dai Zuhra wasa kike ko? Tace da akayi me fa? Maganar da kika
fada yanzu nake nufi. Yaushe zaki ce abinci zaki je ci. Wuri ya samu ya zauna yana
karanta mata yadda zata yi a gidan miji. Hajara sai dariya saboda Zuhra rufe kanta
tayi da mayafi. Irin wannan bayani na Sahabi yafi karfinta. Shi kuwa ya dauketa
kanwarsa ne tunda duk unguwarsu daya.

An kawo lefe akwati shida da kit. Komai Alhaji ne ya siya. Makota da yan uwa suna
ta san barka. Washegari Baba yayi shatar mota suka dauki kayan suka wuce Ajingi.
Nan ma kowa yace Zuhra tayi goshi. Yan uwanta suka shiga hada mata abubuwan da zata
gyara kanta. Yi kawai take don kada a gane auren da matsala. Cikin wannan lokacin
ko text bai taba hada Hamza da Zuhra ba. Har Umma sai da tace naga kwana biyu shiru
yaron nan. Zuhra tayi yake muna waya kullum Umma. Wani aiki ne yake son karasawa
kafin bikin. Umma tace to Allah Ya bada saa.

Alhaji ya sake tuntubar Hamza inda zai ajiye Zuhra. Takardun tsohon gidansa ya
dauko ya mikawa Alhaji yace na riga na gama komai ya zama mallakin Nura. A sabon
gidan akwai dakuna sai ta zauna a cikin daya. Alhaji yasa masa albarka sannan ya
tura Mama ta gano dakin da za'a bawa Zuhra. Dakina ne babba a kasa da toilet a
ciki. Mama tace sam amarya ma a sama zata zauna. Dakunan saman uku ne har an gama
jera kayan su Khalifa a ciki. Bisa umarnin Alhaji dole aka dawo dasu kasa ba da son
ran Izzatu ba aka sabonta fentin. Katon daki ne kamar na Izzatu da toilet. A ciki
aka jerawa Zuhra gadonta daga wani gefe da yayi dan tudu. Dayan gefen kuma
kujerunta da su tv. Mama tace kuma lallai ayi kitchen kabinet a daya daga cikin
dakunan kasan saboda a raba musu kitchen.

An fara biki cikin kwanciyar hankali. Baba yana ta yabon Hamza saboda yana yawan
kiransa a waya su gaisa. Hakan yasa suka cigaba da tunanin komai lafiya tsakaninsa
da Zuhra. Anti Faiza kuma ta sake ja mata kunne akan tayi shiru da bakinta. Sannan
tayi mata nasiha akan kwalliya da tsafta. Ni girar nan da kike ja ce bana so Zuhra.
A shagwabe tace nufinki bana yin kyau Anti Faiza. Kinsan ni gaskiya zan fada miki.
Bata miki kyau don ba iyawa kika yi ba. Kuma babu ruwanki da Izzatu ki kama kanki
kinji ko. Zuhra ta gyada kai. Kinga yadda iyayensa suka tsaya miki sosai. Ina so ki
kyautata musu daidai gwargwado. Babu fitsara ba rashin kunya. Nagode Anti Faiza in
sha Allah zan kiyaye.

Anyi kamun Zuhra a unguwarsu washegari alhamis suka tafi Ajingi. Jumaa bayan
masallaci aka daura auren Arch Hamza Nasir Hamza da Fatima Bashir Ajingi. Kai ka
dauka auren yar wani maikudi ake yi saboda yadda mutane suka zo. Asabar da safe
suka dawo kano aka fara shirin kai amarya.

Jikin Zuhra a sanyaye tunda aka daura auren. Shikenan zata bar iyayenta ta zauna da
mutumin da babu soyayya a tsakaninsu. Ba'a tashi kuka ba sai da motocin daukar
amarya suka zo. Aka rasa yadda zaayi a raba Zuhra da Umma. Gabadayansu kuka suke yi
tamkar sun rabo kenan. Baba ya shigo yana fadan sun bar mutane a waje. Sai dai
Zuhra na rungumeshi ya soma hawaye. Daki yaja hannunta suka koma. Yana kuka yana
mata nasiha....uwata ki rinka tsafta kinji ko, ki rike Allah da ManzonSa SAW komai
zaizo miki da sauki. Ki rinka taimakon mijinki. Kuma banda katuwar loma a gaban
miji. Murmushi tayi hade da kuka ta sake fadawa jikinsa. Baba wa zaku rinka gani a
gidan nan idan na tafi? Umma ce ta bata amsa bayan ta fyace hanci cikin yaran Yaya
Shafiu matarsa tace na dauki duk wadda nake so. Baba ya dauko wata leda ya damka
mata. Ga wannan dubu hamsin ne. Cikin kudin da na samu ne. Zan ajiye miki sauran.
Ki rinka amfani dashi. Allah Yayi miki albarka. Basu fito ba sai da Malam babansu
Hajara yazo ya buga kofar. Haka suka tafi tana ta rusa kuka ita da Hajara. Anti
Faiza tace gulmammu duk wadda bata son auren sai mu koma da ita. [9/25, 3:48 PM]
#+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #29

Batul Mamman(Mrs)#




Idan kaga dakin Zuhra baka ce na yar Mal Bashir kafinta bane. Tabbas duk dakunan
gidan sunfi nata kaya masu kyau da tsada. To amma itama nata iyayen sunyi kokari
sosai. Gida ya cika da yan kawo amarya. Izzatu ita kadai ce a daki dama ita ba mai
rakice rakicen kawaye bace. Daga ita sai 'ya'yanta. Duk da tasawa ranta bazata kula
Zuhra ko tayi kishinta ba sai da tayi kuka da aka shigo ana guda. Adabiyya da
Hamida sunfi kowa rawar kafa Yaya yayi amarya. Hakuri da nasiha aka sake yi mata
sannan suka tafi. Hajara da wasu yan uwanta ne karshen tafiya bayan sun sake gyara
mata daki. Tashi tayi ta cire mayafin jikinta saboda su hudu ne kawai a dakin.
Hajara tayi saurin mayar mata.
"Abinda ake son amarya da jan aji. Kin wani cire mayafi, idan wasu suka sake
shigowa fa."

Sake cire mayafin tayi "ke kyaleni nasha iska. Da zafin gari zanji ko na rabuwa
dasu Umma." Tana magana idanunta suka cika da hawaye.

Hajara ta ja hannunta suka koma kan gadon. Sake gyara mata dauri tayi aka fesa
turare."to mu zamu tafi amarya. Kada ki tashi nasan ango na hanya. Kuma ki dena
kukan su Umma haka. Irin haka sai yaga kamar auren dole aka yi muku.

A zuciyarta Zuhra tace meye maraba. A zahiri kuwa godiya tayi musu suka tafi. Sai
da taji dakin tsit ta tashi tana leka ko ina. Wurin yayi kyau sosai ga kamshin
turaren wutar da kanwar Umma ta hada mata. A hankali ta bude kofar toilet ta shiga.
Wani murmushu tayi. Irin wannan bandaki kamar a gidan shugaban kasa. Ta mika hannu
sink taga ruwa ya fito tun kafin ta kunna famfon. Zabura tayi da gudu zata fita don
a zatonta famfon ya lalace ne , kada ace ita ta lalata. Ko da ta juyo sai taga
ruwan ya dauke. Gabanta na dukan uku uku ta sake komawa tana mika hannu saman zata
kunna sai taga bai sake fitowa ba. Har tayi ajiyar zuciya ta sake saka hannu a
wurin fitar ruwa sai gashi ya sake fitowa. Fita kawai tayi ta rufe toilet din.
Allah Yasa tayi sallar Isha. Dama nafila take son yi, sai ta hakura.

Tun tana jira ko angon nata zai shigo har ta fitar da rai. Dama bata sa a ka ba.
Wuri ta samu a tsakiyar gadon tayi kwanciyarta ko kaya bata chanja ba. Bata dade ba
bacci mai nauyi yayi gaba da ita.

Hamza bai shigo gidan ba sai shadaya da rabi na dare. Tun kayan jikinsa na daurin
aure bai dawo gida ba. Babbar rigarsa da hula duk a hannu ya shigo dasu ya hadu da
Tala tana ta gyara gidan. Ita kam dole a yaba mata wurin tsafta. A gajiye yake
sosai, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama.

Sai da yaji ba dadi da ya kalli kofar dake hagun dakinsa. Wai matarsa ce a ciki. Ko
alamar zuwa baiyi ba. Kofar dakin Izzatu ya taba yaji bata rufe ba. Muryarta a
shake alamar taci kuka yaji tace
"Waye?"
Shiga yayi ta taso da sauri ta rungume shi tana kuka. Bai hanata ba sai da tayi
shiru don kanta.
"Ina su Nana?" Ya tambaya lokacin da yake cire takalmansa.

"Suna sabon dakinsu. Tala zata rinka duba min su." Yadda take maganar kasan har
yanzu tana bakin cikin canza musu daki da aka yi.

Kiss Hamza yayi mata a kumatu." Goodnight Izzy. Kije ki kwanta" Ya juya zai fita.
Kansa ke ciwo kamar ya tsage. Yau baici wani abin kirki ba tun safe. Yana son
tambayar Izzatu amma yasan idan bata da nutsuwa girki ma baya gabanta.

Saurin biyoshi tayi. Ta rike masa hannu" Don't tell me wurin Zuhra zaka kwana".

Hannun nata ya saki." No, dakina zani. Na gaji kema ki kwanta haka"

Kallon tuhuma take masa." Are you sure?". Kai ya gyada mata. Baya son magana saboda
yadda kansa ke sarawa "Ko nazo mu kwana? Ina fargabar ranar da zaka kwana dakin
yarinyar nan. Zan iya mutuwa saboda kishi." Ganin baya son magana yasa ta kyale
shi. Tasan bazai fadi magana ba yaki cikawa.

Bayan ya tafi itama sake gyara jikinta tayi tabi bayansa. Da ya tambayeta abinci
tace babu amma bari tayi sauri ta dafa masa wani abin. Jallop din taliya tayi
masa. Kafin ta gama yayi wanka. Abinci yaci ya dan zauna ya fada masa. Suka kwanta
shi da Izzatunsa. Ba wata hira tsakaninsu domin kuwa akwai abinda ke damunsa.
[9/25, 3:49 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #30

Batul Mamman(Mrs)#




Zuhra anji dadin bacci saboda gajiyar da ta tara ta biki. Ba ita ta farka ba sai
bayan tara. A firgice ta tashi ganin hasken rana a dakinta. Ko sallar asuba batayi
ba. Sai da ta shiga bandakin ta tuna da matsalarsa ta jiya. Gashi ta makara sallah.
Banda bahon wanka daga gefe wata yar matakala ce mai karamin bene da yayi kasa
akwai shower a wurin. Kunnawa tayi ruwa ya watso mata saboda yayi karfi. Da kyar ta
iya rage karfin ruwan. Cire kayanta tayi ta koma tayi wanka tare da alwala.

Tun kafin ta gama shiryawa cikinta ya soma kukan yunwa. Nan fa ake yinta. Zuhra
bata jurar yunwa gashi tunda aka kawota ko motsi bataji a kofar dakin ba. Haka ta
gama duk abinda zata yi ta sami wuri ta zauna. Tunanin iyayenta ne ya zo mata ta
soma kuka.

Izzatu da Tala sun gama hada komai na breakfast suka jera akan dinning table. Sama
ta hau ta kira Hamza. Sanye yake da jallabiya light brown sai kamshi yake. Yayi
kyau sosai sai dai fuskarsa da ta zama maabociyar damuwa yan watannin nan. Yaransa
duk suka yi masa kiss a goshi kamar yadda suma iyayen suka saba yi musu. Sannan
suka zauna Izzatu tayi serving dinsu. Lomar farko da zai kai bakinsa ta tuna masa
da Zuhra da ke daki tun jiya ko lekata baiyi ba. Tsaki tayi ya tura kujerarsa ya
tashi.

"Baby what is wrong?" Izzatu ta tambaye shi itama tana mikewa tsaye.

Sama ya kalla ya sake yin tsaki "zan kira yarinyar nan tazo taci abinci ne."

A take Izzatu ta hade rai. "Ka bari Tala ta mika mata mana. Ai ba sai kaje dakinta
ba."

"Hakkinta ne na ciyar da ita" yana fadin haka ya hau saman.

Ya kusa minti biyu kafin ya murda kofar ya shiga. Akwai kamshi dai saboda dakin
amarya ne sai dai zafi sosai duk da tagar a bude take. Ko meyasa bata kunna AC ba
oho.

A tsaye take tana jera kayanta a wardrobe har ta kusa gamawa taji an taba kofar.
Cikinta sai da ya bada sauti saboda tsoro. Ko da ya shigo duk rashin kunyar da taso
yi masa sai ta fasa saboda yadda ya cika mata ido. Bata taba kare masa kallo ba sai
yau. Da ace zaman lafiya suke yi da ta fada masa yadda yayi kyau. Shima ita yake
kallo. Riga da skirt tasa na atampa fuskar nan tasha farar hoda. Kana ganinta ita
daban fuskar ma daban. Ga hannun breziya ya fito ta kowane gefen hannun rigarta. Ya
dan tabe baki....kai kuma irin taka jarabawar kenan Hamza.

"Ke baki iya gaisuwa bane?"

Saurin durkusawa tayi tare da jin kunya.
"Ina kwana, an tashi lafiya"?

Bai amsa ba ya juya"ki sauko muyi breakfast".

Kafin ya kai kofa ta biyo bayan shi. Yunwa take ji sosai. Ace yau har shadaya saura
bata ci abinci

9 / 36