Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
saka masa kuka hawaye na
ambaliya a kumatunta. Rungumeta yayi yana shafa kanta...Cutie me ya sameki? Ki bar
sakar haka muje ki kwanta. Iya karfinta ta soma kokarin ture shi tana tura
baki....ni ka kyale ni idan nagama zan tafi na kwanta. Sake riketa yayi haba
Fadimatu fada min waye ya saka min ke kuka, waye yake son yau na hana shi bacci
tunda ya taba min Cutie.
Marairaicewa ta sake yi tace ba kaine ba....Ya dan ware ido, ni da kaina Cutie? To
fada min me nayi. Da yatsanta ta nuna masa lebenta da yayi ja amma yanzu babu
kumburin. Ya Salam Cutie am so sorry, dazu ne a asibiti ko? Kai ta gyada yace kuma
ka dena kulani duk da ina son baka hakuri akan abinda ya faru.
Shhhhhh ya fada tare da dora yatsansa a bakinta. Kiyi shiru Cutie babu laifinki a
dukkan abinda ya faru. Raina ne ya baci lokacin amma hakan bai zama dalilin da zan
share matata ba. Kice kin hakura.
Murmushi tayi tare da noke kafada. Yace please, please, please. Sake noke kafadar
tayi yace to tashi muje mu kwanta kinga shabiyu ta kusa. Abin sakar ta kama ka bari
wannan ce karshe saura kadan na gama.
Kusa da ita ya zauna har ta karasa tace gobe sai ya kai musu. Godiya yayi mata da
addu'a sannan ya kama hannunta suka tashi. Jikinta duk yayi tsami saboda zaman wuri
daya.
Sai da suka fito falo yace kince abinci kuwa. Tace a'a zata sha tea yanzu. Dariya
yayi duk kaunarki da abinci ki kare a shan tea lallai nayi laifi. To muje na soya
miki kwai kici da bread. Zuhra tayi dariya kaji ka Ya Hamza ka iya girki ne?
Hannunta ya rike muje kiyi kallo yarinya.
Kujera ya tura mata ta zauna sannan ya hada mata tea. Bayan ya gama ya dauko kwai
guda uku a fridge Zuhra tace biyu zata ci. Yace shima zai ci. Tana kallo ya dora
mai ya dauko maggi da cokali. Tana jira ya dauko roba ya fasa a ciki sai kawai taga
ya fasa a cikin frying pan din. Da sauri ta taso Ya Hamza wace irin suya ce wannan?
Bai kula ta ba ya barbada maggi kadan a saman ya dauko plate. Zuhra sai girgiza kai
take yi taga ya juya kwan daya barin ma ya soyu sannan ya juye a plate. Kinga suya
ba irin taki ba, muje falo kici ki ji.
Bata yarda zata ji dadin suyar tasa ba sai da ya tura mata a baki. Sai da cinye na
bakinta tayi murmushi tace da dadi....Hamza ya dauke plate din to kinci rabonki.
Rokonsa ta fara yi taga yaki kawo mata, wuri ya samu ya zauna yana ci. Ta zauna ta
soma kukan karya sai ya kawo mata. Tare suka karasa ci suna hira. Suna gamawa ya
kulle gidan yace to sai bacci.
A kofar dakinta tace masa zata je tayi wanka. Yace ke da kika gaji, muje ki dauko
kayanki a dakina zaki kwana. Duk abinda zata bukata shi ya dauko mata sannan suka
tafi dakinsa.
Kai tsaye ta shige toilet zata yi wanka. Ta gama tara ruwa mai zafi saboda
hannuwant da kafada duk sunyi tsami tana son gasa su taji an bude kofar. Wani irin
ihu ta saka ganin Hamza a tsaye daga shi sai dogon wando. Da sauri yaje ya toshe
mata baki da nasa. A haka ya karasa cire mata riga. Kuka take masa kamar wadda zai
yanka yayi murmushi kin fiye tsoro Cutie. Ni taimakonki nazo yi kike min kuka.
Hannunta ya kama tana ta harararsa ya sakata a cikin bahon sannan ya dauko karami
tawul ya saka a ruwan zafin ya danna mata a kafada. Wani ihun tayi ta mike zata
gudu ya riketa sosai. Kinga idan baki zauna ba matseki zanyi. Ki cigaba da hararata
sai idanunki sun fado.
Kunya taji ta dena harararsa. Kamar mai rada tace Ya Hamza ka dan rufe ido mana.
Ki dena magana ba'a son surutu a toilet. Daga nan duk kauce kaucenta haka ya gasa
mata jiki sosai sannan yayi mata wanka. A katon tawul ya nadota ido duk sunyi ja
saboda kuka. Da kansa ya shiryata sannan ya dauko wata katuwar shirt dinsa ya saka
mata. A bakin gado ya zaunar da ita shima yaje yayi wankan ya fito. Har ya gama
shiryawa Zuhra na tura baki. Cak ya dauketa suka kwanta ta janye jikinta can gefe.
Haka kawai kayi min wanka kamar wata yarinya karama. Ni bazan sake wanka a dakinka
ba.
Yana ji tana mita yayi dariya...zo na baki hakuri kinji my cute baby.
Matsawa tayi gefe yasa hannu ya janyota ta fado jikinsa. Fuskarta yake shafawa da
hannunsa daya yace duk abinda nayi miki kiyi hakuri harda wanda zanyi miki ma.
Tace wanne kuma.....bai barta ta karasa maganar ba ya katseta ta hanyar kissing
dinta da nuna mata soyayya irin wadda ya jima yana fatan zuwan ranar da zai nuna
mata. AL'ADUN WASU #68
Batul Mamman(Mrs)#
Babu irin yadda Hamza baiyi ba domin ya tashi Zuhra da asuba taki tashi. Ganin yana
neman rasa sallah yasa ya rabu da ita yaje yayi wanka ya tafi masallaci. Niyarsa
idan ya dawo sai ya sake tashinta.
Tana jin sautin rufe kofar ta yaye bargon jikinta ta tashi jiki babu kwari. Abinda
Ya Hamza yayi mata ne yasa ta tashi da wata irin kunyarsa, da wane ido zata sake
kallonsa ma. Shiyasa tayi shiru tamkar bata jinsa lokacin da yake ta kokarin
tashinta.
Dama ita bata iya jin ciwo ba ta rinka raki da koke koke kenan to yau an sami
maidalili. Da kyar ta iya zama cikin ruwan zafi sannan daga baya tayi wanka ta
fito. Don kokari harda dan fesa turare tunda an zama 'yan gayu sannan tayi sallah.
Zama ta cigaba tana azkar bayan ta idar taji har taji alamun antaba kofa.
Jiki na rawa ta tashi ta jefar da hijab dinta ta haye gado. Har kanta ta rufe ta
koma ta kwanta ko numfashin kirki bata yi.
Dariya ta bawa Hamza da ya kula tabbas tayi sallah bayan fitarsa. A gefenta ya
zauna yana mata magana a hankali.
Cutie bazaki tashi mu gaisa ba?
Shiru tayi babu amsa sai alamun tana kuka da yaji.
Da kyar ya iya budeta ya kwantar da ita a jikinsa. Yace dama matsalar irinku kenan
wadanda suke tashi babu wa babu kani. Kunfi kowa iya shagwaba. Yanzu duk kukan da
kika yi jiya bai isheki ba shine zaki tashi da wani sabon.
Tashi tayi suka hada ido tayi saurin juyar da kanta, to ba kai bane ina ta......
Yace na fa baki hakuri tunda wuri kuma me ya rage? Hmmm ko baki gane lesson din
bane da kyau. Ya fada yana kashe mata ido.
Murguda baki tayi ni bance ka koya min irin wannan ba.
Eyye, Cutie ashe baki dena tsiwa ba. Lallai ya kamata a maimaita karatun ko zaki fi
dauka. Irin wannan juya baki kamar idan na fara kissing kada na saki.
Ido ta rufe ta kwanta a jikinsa...ai nasan Ya Hamza yana da kirki bazai kara sani
kuka ba ko. Don Allah kayi hakuri na dena yi maka tsiwa.
A hankali yace gaskiya banyi miki alkawari ba. Ke ko irin addu'ar da maza ke yiwa
matansu da safe irin haka baki bari nayi miki ba sai korafi. Tashi zaune kiji
wannan kwanciyar da kike yi a jikina sake kashe min jiki kike yi.
Yadda yake magana yasa da saurinta ta tashi harda matsawa gefe. Hamza ya rinka
dariya...matsoraciya kawai. Sannan ya kama hannunta...nagode miki Allah Yayi miki
albarka Ya bamu zuri'a dayyiba. In sha Allah Zuhra zan rike ki amana kuma zan so ki
fisabilillah. Idan har nayi miki wani abu ba daidai ba ina so ki rinka fada ba ki
barshi a ranki ba muzo muna samun rashin fahimtar juna. Naso ace kinyi wanka a
gabana dazu domin nasani ko akwai gyara duk da nasan matar tawa tana da ilimi. Amma
kamar yadda naji wata malama Ummi Aisha tana fada yana da kyau duk miji ya san ko
matarsa ta iya tsarki.
Zuhra dai kunya duk ta isheta ta sunkuyar da kanta kasa. Hamza yace ina jinki fada
min yadda kika yi ko muje nayi miki da kaina. Sanin ba karamin aikinsa bane yin
hakan yasa ta soma yi masa bayani a hankali kamar wadda aka kamawa baki. Ya gamsu
sosai da amsar da ta bashi yace to yanzu me ya rage?
Zuhra tace naje kitchen nayi girki ko don asibiti...tana magana ta tashi da sauri
saboda su Junior da ta tuna.. .Ya Hamza su Khalifa yau bazasu school ba? Tashi ka
kaisu gashi har bakwai da kwata.
Murmushi yayi...kinsa miji a daki kina masa dadin baki ba dole ki manta da yaranki
ba. Ta tura baki ta fara jan hannunsa, don Allah ka tashi kada su makara yau. Yace
to laifin waye? Ko kadan bai damu ba harda kishingida akan pillow Zuhra tana ta
kokarin tayar dashi.
Gajiya tayi ta hakura bari naje kasa nasan Tala tayi musu wanka. Don Allah ka taso
kaji Ya Hamzana. Har wani fari take masa da ido duk don ya tashi. Sai da ya bari
taje kofa sannan ya kirata. Da sauri ta dawo amma hankalinta yana kan yaran da
tasan tun waccan alhamis din bayan dawowarsu daga Kaduna suka fara jarabawa.
A gabansa ta dan durkusa tana jiran taji dalilin kiran. Bakinsa ya nuna mata...yau
bamu gaisa ba. Idan kina so na tashi kizo mu gaisa. Kuma ki dena tafiya da sauri
sauri kafin kizo kina min raki anjima.
Kallonsa kawai take yi yadda yayi kwanciyarsa kamar bai damu da zuwan nasu
makaranta ba. Bakinsa ya sake nuna mata tace jiya fa kaji min ciwo har ya kumbura
ko ka manta? Dariya yayi ....you are not serious, duk abinda kika yi da bakin nan
jiya sai yanzu zaki tuna da ciwo. Ko dai kiyi abinda nake so ko yaranki su zauna a
gida yau.
Da sauri ta fada jikinsa saboda tana hangowa su Khalifa makara sannan ta hada
bakinta da nasa. A hankali Hamza ya rinka janta har ta saki jiki. Da kyar ta iya
tuna masa su Khalifa...yace don't worry sun gama exams jiya so bazasu school ba sai
ranar friday da zasuyi class party. Ta dan daki kirjinsa amma shine....bata sami
damar karasa maganar ba ya katseta da wani salon soyayyar tasa.
****
Sai shadaya saura ta samu Hamza ya kyaleta ta fito. Wanka ta sake yi ta saka wani
lace dinta mara nauyi. Dinkin yayi mata kyau riga da zani tayi kwalliya sai kamshi
take yi. Dakinsa ta fara shiga ta same shi zaune akan gado da laptop bashi da
niyyar tashi. Ya dago mata hannu alamun ta je wurinsa...Cutie kinyi kyau. Har nan
nake jin kamshink mai dadi. Murmushi tayi a kunyace tace ina daga nan Ya Hamza. Ni
yanzu ko hannunka tsoron tabawa nake yi. Yana daga zaune ya rinka dariyar
maganarta. Ka fada min me zaka ci ni yunwa nake ji. Kansa ya kada irin ya zama abin
tausayi tunda taki zuwa. Zaki kawo kanki ne yarinya. Yanzu dai ki hada min tea kuma
idan akwai sauran tuwon jiya ki dumama min.
Bata jima ba ta kawo tea din falonsa da tuwon suka ci sannan tace zata dora abincin
rana. Rabin cin abincin duk Hamza ke tsokanarta tana ta sunkuyar da kai. Can tace
ni har kunya nake ji ba'a kai abincin safe ba asibiti kuma duk laifinka ne. Ya
dauke kai su Mama sun aika shiyasa kika ga ban damu ba. Abincin ranan ma kiyi wake
da shinkafa amma da manja shi nake sha'awa yau. Zuhra tace to abincin asibitin fa.
Ya dan sha kunu, suma shi zasu ci ko akwai matsala ne? Zuhra tace babu, sannan ta
kwashe kwanukan ta sauka kasa. Amma a zuciyarta tana tunanin yadda mara lafiya zata
ci wake da shinkafa da mai duk da Izzatun ta fara cin abinci.
Kafin azahar ta gama komai na abincinta ta hada salad da kunun aya yasha kankara.
Su Junior duniya sabuwa sunji dadin abinci sai karawa suke yi. Bayan sun gama ta
shiryasu saboda Hamza yace tare dasu zasu je asibitin.
Sai da yayi sallah ya gama nuko nukonsa sannan ya fito suka tafi. Duk motsin Zuhra
akan idonsa jin kansa yake kamar sabon shiga a aure saboda irin son da yake yi
mata. Makarantun da suka bada aikin saka suka fara zuwa ya kai musu duk suka biya
suna yaba kyan aikin da saurin da akayi aka gama. Sai gashi ya tashi da dubu dari
uku da arba'in da hudu kudin da duka makarantun suka biya. A mota ya rinka yiwa
Zuhra addua yasa su Nana suce Amin. Bakinta kamar gonar auduga don farinciki saboda
yadda taga Hamza yayi murna. Har cewa yayi washegari zai karbo mata form ta cike
zai bude mata account. Dubu dari biyu da hamsin zai saka mata a cikin kudin sauran
suyi amfani dashi a gida. Tun a wurin tace bata yarda ba yace to abar magabar sai
sun koma gida.
*****
Duk magiyar da Raliya tayiwa Izzatu sam taki yarda taci abincin da aka kawo daga
gidansu Hamza da kuma na gidan Anti Larai tace tana jiran Hamza tasan duk tsiya
bazai barta da yunwa ba. Anti Larai dai ko kulata bata yi ba dama ba shiri take yi
da Izzatu ba. Tun su Hajiya na asibitin ake cewa taci taki cin komai har suka tafi.
Raliya tace ke yanzu banda baki da kunya yaushe zaki jira Hamza mutumin da kika
batawa rai. Kina kallo yau tun safe bai zo ba shi da yana kai yara makaranta yake
tahowa. Izzatu dai ta kafe bazata ci abincin ba dole Raliya ta kyaleta.
Sai wurin karfe uku suka iso asibitin. Su Khalifa ne suka fara shiga dakin da gudu
Hamza da Zuhra na bayansu. Shi ya dauko kwandon abincin ma sannan suka shiga dakin
yana rike da hannunta yana tsokanarta tana dariya.
Kiris ya rage Izzatu ta hadiyi zuciya sai dai ta hakura. Tunda yazo tasan baya iya
dogon fushi da ita. Wannan 'yar banzar yarinyar kuwa sai tayi maganinta.
Zuhra da Hamza suka gaisa da Raliya sannan Zuhra tayiwa Izzatu ya jiki. Kamar tayi
magana da dutse haka ta shareta. Khalifa yace Mummy baki ji Maama tana yi miki ya
jiki ba? Izzatu ta dan matse banji ba Khalifana. Junior ya dora hannuwansa biyu a
baki yace Daddy kaji Mummy tayi karya ko? To mai karya dai dan wuta. Mu duka a
dakinnan munji sai ke kadai. Hmmm, Maama fadawa Mummy idan jirgin aljannah yazo a
nan zamu barta. Hamza ya kwashe da dariyar mugunta yace haka ne Junior Allah Ya
shiryi masu karya. Yara suka ce amin. Ran Izzatu ya gama baci tace zuwa kayi ku
wulakantani kai da matarka? Shine zaku saka 'ya'yana ma su tsaneni ko. Zuhra ce
tayi karfin halin bata hakuri, shi kuwa Hamza dariya ya sake yi ya cigaba da wasa
da yaransa.
Raliya ta bude abincin zata zubawa Izzatu. Tana daga kan gado amma idanunta na ga
abinda mamanta ke yi. Kamar tayi kuka tace Mum me nake gani kamar wake da shinkafa.
Raliya tace shine kinji kamshin kayan salad ko? Tana bude man Izzatu ta sa ihu, Mum
manja ne fa. Raliya tace to sai me kike yamutsa fuska kamar kinga abin kyama.
A raunane Izzatu ta kalli Hamza,Baby wane irin abinci ne wannan kuka kawo min? Yace
irin abincin da muke ci ni da iyalina. Sai nanatawa take yi a ranta wake da
shinkafa. Basu taba yi ba tunda suka yi aure. Kamar tayi kuka tace ko dai ka sami
karayar arziki ne, shi kadai ne dalilin da zaisa a fara cin irin wannan a gidanka.
Junior ya dubi abincin da Raliya ta gama hadawa yayi kyau yace Mum ki bani inci,
Maama ta iya girki.
Izzatu tace haba ko da naji,ashe Zuhra ce ta dafa. Kaga irin abinda nake fada maka
ko. Yarinyar nan bazata ta taba wayewa ba. Kamar kai Baby aci wake da shinkafa a
gidanka sai kace wani talaka. Jikin Zuhra duk yayi sanyi.
Hamza yace Cutie ga key ku tafi mota da yaran ina zuwa. Tana fita ya zauna a gaban
Izzatu ya warware mata halin da yake ciki da irin gudummawar da ta bayar wurin
fadawarsa wanda yasa ta mugun mamaki. Ya mike tsaye...saboda haka Izzy ki kiyayeni
domin ko banyi aure ba ina gab da sakinki wallahi saboda kin jefani cikin tashin
hankali sannan dayake kinfi amara son biki kika tsallake kika barni. Izzatu tace
don ka sami matsala sai kayi min sharri? A take ya tuna mata duk abubuwan da tayi
wadanda sukayi sanadiyarsa fadawa wannan halin. Baki bude haka ya fita ya bar
Izzatu da Raliya don ma bai fada musu yadda Zuhra ta taimaka masa ba. AL'ADUN WASU
#69
Batul Mamman(Mrs)#
Daga asibitin gidan 'yan uwansa mata suka wuce. Dukkaninsu sunyi farincikin ganin
Zuhra kowacce tana janta a jiki. Daga nan suka je gidan Anti Faiza wadda ta rasa
inda zata sa kanta don murnar ganin Zuhra da Hamza tare. Dabarun kula da miji ta
sake karanta mata da kyau sannan na karshe suka je gidan Ibrahim. A nan suka ci
abincin dare sannan suka taho bayan Hamza da Ibrahim sun dawo daga sallar isha.
Kafin suje gida su Khalifa duk sunyi bacci sai Hamza da Zuhra ke ta hira. Kayan da
suka biya suka siyo Zuhra ta iya dauka yaran kuwa Hamza ne ya dauko su. Dama sauri
take su iso gida gabadaya bata jindadin jikinta tun yamma daurewa kawai take yi
tana tafiya.
A dakinsu ya kwantar dasu Zuhra ta fadawa Tala taje ta kwana dasu sannan ta hau
sama. Tana tafiya Hamza na binta da ido, jan kafa kawai takeyi tana tafiya da kyar.
Tun yamma ya kula da yadda tafiyarta ta canja amma idan taga mutane sai ta daure ta
rinka tafiya daidai tana bata rai. Girgiza kai yayi saboda yasan meye matsalarta.
A dakinta ya sameta tana daura tawul zata yi wanka yace ta jira shi yana zuwa. Turo
baki tayi ...Ya Hamza don Allah kada kace zaka yi min wanka yau ni bama ni da
lafiya. Yace to Allah Ya sauwake, maganin ciwon naki zan baki. Idonta har ya fara
kwalla tace kasan me ya sameni ne? Cike da tausayawa yace na sani Cutie, bari ki
gani ina zuwa.
Toilet dinta ya shiga ya tara ruwa mai zafi sosai a katuwar roba ya sirka shi kadan
sannan ya fito ya cire rigarsa ya bar singlet yace muje. Duk ta gama tsorata ta
fara ja da baya. Bai tsaya sauraronta ba ya dagata tanata dukansa. Tawul din kawai
ya zare ya sakata a cikin ruwan zafin. Ihun da tayi yana tsammanin har maigadi sai
yaji domin ba wutar inji bace bare ya rage sautin karar.
Zuhra kuka take yi sosai tana kokarin tashi Hamza ya tsaya daga bayanta ya danna
kafadunta. Ya Hamza akwai zafi sosai.
Na sani kiyi hakuri, son jiki irin naki yasa baki shiga ruwan zafin tun da safe ba.
Yayi 'yar dariya... Yau duk mai hankali kin gama tona min asiri a wurinsa da wannan
tafiyar taki.
Sharkaf haka fuskarta ta jike da hawaye tace na shiga ruwan zafin da asuba.
Hannuwanta ya rike da take neman tashi tsaye yace nasan kin shiga ruwan da kika
gama sirkawa ba. Wannan idan kika haihu da kaina zan miki wankan jego don kada ki
cuce ni.
Muryarta har ta soma dashewa tace