Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
jikinsa Izzatu ta zauna tana ta wani
shige masa. A haka Zuhra ta shigo ta same su. Tamkar tasa ihu haka taji. Hamza yayi
ta kokarin ture Izzatu tana kara manne masa. Karshe da yace ta dan matsa sai da
tayi masa kiss a kumatu ta matsa gefe. Yana kallon sanda hawaye ya zubo daga idon
Zuhra tayi saurin gogewa. A take yaji tausayinta ya kama shi kamar yaje ya dauketa.
Gyaran murya yayi sannan ya fara da ambaton Allah kafin ya sanar dasu dalilin
kiran.
Duk su biyun yake kallo yace...kamar yadda kuka sani duk wani magidanci yakan tara
iyalinsa a lokacin da ya kara aure domin ya sanar dasu abinda yake bukata daga
garesu na dangane da zaman lafiya a gidansa. Kowacce a cikinki sadaki na biya na
aureta saboda haka babu wadda zan wulakanta kuma bazan yarda wata cikinku ta
wulakanta ta ba. Abubuwa da dama sun faru tun kafin auren nan har zuwa yanzu amma
ina fata mu manta da komai mu gina rayuwarmu bisa doron addini. Zaman lafiya da
kwanciyar hankali nake bukata daga gareku ni kuma in sha Allah zanyi kokarin yin
adalci a tsakaninku. Sai maganar rabon kwana....
Izzatu tayi saurin katse shi...rabon kwana ai ba sai anja zance ba a rinka yin sati
sati...
Da sauri Zuhra ta dago suka hada ido da Hamza. Ko batayi magana ba yasan yadda ya
hango shirme a shawarar Izzatu itama haka ta gani...Izzy sati daya yayi yawa,yadda
muka saba ji anayi muma haka zamuyi wato kwana bibbiyu.
Izzatu tace to naji amma sai an rama min kwanakin da nayi da bana nan. Ga sati
biyun zuwa Kaduna da Abuja sannan ga kwanakin zaman asibiti tara.
Hamza yace wannan sunansa lalura saboda haka ki manta dashi kawai. Gobe Cutie zata
karbi girki and that is final. Sannan babu takura kowa zata yi girkinta. Wadda take
da girki zata yi dani da su Khalifa da masu aiki. Abu na karshe dole mai girki tayi
breakfast kafin tara ya zama ready, abin rana kada ya wuce azahar sannan na dare
kada ya wuce magriba. Akwai mai tambaya?
Zuhra tace babu, ina iya tafiya?
Hamza yayi murmushi yana kallon rigima ta Zuhra. Ita da gaske fushi take yi
dashi...to idan babu ni ina da abin fada. Nan ya sanar dasu sakon da ya samu daga
wurin minister.
Wani ihun murna Izzatu tayi sannan ta haye cinyarsa ko la'akari da Zuhra bata yi
ba....ni nasan abinda yafi wannan ma zaka iya Baby. Am so proud of you.
Tana ta kankame shi wani abin ma da gayya take yi Zuhra ta tashi don bazata juri
kallon wannan kayan bacin ran ba. Tana fita Izzatu tayi dariya a ranta tace yarinya
baki ga komai ba. Hamza dai tureta yayi yabi bayan Zuhra.
*****
A kan kujerar dakinta ya sameta tana kuka. Ya rufe kofar harda saka key ya dawo
kusa da ita ya zauna. Jikinsa ya janyota ta ture shi. Hannuwanta ya kama yace kalle
ni nan Cutie.
Bata iya masa musu ta dan daga kai amma bata kalli cikin idonsa ba.
Yace idan kina irin wannan kishin to kishiya ta gama dake. Wa ya fada miki ana
share miji saboda kishi? Baki san sai nayi fushi ba nima na dena kulaki. Wadda tafi
kulawa dani sai na tare a wurinta ke kuma sai lokacin da naga dama zan nemeki.
A dan tsorace Zuhra tace...Allah ko? To ya zanyi Ya Hamza?
Cike da tausayinta ya dorata a cinyarsa tare da rungumeta a jikinsa...kinsan wani
abin yi za'ayi kawai don kiji haushi saboda haka ko anyi kiyi kamar baki gani ba.
Sannan ki yawaita addua Allah Ya rage miki kishin da zai cutar dake. Ranar da nake
tare dake kuma kema sai ki dage wurin kyautata kin yadda zanyi ta tunaninki koda
bama tare.
Murmushin jindadi tayi...nagode Ya Hamzana..dazun ma kune kuke ta wasu abubuwa a
gabana. Don Allah ai kaga dole naji babu dadi.
Fuskarta ta rike a tsakanin tafukan hannunsa...nasan fushin duk na meye bari kema
na baki rabonki.
Matsowa taga yayi yana neman hade bakinsa da nata tayi saurin sa hannu ta tare. Ya
Hamza babu kyau irin wannan fa. Yanzu idan gobe kayi min haka bansan irin kukan da
zanyi ba...ta tashi tsaye ka koma wurinta amma gobe..sai ta kasa karasawa.
Dan bakinta ya shafa yace gobe zaki fanshe kwana biyun nan ko yana daga mata gira.
Ita dai bata ce komai ba ya fita. Tsalle tayi ta dire akan gado tana hango zuwan
gobe. Tana juyinta cikin murna text din Hamza ya shigo wayarta. Sanar da ita yake
ta fara shiri da ita zai tafi Lagos ranar litinin.
Kasa boye murnarta tayi wanda duk abinda Izzatu tayi mata ya dena tsaya mata a rai.
Washegari da ta karbi girki kuwa banda sauran mutan gidan da suka san anyi canji
Hamza yaga soyayya daga Zuhra irin wadda bata taba nuna masa ba. 'Yar kunyar nan da
take hanata sakewa gefe ta ajiyeta na wannan lokacin. A wannan kwana biyun ko
sabuwar amarya taga su Zuhra sai ta kara kallo.
An turowa Hamza kudin jirgi shiyasa da kudin hannunsa ya biyawa Zuhra. Tunda a
hotel zasu zauna yasan dai zata sha kadaici idan ya fita amma duk yamma zuwa dare
zasu kasance tare. Ana gobe zasu tafi ya bata kudi yace taje tayi kitso da kunshi.
Unguwarsu tace zata je shiyasa ya kaita gida da kansa.
Bakin Umma ranar kamar gonar auduga. Zuhra tayi fes da ita kamar ba ita ba. Suna
tare har Baba ya dawo. A tsakar gidansu aka kira mai kunshi tazo ta rangada mata
mai kyau. Safara'u 'yar wan Baba da take zaune a gidan yanzu ita tayi mata kitso
kanana mai kyau bayan ta wanke kan. Sai dare da Hamza yazo daukarta yake sanar da
su Baba zancen tafiyar. Yasha addua da fatan alkhairi. Har gidansu Hajara sai da
suka shiga dashi ya gaishe da su Mama sannan suka wuce gida.
Izzatu ta gama yanke shawarar biyawa kanta kudin jirgi ta bi Hamza. Har kaya ta
gama hadawa ta ajiye kusa da jakar kayansa wadda Zuhra ta hada ranar da zata fita
girki. Surprise zata yiwa Hamza idan ya dawo yau. Tasan dole yaji dadi tunda ya
sauko ya dena fushin da ita. Bata san kokarin ya kamanta adalci tsakaninta da Zuhra
yasa taga saurin shiryawarsu ba.
Da suka dawo kowa dakinsa ya nufa. Izzatu ta kawo masa abinci yaci sannan yake
tambayarta game da jaka da ya gani kusa da kayansa. Da dan murmushinta tace kayana
ne na tafiyarmu gobe.
Ba shiri ya tashi yana kallonta. Wane irin kayan tafiyarmu gobe? Ni nace zan tafi
dake ne ko me?
Izzatu tace kwantar da hankalinka zan biyawa kaina kudin jirgi. Shiyasa ban fada
maka ba saboda nasan zaka ji dadi idan na fada lokacin da baka tsammani.
Hamza ya hade rai...to kinyi kuskure da Zuhra zani....
A fusace ta tashi itama...wallahi baka isa ba Hamza. Ni zaka rinka wulakantawa akan
wannan yarinyar. Shekararta ashirin da daya fa har zaka hada ta da mace kamar ni.
Kuma meyasa baka fada min ba da wuri?
Girgiza kai yayi yana mamakin yadda take daga masa murya. Ban fada miki ba saboda
gudun kada kizo ki tayar min da rigima kice sai kinje. Amma naga alama hakan ya
zama kuskure. Ki zauna a gida ki karasa jinyar jikinki lafin mu dawo. Kuma bana son
cigaba da maganar nan don banyi niya ba saboda haka idan wata tafiyarar tazo sai
nayi dake idan naga dama.
Ficewa tayi daga dakin ta tafi dakin Zuhra rai a bace ta buga kofar da karfi tana
masifa....Zuhra ki kiyayeni wallahi. Ki bar ganin na kyaleki lokaci na baki kafin
na koreki daga gidan nan.
Hamza da yake bayanta yace tunda ki kike auranta ba. To kema ki kiyayeni wallahi ko
gobe mu tafi airport tare ki koma gidanku. Kada ki kaini bango Izzy darajar 'ya'ya
kawai kike ci kema kuma kin sani.
Zuhra dai kallonsu take daya bayan daya ta kasa magana. Tana kallo Hamza yaja
hannun Izzatu suka fita. Ranar basuyi baccin arziki ba saboda yadda take ta fada.
Sai da Hamza yace idan ta saki bude baki a bakin igiyar aurenta. Cikin masifa tace
guda nawa? Yace sai kinyi maganar zan sanar dake ko nawa kika tsinke. Ba arziki ta
yi shiru amma ta gama sikewa da Zuhra. Dole tasan yadda zata yi da ita kafin tayi
sanadiyar kashe mata aure.
Tun bayan asuba Zuhra tayi wanka ta gama shiri saboda Hamza ya fada mata jirginsu
karfe bakwai zai tashi.
Shima da wuri ya shirya ya shiga dakinta. Sai kai kawo take yi a tsakar daki. Tana
ganinshi ta gaishe shi yace wannan tafiyar ta meye? Kinci abinci kuwa? Zuhra tace
wane irin abinci Ya Hamza? Cikina sai kullewa yake saboda fargaba. Anya zan iya
shiga jirgin kuwa. Yayi dariya idan bazaki iya ba sai na tafi da yayarki.
Jin haka Zuhra ta fita daga dakin da sauri har tana tuntube. Shi ya dauko mata
akwatin kayanta yabi bayanta.
Da kyar ya samu tasha tea duk hankalinta baya jikinta. A tsorace kawai take da
maganar shiga jirgi. Basu dade ba Nura yazo daukarsu shi zai kai su airport din.
Har suka fita Izzatu ko kofar daki bata fito ba.
Ana shiga airport Zuhra na kara razana. Gabadaya a tsorace take. Hamza kuwa sai
dariya yace yau ga 'yar kauye ga jirgi. Kamar tayi kuka tace Ya Hamza ko dai mu
tafi tasha ne mu sami mota. Ya kama hannunta ya rike....Cutie kada ki damu babu
inda zanje in barki kinji ko. A hankali ta gyada kai.
Cikin dan lokaci ya karbar mata ticket suka fita inda jirgin yake. Layi suka bi
tare da wasu masu tafiyar. Zuhra sai kallo wai ita ce yau zata shiga jirgin sama.
Ga wasu manyan jiragen da suka fi wanda zasu shiga ma. Tana rike da hannun Hamza
tace kuma yanzu a iska dreban jirgin yake gane hanya ko akwai alama da ake sakawa
yadda bazasu bata ba? Yace wurin tukin nasu ne yake aiki da na'ura mai kwakwalwa
tana nuna musu hanya sannan daga can airport dinma ana yi musu bayani... Suna shiga
ciki har suka zauna ya daura mata seat belt yana mata bayanin yadda jirgi ke tafiya
a sama. Kusa da taga ya zaunar da ita shi kuma yana gefe. Sai da ya gama bayaninsa
tace ni dai duk bangane ba. Hamza ya ja mata kunne,amma shine kika barni ina ta
surutu ko?
A hankali jirgin ya fara tafiya a kasa cikin Zuhra ya murda don tsoro ta kankame
Hamza. Ihu taso yi lokacin da ya fara tashi har ta bude baki yayi saurin rufe shi
da nasa. Bai kyaleta ba sai da yaji sun daidaita a sama.
Da sauri da sauri take fitar da numfashi ta dan bata fuska Ya Hamza muna cikin
wannan yanayin wa yake ta soyayya? Sai da ya ja hancinta sannan yace ai magana ta
kare tunda soyayyar ta hana ki cikawa mutane kunne da ihu. Harda wani kara lafewa a
jikina,kai wannan yarinya kin zama abinda kika zama. Kunya taji da kawar da kanta
tana kallon waje.
Daga nan hirar ta koma ta abubuwan da take gani. Suna haka aka kawo abinci. Zuhra
tace kaji fitina har mutum yana da nutsuwar cin abinci a nan. Hamza yayi dariya yau
yaga shirme wurin Cutie kala kala. Har dan bacci tayi wanda ta farka lokacin da
jirgin ya fara sauka kasa.
Taxi suka samu zuwa hotel din da aka ce suje ana ya hadu da wasu mutum biyu da suma
basu dade da zuwa ba suka gaisa. Mukullan dakunansu aka basu sannan mutumin da aka
turo wurinsu ya sanar dasu karfe goma mota zata zo daukarsu saboda a yau zasu fara
abinda ya kawosu.
Sai da Hamza ya tabbatar Zuhra ta sami nutsuwa sannan yayi wanka ya shirya. Kashedi
yayi mata kada ta bude kofar sai karfe daya lokacin da yayi magana da receptionist
za'a kawo mata abincin rana. Kamar kada su rabu lokacin da zai fita. Tayi ta masa
addua sannan suka yi sallama.
Hajiya Izzatu har karfe uku bata fito daga daki ba. Tala ce tayi komai. Wayar
kawarta wata baturiya Laura ta kira ta sanar da ita halin kuncin da Hamza ya sakata
a ciki. AL'ADUN WASU #72
Batul Mamman(Mrs)#
Laura ta gama jin korafin Izzatu tayi tsaki tace....
Duk laifinku ne 'yan Nigeria. Kuna bawa iyayenku mahimmanci fiye da yadda ya
kamata. Na tabbata duk abinda mijinki yake miki yanzu don ya faranta musu ne.
Izzatu tace hakane amma kinsan mu addininmu da al'ada duk basu yarda da rashin
biyayya ga iyaye ba.
To ai kuwa bazaki dena ganin bacin rai ba Izzy...Laura ta fada tana kara jin
haushin al'ada irin ta hausawa....idan baki manta ba sai da nace kada ki yarda kuyi
aure. Ku zauna tare ku haihu kamar yadda nayi. Duk lokacin da kika gaji dashi ki
tattara ki bar masa gidan amma kika ki. Shawara daya zan baki shine kice ya zaba ko
ke ko iyayensa da wannan matar da ya auro. Ni kinga mahaifiyata ce bata son Phil
kinga tuni na yakiceta. Sai karshen shekara muke haduwa a wurin anniversary din
mutuwar babana.
Izzatu tayi kasake tana jin gurguwar shawarar Laura. A ranta tace duk ranar da ta
bawa Hamza wannan zabin to ko minti biyar tasan bazata kara a gidan ba. Su turawa
basu san al'adunmu akwai bambanci ba. A gurguje tayi sallama da Laura domin ta
fuskanci shawararta tamkar ta kama kafar wala ne. Dole ta sake sabuwar shawara amma
zaman Zuhra a gidan nan bazarana yake ga igiyar aurenta.
******
Kullum karfe goma Hamza yake fita sai takwas na dare yake dawowa. Kafin ya dawo
Zuhra zata wuni bacci amma yana dawowa to fa sai a bude soyayya. Zamansu suke
lafiya cike da kwanciyar hankali. Basu da wata damuwa sai ta junansu. Kullum dai
zai kira Izzatu kuma zai gaisa da 'ya'yansa. Rashin lokaci yasa bai sami damar kai
Zuhra ko'ina ba. Amma ita kasancewarsu tare ya isheta shiyasa bata damunsa da su
fita.
Ranar da zasuyi jarabawa Zuhra tayi ta masa addua. Karfe uku ya dawo ranar ya
dauketa suka sami taxi suka fita gari. Shine har bakin ruwa(beach)ya kaita. Suka
dan zagaya kasuwa ya siyawa Zuhra kananan kaya masu kyau don yaga bata dasu sosai.
Wata rigar idan ya dauko sai taji kunya.
Asabar da lahadi ma duk yawo ya kaita sai ranar litinin suka biyo jirgin safe suka
koma Kano. Wannan karon kauyancin Zuhra ya ragu. Nura ne ya sake zuwa daukarsu amma
sai da ya biya gida ya gaisa da iyayensa sannan suka wuce nasu gidan.
Tun asuba Izzatu tasa Tala guaran gida ita kuma aka shige kitchen girkin tarar
maigida. Tana jin tsayuwar mota tun daga bakin kofa ta taresu ta kankame Hamza tana
murna. Kiss take zuba masa ko ta ina a fuska ga Nura a bayansa dauke da jaka sai
kawar da kai yake sannan ga Zuhra da ta hade rai. Izzatu tayi dariyar keta, ko babu
komai tasan Zuhra bazata iya yin abinda tayi ba. Shi kanshi Hamzan yanzu sai da
yaji kunya sabanin da da suke abinsu hankali kwance.
Ko zama baiyi ba taja hannunsa suka tafi daki tana fada masa yadda tayi missing
dinsa. Zancen yaya aikin da ya kaishi kuwa ko a waya bata yi. Bata da zance sai na
korafin ya tafi ya barta.
Haka rayuwa ta kasance musu kowacce ranar girkinta tana kokarin farantawa mijinta
rai. Kwanansu biyar da dawowa Hamza ya sami sako cewa yayi na uku a jarabawarsu ana
bukatar ya kai passport dinsa Abuja ofishin minister domin neman visa. Da
farincikinsa ya sanar da Izzatu saboda ranar girkinta ne. Tana jin haka ta tashi ta
nufi dakinta.
Hamza ya bi bayanta da sauri don ya zata wani abin ne ya faru...Izzy saurin me kike
yi haka ko gama sauraron abinda nace bakiyi ba?
Wardrobe ta bude ta janyo wata jaka sannan ta fuskance shi...naji abinda kace mana.
Sai dai Sweety nasan ba abin mamaki bane idan kayi nasara saboda I believe in you
my darling. Kayana zan hada na tafiyarmu Abujan....ta daga jakar sama, kana ganin
wannan zata isa ko tayi kankanta?
Rasa bakin magana yayi sai binta yake da ido kamar lokacin ya fara ganinta. Babu
godewa Allah, babu taya shi murna sai jaka da ta dauko zata hada kaya bayan shi
kanshi bai sami cikakken bayani game da tafiyar ba. A kalla jakar zata dauki kaya
bakwai zuwa goma idan an cusa su sosai. Ko ya fada mata a Abuja zasu yi course din
ne bai sani ba. Haka ya fita ya barta ba tare da ya bata amsa ba ya tafi dakin
Zuhra.
Kulu ne tumuli guda a gabanta tana warewa saboda ya samar mata wata makarantar sun
bada kwangilar sakar rigunan sanyin makaranta.
Da murmushi ta tarbe shi tace Ya Hamza ba na hanaka satar kwana ba? Shima murmushin
yayi ai kece satar kwanan. Ace mutum bashi da ikon ganin matarsa sai ranar
girkinta.
Kusa da ita yaje ya zauna ya kama hannunta ya rike.
Cutie albishirinki? Idonta a kan fuskarsa tace goro Ya Hamzana.
Me zaki bani idan na fada miki?
Duk abinda kake so indai baifi karfina ba.
Ya shafa lebenta da yake kyallin lip gloss da ta saka mai kyau...so nake ki soni
har abada kuma kada ki taba rabuwa dani.
Maganarsa tasa jikinta yayi sanyi saboda ta lura kamar yana cikin damuwa. A
hankali tace Ya Hamza har a aljanna ni matarka ce in sha Allah. Amma nan...ta nuna
lebenta...kai dashi sai jibi. Tana magana tana masa dariya. A hankali ya rinka
sakewa. Dama bacin ran abinda Izzy tayi masa ne.
Cutie nayi nasarar cin wannan jarabawar har ana bukatar ganina a Abuja. Da murna
Zuhra ta rungumeshi tana cewa Alhamdulillah. Can sai ta sake shi ta durkusa tayi
sujjadar godiya ga Allah SWT. Tayi kusan minti biyu tana hamdala da takbir. Ko da
ta dago kanta wasu zafafan hawaye ne suka sauko daga idanun Hamza. Kullum Zuhra
daban yake ganinta.
A tsorace ta tashi yana daga zaune ta rungumeshi a kirjinta. Murya a raunane tace
Ya Hamza me yasa ka hawaye?
Muryarsa a can kasa yace Cutie ina sonki. Ina sonki. Ina sonki. Kuma nagode miki
for being who you are.
Sake kankameshi tayi tace nima ina sonka Ya Hamza. Uhmm sai dai dan turancin nan na
karshe kace who you are ko.. Toh, I am Fatima Bashir.
Mai Hamza zaiyi in ba dariya ba. Zuhra tayi kicin kicin da fuska ita tayi fushi.
Hamza ya rike habarta haba my darling Zuhra? Kada kiyi fushi dani. In sha Allah
idan komai ya daidaita na wannan course din da za'a turani zamu fara English
lessons dake. Dole na ware lokaci na koya miki da kaina.
Zuhra ta turo baki ni bazan koya ba kuma ka tashi ka koma dakinka ni munyi fada.
Cakulculi Hamza ya rinka yi mata har ta soma dariya sannan ya fita zuciyarsa fari
kal.
Washegari da safe ya sami cikakken bayani game da zuwansa Abuja. Da yake abin na
gwamnatin tarayya ne kuma da izininsu kwana biyu aka ce zasu yi a tantance su. Babu
wani zancen masauki alamun kowa yayi ta kansa kenan. Harda dariyar mugunta ya
fadawa Izzatu basu da masauki saboda haka bazai tafi da ita ba. Kila yaje gidan
abokinsa ya kwana. Itama dariyar tayi tace ta riga ta sanar da iyayenta batun
zuwansu har an gyara musu wurin kwana a gidansu. Baiji dadin wannan karambanin ba
shiyasa yace mata baza shi ba. Ko minti ashirin basuyi da maganar