Advertisements
Chapter 16 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   16 / 36

45K to 48K   out of 106K words

na taya mijina neman aljanna ta hanyar kyautatawa
iyayensa da sauran ayyukan kirki. Kaga yanzu kafin ka sake ni ko dan yaya sai nayi
abinda tace ko? Sai kuma ta rufe baki da hannu daya...ka ganni ko? Umma cewa tayi
ba fada maka zanyi ba sai dai ka gani a aikace. Don Allah kada kace na fada. A
shagwabe take masa maganar wadda tayi matukar tasiri a ransa. Har wani dan dukan
bakinta take yi ita a dole tayi laifi. Allah kadai Yasan farincikin da Hamza yaji a
wannan lokacin. Yau shine da matar da take nuna damuwa akan mahaifiyarsa fiye
dashi. A wannan lokacin gani yake Zuhra tafi masa kowace mace. Bai yarda sonta yake
ba amma a shirye yake ya kyautata mata iya karfinsa...a hankali take samun masauki
mai daraja a zuciyarsa. Ido ya zuba mata kawai yana kallonta. Ita kuwa kuwa tana
kare maganarta tayi gaba da flask din ba tare da ya tareta ba.

A dan plate ta zuba daidai yadda zaici ta hada sauran wuri daya. Takaici ma take
bata sani da wuri ba ai da tayu mai yawa. Naman da ta soya ta diba ta zuba a kai
saboda farfesun tayi shi da yaji tunda Hamza na mura.

Tunda Zuhra ta fita yake ta kai kawo....ya tsani ta tayar da maganar sakin.
Shigowarta tasa ya sami wuri ya zauna ta mika masa plate din. Jan hannunta yayi ya
zaunar da ita a gabansa. Nasan kin fini jin yunwa ki ci ni ga nawa abincin ya nuna
mata farfesun....cikinta har wani kullewa yake ta yi murmushi da gaske ka bar min.
Hamza yace eh...plate din ta janyo gabanta ta soma ci da sauri. Ya kama hannunta
lesson two yar kauye, ki dena cin abinci da sauri kuma banda katuwar loma. Ta danji
kunya sai tace to yaya zanyi? Dan madaidaici ya diba a spoon din ya nuna mata. Tace
dama Babana yace kada nayi loma a gabanka...Allah Yasa na iya denawa dai. Amma meye
kake cewa lesson one da two? Kallonta yake ya rasa me yake ji game da ita so nake
ki zama yar gayu kafin lokacin rabuwarmu, yadda zan dena kiranki yar kauye. Washe
baki tayi da gaske don Allah? To ai da ka fada min da wuri yadda zan kiyaye duk
abinda ka gyara min. Rabin abincin taci ta ture plate din ni na koshi. Hamza yace
don nace ki rage loma? Yamutsa fuska tayi a'a cikina ne ya kulle tea zan sake sha.
Sannu yayi mata sannan yaja plate din ya ci sauran tare da shan farfesun. Kamar
kullum yau ma abincin Zuhra yayi dadi. A zuciyarta kuwa dadi taji ta bashi dambun
saboda tana ganin irin kallon da yake yiwa abincin tunda ta soma ci.

Yana gamawa ta hada masa wanda zai kaiwa Hajiya a wata yar jaka ta bashi. Yace to
daga can zai biya office. Har ya isa gidansu ko na sakan daya bai dena tunanin
Zuhran Baban yara ba.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #49

Batul Mamman(Mrs)#




Da yake weekend ne a falo ya tarar da mutan gidan suna kallon wani shiri da akeyi a
Sunna TV. Kannensa suka gaishe shi ys amsa da sakin fuska. Sannan ya gaishe da
iyayensa. Mama tace Yaya yau ina office din? Zama ya fara yi sannan yace mura ke
damuna amma tayi sauki. Yanzu ma can zan wuce, aiko ni aka yi wurin Hajiya. Hajiya
tace ni kuma? Jakar hannunsa ya tura mata gabanta gashi inji Zuhra. Hajiya dai
kunyar bude jakar tayi Mama tace kaga Yaya miko min nagani.

Kowa a falon zuba ido yayi yaga abinda ke jakar sai ga Mama ta fito da food flask
mai kyau. Tana budewa dambun shinkafa ne ke kamshi mai dadi. Muryarta a shake kamar
tayi kuka tace Adabiyya, Nura, Hamida ku shiga ciki. Ba musu suka tashi suka barsu
su uku a falon. Mama ta turawa Hajiya flask. Kinga abinda ke ciki kice wani abu.
Murmushi Hajiya tayi nagani Mama amma me zance? Ga mamakinsa duka su biyun hawaye
sukeyi. Hankalin Hamza yayi matukar tashi ya fara basu hakuri. Mama tace Yaya ko
kasan tunda kayi aure abincin gidanka bai taba shigowa gidan nan ba sai yau. Kasan
gidan iyayenka babu yunwa amma a tamu al'adar lokaci zuwa lokaci mace takan yi
girki na marmari ko da da sallah ne ta aika gidan surukanta. Irin haka yana sa
iyayen miji su so matar musamman idan tana da tarbiyya. Shima mijin indai yasan
kimar iyayensa dole matar ta sake samun wuri a zuciyarsa. Hannuwansa ta kama gam ta
rike...Yaya yanzu kayi aure, nasan zaka ga kamar muna kin Izzatu amma ko kai shaida
ne akan bambancinsu da Zuhra. Kwalla ce ta cika masa ido shima ya basu labarin
yadda akayi ya kawo dambun. Hajiya dai kasa rike kukanta tayi ta tashi ta bar
falon. Ashe tana da rabon ganin Hamza ya auri macen da zata saka shi a hanya..Allah
Yayi mata albarka. Ko ba'a fada ba tasan shima ba karamin dadi yaji ba.

Tana tafiya Mama ta share hawayenta. Yaya ka rike Zuhra amana Alhaji bai maka zaben
tumun dare ba. Idan ka cutar da 'yar mutane saboda dalilin da ya jawo aurenku Allah
zai kamaka da hakkinta. Tana gama magana tace jirani ina zuwa. Kafin ta dawo Hamida
tazo tace Yaya gobe bayan laasar zamu zo ni da Adabiyya muyi weekend. Yace to Allah
Ya kaimu.....shikenan zasu zo su takura masa idan yana tare da Zuhra. Shima weekend
din yake jira yini biyu a gida ba fita.

Mama dakinta ta tafi ta dauko dubu sababbin dari dari ta bawa Hamza ya kaiwa Zuhra
tukwici. Tunda yake bai taba tunanin irin haka na faranta zuciyar iyaye ba sai yau.
A hankali yace God bless the day I met you Fatima. Allah Yayi miki albarka. Ko
flask din bai jira ba ya fita ya tafi office. Duk aikin baya masa dadi so yake yaji
muryar Zuhra tana masa shirmenta ko shagwaba. Har mamakin kansa yake, ga babban
abin kunya bashi da numbar wayarta ma. A lokacin ya tuna wayar tata tana da
matsala, bayan sun gama cinikin filayensa da wani dillali ya tashi. Beirut road ya
wuce ya siyo wata sabuwar waya kirar Samsung mai kyau. Nasa tukwicin kenan na
abinda Zuhra tayi masa yau. Daga nan ya biya wani shago yayi yar siyayya ya tafi
gidansa.

Yana ajiye mota ko gida bai shiga ba ya fita masallaci saboda a hanya yaji kira.
Can ya zauna har aka yi sallar Isha sannan ya dawo ya shigo da kayan da ya siyo.
Duhun da ya gani ya tuna masa bai nemi wani maigyaran injin ba gashi har dare yayi.
Zuhra ce ta fado masa ita da ko wayar kirki bata da ita. Nemanta ya shiga yi daki
daki baiji motsinta ba. Abin ya bashi mamaki ko bacci take yi ne? Yana hawa sama
tana fitowa daga dakinsa da fitila a hannu daya, daya hannun kuma tsintsiya ce da
abin kwasar shara. Har ajiyar zuciya yayi, ita ta fara magana tace sannu da zuwa.
Murmushi yake yauwa yar kauye. Me kike yi da tsintsiya a duhun nan? Tsoro na rinka
ji ni kadai sai kawai na fara shara da wankin bandaki. Amma dai ban bata maka rai
ba da na shiga dakinka ko? Naga yanzu kana min kirki shine nace bari nima na gyara
maka daki. Bai amsa mata ba sai da yazo gabanta...baki yi laifi ba yar kauye,
nagode. Ki je kasa akwai kaya a falo ki kai kitchen dinki bari nayi wanka.

Bai shiga dakin ba sai da ta saukq kasa. Dadi yaji sosai har da turaren wuta ta
saka. Ta gyara gadon tayi shara. Toilet din ma ta wanke shi tas har boxers dinsa da
vests da suke cikin wani abin zuba kayan wanki duk ta wanke amma bata shanya ba
saboda wurin shanyar yayi mata tsaho. Sau uku take niyar wankewa sai ta fasa wai
kada yace bata da kunya. Sai daga baya ne ta daure zuciyarta ta wanke su harda
kawar da fitilar gefe ita bata kalla ba bare ace mata 'yar iska.....

Ba jimawa ya sauko yace mata tayi girkin dare ne tace a'a amma zata dora yanzu. ki
dafa mana indomie kawai akwai a cikin kayan da nazo dasu. Cikin 'yan mintuna ta
gama ta kawo. A plates daban ta zuba musu. Maigadi kuwa dama ana magariba ta dafa
masa taliya. Hamza na kallonta har ta zauna zata fara ci ya dauko nasa plate din ya
dawo gabanta, tasa ya juye a cikin natan sannan ya soma ci batare da yace mata
komai ba. Ido ta zuba masa ta kasa ci saboda tana gudun tsokanarsa. Ya dago kai
suka hada ido....lesson three, yana da kyau mata da miji suci abinci tare. Yana
kara musu shakuwa da son juna. Kyakkyawan murmushi tayi...Allah, to amma ba da kai
ya kamata naci ba kada mu shaku gashi zamu rab....hannunsa yasa ya rufe mata baki
ta daga ido tana kallonsa. Ki dena zancen rabuwarmu akwai sauran lokaci. Just eat.
Babu abinda yaki jini yanzu kamar tayi zancen rabuwarsu, idan lokacin yayi sai asan
abinyi amma for now so yake yayi enjoying moments dinsu tare.

Sai da Zuhra ta gyara kitchen sannan tace masa sai da safe Allah Ya kara sauki.
Lokacin aiki yake da laptop a gabansa. Suma yan nepa kamar sunsan injinsu ya lalace
suke kim basu wuta sosai.

Wanka ta dauki lokaci tayi don so take duk abinda ya koya mata ta rinka yi. Zafin
yau da sauki akan na jiya shiyasa ta dan shafa mai kadan sannan ta shiga barnar
bodyspray. Har humrarta da bata taba shafawa ba ta dauko kwalba daya mai kamshi ta
rinka bin duk gabobinta tana shafawa. Rigar baccin da ta dauko yar karama mai
siririn hannu har tafi ta jiya kankanta da rashin kauri. Wani dadi take ji ashe
haka tsafta ke da dadi...gadonta ta haye ta ajiye fitilar a bedside drawer tayi
kwanciyarta. Zafi baisa ta rufa ba amma ba bacci ma take ji ba. Tunani take ko me
Hamza yake yi yanzu.......

Kusan rabin awa kenan da yayi wanka ya gama shirin kwanciya sai dai ko alama babu
bacci a idanunsa. Zuhra yake son gani amma yana kokarin hana zuciyarsa sabawa da
son kasancewa tare da ita. Sakon kudin da Mama ta bashi ya tuna yana wallet dinsa
ga wayar da ya siyo mata duk bai bata ba. Murmushi yayi ya tashi don ya sami
dalilin zuwa dakinta. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #51

Batul Mamman(Mrs)#




Kiran farko na assalatu Hamza ya bude idonsa. Murmushi ne ya bayyana a kyakykyawar
fuskarsa saboda jin har yanzu Zuhra na jikinsa. Hannunta ya zagaye cikinsa, ga
kanta a wurin wuyansa. Yana jin lips dinta a wuyan nasa. Sake matseta yayi
zuciyarsa na fada masa yayi a hankali kada ya fada soyayyar da zata iya zame masa
rigima nan gaba. A hankali ya rinka shafa kanta yana kiranta da sabon sunan da ya
rada mata. Cutie ki tashi asuba tayi. Sake makalewa tayi a jikinsa batare da tasan
halin da hakan ke sake jefashi ba. Cikin dabara ya fara janye jikinsa sai itama ta
bude ido. Ji yayi ta tashi da sauri Ya Hamza ba dai a haka muka kwana ba. Mikewa
yayi ni bana son gulma kin gama makale min a jiki kamar babu pillow a kan gadon
zaki wani wayance yanzu. Kunyarsa sosai take ji ta koma cikin bargo ta dukunkune
kanta. Gudun kada ya makara sallah yasa yayi murmushi kawai ya fita. Sai da taji ya
rufe mata kofa ta tashi ta shiga toilet. Har addua tayi bayan ta idar da
sallah,kada yayi mata kallon mara kamun kai.

Tana idarwa dakinta ta gyara da toilet sannan ta sauka ta share falon tayi mopping.
Falon ne da girma shiyasa taga gara tayi aikin da wuri. Tun dare ya fada mata bread
kawai zaici da safe da tea, wani maidadi ya siyo a Grand square. Ruwan zafi ta dafa
ta juye a flask ta hada da kayan tea ta kai dinning table ta ajiye. Ta sallami
maigadi ma sannan ta koma daki ta tsefe kitson kanta ta kama gashin da ribbon.
Wanka ta shiga ta bata lokaci a bandaki don yanzu an dena jika jika. Ta zauna gaban
mudubi ta shafa mai sannan ta rinka feshe jikinta da turaruka. Ta kula Hamza na son
kamshi sosai, yau so take ta burge shi yasan tana daukar karatun da yake mata. Wani
dogon wando tight baki ta saka ta hada da riga pink wadda ta kusa gwiwarta mai
hannu three quarter. Rigar da dan matseta daga sama sannan ta yi fadi kadan daga
kasa. Da Hajara suka je kasuwa aka siyo kayan da kudin sakarta. Hoda tasa da
kwalli sai dan janbaki kadan pink wanda tayi lining lips dinta da liner pink amma
mai dan duhu. Har wani tsalle tayi da tafi ganin tayi kyau. Ta fesa turare a
kayanta sannan ta dauko karamin pink da bakin mayafi ta daura irin yadda dai 'yan
gayu suke yi. Kasa ta sauka har lokacin Hamza bai sauko ba gashi har takwas da
rabi. Tana son zuwa ta duba ko bacci ya koma bayan ya dawo daga masallaci amma tana
jin kunyar kayan jikinta.

Wayarta da ta dan sami chaji ta duba taga text din Hajara tana sanar da ita zata zo
wurin shabiyu ta kira wayar tun jiya taji a kashe. Wayyo dadi, Zuhra sai murna.
Kada Hamza yace wannan karon bata fada masa zata yi bakuwa ba ta yanke shawarar
zuwa dakinsa.

A darare tayi sallama ta shiga falon sai taji ya amsa daga cikin daki. Kanta tsaye
ta shiga ciki ta ganshi daure da tawul yana tsaye a gaban wardrobe dinsa yana neman
kayan sawa. Kafin ya juyo ta runtse idonta tana cewa yayi hakuri. Dariya yaso yi
sai dai shigarta ta matukar daukan hankalinsa. Ji yake kamar ya dauketa yayi
hugging. Zata fita yace tsaya a nan ina zuwa. Kayan ya saka sannan ya taho gabanta
da coat a hannunsa da necktie. Kamshin turarensa ya sanar da ita isowarsa. Cikin
murya mai jan hankali yace bude idonki Cutie. A hankali ta budesu ta ganshi tsaye
da shirt dinsa duk maballan a bude. Yace jiya na fada miki ana taimakawa miji yasa
kaya ko? Kai ta gyada kawai tana kallon kasa. To balle min buttons dinnan naga ko
kin koyi karatun. Ta dan zaro ido tana kallonsa. Come on Cutie ina da meeting kada
na makara. Hannu na rawa ta soma ballewa daga kasa. Shi dariya take bashi ga tsoro
ga baki. Har tazo na karshen wuyansa jikinta sai bari yake. Bayan ta balle ya bata
tie din saura wannan. A sanyaye tace ban iya daurawa ba. Gwada mata yayi sannan ya
ware ya bata ta daura masa. Kallon da yake mata yasa hannunta ya kasa tsayawa
sosai. Nasa hannun ya saka ya taimaka mata har suka daura tare. Yau duk ta kasa
kallon shi ya dago kanta da hannunsa sai kawai ta rufe ido tace Ya Hamza kunyarka
nake ji ka barni na fita. Zagayeta yayi da hannuwansa sannan ya matso da ita
gabansa. Cutie kinyi kyau. Ta danyi murmushi da gaske? Yace da wasa. Kafa ta buga a
kasa cike da shagwaba tace haba Ya Hamza mana kace nayi kyau don Allah. Hancinta
yaja sannan yace kinyi sosai shiyasa na saka miki Cutie. Muje muyi breakfast kada
na makara. Dan tsayawa tayi yau ban gaisheka ba, sai ta durkusa ina kwana ya jiki?
Tayar da ita yayi tsaye kinga irin wannan gaisuwar bata dacewa da miji da mata.
Kinga yadda ake yi ko don gaba. Duka hannuwansa yasa a kafadunta yayi kissing din
lips dinta lightly. A take taji wani abu yana yi mata yawo a ciki. Shi kuwa jan
hannunta yayi suka sauka don yasan ko rabin minti suka kara a wurin abinda zai mata
sai ya fi wannan.

Yau cin abinci nasu babu wata hira ake yi domin dukkansu tunani suke. Hamza sai
tambayar kansa yake ko dai ya fara son Zuhra ne? Itama Zuhra tambayar da take yiwa
kanta shin zata iya rabuwa da Ya Hamza. Suna gamawa ya tashi tace anjima Hajara
zata zo kanwar Anti Faiza. Yace nima kinga na manta su Adabiyya zasu zo kwana. To
da safen nan kuma naga text din Jidda ita da Mariya da matar Ibrahim kanina zasu
zo. Inajin duk da yaransu zasu zo anya zaki iya da baki da yawa haka? Ga mamakinsa
murna take yi sosai, zan iya mana in sha Allah. Gara na dora girki da wuri saboda
yara ma. A dawo lafiya....bata saurare shi ba shige kitchen tana tunanin abinda
zata dafawa bakin nata. A hadith na shabiyar a Arba'una Hadith Manzon Allah SAW
yace duk wanda yayi imani da Allah da ranar karshe to ya karrama bakonsa. Kuma
tarbiyar Ummanta da Baba kenan. Ita yanzu me zata dafa ta burgesu kuma kowa yaci ya
koshi?

Hamza ya gaji da tsayuwar mamakin irin wannan murna da Zuhra keyi ya dauki jakarsa
ya fita. Izzatu bata taba son 'yan uwansa su zo gidansa ba. Idan sunzo ma zasha
ruwa ne da juice su koma gida. Zuhra daban take.... Sai da ya shiga mota ya tuna da
sabuwar wayarta ya dawo ya dauko har lokacin tana kitchen. A tsaye ya ganta ta rike
haba ita a dole tunani take. Tana ganinsa tace yauwa Ya Hamza dan bani shawarar
abinda zan dafa mana. Yace naki din, nida kika tafi kika barni daga cewa zaki yi
baki. Ta marairaice masa to yi hakuri kaji Ya Hamzaaaaa. Murmushi yayi Cutie kina
abinda kike so. Tayi murmushi tana kallonsa. Shima yayi mata kyau. Zo ga wannan I
hope you like it. Da dan murmushi tace ina fa dan gane turanci kalma me tsauri ce
dai bana fahimta. Amma dan fassara min abinda kace yanzu turancinka ba irin na
malamin English dinmu bane. Fassarawar yayi yana dariya ya mika mata wayar. Gashi
nan na saka miki wani sim din sai ki saka na daya wayar tunda mai sim biyu ce. Bade
baki kawai tayi tana kallonsa. Sai kuma hawaye Ya Hamza wannan tawa ce? Ya gyda
kai, tace Allah Ya saka maka da alkhairi Ya baka ladan faranta min. Allah Ya kareka
daga dukkan sharri. Nagode sosai. Wayar dubu ashirin Zuhra kewa kuka da wannan
addua, Izzatu kuwa dubu dari ya bata da zata yi tafiya amma kirikiri ta nuna ta
raina. Matsowa yayi gabanta ya goge mata hawayen da hannunsa sannan yace nagode da
adduarki. Su kuma bakin kiyi musu danwake idan kin iya, a iya sanina dasu Mariya
duk mayun danwake ne. Yana gama magana ya fita tabi bayansa. Sai da motarsa ta fita
daga cikin gidan ta dena daga masa hannu.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #52

Batul Mamman(Mrs)#




Zuhra aiki ya kankama. So take ta gama abincin kafin su iso yadda ba zasu zauna da
yunwa ba. Katuwar roba ta samu ta dora danwake sai da tayi tukunya uku tana yi tana
juyewa a wata roba mai dan girma. A kalla mutum goma sha biyu zasu ci su koshi
sosai. A ranta tace idan bai isa ba sai ta kara. Bata san adadin yaransu ba ga
maigadi. Bayan ta gama ta dafa kwai guda goma, ta wanke tumatir, albasa, koren
tattasai da cucumber ta ajiye

16 / 36