Advertisements
Chapter 36 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   36 / 36

105K to 106K   out of 106K words

ranar haihuwarta
saboda ta iya kuka da raki. Shi da Izzatu suna waje kowa hankali a tashe. Zuhra na
kuka a ciki Izzatu tana yi masa nata a waje. Ya rasa inda zaisa kansa.

Sai da ya tafi sallar asuba sannan Zuhra ta haihu. Nurse ta fito ta kira Izzatu
bayan sun gyarawa Zuhra jiki. Wani sabon kukan ta saka da taga Izzatu. Nurse din ta
soma tsokanarta wai sun gama ganin rakinta.

Izzatu ta rike mata hannu sannu Maama. Kukan kuma na meye ai an gama wannan saura
na gaba kuma.

Fuska a kwabe Zuhra tace wane irin na gaba. Don Allah dena fada. Duk kankantar
yaron nan sai da yaja min dinki. Kunji salati na da anayi ko?

Nurse tace salati ko kuka. Da kyar fa muka yi duk taki tsayawa. Ina ganin idan
likita ta dawo daga inda suke duba baby din sabo zata bukaci yi miki.

Shigowar Hamza yasa duk hankalinsu yayi bakin kofar. Bakinsa kamar gonar auduga duk
da basu ga baby din ba. Izzatu ta dan wayance tabi bayan nurse don ta basu wuri.

Tana fita kuwa Hamza ya karasa wurin gadon ya rungume Zuhra....'yar shagwaba yau ta
shiga labour room.

Ta turo baki...tsokanata ma kake yi ko? Baza'a sake ba daga wannan.

Rufa min asiri Cutie ai an bude kofar kenan. Daga wannan sai munyi tara.
Uhmm kai da wa? Ni dai na gama. Kaje ka duba mana baby din ko ganinsa banyi ba.
Allah Yasa dai yayi kama dani don nasha wahala.

Hamza yayi dariya kada ma kisa rai. Mu jininmu akwai karfi duk jikokin Alhaji dashi
suke kama yadda muke kama dashi. Bari naje idan zasu barni na ganshi zanyi masa
huduba da sunan babanmu Muhammad Bashir.

Dadi ya mamaye zuciyar Zuhra tace Ya Hamza nagode ko baiyi kama dani ba babu komai.
I love you.

Kiss yayi mata a goshi yace I love you more.

****
Tun daga ranar asibitin kullum a cike da 'yan uwa da abokan arziki. Gwaggo Hasiya
yayar Umma ita ke kwana da Zuhra. Gabadaya Izzatu bata hutawa daga gida zuwa
asibiti. Yadda take kulawa da Zuhra yana bawa kowa sha'awa. Raliya ma tazo barka da
kanwar Izzatu.

Duk da ba'a sallame su ba amma Hamza ya gama tanadin radin suna. Raguna biyu ya
siyo manya aka daure a cikin gidan. Ana gobe suna da daddare Zuhra na cin tuwo kowa
ya tafi suna hira da Gwaggo Hasiya tace kina nan da cin abincin nan naki ko Fati.
Gashi kin haihu yanzu rumbun Hamza zai girgiza.

Zuhra tace ni da labari yazo min cewa a wurinki na gada.

Kaniyarki, Gwaggo Hasiya ta fada tana dariya ita ma. Dama shawara nake son baki ina
fata kuma zaki dauka. Nasan kin riga kin fada mana sunan yaron nan har kina ce masa
Babana to amma ni ina ganin me zai hana ki kara karfin zumunci tsakaninki da
abokiyar zamanki? Wallahi na kula da gaske take kaunarki. Jiya da za'a gyara miki
dinki ita da Atine har da hawaye saboda kin cikawa mutane kunne da ihu.

Zuhra ta sunkuyar da kai kasa. Gara ta koyi dauriya dai kowa yace ta fiye raki.

Gwaggo Hasiya ta cigaba shagwaba ce su Atine sun koya miki. Batun sunan yaron don
Allah ki daure asa sunan marigayi yaron wajenku. Nasan Izzatu zata ji dadi kuma
zumuncinku zai kara karfi. Idan da rabo sai ki haifi mai sunan Babanyara. Shawara
ce fa kawai na baki bance dole ba. Kada ki dauke shi a matsayin sunan baban
kishiya. Ki dauka yaro yaci sunan wansa ne.

Zuhra tace Gwaggo nagode sosai. Naso saka masa sunan Baba amma shawararki tasa nafi
son yaci sunan dan uwansa.

Tana gama cin tuwon ta turawa Hamza text sai taji tsoron kila yayi bacci kada yazo
bai gani ba sai da safe. Kira tayi kuma tayi sa'a ya dauka. Da yaji bukatarka ba
karamin murna yayi ba yayi ta sa mata albarka. Bai fadawa Izzatu ba ya bari sai da
safe taji. Yasan zatayi murna.

Bayan asuba kuwa Izzatu ta sauko hada kayan abincin asibiti Tala ta shigo kitchen
gaisheta harda dan hawaye tace Hajiya munji sunan jariri Allah Ya raya mana
Muhammad Sunusi. Shikenan sai mu rinka kiransa Junior.

Izzatu taji zancen wani iri tace Amin amma sunansa Bashir.

Tala tace a'a yanzu babansu Khalifa ya fada min sunan kafin ki sauko.

Da sauri sauri Izzatu ta hau sama. Hamza na jin motsinta ya tsaya yana dariya.
Karasawa tayi ta rungumeshi tana kuka. Baby da gaske ne abinda Tala tace?

Sai da ya share mata hawaye sannan yace jiya kina wanka Zuhra ta kirani tace ga
sunan da take so.

Izzatu ta sake kankame shi tana kuka tana dariya.

Kafin taje asibitin sai da ta kira Raliya ta fada mata. Ita ma taji dadi sosai.

Tana shiga dakin kuwa rungume Zuhra tayi tana ta yi mata godiya. Daga murna suka
koma kukan rashin wancan Junior din.

Gidansu Hamza ma duk sun yabawa Zuhra da wannan karamci da tayiwa Izzatu. Da aka
sallamesu bayan sati biyu gidansu ta tafi wanka duk da ba haka Hamza da Izzatu
suka so ba. Har kara'in suna sai da suka yi wanda mutane da dama suka halarta.

Haka rayuwar gidan Hamza ta cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya da kokarin koyi
da addini da al'adunmu wadanda basu sabawa addini ba. Zuhra da Izzatu kuwa kullum
suna kokarin kyautatawa mijinsu da junansu. Yanzu haka ma islamiya ya sama musu a
nan unguwar tasu suke zuwa tare. Junior kuwa idan ka ganshi a wurin Zuhra to yunwa
ce ta kawo shi. Komai Izzatu ke yi masa.

Watansa takwas Zuhra ta fara wani laulayin. Hamza ba karamin dadi yaji ba. Saboda
yadda take wahala aka yaye Junior. Cikin ikon Allah bayan wata tara ta haifi 'yan
matanta guda biyu.
Murna wurinsu ba'a magana su Nana an zama yaya. Yaran suka ci sunn Umma wato Fatima
da Mama wato Ummukulthum ake kiransu Ummi da Ummu. Suma shekararsu biyu aka haifi
Muhammad Bashir. Gidan Hamza ya soma cika da yara. Sai da muyi musu fatan zaman
lafiya mai dorewa.




ALHAMDULILLAH!

Godiya ta musamman taku ce 'yan gidan Batul Mamman Novels. Ni da ku 'yan uwan taka
yanzu ma muka fara. Allah Ya kara zumunci Ya albarkaci rayuwarmu.


Marubuta
Hakika naji dadin kwarin gwiwa da kuka rinka bani a wannan littafi Al'adun Wasu.
Nagode sosai..
Ummu Abdoul
Aisha Yau Kurah
Ummu Nass
Feenat Ja'far
Maryama Mmn Afreen
Baby Maryam
Queen Mimi
Ummi Aisha
Mamu
Ummu Hannan


Groups
Bazan manta daku ba yan...
Feenat Ja'afar Novels
Taskira
Rufaida Omar Fan's duka biyun
Allah Ya saka muku da alkhairi Ya kara mana zumunci.
Sai kuma 'yan uwana na Fikrah Writers Association ina kara mika godiya tare da
fatan alkhairi.


Masu waya da text kuma bazan manta[truncated by WhatsApp]

36 / 36