Advertisements
Chapter 5 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 36

12K to 15K   out of 106K words

kunya. Bayan sun zauna ta gaishesu Mama tace ina Khalifan? Ashe
baiji dadi ba. Izzatu tace eh amma yau da sauki sosai. Zazzabi ne da mura. Hajiya
tace to Allah Ya bashi lafiya. Mama tace kirawo shi mu ganshi. Dazu babansa yayi
min waya da safe shine muka zo duba shi. Izzatu tace Tala ta dauko musu ruwa da
lemo.

Tala na tashi Nana ta fara ihun Mummy na gama da dan gwarancinta. Izzatu tace jeki
kiyi mata tsarki bari na kawo musu. Tashi tayi tana kiran su Junior su zo ga su
Hajita ta shige kitchen.

Ba'a fi rabin minti da shigar Tala ciki ba ta fito falo tana ihu. Gabadaya jikinta
rawa yake sosai tana kuka. Hajiya da Mama suka tashi a firgice suna tambayarta
abinda ya faru. Cikin kuka tace mutanen boye sun bayyana. Mama tace su wa? Tala
tace aljanun. Yau na gansu da idona ra'ayil aini har su biyu. Wallahi sai ga yarsu
zaune akan po din Nana dayan kuma yana mata wasa. Na higa uku na lalace
kwarankwatsa ko a kauyenmu ban taba gamo ba he yau. Izzatu ce ta fito da sauri daga
kitchen tace ke Tala bana son rashin hankalin nan naki.
[9/25, 3:33 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿14

Batul Mamman(Mrs)💖




Tala ta zazzaro idanu tana kallon Izzatu. Na rantse ba karya nake ba. Hajiya da
Mama sai kallonsu suke yi. Tala na maida zance suka ji kukan Nana tana kiran
Izzatu. Tare duk suka yi hanyar inda suka ga Tala ta fito. Hajiya ce a gaba. Sai da
cikinta yayi mugun kadawa saboda abinda ta gani zaune akan po yana miko hannu
alamar ta dauke shi. Na kusa dashi kuma mai siffar kwarangwal ya rugo da gudu zai
rungumeta. Da kyar ta iya cewa Hasbunallahu wa ni'imal wakil sannan tayi baya kamar
zata fadi. Mama tayi saurin tareta itama a tsorace har ta fara tunanin kada aljanun
su rufe kofar gidan su hanasu fita. Tala tace kun gani ko Hajiya ai na fada muku.
Nana dai tasowa tayi ta nufo su shima Junior haka. Khalifa da yake kwance a daki
shima ya fito saboda hayaniyar da yaji. Mama ta karewa aljanun uku kallo tace
Hajiya gidan Yaya ba lafiya. Izzatu ce karshen shigowa tana ganin abinda ya kidima
surukanta ta kyalkyale da dariya harda hawaye, karshe sai da ta kai kasa. Hajiya da
Mama sai kallon kallo a zatonsu ma ko aljanun sun taba ta. Sai da tayi mai isarta
suna kallonta sannan tace Hajiya su Nana ne fa. Kaya ne na saka musu yau halloween.
A gabansu ta cire musu fuskar kayan tana mai cigaba da dariya.

Ransu Hajiya yayi matukar baci. Tala kuwa karasawa tayi gaban yaran tace Khalifa
kaine tana tattaba musu jiki. Ta dago kai tace Hajiya ai kuwa su din ne. Mama ta
dubi Izzatu, hallo...me kika ce? Izzatu tace halloween. 31st October ake yi.
Lokacin da muna Canada muna yinsa sosai. Tsabar bacin rai Hajiya ta kasa magana ma.
Karshen wulakanci da cin mutumci Izzatu tayi musu.

Mama tace Hajiya ai sai mu tafi ko, don banga dalilin zamanmu ba. Su Junior suna ta
binsu suna cewa zasu bi su. Cikinsu babu wadda ta iya kula yaran saboda yadda
zukatansu ke kuna. Izzatu tace muje falo ku sha ruwa don ita bata dauki shirunsu a
matsayin bacin rai ba. Sun kai bakin kofa zasu fita idon Mama ya kai kan wani mutum
mutumi mai siffar mutum kafarsa ta akuya ga kaho har a saman hanci. Shima duk cikin
kayan kwalliyar gidan ne na halloween. Cikin Mama har murdawa yayi, gabanta ya
fadi don abin ya bata tsoro har kafarta ta goce ta fadi kasa. Hajiya tayi saurin
durkusawa ta taimaka mata ta tashi. Junior da Khalifa ma suna ta cewa sannu Grams.
Ita kuwa Izzatu wata dariyar ce ta subuce mata. A ranta tace ko ba komai ta rama
abinda suka yi mata na sa Hamza ya hana su party.

A fusace Hajiya ya dago kanta cikin zafin rai zata yiwa Izzatu magana Hamza yayi
sallama. Ganin Mama na kokarin mikewa yayi saurin karasawa gabanta yana tambayar
abinda ya faru. Dama zuciyar Hajiya a kusa take maimakon ta bashi amsa ta kwashe
shi da mari. Falon a take yayi tsit Tala tayi saurin komawa dakin su Khalifa ta ga
an mari ubangidanta. Falon yayi tsit Izzatu ta hadiye sauran dariyarta. Shi kuwa
hannuwansa biyu yasa ya dafe kumatunsa ya dubi mahaifiyarsa a razane. Mama tace
haba Hajiya ya zaki dauki hukunci kan wanda baiji ba bai gani ba. Murmushin takaici
Hajiyan tayi tace tunda nake ban taba ganin wulakancin da yayi min ciwo irin wannan
ba. HAMZA ka guji ranar da zanyi maka baki.....idanunsa sunyi jawur yana mamakin
sunansa da ta fada da kuma dalilin bacin ranta. Yace da Izzatu me ya faru? Ta dan
tabe baki babu komai. Don basu dade da zama ba suka tashi. Hajiya da Mama suka yi
hanyar kofa yana ta basu hakuri da son jin abinda ya faru sunki sauraronsa. Har
bakin mota ya biyo su. Sai da dreban ya tada motar sannan Hajiya tace wallahi in
dai da raina da lafiyata Hamza bazan kara taka kafata nazo gidanka ba. Mama da yake
tunanin zata bata hakuri ko kallon inda yake bata yi ba. Sai ma kwalla da yaga tayi
saurin sharewa kafin motar ta fita daga harabar gidan.
Da sauri ya shiga gidan yana kwalawa Izzatu kira. Ta fito hankali kwance tace
sweetheart abinci zaka fara ci ko wanka. Izzy kina da hankali kuwa? Ya dubi su
Junior kai ku koma dakinku. Sai da yaran suka tafi yace idan naki iyayen ne suka
fita haka zaki musu? Ki fada min gaskiya me akayiwa su Hajiya. Izzatu tace ni ban
sani ba. Suna ganin su Khalifa suka kama hanyar fita. A daidai can ne mama ta dan
fadi. Hamza yace ta fadi? Ya karasa yaga gunki a wurin ya dago shi..meye wannan
kuma? Izzatu tayi yar dariya na halloween ne. Ka tuna sanda akeyi a Canada? Akwai
da yawa naso gama jerasu kafin ka dawo. Ya ce wane irin hoto kika turo min dazu? Ni
abinda ya dawo dani kenan. Izzatu ta riko hannunsa zo mu zauna babyna. Ta kira
yaran sai a lokacin ya kula da kayan jikinsu. Na nana yafi tada hankali ya mike a
fusace izzy dont tell me haka su Mama suka ga yaran nan. Tace haka suka gansu mana.
So what? Dafe kansa kawai yayi yana karanta Innalillahi a zuci. A hankali yace Izzy
don Allah ki ajiye al'adun wasu a gefe mu zauna lafiya. Yadda Hajiya ta rantse ta
bar zuwa gidana na miki rantsuwa da Allah idan kika sake dauko min wani abu da bai
dace da dabiar musulmi ba sai na bata miki rai. Bacin rai wanda sai kinyi nadamar
aurena. Iya nasihar da zanyi miki nayi nima na gane rashin kyautuwar abinda muka yi
a baya. Kina zaune lafiya da iyayenki baki isa ki rabani da nawa ba. This....ya
nuna ta da dan yatsa is my last warning.
[9/25, 3:33 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿15

Batul Mamman(Mrs)💖




Yana gama magana ya tashi yana kwalawa Tala kira. Da yake tana labe a bayan kofa da
gudu ta fito jiki na rawa yace jeki ki cire musu kayan nan ki kawo min mota ina
jiranki. To kawai tace ta kwasa da gudu tayi ciki. Izzatu ta kalleshi itama rai a
bace kudi fa nasa na sayi kayan nan. Me zakayi dasu?. Ya dan daga gira daya Allah
ko? Tunda kudin nawa ne babu ruwanki da abinda zanyi. A iya zamansu basu taba samun
sabani kamar yadda suke yi yan watannin nan ba. Kirikiri iyayensa ke nuna mata
kiyayya amma zata yi maganin abin. Ta yanke shawarar bazata taba bari maganganunsu
suyi tasiri a ranta ba har ta dena rayuwarta yadda ta saba. Ita tasan iyayenta sun
bata tarbiyya irin wadda ta dace kuma ga yayarta da mijinta suna zamansu lafiya sai
ita kadai ce zasu takurawa.

Horn Hamza ya rinka dannawa da karfi sai ga Tala kamar an jeho ta. Ta mika masa
kayan. Har ya dan ja motar sai ya dawo ya sake kiranta. Ke fada min gaskiya me ya
faru da su Hajiya suka zo dazu? Ai kamar jira take ta soma bayani dalla dalla. Dama
banda tsoron da taji ba karamin mamakin Izzatu tayi ba da tayiwa surukanta dariya.
Fuskar nan ta Hamza kamar bai taba dariya ba ya ja mota ya nufi gidan iyayensa.

Hankalinsa a tashe ya gyara parking din motarsa saboda yaga alamun Alhaji na gida.
Yana shiga falo Adabiyya da Hamida ya gani suna kuka. Gabansa ya fadi yace ku meye
haka? Adabiyya ta taso ta rungumeshi tana cigaba da kukan. Dama duk ta fisu raguwar
zuciya. Hamida tace Mama akeyiwa gyaran kafa. Me kika ce??? A razane yake maganar
tace gocewar kashi ta samu. Matsar da Adabiyya yayi daga jikinsa ya shiga falon
Alhaji. Mama ya gani zaune a kasa tayi gumi sosai Hajiya na rike da hannunta.
Kafarta ta hagu daure da wani farin yadi. Gefe kuma mai dori ne durkushe gaban
Alhaji zai karbi kudinsa. Mai dorin yace in Allah Ya yarda gobe da safe zan dawo na
duba. Allah Ya kiyaye gaba.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka Hamza ya karaso cikin falon. Mama ce kawai
ke kallonsa, ita Hajiya kawar da kai tayi gefe. Alhaji Nasiru ya hade fuska kana
ganinsa kasan yana cike da bacin rai. Kusa da Mama Hamza yaje ya zauna ta riko
hannunsa kawai sai ta soma kuka. Hajiya ta tashi zata bar falon Alhaji ya dakatar
da ita. Hamza yace Alhaji barka da rana. Muryarsa har rawa take bata fita sosai.
Alhaji yace Hamza.....toh fa yau duk su biyun sun kira shi da sunansa. Allah gani
gareKa yace a zuci. Naam Alhaji. Alhaji yace dago kanka ka kalleni.

Kasawa Hamza yayi. Alhaji yace ashe kana da sauran kunya. Dubi yadda iyayenka suke
kuka saboda bacin ran da suka kwaso a gidanka. Yau Mamanka ce a zaune ana mata
gyaran gocewar da tayi a gidanka matarka tayi mata dariya. Wace irin rayuwar aure
kuke yi kai da iyalinka? Me kake son nunawa duniya game da tarbiyar da muka baka?
Ba don tsarewa ta Allah bace duk kannenka koyi zasuyi da irin dabiun da ka kwaso a
turai. Alhaji ya cigaba da cewa duk irin abinda kuke yi babu wanda ban sani ba amma
na kawar da kai saboda iyayenka basu tunkareni da maganar ba. Na basu damar su ta
iyaye mata su saita ka a hanya kuma nasan sunyi iya kokarinsu. Amma yau saboda abin
yayi yawa Halimatu da kanta ta sanar dani abinda yarinyar nan tayi musu. Wulakanci
na karshe Izzatu tayiwa iyalina amma bazan umarceka da rabuwa da ita ba. Sai dai ka
sani wallahi nayi maka rantsuwa ranar da duk kuka sake aro daga munanan al'adun
wasu har kunnena ya jiye min ko ido ya gani zanyi maka hukuncin da baka taba
tsammani ba.

Da sauri Hamza ya kalli mahaifinsa don Allah kuyi hakuri Alhaji. Nasan nayi kuskure
tunda da goyon bayana komai ke faruwa. Amma in Sha Allah zan gyara kuma yanzu zan
daukota tazo ta bada hakuri. Hajiya tayi saurin cewa ban yafe maka ba muddin kace
mata tazo bada hakuri. Indai hankalinta da tarbiyarta basu nuna mata abinda ya
kamata ba shikenan. Alhaji yace ina zaune kike irin wannan zancen Halimatu? Tace
ayi hakuri. Hamza ya dubi Mama wadda kanta yake a kasa ki yafe min Mama don Allah.
Abinda ya faru yau ko kadan bani da masaniya a kai. Alhaji yace halo me ma kuka ce
sunan abin? Hajiya tace yo ni ina zan rike. Kamar ba kalmar turanci ba, yau na fara
jinta ma. Hamza ya sake dukar da kai ko a da bama yin wannan ranar bansan dalilinta
na yi ba yau. Alhaji yace dalilinta ya wuce ta tozarta min iyali ne? Ka tashi ka
tafi Allah Ya kyauta.

Hamza dai kin tashi yayi ya kara matsawa jikin Mama yana rokon ta yafe masa.
Murmushi kawai tayi tace masa ka tashi ka tafi ba komai. Duk yadda yaso Mama taki
tsawaita magana. Hajiya tace ka tashi ka bamu waje magana ta kare. Idan ka fita ka
turo min Adabiyya da Hamida. Jiki ba kwari ya fita ya turo su. Hajiya tasa Adabiyya
sake gyara gadon Mama , ita da Hamida suka kamata suka kaita daki.

Zuwa dare su Ibrahim duk sun zo gidan da iyalansu. Kowa yayi bakin cikin jin abinda
Izzatu tayi musamman dariyar. Ummahani matar Ibrahim tace ni Yaya tausayi yake
bani. Jidda tace tausayin me? Ba fa auren hadi bane da kansa yaje ya kwaso mana
ita. Mariya tace kuma dashi suke komai ba. Dama matsalar ka fara abu kenan. Sai
kaso denawa mabiyanka suce basu san zance ba. Motoci hudu ne a gidan Yaya amma ko
keke bai siyawa ko da Nura ba da yake karatu. Irin abinnan ka daukewa iyaye wani
nauyi ko a jikinsa. Daga shi sai iyalinsa. 'Yan kwanakin baya ne ma naga abin ya
dan canja. Mama dai tana daga kwance tace ku bar zancen nan haka.

A haka sai da Mama tayi sati uku a kwance saboda banda gocewar tayi ta fama da
zazzabi. Kullum safe, rana da dare Hamza sai yazo. Da daddaren ma da su Khalifa
yake zuwa. Izzatu kuwa tunda baice tazo suje dubiya ba itama ta share. A ganinta
yan uwansa ne bazata masa shisshigi ba. Wani lokacin ya hadu da kannensa wadanda
suka hade masa kai. Daga gaisuwa basa kara yi masa wata maganar. Su Hajiya suna
amsa masa gaisuwa amma suma daga nan magana ta kare. Rashin kula shi da Mama keyi
duk yafi komai tada masa hankali. Bashi da aiki sai bada hakuri sai dai tace masa
babu komai.

A haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya har suka dan daidaita. Mama ce dai har yanzu
bata yi masa kamar da. Shi kuwa bai kosa da yi mata siyayya ba kullum. Domin yanzu
ya dauki irin abinda Ibrahim yake yi tun bayan yayi aure. Kullum sai yazo gidan ya
gaishe da iyayensa ko da safe kafin yaje aiki ko bayan magariba.
[9/25, 3:34 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿16
Batul Mamman(Mrs)💖




Wata asabar da safe Izzatu ta nemi izinin Hamza tana son zuwa Abuja tunda su Junior
na hutun makaranta wurin iyayenta. Ya amince har ya bata dubu hamsin ko zata yi
siyayya sannan ya cika mota da mai yasa dreba ya kaisu. Ashe new year celebration
taje gani. Sauran shekarun duk tare suke yi da Hamza, ganin yadda lokaci guda ya
canja mata yasa bata sanar dashi gaskiya ba. Da yaran ta tafi suka je kallo tare da
kannenta. Bayan sati daya suka dawo gida.

Zuhra ce take tafe da katuwar ghana must go shake da kayan sanyin da ta saka. Yanzu
ta kware sosai don sanyin da ya wuce tayi ciniki sosai. Da yake farkon March ake
gari ya soma zafi. Sai dai mijin Anti Faiza ya samar mata wata makarantar primary
sun bata kwangilar sakar rigunan sanyin dalibai. Murna sosai su Baba suka yi. Ta
gama na farko shine zata kai musu. A daidai wani lungu zata wuce bakin titi ta
hango Anas da abokinsa Sani suna busa wiwi. Idonunta kyam a kansu, Anas ne ya fara
hangota yayi saurin taba sani. Dukkansu kashe tabar suka yi suna murmushin yake.
Fitowa suka yi daga lungun Sani yace kaga manyan yan mata. Zuhra ina zuwa haka da
rana? Ta karkace kai tana kallonsu wai nan bagarar dani zakuyi. To nagani kuma sai
na fada. Anas yace don Allah kada ki fadawa Baban yara. Kinga muje mu rakaki inda
zakije ma. Sani ya karbi jakar zai daukar mata. Da sauri ya mayar ya ajiye...ke
yanzu tun daga gida kika dauko jakar nan. Zuhra tace eh menene? Sani yace Anas
dauki ka ji. Anas ma dagawa yayi ya mayar Zuhra haka kike da karfi. Wani murmushi
ta saki da yasa duk munin kwalliyarta tayi kyau. Au ku da rainani kuke yi? Ai kada
ku taba bari dambe ya hada mu don kasa zan kaiku. Sani yace ke dalla can wa ya fada
miki maza na son mata karfafa. Ko ni naji nauyin jakar bare ke. Wallahi ina baki
shawara idan kika yi aure ki nunawa mijinki ke raguwace. Sai yafi sonki. Amma yana
ganin kin fara aje kwanji wata zai dauko a mayar dake maigadi. Zuhra ta sha kunu
amma ka zage ni Sani, kai Anas kayi wa abokinka magana wallahi. Anas yayi dariya
ai gaskiya ya fada miki. Daukar abu mai nauyi ai ba na yanmata bane. Fizgar jakar
tayi ku bani kayana yan wulakanci. Kun tsayar dani kuna ci min fuska..kuma sai na
fadi abinda naga kuna yi. Anas yace to yi hakuri. Yanzu ina kika nufa mu daukar
miki kayan. Dayake dama ta gaji sosai tace bakin titi. Gidan yayar Hajara zani.
Sani ne ya dauko jakar Anas yace yaushe ne bikin Hajara. Nan da sati biyu Zuhra ta
bashi amsa.

A bakin titin suka tarar mata adaidaita sahu. Anas ya mika masa dari biyu yace ya
kaita har kofar gidan da zata je. Tayi musu godiya suka juya. A hanya Sani yace
Baabaa yaushe zaka fadawa yarinyar nan kana sonta ne? Anas yace haba Sani. Zuhra
tafi karfina. Sani yace Zuhran?yarinyar da ko kwalliya bata iya ba. Ko sakandare
bata gama ba fa. Anas yace amma ai tana da tarbiya. Kuma sau nawa Baban yara na
kama mu a wurin nan. Ai da kunya nace ina son yarsa. Sani ya bigi kafadar Anas to
tun wuri gara ka sani ni zan mata magana. Dama don naga kamar ka rigani fara sonta
shiyasa na kyale. Anas ya daure fuska kasan Allah bazan bari ka aureta ba. Zuhra
sai mutumin kirki mai rufin asiri. Sani ya soma gudu bari kaga har gida zan sami
mahaifinta. Da haka suka tafi suna dariya.

Su Zuhra sun kawo kwanar layin gidan Anti Faiza wasu mata uku suka tsayar da mai
adaidaitan. Suka yi ciniki yaji kudi yace Zuhra ta sauka. Rai a bace tace haba
malam ba haka mukayi da kai ba. Jakar nan nauyi gareta kuma gidan yayi dan nisa
daga bakin titi. Naira hamsin ya miko mata gashi ki nemi wani ya karasa da ke. Ba
yadda zatayi dole ta fito tana kunkuni. Ta kalli matan sunsha ado da gani biki zasu
je ta dan murguda baki...ku ma Allah Yasa ku hadu da wanda zai muku abinda kuka yi
min. Dankwalinta ta ciro daga kanta ta gyara hijab din sannan tayi gammo da
dankwalin. Tana kicikicin dora ghana must go din taji horn din mota a gefenta.
matsawa tayi tana tunanin ko ta tare hanya ne. Horn din ta sake ji sai ta dan juyo
taga ko da ita ake. Ba karamin mamaki tayi ba da taga matar mutumin nan mai fadan
tsiya.
[9/25, 3:35 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿 17

Batul Mamman(Mrs)💖




Zuhra ta washe baki tana murmushi tace ke ce? Izzatu itama murmushin take tace
nice. Kingane ni ko? Zuhra ta gyara jakar kanta tace eh mana. To shigo na rage miki
hanya Izzatu ta fada tana bude mata gaban motar. Allah Ya sani kayan da nauyi ba
musu ta sauke tace ina zan saka jakar? Izzatu ta bude mata

5 / 36