Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
na zaune a falo tana waya taga Izzatu ta shigo. Ko sallama batayi ba da
wadda suke wayar ta tashi a gigice. Izzatu lafiya? Me ya faru?? Ina yaran???
Tambaya take tana kuma leka waje taga ko zata fahimci abinda ke faruwa. Izzatu
tayi murmushi Mum kina da rudewa wallahi. Sai watso min tambayoyi kike a lokaci
guda. Tayi maganar tana shirin zama akan kujera. Idanun Raliya kamar su fado don
fargaba muryarta har rawa take yi tace kinga I..Izz...Izzatu bana son jan rai. Idan
wani abinne ya faru ki fada min tun wuri. Hamzan ya sakoki ne ko me? Izzatu tayi
jifa da mayafinta, Ohhh Mum ko ruwa ki bari nasha mana. Ki kwantar da hankalinki
all is well.
Hankalin Raliya bai kwanta ba sai da Izzatu ta gama cin abinci sannan tace Mum nazo
yiwa Dad sallama ne fa na tafiyarsa Japan. Ran Raliya a bace tace Izzatu zan
ci........ki wallahi. Shine zaki zauna ki tayar min da hankali tun dazu ina
tambayarki kinyi shiru. Hawan jini kike so ya kamani ko ciwon zuciya? Kuma ko jiya
kafin mu baro Kaduna sai da muka sake maganar nan dake nace an daga tafiyar tasa.
Munyi maganar nan yafi sau biyu, ina hankalinki ne? Izzatu ta bude baki Mum da
gaske na manta munyi zancen nan. Raliya tace to sai ki kwana yau gobe ki kama hanya
ki koma gidanki. Izzatu ta kalleta sannan tace Mum nifa sai next week zan koma. Na
riga na tambayi Hamza ya barni nayi sati daya a nan. Dariyar takaici Raliya tayi
tace lallai Izzatu baki da kai, sai kace ba kece mai korafi akan auren da yayi ba
shine kika basu wuri su sha soyayyarsu hankali kwance.
Ya zaki rinka fadin haka Mum? Izzatu ta fada kamar tayi kuka.
Ya bazan fada ba Izzatu? Banda satin da kika je kika yi a Kaduna kamar bikin Najah
ake yi kanwarki yanzu kuma kin taho nan zaki kara wani satin. Allah Ya baki sa'a,
ni yanzu nawa ido ne idan kina wannan rashin hankalin.
Tana gama magana ta tashi a fusace ta bar Izzatu a wurin. Itama nata ran a bace
yake tace ni nasan waye Hamza kuma na yarda dashi. Bazai taba kula wannan kazamar
yarinyar ba. Lokaci kawai yake jira ya saketa kowa ya huta.
Washegari tun karfe tara Izzatu ta gama shiri ta tafi dakin Raliya. Rungumeta tayi
sannan tace goodmorning Mum. Raliya ta daure fuska. What is good about the morning
Izzatu? Izzatu tayi dariya wai har yanzu fushi kike yi don nazo? Kina kallo yadda
Dad yaji dadin ganina. Tunda duk yaran nan sun koma school kamata yayi kema kiji
dadin zuwana. Raliya tace jindadi na daya ne ki koma gidan mijinki. Ina jiye miki
tsoron sharrin kishiya Izzatu. Amma, ki cigaba. Ina zaki da sassafe haka keda bakya
tashi da wuri? Izzatu tace aron mota zaki bani cikina ke dan yi min ciwo zani
asibiti. Raliya tace ki jira dreba ya kaiki dai. Wane irin ciwon ciki ne? Dan tsaki
Izzatu tayi saboda bata son yadda mamanta ke jan zancen. Nima ban sani ba shiyasa
zani.
Karfe goma da 'yan mintuna tayiwa Izzatu a wani asibitin kudi. Tayi sa'a babu layi
sosai shiyasa bata dade ba ta shiga wurin likita.
Likitar mace ce Dr Mardiya suka gaisa da fara'arta ta dan kalli file din gabanta.
Izzatu Sunusi ko? Izzatu amsa da gyada kai. Dr Mardiya tace to Izzatu meye
matsalarki. PT strip(abin gwajin ciki na gida) guda uku Izzatu ta nunawa likitan
tace ciki gareni ina jin bazai kai wata biyu ba amma ya dan wace daya. Ina so ayi
aborting din cikin bana so. Dr Mardiya tace baki da aure ne kike son zubar da ciki?
Izzatu tace ina da aure da yara uku sun isheni. Idan cikin ya zube ina so ko dai a
daure min mahaifa ko a cireta gabadaya. Bansan yadda akayi na sami cikin nan ba
bayan ina shan pills.
Sai da likitar ta gama 'yan rubuce rubucenta sannan tace tunda kina da aure bazamu
cire miki ciki ba ba tare da izinin mijinki ba sannan kuma sai munyi bincike mun
tabbatar cikin zai iya zama hatsari ga rayuwarki.
Ran Izzatu ya soma baci, kinga doctor zan biyaku ko nawa ne a cire cikin nan. Plan
dina na haifi yara biyu accidently na haifi ta ukun to sun isa haka. I am just 33
year old amma saboda haihuwa har na fara loosing shape. Boobs dina sun fara
kwanciya saboda shayarwa. Dr Mardiya tayi murmushi tace baiwar Allah ashe da gaske
ne idan dadi yayiwa mutum yawa sai yace Allah gani kasheni. Ko kinsan mata nawa ke
neman haihuwa ido rufe amma irinku da yawa sai suzo zubar da ciki. Har gara wadanda
suka yi na titi ko masu talauci akalla duk da hakan ba dalili bane amma suna da
abin fada. Ke kuwa saboda kada kiyi loosing shape zaki zubar da ciki. To ai dole
shape da kirji ya tafi tunda ko babu haihuwa akwai tsufa. Ina mai baki shawara
kije ki sake tunani zaki gane wannan abinda kike son yi bai dace ba.
Rai na kuna Izzatu ta fito daga office din likitan. Haka kawai zata sakata a gaba
da wa'azi. A Kaduna ta gane tana da cikin shiyasa ta yanke shawarar zuwa Abuja ta
zubar batare da sanin Hamza ba. 'Ya'ya uku dai ai sun ishesu. Asibiti biyu taje
bayan nan duk sai likitocin su bita da nasiha. Karshe wani pharmacy taje ta siyo
maganin zubar da ciki ta tafi gida. Yaushe zata yi ta ciki da haihuwa Hamza ya zo
ya dena ganin kyanta.
********
Zuhra da yara ta kwana a dakinta. Tala ta dauko mata pampers har uku da za'a sakawa
su Khalifa saboda duk suna fitsarin kwance. Ajiyewa kawai tayi don bata da niyar
saka musu. Tsabar son jiki na mata yara sun girma sai muyi ta kakaba musu pampers
bama tausayin masu siyowa da jikin yaran. Hamza yazo yace ta bari su kwana a
dakinsu da Tala tazo ya cigaba da jinyarta tace ita ta warke. Duk yadda yayi Zuhra
taki yarda ta kuma kwana a dakinsa. Ba komai ke hanata ba sai kunyarsa da take ji
da kuma soma sabawa da tayi na kasancewa tare dashi. Dawowar su Khalifa ya kara
tuna mata idan Izzatu ta dawo dole abubuwa zasu canza sannan uwa uba bata san
matsayinta a wurin Hamza ba. Tana so taji ina batun maganar rabuwarsu ta kwana.
Cikin dare alarm ta saka sau uku tana tashi ta kai yaran dukkansu suyi fitsari
hakan yasa da gari ya waye Junior ne kawai yayi shima da asuba ne ta sauka kasa ta
tambayi Tala me ake basu abincin makaranta. Sai da ta gama taje tayi musu wanka.
Suna breakfast Nana kuwa bata tashi ba Hamza ya sauko. Kin kula Zuhra yayi wai yayi
fushi. Dariya kawai tayi sannan ta gaisheshi. Khalifa na murna yace Daddy yau banyi
fitsari ba ni da Nana, Junior ne kawai yayi. Hamza yaji dadi sosai yace da gaske?
Khlaifa yace yes Daddy kuma Maama bata saka mana pampers ba kaimu toilet ta rinka
yi, tace duk mun girma mun zama big boys. Junior ya fashe da kuka ance yayi
fitsari. Maama ba kince sau daya nayi ba. Zuhra ta dorashi akan cinyarta sau daya
ne mana kuma gobe bazaka yi ba in sha Allah. Daddy ayi mana addu'a mu dena fitsarin
kwance. Duk wanda ya sake yi zamu cinye abin dadi bazamu bashi ba. Wani irin kallo
Hamza yake bin Zuhra dashi mai nuni da farincikinsa a fili. Yace to kowa ya daga
hannu muyi addu'a. Bayan sun gama suka dauki jakunkunansu da lunch box suka fita
waje wurin motarsa. Zuhra tana dauke kayan da suka ci abinci Hamza ya dawo ya dan
tsaya a bakin kofa Cutie bazaki rakani bakin mota ba? Yana cikin lessons dinmu fa.
Murmushi tayi tace Ya Hamza ka gama fushin? Daga hannu yayi zai dalli bakinta ta
goce, zan gamu dake ne idan na dawo ya fad yana murmushi. Kiyi min addu'a kinji.
Yau in sha Allah zan biya mutanen nan kudinsu na rabu da bashi. Tace In sha Allah
zanyi, sai ka dawo, Allah Ya tsare. Cike da nishadi kamar ba wanda yake shirin gamo
da matsin rayuwa ba ya kai yaransa makaranta ya wuce office. Yana ganin indai Zuhra
na tare dashi in sha Allah komai zai zo masa da sauki.
[10/4, 1:40 PM] #+234 815 728 4163#: AL'ADUN WASU #60
Batul Mamman(Mrs)#
Zaman Zuhra da su Khalifa abin sha'awa. Kwana biyu da dawowarsu amma sun saba sosai
da ita. Wannan ne ya ragewa Hamza radadin da yake ji a ransa na halin da yake ciki.
A yadda ya kukuta ya hada kudin nan kaf gida da account dinsa bashi da kudin da ya
kai dubu dari biyu da hamsin. Kudin man inji kadai ya ishe shi banda na mota da
sauran abubuwan da zasu iya tasowa. Gashi Izzatu ta sanar dashi motarta da suka
tafi Kaduna ta lalace a ta haya a tafi Abujan ta bar motar a gidan Kawunta . Yana
cikin tunani Zuhra ta shigo falon da sauri kamar wadda aka biyo da littafi a hannu.
Saurin gyara yanayin fuskarsa yayi saboda kada ta gane yana cikin damuwa. Ya rasa
yadda ake take sani sai kace mai gani har hanji. Dan durkusawa tayi a gabansa tace
Ya Hamza don Allah taimaka ka fitar dani kunya. Mtswwww shiyasa Baba yace na dan
maida hankali a karatu ko na koyawa yara homework ne na samu saboda kada naji kunya
wata rana. Gashi abinda yake fada yau ya faru. Suma malaman da kyuyar tsiya sai a
bawa yaro homework biyar a rana. Tunda ta fara magana Hamza ke kallonta yana
murmushi. Zuhra ta iya sawa ya manta da damuwarsa. Lebenta ya hada ya kama da
yatsunsa, to aku sai zuba kike yi baki fadi ainihin abinda ya kawoki ba. Hannunsa
ta nuna da ya rike mata baki, yana saki ta kwabe fuska shine zaka matse min baki
ko? Yace to ko na bashi hakuri ne. Matsawa tayi baya don ta tuna yadda ta kare
ranar da ta nemi a bawa lips dinta hakuri., ba sai ka basu ba na hakura.
Sake matsowa tayi ta dora masa littafin Khalifa akan cinyarsa. Na kusa minti
shabiyar na kasa gano kan aikin nan. Ina tsoron fada masa ba daidai ba yaje yaci
zero. Hamza yayi dariya ai kuwa da ya bazaki a duniya yace Maama bata iya homework
dinsa ba. Littafin ya duba verbal reasoning na 'yan nursery three. A wata takarda
duk ya rubuta amsoshin ya bawa Zuhra taje ta koyawa Khalifa kamar ita tayi. Suna
gamawa tasa suka yi shirin bacci kowa yayi fitsari suka kwanta. Ba jimawa suka yi
bacci. Kasa ta sauko dibar ruwa saboda Nana sai ta kula Hamza na cikin falonsa har
lokacin bai kwanta ba.
Sallama tayi ta shiga yasa computer da takardu a gaba yana ta aiki. Da yaji
motsinta ya dago kai suka hada ido ta sakar masa murmushi. Doguwar rigar bacci ce a
jikinta mara kauri ta daura zani a sama har kirjinta , sai hula a kanta. Hamza yace
maman yara me ya sauko dake? Tace ruwa na manta ban daukarwa Nana ba. Da hannun
yayi mata alama ta karaso gabansa. Tana zuwa yasa hannu ya kwance zanin dake daure
a kirjinta. Cutie bana son daurin kirji. Kunya ce ta kamata saboda rigar bata da
kauri ta fara shirin fita ya rike hannunta ya zaunar da ita a kusa dashi. Tun yanzu
kin dena damuwa dani saboda yara sun dawo ko? Irinku ne masu mayar da miji dan
kallo da kun haihu. A haka ma kina shareni ina ga kin haifi naki. Zuhra ta sha kunu
Ya Hamza nufinka ni ba 'ya'yana bane. Ai ko baka fada ba na sani amma a yadda na
daukeka dan uwana dole naso 'ya'yanka, ko kara ai kayi min naji dadi. Sarkin kuka
tana magana ta soma hawaye. Hamza duk ya rude, ba haka nake nufi ba Cutie ki dena
kuka 'ya'yanki ne mana. Ta share hawaye ba wani nan, don kaga ina kuka ne kace nawa
ne. Rungumeta yayi sosai a jikinsa, duk abinda kika yi yana sani farinciki da
jindadi Cutie amma bazan juri kukanki ba sai ya kara min damuwa.
Idanu sharbe da hawaye ta dago kai tana kallonsa. Ya Hamza indai kana so na dena
kuka sai ka karbi shawarar da zan baka yanzu. Lallai ma yarinyar nan dama kika samu
shine kike kuka mara dalili don ki fake ki fadi abinda ke ranki. Dariya tayi tana
share hawayen, ya akayi kayi saurin ganewa don Allah? Amma da gaske banji dadi ba
sosai don nasan dai wasa kake yi ne. To ina jinki mecece shawarar taki? Zuhra tace
dazu na kula kamar kana cikin damuwa. Hamza ya girgiza kai anya Cutie baki da alaka
da sarkin mayu. Yarinya duk yadda na boye abu sai kin gane. Dariya tayi sosai
sannan tace to Ya Hamza idan ban gane kana da damuwa ba ai babu amfani a zan tare.
Kasan ina yin saka ko? Yace Baba ya fada min. Zuhra tace to idan na hau sama zan
dauko kaga irin rigunan da nake yi. Mijin Anti Faiza ya taba samar min nayiwa 'yan
wata makaranta. Duk da ba babba bace amma akwai riba. Idan zaka iya ka nemo mana
makarantu pravate masu dan tsada ko zasu bani kwangilar sakar rigunan sanyi na
makaranta. Idan nayi kaga zamu sami wata hanyar ta shigowar kudi kafin ka gama
aikin kwangilarka a biya ka. Zuhra bata san yadda take raunanawa Hamza zuciya da
kalamanta da kaifin tunani ba. Yace Cutie ban fada miki matsalata don ki tausaya
min ki taya ni neman kudi ba. Tayi dan murmushi Ya Hamza na tabbatar ba fada min
kayi ba saboda naji dadin labari. Kullum ina tayaka addua Allah Ya saukaka maka
halin da kake ciki, to tunda Allah Ya bani iko sai na taimaka maka da abinda na
iya kafin lokacin rabuwarmu. Ya Hamza nima fa ka taimakeni, da taimakonka na san na
kula da jikina kamar kowace mace batare da ka nuna min kyama ba. Don Allah ka bani
wannan damar nayi maka wani abu. Nan gaba kila ko zumunci bazamu sami damar yi ba
idan nayi aure.
Tashi Hamza yayi ya tasheta tsaye yana kallonta cike da tsantsar kauna. Cutie nima
kin taimakeni da abubuwa da dama ciki harda gyaran tarbiyar su Khalifa. Kada ki
wahalar da kanki a kaina. Hawaye ne yake wanke mata fuska tace don Allah ka bincika
ko za'a sami masu bani aikin. Wallahi na iya sakar sosai. Hannu Hamza ya mika zai
janyota jinkinsa sai ya fasa, yanzu ina tabaki zaki ce wayon tabaki nake yi. Kinyi
min izini na rungumeki?
Rigar jikinta ta kalla sai taji kunya ta sunkuyar da kai. Ya dan leka fuskarta
please Cutie. Kai ta gyada tare da rufe fuskarta da hannuwanta. Hamza ya rage
tazarar dake tsakaninsu ta hanyar rungumeta a jikinsa sosai yana mayar da numfashi.
Bai san inda zaisa son Zuhra a ransa ba. A hankali yace kin yarda bayi kissing
dinki please? Don kunya ji take wani abu na yawo a cikinta ta kara sunne kai a
kirjinsa. Ya Hamza kunyarka nake ji. Ya dago kanta a hankali da hannunsa daya. Ko
na minti daya kawai Fatima. Bai bari ta sake sauke kanta ba ya hada bakinsa da
nata. Ita dai sai yadda yayi da ita kawai. Dukkansu a bakuwar duniya suka tsinci
kawunansu. Ko da ya saketa bai dena kallonta ba yace Cutie ko ban sami school din
ba bazan taba mantawa da wannar ranar ba. You hold a special place in my heart.
Hamza yana godiya da dukkan abinda kike masa na kyautatawa. Ita dai bata iya magana
ba ta dauki jug din ruwa ta haye sama ta barshi yana murmushi.
**********
Kwayoyin guda hudu ne a hannunta da kofin ruwa. Zuciyarta tana dan yi mata wasiwasi
sai dai gaskiya bazata iya yarda ta kara haihuwa ba. Wadannan ukun sun ishesu. Tun
kafin ta hadu da Hamza take da ra'ayin 'ya'ya biyu kawai. Rufe ido tayi ta watsasu
gabadaya daya. Idan cikin ya zube sai ta fadawa Hamza da iyayenta bata ma san dashi
ba. Tana sha ta dauki waya ta kira shi. Lokacin Zuhra bata dade da barin falon ba.
Hira sosai suka yi yana fada mata yadda yayi missing dinta. Har zuciyarta Izzatu
tasan bata kyauta masa ba amma tasan idan ya gane da cikin nan tilasta mata zaiyi
sai ta haifa. Sai da suka gama hirarsu ta masoya ta gyara kwanciya tayi bacci.
Karfe biyar da rabi wani matsanancin ciwon ciki ya tasheta. Tana kunna fitila taji
danshi a inda take kwance. Hannu na rawa ta bude bargon taga jini ne sosai a wurin.
A razane ta kwalla ihu MUMMMMM.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #61
Batul Mamman(Mrs)#
Kamar daga sama Raliya da Dad dinsu Izzatu suka ji ihunta. Kafin su karasa dakin
kaninta Walid ya rigasu. Kokarin dagata suka tarar yana yi ga jini ya jika zanin
gadon. Kuka Raliya ta saka ta soma jijjiga Izzatu sai dai ta suma bata san waye a
kanta ba. Dad dinsu yayi saurin dauko makullin mota shi kuma Walid ya ciccibota ya
sakata a ciki. Hankalinsu a tashe suka tafi asibiti mafi kusa dasu. Raliya sai kuka
takeyi tana kiran sunan Izzatu.
A yanayin da likitoci suka ganta theatre akayi gaggawar kaita ana kokarin ceto
ranta. Sai kai kawo suke yi a kofar theatre din har gari ya karasa wayewa. Suna
kallo nurse zata fito da gudu wata ta shiga. Tsahon lokacin nan babu irin tunanin
da iyayenta basuyi ba. Suna nan tsaye jugum jugum Raliya tace idan ka taho da waya
ya kamata a sanar da Hamza. Alh Sunusi yace haba Raliya, ya za'ayi mu kirashi a
wannan lokacin bayan muma bamu san aininhin abinda ke damunta ba. Ko kin sani? Cike
da damuwa Raliya tace ni bansani ba kuma banga wata alama ta rashin lafiya a tare
da ita ba. Likitoci biyun dake kan Izzatu ne suka fito a tare bayan fiye da awa
daya da sukayi a ciki. Daya daga cikinsu ya dubi Alh Sunusi yace ku biyo ni office.
Raliya tace Doctor kawai ka fada mana a nan idan ta cika. Yayi murmushi noooo
Madam, ki kwantar da hankalinki. She is stable now.
Duk su biyun sun tsirawa liktan ido suna jiran bayaninsa. Glass din idonsa ya cire
ya goge fuskarsa da hankice....duk motsinsa Raliya kamar ana tsikarinta take ji. So
take kawai tasan abinda ya sami Izzatu. Likita yace "yallabai menene matsayin
patient dinnan a wurin ka?"
" 'Yata ce" Alh Sunusi ya amsa masa.
"Tana da aure ko budurwa ce?"
Raliya ta kagu ya fadi abinda ke faruwa tace "matar aure ce harda 'ya'ya uku.
Mijinta yana Kano".
Sai da yayi 'yan rubuce rubuce sannan yace "patient dinnan tasha maganin zubar da
ciki overdose. A ka'idar wanda tasha ma guda daya ake sha amma da kyar ta iya fada
mana hudu tasha a lokaci daya".
Cikin rashin fahimta Alh Sunusi yake tambayar Raliya dama Izzatu nada ciki tace
itama bata da labari.
Likita yace to a gaskiya ba karamin ganganci tayi da rayuwarta ba domin da kyar
muka iya ceto rayuwarta da ta abinda ke cikinta. Tunda yana da lafiya bamu