Advertisements
Chapter 30 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   30 / 36

87K to 90K   out of 106K words

dajin ta tafi da sauri ta shiga ta rufe kofar harda saka
kwado. Juyawar da zatayi idonta ya sauka akan sojoji da bata san iya adadinsu ba.
Dariya suka fara yi mata kafin su saita ta da bindiga su fara harbi.

Hajiya tana idar da sallah ta juya gefen gado inda Zuhra ke kwance tana ta mutsu-
mutsu duk ta hada gumi. Da sauri ta tashi ta tsaya a kanta ta fuskanci kowane irin
mafarki take yi ba na lafiya bane. Kafadar Zuhra ta dafa da niyar tashinta Zuhran
ta tashi a razane tare da kwalla kara. Ganin Hajiya yasa ta kankameta sai kuka ya
kwace mata. Hajiyan tana rarrashinta tana kokarin mayar da hawayen da yake
barazanar fitowa daga idonta. Tashin Zuhra na uku kenan tunda suka kwanta. Kamar ta
sani ta hanata kwana dasu Hamida tace ta dawo dakinta. Sai da Zuhra tayi shiru
sannan Hajiya tace...ki tashi kiyi sallah ba'a dade da kiran assalatu ba. Kuma ki
yawaita addua nima zan cigaba da yi miki musamman na kwanciya saboda wannan mafarke
mafarken da kike yi.
Jiki a mace Zuhra tace to Hajiya sannan ta tashi ta shiga toilet. Tun faruwar
wannan al'amari 'yan awanni da suka wuce Zuhra da Hajiya suka manta da kunyar juna
irin na surukai.

Bayan ta idar da sallah ne Mama ta shigo dakin da gani itama sallar tayi. Zuhra ta
gaisheta ta amsa fuska a sake sannan ta tambayi Hajiya ya suka kwana...wallahi jiya
Alhaji baiyi baccin kirki ba duk ya damu. Kusan a zaune muka kwana.

Hajiya tace to ai nima bamuyi baccin ba. Sau uku bacci na daukarta ta tashi a
firgice. Allah Kaltume da sakin Izzatu a hannuna yake sai da yaron nan ya dawo ya
tarar ta dade a gidansu.

Mama tayi murmushi, Hajiya Halima bata taba sanya kanta cikin lamuran 'ya'yanta
musamman Hamza da ya kasance na fari. Wannan maganar tata ta kara tabbatar da cewa
ba karamin bacin rai abinda Izzatu tayi ya sanyata ba. Haka suka zauna suna taba
'yar hira har gari ya karasa wayewa Mama ta tafi kitchen tare da Hamida wadda ita
ce mai tayin abincin safe yau.

****
Dayake jirgin Emirate Hamza ya hau sun tsaya a Abu Dhabi canjin jirgin da hutun awa
biyu. Wayar Zuhra ya rinka kira yanzu ko shiga ma bata yi. Hankalinsa yayi matukar
tashi. Da ya kira Izzatu bayan sun gaisa lokacin karfe takwas na safe tace masa
Zuhra bata fito daga daki ba. Hankalinsa gabadaya a tashe yake. Yace taje ta
kwankwasa mata kofa tace yace ta kunna wayarta. Izzatu tace ita bazata je ba ta
kashe wayarta ma a cewarta kada ya dameta ita babu ruwanta da matarsa. Haka ya
hakura ya kira iyayensa suka amsa wayarsa kamar babu abinda ya faru. A hira ne ya
sanar da Mama ya kasa samun Zuhra tun daren jiya bayan ya shiga jirgi. Mayar da
zancen nasa wasa tayi har tana cewa ko zai biyata ne taje ta gano masa lafiyar
amarya. Shi dai jikinsa duk babu dadi har ya sake shiga jirgin da zai kaisu
Thailand wanda daga shi zasu shiga mai kaisu South Korea.

*****
Tunda Izzatu ta ajiye wayar Hamza jikinta yayi sanyi. Jiya dai lafiya kalau tayi
bacci amma tunda ta fuskanci Zuhra bata dawo gida ba hankalinta ya kasa kwanciya.
Ita fa a tata wautar ba niyarta wani mugun abin ya sami Zuhra ba. So tayi ta bata
wahala karshe kila ta biyo motar haya a daren. Tunani tayi ko an saceta a hanya
taji wani mugun tsoro ya shigeta. Sai yanzu take danasanin abinda tayi domin batan
Zuhra ba karamin abu bane. Daga baya tayi tunanin ko gidansu Zuhran ta wuce sai
tayi dariya. Karshen abin kenan kila ta koma gida ne tana son ta hadata da Hamza.
Indai hakane kuwa ko a jikinta don tana da bakin kubutar da kanta. Tun daga wannan
lokacin hankalinta ya kwanta.

Mama ce da kanta ta kira Tala wadda take ta hada kaya cikin kwanciyar hankali
saboda Hamida ta tabbatar mata da anga Zuhra amma Alhaji yace kada ta kuskura ta
fadawa kowa. Mama tace tasan yadda zatayi ta dauko wayar Zuhra a motar Hamza ta
kawo mata gida. Wurin maigadi taje ta fada masa. Sai da rana ta fito yace Tala ta
fada mata yace zai wanke mata motar yaga datti a ciki. Babu musu Izzatu ta leko ta
tagar dakinta ta danna remote ta bude masa motar. Dama tana son zuwa shopping
anjima.

Motar ya bude ya dauko wayar ya bawa Tala. Ita kuma bata dade ba tayi sallama da
Izzatu ta dauki kayanta da sunan ta tafi kauye. Gidansu Hamza ta fara zuwa inda su
Adabiyya suka labarta mata abinda ya sami Zuhra. Tala tayi kuka sosai sannan ta
kawo wayar ta bawa Mama. Da aka kira Zuhra ta fito suka gaisa dukkansu sai da suka
yi kuka. Tala tasan uwargidan nasu sai a hankali amma bata taba tsammanin abin nata
yakai ta aikata wannan rashin imanin ba. Tayi musu sallama kuma su Hajiya suka kara
mata guzuri ta tafi.

Wurin shabiyun rana Alhaji ya tara iyalinsa harda na gidan miji su Jidda da Mariya
aka sake sanar dasu halin da ake ciki. A nan ya fada musu cewa bai yarda wata ta
nuna tasan inda Zuhra take ba har Hamza ya dawo. Daga masu hawaye suna tausayin
Zuhra sai masu zagin Izzatu da yi mata muguwar addua. Bayan sun tashi Alhaji ya
wakilta Mama taje tasan da yadda zata yi ta daukowa Zuhra kayan sawa kafin ya dinka
mata wasu. Bayan sun fita yace da Hajiya ta shirya ita da Zuhra zasu je unguwa.

Ibrahim ke jan motar har iya inda mota ke shiga a layin gidansu Zuhra. Yana tsayar
da motar Zuhra ta fita da gudu ta shige gida.

Umma da Baba na zaune a falo suna jiran Safara'u ta gama girkin rana zasu je Ajingi
barka maman Safara'un ta haihu.

Kamar an jehota Zuhra ta fada kan Baba tana kuka. Daga shi har Umma hankalinsu ya
tashi suna tambayarta abinda ke faruwa ta kasa magana. Sallamar Hajiya ce ta
katsesu Umma ta tashi ta tarota. Bayan sun gaisa ta fadawa Baba tare da Alhaji
suke. Da kyar ya daga Zuhra daga jikinsa ya fita ya shigo dasu shi da Ibrahim.

Bayan sun zazzauna Hajiya ta kalli Zuhra da ta lafe jikin Umma, ita kuma Umman tana
shafa mata baya tace...lallai Zuhra ke 'yar shagwaba ce ajin karshe. Umma taji
kunya ta soma ture Zuhra. Baba yace dawo daga nan uwata nima ina da jikin da zaki
tumurmusa. Kasa karasawa tayi ta sunkuyar da kanta saboda kunya. Ita ta manta ma da
surukanta a wurin. Umma da Baba kuwa indai Zuhra zata yi kuka to basu da kwanciyar
hankali.

Alh Nasiru yace nasan zakuyi mamakin zuwanmu a wannan lokacin kuma a irin wannan
yanayin. Dole ce ta kawo haka domin bahaushe yace ranar wanka ba'a boyon cibi. Daga
nan Alhaji ya warware musu gaskiyar lamari game da auren Hamza da Zuhra. Baba da
Umma duk mamaki ya ishesu yadda Zuhra bata taba nuna musu ba auren soyayya tayi ba.
Alhaji ya cigaba da cewa a yadda na fahimta Yaya da Zuhra suna son junansu yanzu
duk da irin abinda ya faru kafin auren.

Baba ya rike hannun Zuhra yace kada ki cuci kanki kinfi karfin wulakanci muddin ina
raye. Ki fada min gaskiya idan ba kya son auren sai a waraware. Kana ganin Baba
kasan ba karamin bacin rai yaji ba game da labarin April fool da aka yiwa 'yarsa.
Kanta a kasa Zuhra ta kasa magana sai kara rike hannun Baba da take yi. Hakan da
tayi ya bashi tabbacin tana son mijinta. Da akasin haka ne kiri kiri zata masa da
ido yadda tayi da ya taba cewa yaron shagonsa yana sonta. Ya dago kai ya kalli
Alhaji...to yanzu menene yake faruwa kuka dawo da ita gida daga tafiyar Hamzan
jiya?

Alh Nasiru bai damu da yadda Mal Bashir ya canja ba. Abinda yafi haka ma yana da
ikon yi akan 'yarsa. Babu uban da zai zuba ido yaga ana wulakanta masa 'ya'ya komai
talaucinsa. Alhaji ya sake fada musu abinda Izzatu tayiwa Zuhra a daren jiya. Kuka
ne ya kwacewa Umma sosai ta rungumo Zuhra jikinta har rawa yake. Da da ajali a kusa
babu abinda zai hana sojojin nan harbe Zuhra. Hajiya ma wani kukan take tayata.
Hakika duk da rashin wadata sosai amma gidansu Zuhra gida ne mai cike da soyayya a
tsakanin iyayen da tilon 'yarsu. Baba ma idanunsa ja suka yi sosai. Alhaji yace na
zabi fada muku gaskiya saboda halin rayuwa. Ba don mai aikin gidansu ba da tayi
tunanin sanar damu da karshenta yau labari yasha bamban. Mal Bashir ina mai baku
hakuri da neman afuwarku. Wallahi idan Yaya ya dawo zan dauki mataki akan shegiyar
yarinyar nan.

Mal Bashir ya kalli Zuhra yace babu wani abu da ya sameki ko? Tayi masa murmushi
Allah babu komai. Yace to Alhamdulillahi sai mu jira Hamza ya dawo lafiya ya baki
takardarki. Yau ko akuyar gidan nan kike bazan yarda ki koma inda akayi miki wannan
diban albarkar ba, bare 'yata. Alhaji kuyi hakuri amma bazan bari ku koma da ita
ba. Ita kadai Allah Ya bani idan ka duba da wuya idan bamuyi sa'anni da kai ba amma
sai a kanta haihuwa ta tsaya tsaya mana. Wallahi duk kawaici irin na mutumin kauye
bazan iya dauke kai ba idan abu ya shafi uwata. Gara na aurar da ita a kauye da ta
fuskanci rayuwa irin wannan. Umma ta nuna ta goyi bayan mijinta.

Alhaji da Hajiya suka shiga bawa su Baba baki amma kememe Baba yace shi fa bazai
yarda ba. Ibrahim yace Baba idan bazaka damu ba ka bani damar magana. Baba yace ina
jinka amma bazan canja kudirina ba. Murmushi Ibrahim yayi sannan ya sanar dasu irin
canje canjen da ya gani tattare da dan uwansa bayan aurensa da Zuhra. A takaice
abinda iyayensu basu sani ba dangane da irin taimakon da tayi masa bayan
durkushewar kamfaninsa a dalilin Izzatu duk sai da ya fada musu. Mamaki sosai suka
yi Zuhra ta sake samun masauki a zuciyar surukanta. Ibrahim yace shekaranjiya yazo
har office ya sameni ya sanar dani komai yace wasiyyace ya barmin saboda yanayin
tafiya idan har bai dawo ba kada na taba bari ta wulakanta a duniya.

Wannan jawabi na Ibrahim ya sanyaya zuciyar iyayen Zuhra ita kumq yasata kuka sosai
tare da dagewa wurin yin addua Allah Ya bashi sa'a kuma ya dawo dashi lafiya.
Alhaji Nasiru yace bukatarsa daya a wurinsu kada su taba cewa sunsan inda Zuhra
take domin Izzatu da hannunta zata girbe abinda ta shuka.

****
Mama da su Hamida ta tafi gidan Hamza. Ihun su Khalifa Izzatu ta ji suna murnar
ganinsu ta fito daga kitchen a tsorace. Ba dai can Zuhra ta tafi ba. Ai kuwa tasan
Alhaji sai ya bata mata rai. Ga Mama itama wata mara son nata. Gashi uwa uba bata
san takaimaimai inda Zuhra ta tafi ba. Har wayarta ta gwada kira bata samu ba.

Da dan cokalin miya Izzatu ta fito tana murmushin da bai kai zuci ba tayi musu
sannu da zuwa. Mama ta amsa fuskarta a sake tana tambayar ya suka kwana. Izzatu
tace lafiya kalau Junior yace amma yau tun safe bamu ga Maama ba. Inata kiranta
bata amsa ba. Izzatu ta make shi sannan tace tana dakinta kila bacci take yi. Mama
tayi 'yar dariya tace su Hamida su duba mata. Dama da wata jaka mai dan girma da
Adabiyya ta sako cikin hijab. A gaggauce suka debo mata kayan sawa, 'yan ciki da na
bacci suka sauko. Hamida tace Mama da gaskiyar Junior Anti Zuhra fa bata dakinta..

Cokalin hannun Izzatu ya fadi don tsoro tace au na tuna tun safe ta tafi gidansu
tace a can zata yini.

Adabiyya da Hamida suka kalli juna suna dariya kasakasa. Mama ta dauke kai kamar
bata gansu ba tace to ga wannan dama Alhaji ne yace na duba ku. ..dubu biyar ta
bawa Izzatu...idan Zuhran ta dawo ki gaidata. Daga nan suka fita suna mamakin
karyar da Izzatu tayi musu.

Suna fita tayi ajiyar zuciya hankalinta ya kai karshen tashi. Yanzu idan Zuhra bata
dawo ba ina zata fara nemanta? Dole ta kai cigiya wurin 'yan sanda tun kafin a kara
dawowa nemanta.

****
A gidan Zuhra ta yini sai dare Nura ya dawo ya dauketa saboda washegari zasu tafi
Ajingin da suka fasa zuwa a yau.

Tana zuwa gidan wayarta tayi chaji. Sakonnin text goma ta gani na Hamza masu nuna
damuwarsa da rashin samunta a waya. Wurin shadayan dare ya sake kira lokacin suna
masaukinsu a wani hotel. Ba karamin dadi yaji ba da ya sameta. Tayi ta bashi hakuri
akan cewa wayar ce ta fada kasan kujera a motar bata ganta ba. Hirarsu suke ta
masoya har Hamida da Adabiyya suka bar mata dakin suna tsokanarta don ta dage ita
wurinsu zata rinka kwana. Alhaji yace kada ta nunawa Hamza komai yanzu saboda kada
ya kasa yin abinda ya kaishi. Ta nuna masa tana gida kamar yadda yake tunani.

****
Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Alhaji babu irin gatan da su Hajiya basa
nuna mata. Haka sauran 'yan uwan Hamza ma. Umma da Baba kullum sai sun kirata a
waya. Lokacin da ta cika sati biyu ne suna kitchen ita da su Hamida suna aiki Zuhra
tana wankin nama taji zuciyarta na tashi. Abu kamar wasa ta fara cewa naman yayi
karni da yawa Adabiyya tace ai kuwa yana da kyau. Bata kara magana ba ta soma amai
kamar kayan hanjinta zasu fita. Kofar kitchen din ta baya ta fita tayi aman tana yi
tana kuka. Hajiya da Mama aka kirawo suka shigo kichen din. Ita dai Hajiya tana
ganin aman da Zuhra take yi murmushi kawai tayi ta ja da baya, Mama ta wuceta ta
taimakawa Zuhra. Yadda take aman har kirjinta na amsawa yasa take kuka. Mama tace
oh ni Kaltume haka kike yiwa Yaya wannan kukan shagwabar? Gaskiya Umma Atine ta
shagwaba mana 'ya. Hajiya na daga gefe tace don ba tare muka je gidan dake ba da
kinsha kallo. Yadda kika san ta shige ciki. Zuhra duk kunya ta kamata ta tashi da
gudu. Mama tabi bayanta da sauri tana dakatar da ita...haba Zuhra yanzu kuma ai
lokacin tattalin jikinki ya kama sai kinbi a hankali. Bari na kira Nura a waya yazo
ya kaimu asibiti don a tabbatar mana da abin alkhairi. Kan Zuhra a kasa ta kasa
cewa komai. Itama tana zargin abinda Mama take fada saboda 'yan alamun da ta gani
daga irin hirar 'yan mata da kawayensu. Da yamma suka je asibiti aka tabbatar tana
da ciki wanda ke cikin watansa na biyu. Tun a hanya Mama ta kira Hajiya harda
Alhaji tayi musu kyakkyawan albishir. Siyayyar 'yan kayan kwadayi tayiwa Zuhra
wadda don kunya ta rufe fuskarta da mayafi.

Shima wannan labarin bata sanar da Hamza ba a lokacin da sukayi waya. Tafi son ya
gani da idonsa. Sai dai suyi ta hira yana tambayarta me tayi yau. Kulawa kuwa a
wurin 'yan gidansu sai godiyar Allah.
****
Izzatu sam bata da kwanciyar hankali a gidanta. Ga Tala ta tafi gida ga yara su
dameta. Junior da Nana sunki yarda ta saka musu pampers ko ta saka musu sai sun
cire. Dakinta har zarni yake saboda fitsarin da suke mata a kwance. Kafin ta gama
girki kullum sai Nana tayi kuka saboda ta riga ta saba da kin dorawa da wuri. Idan
ta zuba musu anjima kadan suce yunwa tunda bata zubawa da yawa. Duk wannan bai
dameta ba kamar rashin sannin inda Zuhra take. Hamza dai ya dena tambayarta Zuhra
shiyasa take mamaki. 'Yan kwanakin nan har mafarkinta take yi. Don tsananin tashin
hankali ko shara bata yi a gidan ga uba wanke wanke ta tara. Tunani ne ya isheta
wata rana bayan ta dauko su Khalifa daga makaranta ta wuce airport. Ya zama dole ta
fara neman Zuhra tun kafin Hamza ya dawo kashinta ya bushe.

Daga bakin gate tayi parking ta fito ta tafi wajen masu karbar kudin shiga ta
tambayesu ko sun ga wata mata da bata wuce shekara ashirin da daya ba sati biyu da
suka wuce da daddare. Wanda ta tambaya yace ranar bashi bane da aiki amma bari a
tambayi sojojin saboda yawanci a nan suke.

Da tafiyarta ta 'yan gayu ga takalmi mai tsini Izzatu tabi bayansa zuwa wurin
sojojin. kafin su karaso yawanci duk sun taho wurinsu. Mutumin ne ya tambayesu
abinda Izzatu tace ai kuwa wani gabjeje a cikinsu ya daka mata tsawa yace tayi
kneel down a nan. Kamar ta saki fitsari don tsoro tayi abinda yace tana rarraba
idanu. Ya kalleta sama da kasa yace...chege kaine ka bar kishiya a nan ko?


Izzatu tayi saurin girgiza kai alamun ba ita bace.

Wasu mutum biyu suka nunata da bindiga tayi saurin cewa nice, wallahi nice.

Katon yace dama kaine kawai zaka ki zuwa nemanta sai bayan two weeks. Mugu yau sai
munci ubankaaaa. Ya fada yana wata irin dariya mai ban tsoro.

A take Izzatu taji saukowar fitsari daga mararta saboda tsabar kidima.
[10/23, 5:48 PM] #+234 806 611 3313#: AL'ADUN WASU #75

Batul Mamman(Mrs)#




Wani soja musulmi wanda baiji dadin lokacin da suka sa Zuhra cire hijab ba, don
babu yadda zaiyi ne saboda yadda ake amfani da hijabi ana cutar mana da addini da
sauran musulmi. Muguwar harara ya dankarawa Izzatu sannan yace banda kneel down ta
daga hannu sama. A dole tabi umarninsa babu inda baya rawa a jikinta. Tana daga
hannu mayafinta yayi sama sai ga shatin fitsari a jikin zanin shaddarta. Kafin ta
ankara ta rufe wurin sun gani suka rinka dariya. Sauran mazan dake gefe ma dariyar
suke yi. Izzatu yau taga wulakanci irin wanda bata taba gani ba.

Daga nan suka rinka yi mata fada akan me zata bar yarinyar mutane a airport da
tsakar dare. Ita dai Izzatu babu bakin magana bare ta tambayesu ina suka ga
yarinyar tayi.

Su Khalifa ne suka hango mamansu daga cikin mota a wannan yanayi suka soma kuka.
Wani soja da yaso sata tsallen kwado ya kula da yaran ya fadawa ogansu. Ogan yace
to albarkacin yaran nan ta koma motarta da rarrafe sannan sun bata sati daya ta
nemo kishiyarta ko su zo har gida su tafi da ita.
Abin tausayi haka Izzatu ta rinka rarrafe akan gwiwarta duk tsadar shaddar jikinta
haka ta rinka jan jiki zuwa motarta. Khalifa da Junior sun sha kuka. Itama da kukan
ta karasa wani soja yana binta a baya yana zungurinta da kasan bindiga.

Tana shiga motar Khalifa yace Mummy laifi kika yiwa Uncle dinku ya saka ki kneel
down?

Idonta ta share tace a'a Khalifa takalmi na ya tsinke shine na gwada yadda muke yi
da muna yara.

Motar ta tayar sai dai ga mamakinta sojoji biyu ne suka shiga wata motar a bayansu
suka bi bayanta. Zuciyar Izzatu har bugawa take don tsoro tace yau na shiga uku.
Maimakon ta tafi gida haka tayi ta yawo a titi. Tun su Nana na kukan yunwa har duk
suka yi bacci don wahala. Man motar har kusan karewa yayi ta shiga gidan mai.
Motoci wurin goma ne a gabanta amma bata damu ba. Burinta kawai wadannan sojojin su
gaji su dena binta. Lokacin da ta fito daga gidan man tayi sa'a bata gansu ba. Sai
biyar

30 / 36