Advertisements
Chapter 29 Reading MASIFAFFAN NAMIJI by Jamilaumar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MASIFAFFAN NAMIJI by Jamilaumar

Author :  Jamilaumar Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 48

84K to 87K   out of 143.7K words

gabansa Allah Barshi bayan anyi sai ya maida Hankali ko loan zai iya ci a Wajen aikinsa Ya karisa komai kafin Hafsah ta Haihu Allah barshi a rika Cireewa a albashinsa.

Sai 2pm na Rana suka Rabu da Abdlullahi a gidan Mama ya barsa ya koma gida Shi kuma ya Shiga Dakin Auwal jidda tazo ta sameshi sukayi Hira Duk dai kan mganar tsare tsaren Biki ne La"asar nayi yayi mata sallama Ya wuce bayan ya zo mata da leda guda na Shopping din kayan kwalliya jidda sai wani yanga ake Mariya da Auwal na mata Dariyan Da tace bataso Mama ce ke Shiga Cikin mganar tace akyalemata autanta Da Daddare sai ga Baba wada yazo Shi ya kora ma Mama yadda komai ya Gudana yace ta kwantar da Hankalinta komai ya wuce taji Dadi Har ranta Tana ta mai godiya.


*******

Tafe Tafe kwana Nesa Wuni yana karewa muna Shiga kwana,kwana yana karewa muna Shiga Satittika,Satittika yana kwarewa muna Shiga Shekara da Haka muke Cinye Sauran kwanakinmu a Duniya Bamu sani ba Allah ka Bamu Dacewa Ameen.

Gashi yau Bikin Jidda Sauran Sati Hudu Cif ta kowani Bangare Shirye Shirye keta Gudana Ta Bangaran Abdullahi Kuwa Kudi ya Bada Mama da Ita kanta Jiddan da Subai"atu suka je Jaji suka Zabo mata Kujeru da gado da Katifa masu kyau da Tsada, masu kyau Ita kuma Zannira tayi mata Gadon karfe da kuma kayan Kallo sai Subai"atu datayi mata Fridge,da Labulai sai Center Cafet,Hajiya Sa"a kuma Taga ba Sarki sai Allah ta saki Tunda dai Auran nan na yarta ce ba na wani ba Tuni ta watsar da komai ta shigo Cikin gida anayin komai da ita,shi kanshi Nazifin yanzu a gidanta ya zama Dan gida Tunda Tun bayan Faruwar haka indai yazo Zai Dauki jidda Ta rakashi Suje ya gaisheta Tun Tana wani basarwa Har tazo taDaina Hakama Hajiya Lariya itama yaje gidanta wajen Sau Biyu Sun gaisa ita ta sakama Jiddan ta Rakashi Family Hause din Mamarsu ya gaisheshi Suka ganshi Harda Babban gidansu na na Barayin Inda su Nazifin suka Taba zuwa Wani Lokacin ma in ya Shigo Garin a Chikan yake samunta in taje ma Sa"ar Weekend,Yanzu kuma Tsakanin Jidda da Nazifi wata irin Soyayyace mai karfi da Shakuwa ta Shiga Tsakaninsu in ka gansu sai kace Damam chan Masoya ne Nazifi dan Rayuwa ne yasan kan Mace Sosai kawai waje ne bai samu ba sau yanzu matukar so da kulawa yake nuna ma Jidda itama Haka sai dai Tana Kokarin Bashi Girmansa a matsayinsa na abokin yayanta gefe Daya,kuma Suna Shan Soyewarsu.

Goggo Habiba 50k ta kawo Gudummuwa Da nata dana Ya"yanta Domin Bata da bakin Godema Ya"yan yayan nata Kowani Sha"ani da Jiikinsu da aljihunsu ake musammanma Yaya Abdullahi sai Ammi ma 50k Hafsah ta kawo Mama taji Dadi Harda Hawayen Dadi,Sai Umman Sadiq itama ba"a barta a Baya ba 30k ta aiko ma Abdullahi tace Gatata Gudummuwar nan Mama ma yan"uwanta sun Hadamata Dubu 50k Dashi a kahada akaje kano akayi ma Jidda Siyayyar kayan Kitchen da Duk Abun ya kamata Tunda Flat House ne mai Dan Girma Nazifin ya kama anan Famwaki Tunda ginin dai bai gamu ba nan za"a yima Jidda Jerenta in sun gama Cin amarsun zai mai data kaduna,Daman Dubaran Hakan in ya tashi komawa Sabon gidansa basai an Wahala ba Tunda wanchan gidan Sakina Ta Cikashi da kayanta sai ya barmata Sai ya yanke Hukunci na Zaria gidan Jidda ne,In sunzo basu da mtsala wajen Sauka Chan kaduna kuma ko Dakinsa Zasu zauna Suyi Rayuwarsu Cikin Soyayyah da kaunar Juna.

Hajiya Sa"a Tazo Ta Tambayi Mama Abunda Ba"a siya ba Mama tace komai an Siya sai Abunda ba"a rasa ba Wannan Dalilin yasa Mama ta mata Bayanin komai kawai sai takoma Gida sukayi mgana da Lariya sukaje suka Siya katifa da Fridge Babba mai Biyu sai Gas na Zaune mai Shidda,sai Labulai da kuma Zannuwan gado,Dama tana da wasu Datazo mata dashi Daga Chan Saudiya,sai wasu Expansive kololi masu kyau da Tsada Data kara mata,sai Home Theater,Sauran Abubuwa dai masu Tsada ta Siya dasu Dinning Kuma Bayan sun yo Siyayyah Direct Gidan Mama ta wuto Dashi Mama nata Godiya Sosai Abdullahi ma Dayazo ya gani bai ce komai Ba Duk da yanzu ba irib da Bane suna gaisawa sama sama da Hajiya sa"an.

Bangaran Amarya da kawayenta Kuwa Rumana ne sai wasu Wadanda suka gama Makaranta Tare,sai Mariya 50k suka nema ya basu na Walima da Shagalin Biki,Kayan akwati kuwa Wata matar abokinsa ta Hada komai akwatuna Bakwai,Shake da kaya sai Wanda yagani Da kanshi ya kwaso ya kai gidansu Su Inna Abu suka gani,Sai da Biki ya Rage Saura kwana Goma kana Aka Hadu aka kai kayan Yan"uwan Inna Abu da makota sai kannensa Suka kawo kayan Gidan Mama acikin masu karban kayan Harda Hajiya lariya  Sa"a dai Tana gida Masha Allah kaya Sunyi kyau Sosai Dayake Abun Gidane haka aka gama ganin kaya ana saka albarka Sunci Sunsha Harda Tukwaici aka basu suka Ki karba sai da Zannira ta matsa kana suka karba Dayake Tazo Ranar da za"a kawo kayan Dasu Hafsah wacce Cikinta dan Wata Shida gayinan ya Fito yayi Girma kamar CikinFari.

Baba wada ne ya Kira Nazifi yana Tambayanshi yako gayama Matarsa Sakina yace "A'a ammh Cikin Satinan zai gayamata.."Fada Baba wada ya Fara mai yana Fadamai bai kamata ba Tana da Hakki ya gayamata zai kara aure yace Insha Allahu zai gayamata Dama yayi Niyyar sai ya samu wasu Kudi a Hannunsa ne ya Damkamata Na siyayyarta in ta karba Shikenan in bata karba ta Rasa Da Haka suka Rabu da Baba wada Wanda shi Daman ya Riga ya Bari sai in tazo Weekend din wannan Satin Tunda Rabonta da kaduna wajen Sati uku kenan Toh a ina zai ganta..? Shiyasa bai Fadamata ba har yanzu...!

******

*Kaddara ta sake Hadasu...*

Yau Ta kama Jumma"a wacce tayi Daidai da Saura kwana Takwas Bikin Jidda da Nazifi da misalin karfe 6:30pm na yammah a Kofar main get na ABU SAMARU,yan makaranta ne Birjit suna Tsaye wasu kuma Suna Tafiya ne,Ayayinda wasu kuma ake ta zuwa Daukansu,Kowa dai kagani yana ta Haraman komawa gida ganin Ga Mangariba ta kawo Jiki kuma Dare ya Fara Shiga.

Tana Tsaye a bakin Titin Duk inda Hankalinta yake yakai kololuwar Tashi ganin Duhu yayi bata samu Bus ba,Koda tazo duk sun Cika,agogon Fatan Dake Hannunta ta kaima Duba Lokaci Daya ta saki karamin Tsaki acikin Ranta tana jin Takaichin Rashin samun accomadation da batayi ba,dayake ta Shiga aji Hudu da ta samu mai zai jamata wannan Jiran,Yanzu ita Tunaninta ma Daya koda ta samu Abun Hawa Lokacin da zata bata kafin ta kai gida Shine Abun Tunaninta,Sake sakin Wani Tsakin Tayi tana gyara zaman gyalen Abayar Dake Jikinta.

Doguwar mace,wacce ke sanye da wata bakar abaya da gyalensa tayi Rolling,sai Kafarta sanye da wani bakin Takalmi mai tudu Katadarta Rataye da wata bakar Jaka sai Hannayenta Dauke da wasu manyan littafai na karatu Fuskarta sanye da wani Farin gilas na gayu,Daga ganin Fuskarta Tana Cikin Damuwa Duk da bata son Hawa mashin Sai ta yanke Shawaran Bari kawai ta Hau mashim Din Tunda bata da mafita Hannu ta sanya tana Tsaida Masu mashinan ammh su kansu sunki Tsayawa.

Fitowar Abdullahi kenan Daga Cikim makaranta Shima ya tsaya yin wani Abu ne yasa yakai yammah haka,Ya fito kenan yana Kan Mashin dinsa kamar wasa ya Hangota tana Tsaye kamar tana Tsaidashi har ya wuce Sai kuma yayi wani Tunani kawai ya Juyo yana Tunanin mace ce kuma ga Dare ya Kawo Jiki Tana Bukatar Taimako Shi kanshi bai Taba Daukan wata mace a mashin dinsa ba in ba Hafsatu ba ammh sai gashi yau ya tsaya gaban Wata mace yana Tambayanta inda zata Abunda bai san ya akayi hakan ta Faru ba.




*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*




*Anitha...*
4/9/21, 1:58 PM - 😂😂: *MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*

*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!



*028*

"ko a mafarki Taji wannan Muryan bazata Taba mantawa da ita ba Muryan Datake kwana Da ita Tatashi da ita cikin Ranta,Muryan da ko Mutuwa tayi ta Dawo Bazata taba mantawa da ita ba..

Idanuwanta Dake Cikin glass ta Zaro Tana kallon Abdullahi Shima ganin irin kallon Data kemai ne yasa ya Zura mata ido yana Binta da kallon mamaki Gefe Daya kuma na Zuciyarsa na so ya Tuna inda ya san Fuskarnan Tunda wajen akwai Wadatar Filitu masu Haske sun Haske Fuskarta Sosai.

Ya Bude baki yana Shirin yayi mgana Wata Budurwa Dake karisowa kusa dasu Ta kira Sunanta.."BARKAT SHEHU...'"Tafada Tana Dafa kafadarta Lokaci Daya Da Mamaki Abdullahi ya kara Bude Manyan Idanuwansa yana kallonta sai da aka Kira Sunanta ya Tuna inda ya santa Gidansu Salisu Karya wuya yayi yana kallonta yadda ta Juya tana mgana da wacce ta Kira Sunanta.

"Barkat kin samu Leap ne..? Zaman Littafan Hannunta Barkat tagyara tana Fadin"A"a abokin Yayana ne zai Ragemin Hanya..Dare yayi gashi Ban samu Bus ba.."Yana jinta Sai da ya kara kallonta Cikin mamaki acikin Ransa kuma yana Fadin komai nata bai Sauya ba,Sallama sukayi da yarinyar kana ta kariso kusa Dashi  Tana kallonsa Ido Cikin Ido Tace"Tudun Wada zani.."

Ta fada Cikin yanganta da kuma Jin kai,Shima kai tsayen ya kalleta yana Fadin"Ok...Allah ya sa zaki iya Hawa mashi..Kinsan Abunka ga Talaka da ita muke Lallabawa..."Kai Tsaye yana kallon Gefenta Saboda bayason kallon kwayan idanuwanta yana jin Wani iri acikin Ranshi.

Kai ta Rausayar Tana Fadin"Waye Ubana da zanje Bana Hawa mashin..? Muje Allah ya kaimu lafiya..'Jin haka yasa ya karkata mata Mashin Din yadda Zataji Dadin Hawa Rigarta ta Tattaare ta kasa,Dama kuma Barkat bata iya Hawa Mashin ba sam,Ta Yunkurawa ta Hau sai Littafan Hannunta suka Subuce suka Fadi kasa,Tsayawa tayi Tana kallonsa Cikin Wata Shagwababbiyar Fuskar da bata san Tana Dashi ba Saurin kauda kai yayi yana Fadin"Kamar kaya yayi miki yawa ko..?kwaso na Rike miki Anan gaba.."Da sauri ta Duka ta Tattaro ta mikamai ya karba Tana kallonsa Tace'Nagode..."

Duk yadda yayi mata Wajen Hawa sai da ta kusa Faduwa Yayi Saurin Riko Kafadanta,ita kuma sai ta Cakume Bayansa Dukkansu Sun ji Sanda bakon yanayin ya Ziyarcesu mussmman ma Barkat wacce Taji Abun har Cikin Kokon Ranta Saurin matsawa gaba yayi Saboda Bayason Kusancinsu Shima Tsausayi ne ya kaishi Daukan Wata mace a saman Mashin Dinsa ammh bai sababa.

Sai da Ta Daidaita zama kana suka Fara Tafiya ga Iska yana ta kadawa Sai Barkat ta kamkame Jikinta tana Kallon Bayan Abdullahi Cikin Wani yanayi na Shauki da muradi mai Girma acikin Zuciyarta kuma kara godema Allah take daya Hadata da Sanyin Idanuwanta wanda yasa Bata ganin kowani Namiji da gashi sai shi Tun Ranar Data ga Abdullahi bata kara Sukuni ba Tun Tana Daukan Abun Wasa Har ta Fahimci da gaske ne,,Tasha ta Kwanta tayi ta kuka ko kuma ta kaima Allah kukanta Cikin Dare kan Allah yaye mata Abunda Take ji game da Abdullahi ammh Abu yaci Tura,Sai ma karuwa yake Kwanakin nan duk ta Rame ta lalace Ga karatu ga Tunanin Abdullahi Yan"uwanta da Mahaifiyarta suka Shiga Damuwa Sosai sanin Halin Barkat,wacce Bata iya Bayyana Abunda ke Damunta Bata da Hayaniya Sosai Hajiya Amina Tayi Tambayan Duniyan nan Ammh Barkat ta kasa cemata komai Harta ya"yansu Salisu sai da ya Tsareta da Tambaya shima Taki gayamai sai yayi mata Nasiha ya kyaleta,Taji saukin Abun kwana Biyu,saboda Tana addu"a sosai ammh bawai Soyayyar Abdullahi ta Fita Daga Ranta ba sai gashi Alokacin Da tagama Fidda ran Kara ganinsa Allah ya Hadasu Lalle Allah Abun Godiya ne.

Kamar Daga sama Taji muryansa.."Meyasa kike kai Dare a cikin makaranta alhalin Kina mace..? Cikin Sanyin muryanta tace"6pm na tashi lacture,kafin na Fito Daga Cikin makaranta Duhu ya Shiga nayi kokarin na samu Mota Bansamu ba.."Abdullahi ya kada kai yana Fadin"Gaskiya akwai Hadari a matsayinki na mace ki Rika kaiwa Dare a irin wannan yanayin.."Kara Saussauta Murya tayi Tana Fadin"Insha Allahu..Yau din ne ma Dama in Dare yayi min Wajen Bahi nake zuwa na kwana Tunda ni ban samu accomondation ba.."

Bai kara mgana ba ya Cigaba da Tukinsa Kimanin Minti Talatin sai gasu Har Kofar gidansu,Barkat din Ta Sauka ya mika mata Littafanta ta karba Tana kallonsa kafin tace"Nagode Kwarai..Allah ya saka da alheri.."Bai mata mgana ba sai ga Salisu engr.ya Fito Daga Gidan ganin Abdullahi yasa ya saki Baki yana Kallonsa kafin ya Kariso yana Fadin'"Wa nake gani kamar Abdullahi Usman..?

Abdullahi yace"Nine Alhaji Salisu..'Yafada yana yar Dariya karisowa yayi sai suka kusa Cin karo da Barkat Cikin Mamaki yace"Ke kuma Daga ina..? Kafin Tayi mgana Abdullahi ya Rigata da Fadin'"Daga makaranta....Ni na kawota na ganta bakin makaranta ga Dare.."Salisu yace"Ayyah...Mungode.."Daga haka ya bashi Hannu,suka kara gaisawa Yana mai murnan Auran Jidda da Nazifi sai da Abdullahi yaji kunya ammh Shi Salisun bai Nuna komai ba Domin a yanzu hakama Shigarsa Gida zencen suke da Hajiya Amina tace matar Mutum kabarinsa,Nazifin da kanshi ya Kirashi ya gayamai Bayan ya Turamai katin Bikin..

Bayan Sun gama gaisawa sai Salisu yace Abdullahi ya bashi Lambarsa bai Dashi Barkat Dake labe Daga kofar gidansu Taji kamar an sakata acikin aljannah Domin Tasha Satar wayar yayan nasu Domin ta Duba Lambar Abdullahin,Sai dai tayi Rashin sa"a ta Dauki na wanda bashi ne ba,Yana karantoma Salisu itama Dagachan tana Daukewa,Murna Ta Cika mata Ciki Sosai Jin Sunyi sallama Abdullahi yaja Mashin Dinsa yaTafi Shi kuma Salisu ya Tunkaro gida,Jin haka yasa ta Zura da Gudu zuwa Cikin Gida.

Hajiya Amina da Bahijjat dake Falo Suka Dago Suna kallonta a Razane Hajiya Amina tace"Ke Barkat lafiyanki kuwa..?meya faru.?Baki Barkat ta kama Tana Fadin"Hajiya magen gidansu Maimun  ne ta Biyo ni.."Tsaki kawai Hajiya Aminar Taja ta kauda kanta gefe ita kuma Bahijjat Dama Assigement Take sai ta maida kanta ta Cigaba da Abunda Take ganin haka yasa Sum Sum Barkat ta Karisa Dakinsu Tana zuwa ta Fada kan Gado Tana Fadin"Finale..yau dai na samu Burin Raina...Insha Allahu Burina zai Cika..."Ta ke Fada Cikin wani Tsantsan Farinciki Tana Rumgume Duka Hannayenta a kirji adanuwanta a kulle tana Tuna Abdullahi da komai nashi.

Abdullahi kuwa koda ya koma Gida Hafsah na Tambayansa taga yayi Dare sai yace mata ya tsaya wani Abu ne,alwala yayi yayi sallar mangariba da Isha"i ba Dadewa sai ga Auwal ya kawomai sakon katin Bikin Daya sa aka Bugamai guda 100 wanda zai Rabama Mutame,Guda 50 ya Cire yabama Auwal Sauran yace ya Dauka Sauran kuma ya kai ma Mama Ya Dade agidan sai Wajen Goma ya Tafi Gidan Mama.

********

Tun Jiya Nazifi ya Kira Sakina awaya yana Tambayanta yaushe zata Shigo..? Abun ya bata mamaki sanin yanzu Nazifi ya Daina Damuwa da Zuwanta da Rashin Zuwanta,Sai tacemai sai Gobe asabar zata Shigo yanzu hakama Tana kano ne,Mamaki ya Cikashi Domin Shi dai bata gayamai ba bai Nuna mata komai ba yace Allah ya kaimu.

Washegari sai Wajen 1pm na Rana Sakina ta iso Abun da ya kara Bata mamaki ganin Nazifi ya Sauya Funitures din Falon Da komai da komai mamaki ya Cikata Sosai sai dai kuma koda ta Shigo Nazifi baya gidan Zuciyarta kuma ta kasa Natsuwa a acikin Zuciyarta kai Tsaye ta Daga waya ta Kirashi tace Gata Ta Shigo ammh baya gida yace mata yaje wani Waje ne ammh gashinan zuwa.

Shuru Shuru ba Nazifi ba Dalilinsa Zuciyarta ta kasa Natsuwa ta Sake Kiranshi sai bai Daga ba,Sai bayan Isha"i kana Nazifi ya Shigo Gidan,Ya iske Sakina Afalo Tana aiki Bisa System Dinta Tana ganinshi Ta Mike ganinsa da Ledoji,Kan Center table din Falon ya ijiye yana kallonta kafin yayi mgana Ta Rigashi da Fadin"Wai ina ka Shige ne..?

Sai da ya zauna Kujeran Dake kusa da ita kana yace"Wani Uzuri ne ya Tsaidani..An dawo lafiya..?"Komawa tayi ta zauna Tana amsawa Lokaci Daya kuma Tana kallonsa Shi kuma sai ya basar da ita ya waiga yana Fadin"Baki Dafa komai bane..?Kai Tsaye tace"Me zan iya Dafawa..? A gajiye na Shigo gidan.."Bai yi mamaki ba yace"Eh kwarai aikin Mijinki Shine na gajiya ammh aikin gwannati bana gajiya bane Tunda gashi nan Shi na Shigo na samu kina yi.."

Bata Kalleshi ba tace"Wani aiki zan Turama Manaja Tun Shekaran Jiya yake Jirana ..kuma kasan yanayin aikina bai kamata kana yawan korafi ba.."Baki kawai ya Tabe yana Fadin"Wazan ma korafi..?ko nayi Ba"a karbansa Shiyasa ma na kama kaina..Allah bada sa"a ma"aikaciyar Jarida Hajiya Sakina Badamasi.."Cikin mamaki Ta kallesa sai ya Fara mata Dariya Dauke kai Tayi Tana bin Falon da Kallo Take Fadin"Naga Gida yasha gyara...Hala wasu kudade ka samu..?"

Kishingida Yayi Jikin Kujera yana Fadin"A"a me kika gani..? Abunka ga Talaka Bawan Allah Na Sauyasu ne ganin Tunzuwanki basu samu Chanji ba...."Yafada Lokaci Daya yana Fito da wayarsa yana Dannawa kai ta Jinjina tana Fadin"Saura na Dakunan barcinmu.."Kansa na Bisa wayarsa yace"Naki ne ya Rage..Nima nawa na Sauya komai.."Ido tasakarmai Tana Fadin"Au...Nifa..?Kai Tsaye yace"Ni ai banyi kudin da zan Sauya miki kayan Daki ba Sakina ko Kin manta Lokacin da kika Fadamin haka..? Ya fada yana Tsareta da ido bata samu Zarafin bashi amsa ba yace"Duba wayarki na Tura miki Sako.."Jin Haka yasa ta Jawota daga Gefenta ta Duba Dagowa tayi Tana kallonsa kafin tace"Naga kudu Har Dubu Dari da Hamsin na Miye ne..?

Kai Tsaye yana kallonta Ido Cikin Ido yace"Kudi ne ki kara Siyayyah..Aura zan kara Ranar Sati mai zuwa sanin ku Manya ne bakomai yake Burgeku ba ban Siya miki komai ba nace gwara na baki kudi..Ga wannan.."Ya Fada yana Mikamata katinan Daya Zaro Daga aljihunsa Bata karba ba illah Ido Data Zuramai Tana Binsa da kallo kamar Mutum Mutum Kan Cinyarta ya ijiye mata yana Cigaba da Fadin"Autarsu Abokina Abdullahi Zan aura Hauwa"u jidda..Zamu Fara zama azaria kafin Hutun Dana Dauka ya kare in ya kare zan Dawo da ita Kaduna....Kinga kenan baki dawata matsala yanzu..Na Zabi hakane saboda na baki yancin Samun Damar kula da aikin ki Da kyau..Ni kuma na Samu wacce zata kula Dani daDuka Hakokina

29 / 48