Author : Jamilaumar Category : Complete Novels
1:52 PM - 😂😂: *MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..!*
*007*
"Yadda ya Fita Daga Gidan Mama ransa bace haka yaje ma Hafsah Cikin wannan Fushin da Bacin Ran,Koda yashigo Tana Zaune afalo Su Amira suna Homewark dinsu yau batayi Girki Da Daddare ba Sauran Abincin Rana ne ya Ragu basu Cinye ba sai Sauran kazan Jiya Wanda Tunda taga megidan bai kula ba tasan bazai kula ba,Kuma koda ma Tayi abincin baya ci ballatana ma yabi ta kanta.
Kansa Tsaye ya Shigo Falon ko Takalmin kafarsa bai Cire ba,Sawun Cikinsa Dasu ya Shigo Har Tsakiyar Falon su Amira suka Tashi suka Rikesa suna masa Oyoyo,Kan Amira ya Dafa Shi kuma Amir ya Dagasa sama yana mai waasa,Hafsah Dake gefe ta mike tana Fadin"Sannu da zuwa.."Dama bata san ran zai amsa ba,kuma bai amsa ba Din yaja Ya"yansa Zuwa Ciki,Komawa tayi ta zauna kan Daya Daga Cikim Kujerun Falon Ta Zabga Tagumi kawai Domin Abun na Abdullahi ya Fara isarta.
Chan sai gasu sun Fito da Robobin Ice cream a Hannunsu Kowa Dai dai,Dama taga ya Shiga da wata Bakar Leda,Suka zo suna Nuna mata tace tagani susha abunsu sun zauna suna Cikin Sha sai Fada ya kaure Tsakanin Amir da Amira ta Tabamai Ice Cream dinshi Shi kuma ya Cika Fitina ya Fara Dukanta Hafsah na zaune ta Dakamai Tsawa yaki Sauraranta kawai sai tace"Amira in ya kara Dukanki ki Mareshi Tunda Bayajin mgana.."
Ita kuma Amira yana kara Dukanta ta saka Hannu ta makeshi ya kara Sakin kuka Ashe Duk Abdullahi na Ciki yana Jinsu Bai Fito ba sai da yaji Amiran ta Daki Amir din kana ya Fito da Sauri Cikin Bacin rai Har ya Sauya kaya ya saka Dogon wando baki da kuma Wata karamar Riga Fara,Kirere ya tsaya gaban Hafsah yana Fadin"Waya Dake shi..?
Hafsah ta Dago ta kalleshi kafin tace"Dukan Amira yake yi na Hanashi yakiji ni kuma nace in ya kara Tabata ta Dakeshi.."Tsayawa kawai yayi yana mata wani Irin kallo wanda sai da Hafsah ta sadda kanta kasa Tana wasa da Zoben Hannunta,Bai mata mgana ba illah Amir Daya Dauka yana Lallashinsa kafin ya kalli Amira yana Fadin"Mamana karki kara Dukansa kinji ko..?.
Kai ta Gyadamai Cikin Taushin Murya yace"Komai zai miki kar ki yarda wani ya kara cewa ki Dakesa ki Dakesa Kinji ko..? Kaninki ne kece Babba Watarana sai Labari.."yafada yana Hararan Hafsah wacce Tasan da ita yake Bata tankamai ba yaja hannun Amira Zuwa Ciki suka Barta nan da kallo ta Bisu tana Sauke ajiyar Zuciya.
Ranar dai su Amira wajen Abdullahi suka kwana ita kadai ta kwana Cikin Daki Abun yana Damunta ammh bata da yadda zatayi Tunda Ko zatayi mganan Duniyan nan Abdullahi baya Tankamata gashi ita kuma Bata da Dabi"ar Gayama wani Sirrin Mijinta balle ta gayama wani ko Zai bata Shawara,Subai'a ma ta Kirata tana Tambayanta Komai Lafiya ita da Abdullahi sai kawai tace mata komai ya wuce saboda bata Cika son Fadin wani Abu Daya Dangancin Auranta ba.
*****
Cikin wannan zaman Doya da Manjan Tsakanin Abdullahi da Hafsah wanda tayi iya yinta Domin Taga komai ya Daidaita ammh Abu ya gagara,sai kawai ta Zubama Sarautar Allah ido ta barma Allah komai.
Yau Takama Jumma"a ce,Bayan su Amira sun Dawo makaranta Mai mashin dinsu ya sake kwasansu zuwa Gidan Mama tare da kayansu da kuma Uniform din Haddarsu ta asabar da Lahadi Tunda chan Abdullahi ya sakasu Ranar jumma"a suke Tafiya chan Gidan Mama sai Lahadi kuma da Daddare Abdullahi ke zuwa ya Dawo Dasu.
Tun Bayan Tafiyarsu Gidan yayi ma Hafsah Shuru sai kawai ta Tsiri wankin kayan yaran da kuma nata,Sai Gabda mangariba ta gama tana gamawa ta Fada wanka Jikinta yayi mata wani Nauyi,bayan ta gama wanka sai ta Dauro alwala ta Fito ta Shafa mai ta saka Riga da Sikat na wani Boyel wanda Abdullahi ya Dinkamatashi Lokacin da zasu kaduna Zanniratu ta Haihu,Akamata Dinkin Buba,kayan sun mata kyau alokacin Haka Abdullahi ya Dinga yaba kyan Datayi Shiyasa ta sakasu yau zata jawo Ra"ayinsa Batayi kwalliya ba ta bari sai ta Idar da sallah Tukunnah.
Ta Shinfida Sallayar ta Tada sallar Raka"ar Farko Taji wayarta Dake Falo ta Dauki Ringing,Tana sallah Tana ji ana ta Kiran Wayar nata Haka Kurum taji gabanta ya Fadi Dakyar ta salallame sallar ta Fito Falo da Sauri Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon ta ijiye wayar Dazu da sukayi mgana da Umman Sadiq Daga gusau,Da sauri ta Dauka Ganin Ammi ce ta Kirata Har sau Biyar yasa Jikinta Haka Kurum ya Fara rawa Ballatana ma Tun Dazu take Kiran layin Daddy bata Shiga Daga Baya kuma sai Taji wayar tana kashe Ta kuma Kira Ammi Har sau Hudu bata Dauka ba Tun Lokacin Jikinta ya bata ba lafiya.
Kiran tabi baya sai da wayar ta kusa katse kanta kana Ammi ta Daga Kiran Cikin Sanyin Murya tace"Autana ina kika Shiga kika bar wayarki ina ta Kiranki Shuru..? Yadda Hafsah taji Muryan Ammi yasa Kafarta ta Fara rawa Da sauri ta nemi gefen Kujera ta zauna Tana Fadin"Ammi kin kirani ina sallah ne..? Lafiya naji muryanki wani iri..? Ina Daddy nayi ta Kiran wayarsa Tana kashe kema na Kiraki baki Daga ba? Wani Abu ya Faru ne..?
Ammi tace"Auta irin wannan Jerin Tambayoyi wanne kike so na Fara amsa miki..? Hafsah tace"Duka Ammi..."Da Sauri kamar ta kagara taji ko lafiya ajiyar Rai Ammi ta Sauke kafin tace"Dama ba wani abu ne,Daddynku ne ba lafiya Tun Jiya Da Daddare Hawan Jininsa ya Tashi Haka muka kwana da Safe muka tafi asibiti a almadina muka Wuni yau sai yanzu muka Dawo Gida.."Da sauri Hafsah ta mike tana Fadin"Innalillahi Ammi Shine baki kirani kin gayamin ba.."Tafada Cikin matsanancin Damuwa.
Ammi tace"Shi ya Hana yace kar na Kiraku keda Hadiza Yasan ku da Rudewa yanzu hankalinku zai Tashi,Jikin da Sauki Gashi har mun Daawo Gida,lokacin muna asibitin ne ban Daga Kiranki ba Bayan mun Dawo ne na kiraki baki Daga ba sai na Kira Mijinki yanzu muka gama mgana Dashi ma.."Hafsah tace"Wayyo Daddy..Ammina ya Jikinsa..? Yaji Ssuki..? Yana iya cin Abinci..?ko barci yake ji..?
Ammi Tayi Dariya kafin tace"Kai Autana Irin wadanan Tambayoyin fa..? Ki bari in kikazo kya gani Abdullahi yacemin yana Hanyar zuwa Gida zai Daukoki ku Taho tare.."Hafsah tace"Ammi ki gaida Daddy sai munzo..Don Allah ki bashi abinci ya koshi.."Ammi tace"Ohoni Da ke da Hadiza bansan wanne yafi wani Son Daddyn nan ba itama dana Kirata Fadi take Ammi yaci abinci..? Yayi barci..? Ya jikinsa..? Ki bashi abinci karki barshi da yunwa hala kunfi son Mijina ne da kuma yadda zan kula Dashi.."?Ammi ta karishe Fada Cikin Zolaya tana Dariya ganin yadda Mahaifinsu Hafsah ke ta Dariya Shida kaninsa Alhaji Mustapha..."
Tura Baki Hafsah tayi kafin tace"Mudai mun fi Son Daddynmu.."Ammi tace"Ehe lalle Bari kizo sai Daddyn naku ya zaba ko ni ko kuma ku.."Daga haka ta yanke Kiran tana Mita Ita kadai Alhaji Hamza Dake Zaune kan Gado acikin Dakinsa zama irin na marasa Lafiya Bayansa Kaninss Alhaji mustapha ya karamai Filo,Farin Dattijo ne mai kima da Dattako Dan Kimanin Shekaru 63 aduniya Fuskarsa tana Cike ne da yalwar Fara"a da Haiba.
Cikin Muryan Ciwo yace"Banda Abunki Zinariya wazai Hada mata da ya"ya..? Kowa matssyinshi Dabam ko Mustapha..? Alhaji Mustapha na Dariya yace"Haba ina ma za"a Hada ai sai ana son mata ake son ya"yanta.."Mirmishi tayi kafin tace"Allah Baban Abdul Iyayin yaran nashi ne ya Isheni kowacce ta Isheni da Ammi Don Allah ki ba Daddy abinci ya koshi.."Tafada Tana kwaikwayon Muryansu Dariya ta kama Alhaji Mustapha da Alhaji Hamza ganin yadda Ammin tayi.
Hafsah kuwa Bayan Ammi ta kashe wayarta sai ta Sulale kan Kujera ta zauna Tsausayin Daddynta ya Isheta sai ga Hawaye Sharr sun zubomata ta Tuna Shekaranjiya da Damuwa ta mata yawa Shi ta Kira suka Sha Hira yana ta Zoyalarta Dayake sunan Marigayiya Ayya aka samata Mahaifiyarsa Shiyasa yafi sonta daji da ita komai ya samu Mamana Shiyasa Tun tana Gida akwai Shakuwa Sosai a tsakaninsu Wani Lokacin Ammi tayi ta Fadan Irin Koda yaushe yana Tare da ita tana fadin watarana Aure Hafsah zatayi ta barshi Tunda Dukansu mata ne sai yace ba komai mijinta zai Dinga kawota ina ganinta Domin zan gayamai matarsa Ba irin Sauran mata ne bane, Autan Hamza ne kuma Uwa take garesa,In ya Fadi haka Daga Ammin har Hafsah dariya sukemai aikuwa Lokacin da Hafsah ta kawo Abdullahi sai da Alhaji Hamza ya gayamai Ya kular mai da Mamansa da kuma Autansa Hafsatu.
Tana Cikin wannan Tunanin ne taji Sallaman Abdullahi acikin Falon Tayi Zurfi Cikin Tunani batama Ji Shigowarsa ba,Dago ido Tayi ta kallesa yana Sanye Cikin wata Blue din Shadda mai kyau da yarari da kuma Tsada Riga da wando Dinkin zamani kafarsa na sanye Cikin Budadden Takalmi Haka Kansa sanye Cikin Hula kube mai kyau da Tsari.
Ganin Fuskar Hafsah tana Hawaye sai da gabansa ya Fadi Dayake aikwai wuta shiyasa ya samu Damar ganin Hawayenta Cikin mamaki yama manta da Fadansu da Fushinsa yace"Hafsah lafiya kike kuka..? Jin Haka yasa Zuciyarta ta kara Rauni kamar wacce aka ce Daddyn nata ya mutu ne kawai ta mike ta isa ga Abdullahi sai Ji yayi kawai ta Fada Jikinsa ta Rumgumeshi Lokaci Daya tana sakin mai kuka.
Da Sauri ya Tallabeta jin yadda ta Sakarmai Jikinta Hannuwansa Shima ya saka Duka Biyun ya Zagayen kugunta Dashi yana Sauraran Kukanta Cikin Sanyin Murya yace"Wannan kukan fa..? Wani Abu ne ya faru..? Cikin Kuka tace"Abban Amira Daddy ba lafiya yau Ammi tace ma a asibiti suka wuni.."Tafada tana kara Shigewa Kirjinsa.
Ajiyar Zuciya ya Sauke jin Abunda tace da Farko Hankalinsa ne ya tashi yana tsoron ko wani Abu ne ya Faru Bayanta ya Shiga Bubbugawa alaman Lallashi yana Fadin"Shiii..Ya isa...Meye Abun kuka kuma..? Munyi mgana da Ammi tace min da sauki kuma ma yanzu dawowar danayi Domin na Dauke ki muje mu Dubashi ne.."
Ya fada Cikin Sigar lallashi Saurin Dagowa Hafsah tayi Tana Fadin"Yauwa..Toh muje.."Tafada Cikin Rudewa kallonta yayi kafin yace"Haka zamu tafi Fuskarki Duk Hawaye..? Jin haka yasa ta kwashi Gudu zuwa Daki ta Shiga Tailet ta wanko Fuskarta ta Fito Falo ta Dauki wayarta tana Fadin"Na wanke Hawayen Abban Amira...'"yana tsaye yana kallonta Cikin mamakin ganin kamar bata Cikin Natsuwarta ganin haka yasa yace"Dauko key din Gidan.."
Da sauri ta koma Daki ta Dauko ta mikamai ya karba suka Fito Daga Dakin Shi ya kulle Dakin ya Hada Harda Kitchen kana suka Fita waje dama bai Shigo da Mashin dinsa Ciki ba Tana tsaye ya saka key ya Kulle Gidan kana ya Hau mashin din yamata key ya karkatamata yana Fadin"Ki Rikeni in zaki hau Domin naga har yau baki kware wajen Hawa mashin ba Duk da ita mijinki ya mallaka.."Bata ma Tsaya Sauraransa ba,kawai ta Dafashi da Hannuwanta Duka Biyu ta Haye Mashin Din yaja suka Fara Tafiya Sun Hau Titi kenan iska ya Fara kadawa Cikin wani yanayi wanda ke saka Masoya Cikin Wani Shauki wanda su kadai ke iya ganin irin yanayin.
Jim wannan iskar yasa kawai Hafsah ta kwanto Jikin Abdullahi ta Nannadeshi ta Saka Hannuwanta Duka Biyu ta zagayo Dasu ta Cikinsa lokaci Daya ta maida kanta Bisa Bayansa ta kwanta tana maida Numfashi Gabadayansu atare Suka saki Numfashi saboda yadda Jikinsu ya Hadu waje Daya Cikin wani irin kasala da wani irin Soyayyah wacce Sai ma"abota Soyayyah da kuma Kauna kadai ke iya ganewa Abdullahi ya lumshe ido ya Bude Cikin sanyin murya yace"Hausi kina so ki sakamu muyi Hatsari ne..?
Yafada Cikin Wata murya mai Cike da Shauki,Cikin Shagwaba Hafsah tace"sanyi nake ji toh..."Tafada Cikin Tabara da Sangarta,Kafin ta kara Fadin"Ko in tashi ne..? Tafada tana kokarin Sakinshi da Sauri yace"Kwanta abunki wazai Hana Hafsatu Kwanciya Jikin Abdullahinta.."kalamansa sun sanyayamata Rai Sosai har bata san Sadda tayi mirmishi ba kafin ta Furta.."Allah nagode maka Daka Saka Mijina ya yafemin Laifina..."
Jin haka yasa kawai sai ya dan Murmusa sai Lokacin ma ya Tuna da Suna Fada,Har suka kai Tudun wada Layin Bare bari Gidansu Hafsah ba wanda ya kara mgana sai dai zuciyoyinsu Dake Bugawa Lokaci Daya Har Cikin Haraban Tamgamemen Gidansu Hafsah Abdullahi ya Shiga da mashin dinsa Gidansu Hafsah Gidane Daya amsa Sunansa Gida mai kyau da Tsari,Haraban Gidan Motocin Alhaji Hamza wajen Guda Hudu sai ta Ammi Guda Daya hudu kenan.
Karkatamata Abdullahi yayi ya taimaka mata ta Sauka ta tsaya ta Jirashi har ya kafa mashin din,Sai da suka gaisa da Baba megadi kana suka Nufi Cikin Gida afalon Gidan babu kowa Hafsah ta kalli Abdullahi tana Fadin"kila Ammi tana Shashen Daddy bari na Shiga na gaya mata.."kai ya gyada mata Kafin ta Wuce Wani Shashe Dake Cikin Falon Shi kuma sai ya samu Daya Daga Cikin kujerun Falon ya zauna Chan sai ga yar aikin Ammi ta Shigo Falon ganin Abdullahi yasa ta rankwafa tana gaisheshi ya amsa cikin kauda kai,Ruwa ta kawomai da Lemo ta ijiye Dayake a koshe yake bai ko kalli Barayin ba.
Hafsah kuwa da Gudunta ta karisa Shiga Dakin Daddynta Tana Fadin"Daddy...! Daddy...! Take Fada Lokaci Daya tana Shiga Bedroom din na Daddy Ammi Dake Tsaye Gefen Alhaji Hamza Tana Bashi Fruit,Alhaji mustapah kuma na Gefensa zaume suna Hira Sai ga Hafsah ta Shigo kamar Daga sama Tana Kiran Daddynta.
Alhaji Hamza ya Dago kansa yana Fadin"Gani nan Mamana..."Yake Fada yana miko mata Hannu Da Sauri ta karisa Gabansa Har tana Ture Ammi Wacce ta sake baki Tana kallonta Kusa Dashi ta zauna ta Riko Hannunsa tana Fadin"Allah Sarki Daddyna..Duk ka Rame sannu.."Take Fada Hawaye suna gangaro mata Alhaji Hamza ya Saka Hannu yana Sharema Hafsah Hawaye Lokaci Daya yana Fadin"Toh kuma miye na kuka Mamana..? Baki ganni ba naji Sauki Sosai nama warke har Gudu zan iya yi..'"
Yafada Cikin Zolaya Mirmishin Hafsah tayi kafin ta yada kanta Gefen kafadarsa Tana Fadin"Allah Baka lafiya Daddyna."yana Mirmishi yana Shafa kanta yana Fadin"Ameen Ameen Mamana..."Ammi Dake Tsaye tatabe baki Tana Fadin"Masu Daddy manya..Shi kadai kika gani..? Ga Babanki mustapha zaune kin Wucesa ko..?
Sai alokacin Hafsah ta ga Alhaji Mustapha,Kunya ta kamata ta tashi Tsaye tana Rufe Fuska,Tana Fadin"La Abba Wlh ban ganka ba..Ina Wuni ya gida..? Yasu Mama maimuna Da Hajiya gaje..? Yana Dariya yace"Ina fa zaki ganni Mama ai sai kin gama da Daddyn naki..lafiya kalau ya Megidan na ki..?Hafsah tace"Lafiya lau Abba tare ma muke Dashi..".
Baki Sake suke Kallonta Ammi tace"Tare kuka zo Dashi..? Toh kika barsa a ina..? Hafsah tace"Yana Falo nace bari na Shiga na gayamiki.."Salati Ammi ta saki kafin ta sakarma Hafsah Dakuwa Tana Fadin"Kinci Gidanku Hafsah yanzu Fisabillahi Kin zo Tare da mutum ammh ki barsa afalo ke ki Shigo Ciki..? mintinki nawa Da Shigowa..?
Tura Baki Hafsah tayi kafin tace"Toh ba mantawa nayi ba..Na Zagu naga Daddyna.."Ammi ta Zabgamata Harara Alhaji Hamza Ya kalli Ammi yana Fadin"Ki mata ahankali mana Baki ga yarinya bace..Mamata maza kije ki Shigo Dashi Abdullahi ai dan Gida ne.."Ya fada da Sigar lallashi Baba Mustpha yace"Yaya wa kenan yarinya..? Ya"yanta Biyu fa..?
Alhaji Hamza yace"Ah to ko ko ya"yanta goma ne Mamata ayarinya nake Daukanta Ko Zinaru a yarinya nake Daukanta Ballatana Mamana.."Ammi ta Saki Mirmishi kawai Baba Mustapha din ma Dariya yayi Hafsah ma sai da ta Dara kana ta Fice Daga Bedroom din.
Zaune ta iske Abdullahi yana ta latswa Wayarsa Zuwanta yasa ya Dago yana kallonta Cikin kunya tace"Kayi Hakuri Abban Amira ganin Daddy yasa na manta Dakai afalo.."Mikewa yayi yana Fadin"Bakomai..Tunda Daddynmu ne.."Yafada Cikin Zoyala Gaba ta Shige Ya Bita abaya Har Zuwa Shashen Daddy.
Da Sallama Abdullahi ya Shiga Bedroom din Daddy,Hafsah na gaba yana Binta abaya Har gaban Gadon Daddy,Ammi ya Fara gaisawar Bayan ya Duka har kasa Ammi ta amsa tana Fadin"Kayi Hakuri Abdullahi Shirmen matarkace maimakon Tun Shigowarta tace tare kuke bata ce ba,Sai da ta gama Hira da Daddynta,Sai ma da Baban Abdul ya tambayeka ne kana tace Tare kuka zo.."
Abdullahi ya Dukar Dakai Kawai yana Mirmishi Daddy yace"Kedai Zinariya kina son Rura wata Wutar..Abdullahi da Mamana Duka Daya ne.."Abdullahi yayi mirmishi kafin ya Dago kansa yana Fadin"Daddy ina Wuni ya karfin Jikin..?
Daddy ya miko Hannu yana Fadin"Ya ka nan Abdullahi...Kazo ka zauna kusa dani kamar yadda Mamana keyi Duka Daya na Daukeku.."Baba Mustpha yace"Tabbas..Wannan haka yake.
"Abdullahi ya mike yana gaida Baba Mustpaha ya amsa yana Tambayansa su Amira Ammi tace"Suna Gidan mama gobe suna da Hadda.."Baba Mustpha yace"masha Allah..."
Kusa da Daddy Abdullahi ya Zauna Daddy ya Riko Hannunsa yana Fadin"Abdullahi ya gida..? Ina Matata take ne..? Kardai Taji Tsoron Fadan Zinariyata taki Dawowa.."Abdullahi na Dariya yace"Haba Daddy ai ita bata Tsoro Amaryan taka Suna gidan mama gobe suna da Hadda,ammh kasha kuruminka Zata zo ta Gaisheka da kayan Dubiya.."Daddy ya saki Mirmishi yana Fadin"Yauwa yanzu naji Batu."Ammi dai na gefe tana Mirmishi ita da Hafsah Nan Daddy suka kara gaisawa da Abdullahi sosai ya masa ya Jiki yace da Sauki,Shi kuma yana ta Tambayansa Wajen aikinsa yana Bashi amsa.
Ammi da Hafsah fitowa sukayi Falo suka barsu suna Hira,Ferfesun kayan Ciki Ammi ta Tasama Hafsah tana ci suna Hira Har Hadiza ta Kira waya sukayi mgana da Hafsah,Tace gobe itama tana Tafe Sai wajen goma da wani Abu Kana su Hafsah suka Bar Gidan Shima sai da Daddy yace su tashi su Tafi Gida Dare yayi,Baba Mustpah ya Rigasu Tafiya Kula Guda Ammi ta Cikama Hafsah kula da Ferfesun kayan Ciki tace in sunje Gida suci Ita da Abdullahi Daddy ma Fadi yake Zinariya kin Zuba musu kuwa..? Ki zuba musu su Tafi Dashi mana Ammi Da tagaji tace mai"Wai Shin ko zaka tashi da kanka ne ka Zuba musu..? Sai yayi Dariya yace"Kedai zaki Zubamusu Zinariya.."Daga Abdullahi har Hafsah Dariya suka saka inda sabo Abdullahi ya saba ganin Diramar Ammi da Daddy kan ya"yansu Domin Shima kamar Dan Gida ne Shiyasa ko Nazifi yace Wani Abu kan iyaye masu kudi sai ya karyata Domin iyayen Hafsah Mutane masu Dattako ba irin irin iyayen Sakina ba
Kamar Tafiyar farko wannan karon ma kara Nademai Tayi Suna Tafe iska na Hurasu Cikin wani Shauki da Muradi mai Girma.
*NOTE:Labarin Masifaffan Namiji Labari ne da zai Taba Bangarori Da yawa,Labarine da zai yi Duba zuwa ga Abubuwan Dake Faruwa a gidajen Auranmu, Labari ne da zai Dubi Bangaran zamantakewarmu Labarine da zai Dubu bangaran Rayuwar mu ta yau da kullum,Labari ne da zai yi Duba kan Yadda Iyaye da Yayyi suke da Rawa mai girma wajen Tarbiya da kuma