Author : Jamilaumar Category : Complete Novels
Matsawa Baya Shi kuma ya Rabata ya Wuce Hafsah sai dai Tabishi da kallo kawai gefe Daya na Zuciyarta na addu"ar Allah ya saukar da wannan Fushin Data gani a Kan Fuskar Abdullahi.
Bayanshi Tabi Bayan ta Ijiye ledan maganin Sauron Abunda tagani ne ya Bata mamaki Abdullahi ya zage yana Cika Botikin Daya Fito Dashi Da Ruwa a Rijiya Cikin mamaki ta karisa Tana Fadin"Abban Amira me zakayi da Ruwa kuma..? Alhalin Duka Bombin Tailet Cike suke da Ruwa Hakama na wajen nan.."In Iskar Dake wajen ta Tankanta toh Abdullahi ya Tankata,yayi mata Banza bai Dakata ba sai da ya Cika Botiki tsaf kana ya Dauka da Hannunsa tana Tsaye ya wucewa Zuwa Ciki da Sauri tabi Bayanshi Har Cikin Tailet din Abunda ya Bata mamaki bai Juye Ruwan Kittle ba Taga kawai ya Fara Kwabe Rigar Jikinsa alamun wanka zaiyi baki sake take Binshi da kallo Shi kuma yaki yarda ya kalli Barayinta ganin bata Niyyar Fita yasa ta Tube Duka kayansa ya Wurga Cikin kwandon tara kaya wanki ya Fara watsama Jikinsa Ruwan sanyi.
Batazata iya Juran ganinsa Haka ba Koda suka Haihu har sau Biyu Tana da kunyar ganin Tsaraicin wani kawai sai ta kada kai ta Fito Zuwa Cikin Bedroom din Hawaye sun kawo Cikin idanuwanta gefen gadon ta zauna Kawai Tana Tunanin mafita da kuma makomar wannan Shariya ta Abdullahi wanda komai nata yanzu baya Bukata,Tana nan zaune ya Fito Daure da Babban Towel ta gabanta ya wuce zuwa Jikin Wardrope ya Bude ya Dauko Jallabiyansa Baka ya saka kana ya koma Toilet din da Towel Din Dake Hannunsa,sai chan kuma ya Fito gaban madubi ya koma ya Fesama Jikinsa Spry, Tana kallonsa ya koma Bisa gado ya kwanta Bayan ya kashe wayarsa,Har kuma ya kwanta sai kuma ya mike yaje ya Kashe Wutar Dakin ya koma ya kwanta Harda Jan Bargo kamar bai sam da zaman mutum a gefen gadon ba.
Ganin haka sai Jikin Hafsah yayi sanyi Cikim karfin Hali da Shawaran Zuciyarta ta Mike ta isa Kusa Dashi dan Dukawa tayi tana Fadin"Abban Amira.."acikin Taushin Murya da kuma Lallashi Tsit yayi kamar bai jita ba sanin yana Jinta yasa tacigaba da Fadin"Don Allah kayi hakuri kan Abunda ya Faru yau..Wlh ba laifina bane laifin Subai"a ce Zan taho Tun bayan La"asar ta Daukemin Jakata da Hijabina taki Barina natafi..Allah ba laifi bane.."Ta karishe Fada Cikin Rawar Murya kamar zatayi kuka Shurun ya sake mata sai ma kawai Taga ya gyara kwanciya ya Juya mata Baya bata Hakura ba Ta kara Bude baki tana Fadin"Kayi Hakuri...Ba..."Bata karisa ba Taga kawai yayi Zunbur ya mike Har sai da Ta Tsorata tatashi da Sauri kawai sai taga ya Dauki Filo da Blanket din kawai ya Bar mata Dakin Galala Hafsah ta Bishi da kallo kafin ta Hadiye wani miyau mai Zafi wanda ya wuce ta Cikin mangwaronta bai Shirya ba.
Bayaansa Tabi Cikin sanyin Jiki nan ta iskeshi kwance kan Doguwar kujera,yayi kwanciyar Rigingine yana kallon Celling gefe Daya kuma ya goya Hannayensa Akan Kirjinsa ya kuma Lumshe Idanuwansa kamar mai Barci Hafsah tayi kasake kafin ta karisa Tana Fadin"Ka tashi ka koma Ciki Don Allah..kasa ina jin wani iri Abban Amira.."Ko alaman yajita ma bai yi ba,Balle ta saka Ran zai amsata Ganin haka yasa ta kara marairaicewa Lokaci Daya tana Riko Blanket din Daya Rufu Dashi Tana Fadin"Kaji..Don Allah ka tashi ka koma ci..."Bata karisa ba Taji ya Daka mata wata Gigitattaciyar tsawa Wanda sai da ta sa ta afirgita ta saki Bargon ta koma Baya Cikin wani Zafin nama ya Tashi zaune yana kallonta kafin yace"Kinga malama indai bakina so na barmiki Gidannan bane ki Tafi ki bani Wuri i don"t want to see u in my Side plz.."Yafada Cikin Kakkausan Murya mai nuna Bacin Rai..
Hawayen Idanuwan Hafsah suka Zubomata ta saka Hannu ta Share Cikin Muryan Rauni da karaya tace"A"a bari na tafi Dakinsu Amira na kwana..Allah ya Huci Zuciyarka.."Tafada Lokaci Daya tana Hucewa Cikin Sharan Hawaye ya Bita da kallo acikin Ransa kuma sai yaji Tsausayinta kamar ya Tsaidata sai Wata Zuciyar ta kwabesa Da cewa gwara ka kyaleta ta gane Kuraanta in kayi Saurin saukowa shikenan ta samu Dama gaba sai Tayi Abunda ma yafi haka da wannan Shawaran ya kwashi kayan kwanciyarsa ya koma Cikin Dakin yana sakin Tsaki.
Ita kuwa Tana Shiga ta Fada Gefen Amira kan katifa lokaci Daya Tana Fashewa da wani Irin kuka mai Tada Hankalin mai Sauraro Dama Abunda Ta gudanar ma kanta kenan Tana ta Fadama Subai ammh Taki yarda da Ita gashi dai Abunda ta Gudanar kuma ya Faru har ma ya Zarce Tunaninta,kuka take mai Cin Rai,da kuma Rauni Bata san iya Adadin Lokacin Data Dauka tana wannan kukan ba Sai da Tagaji tatashi Zuwa Falo nan ta iske bayanan gabanta ya Fadi Tana Tunanin Allah sa ba gidan ya Bar mata ba kamar yadda ya Fada,sadaf sadaf ta Leka Bedroom din chan ta Hangoshi yana Barci yayi kwanciyar Ruf da Ciki,ya saka Filo a gefensa ya Rike blanket din Daya Rufu Dashi ma ya Jaye gefe ganin haka yasa ta Shiga Ciki a Hankali Tana bin Hasken Farin watan Daya ke Shigowa ta Labulan Window Bedroom din,Blanket din Taja ta gyaramai,kawai sai ya motsa ya maida kansa yana kallon sama Acikin Barci ganin haka yasa tayi Saurin Fita Tana Maida Numfashi,Waje ta fita Tayi alwala kana tazo ta kulle kofar Sai Lokacin Taga agogo karfe 1:30am na Dare,Dakin su Amira ta ta wuce Ta Shinfida Sallaya ta Tada sallah da Hijabin Jikinta sai da tayi Raka"a Tara ta Cike da Shafa"i da Wuturi Ta Dade tana addu"an Allah ya Saukar da Fushin da Abdullahi yayi akanta Allah kuma ya Huci Zuciyarsa sai wajen uku saura na Dare ta Sulale nan saman sallayar Barci ya kwasheta Batare Data sani ba.
****
Washegari ma Abun bai Chanza Zani ba Domin komai Datakemai Yau din bai nemi Taimakonta ba,Ta Juyemai Ruwan wanka ammh yakiyi Dashi sai yaFito kamar Jiya yaja Ruwa arijiya Ruwan sanyi yayi wanka Dashi,Breakfast ma nan ya bar mata kayanta,Har tagama Shiryasu Amira tana Sharan kwallah ta sani Abdullahi nada Fada Ta saba tayi laifi ammh bai Taba mata irin wannan Horon ba sai tama gwammace Dama Fadan yayi mata da wannan Shurun Ranar laifinta ya Shafi su Amira bashi yakaisu makaranta ba Briefcase din kawai ya Dauka da Key din Mashin Dinsa ya Fice Bai ce mata komai ba Sai tayi Tunanin kila ita zata kaisu makaranta Amira Har Kofar Gida Tabishi Tana Fadin Abba yau bazaka kaimu makaranta bane,Ita ya fadama mai mashin dinsu zai zo ya kaisu ita Amiran ke Fadama Hafsahn din,Ba Jimawa sai ga mai mashin dinsu yazo ya Daukesu zuwa makaranta...
Abdullahi yana Office wajen karfe 2pm na Rana Nazifi ya Kirasa yana Tambayansa yana ina ne..?yace yana Office ne..Yace gashi nan zuwa,Ba jimawa sai gashi yazo bayan sun gaisa ne Abdullahi yaga Nazifin Duk ya Rame kuma afirgici yake kamar Baya cikin Natsuwarsa Yasa ya kalleshi Cikin mamaki kafin yace"Abokina lafiyarka kuwa na ganka Duk afirgice..?
Nazifi yayi ajiyar Zuciya kafin yace"Hmm bari kawai iskancin Sakina ne Duk yabi isheni Wlh..."Abdullahi yace"Topha..Me kuma ya Faru yanzu..? Nazifi yace"Miye ma bai Faru ba,Jiya Na Dawo Daga Abuja ammh ina gaya maka Mutumina Sai da mukayi kacha Kacha da ita har dai ta kai ga sai da ta kureni na Daga Hannu na mareta.."
Abdullahi yace"Subhanallah Mari..? Gaskiya baka kyauta ba bai kamata ka Daga Hannu ka Mari matarka ba komai ta maka kuwa abokina.."Nazifi ya saki Tsaki kafin yace"Yo In ma Bugu ne ta kama Bani Bugunta..Yarinya ta maidani kamar wani yaron Gidansu Saboda mene..? Ita ke Aurena ko ni ke Auranta..?
Abdullahi yace"Duk wannan bai Taso ba...kowa ya sani kai ne Shugabanta,ammh bazan Fasa Fada maka baka kyauta ba Babu kyau kuma ba Mazantaka Bane,Namiji ya Daga Hannu ya mari matarsa gaskiya ba Dacewa bane.."Nazifi yace"Wlh ni kuma In dai mace zata kawomin Rainin da Sakina ta kawomin yau sai na Bigeta bama Marinta ba.."Abdullahi yace"Koma dai menene Hakuri ake Mutumina Mata sai a Hankali kowa ka karkace su Domin su Gyara Kara Bankare suke Abun ne sai Hakuri kawai.."Yafada Batare Daya Damu ya Tambayi Nazifin meya faru ba.
Nazifi ya gyara zama yayi yana Fadin"Ina gayamaka Mutumina Shekaranjiya naje Abuja Tunda naga wajen Sati uku Rabonmu da Juna,Ita batazo ba Nima Fushi nayi naki zuwa,Daga baya kuma sai nahuce na Bita Chan Mun kwana lafiya lau sai Jiya da Safe kawai naga tana Shiri Dana Tambayeta sai take Fadamin wai Wata Seminar zata lagos Kuma zatayi wajen kwana Hudu,Abun Takaichin ma ba Neman izinina take ba gayamin take don na Tambaya karim ma Abun Haushin ma atafiyar ita kadai ce mace Duka Uku wasu gardawan Maza ne wadanda ba Muharramanta ba,Don na mata Mgana Shine ta tasomin Daga karshe Ni kuma nace na Hana Tafiya,Shine fa ta Faramin Borinta Data saba na kuma ce Wlh bazata jeba,kasan Saboda Raini yarinyar sai kawai taci kwalata Tana Fadin na Bata makullin Gidan Dana Dauka na rufe Kofar Falon saboda karta Fita ina gayamaka Mutumina,Sakina Hardamin Gorin gida da Dukiya,Ni kuma Raina ya baci na Tsinketa da mari na Tureta Gefe na Fito na Barta aranar na kamo Hanyar zaria Bansa yadda ta kare ba.."
Abdullahi Da yayi Sagale yana kallon Nazifi ya saki Nunfashi yana Fadin"Tabdijam...Abu kam baiyi Dadi ba ammh agaskiya Abokina saken kane Tun Farko Sakina ta Rainaka Kana Bani wannan labarin acikin Raina ina Tunanin in nine Wlh mace taci kwalata ina Fada tana Fada yadda na Tsani Raini da sa"in sa Wlh sai na Barta kwance Duk ko ina Daukan Namiji mai Dukan mace Sakarai.."Nazifi yace"Hmm Nima na yarda da Haka Shiyasa nake baka Shawaran kar kayi saken danayi abaya Nima Daga saken ne Komai ya kwacemin shiyasa nake gayama kowani Namiji ya zama Jajirtattace kuma Masifaffe agidansa Hakanne kadai zai sa ya samu lafiya ya kuma sa mace ta Dinga Shakarsa.."Abdullahi yace"Da wannan don wannan kuma ka Fadi gaskiya..Toh yanzu ina ita Sakinar..? Tatafi lagos din ne..?
Nazifi ya Tabe baki yana Fadin"Ohon mata..Tun jiya ina Hanyar Zaria naga Kiran Tsohonta naki Dagawa nasan ta Kirashi ta gayamai karya da gaskiya Shi kuma mai ya' ya ya kirani zai Rainamin wayau naki Daga Kiran,yau kuma Tun Safe Baba ya kirani yace nazo yana nemana Ina zuwa sai yake Min Fada wai Baban sakina ya Kirashi yana ta Fada yana ikirarin sai yamakani kotu na Dakarmai yarinyar har sai da ta Suma..."Abdullahi ya Zaro ido Lokaci Daya yana Fadin"Innalillahi kaji wani Sharri.."
Nazifi yace"Wlh..ai ya saba dama yarda da mganar ya"yansa...Ita zata kara mganar shi kuma ya hau kai mana Nadai ma Baba Bayani Daga karshe yayi tamin Fada kadai san Halinsa.."Abdullahi yace"Kai Abu dai bai yi Dadi ba sam..Allah dai ya kyauta kai Mata Duk haka suke in kayi sake Shikenan Nima Tun Jiya ko mgana bana ma Hafsah saboda ta gama Batamin rai wlh.'"Nazifi yace"Ahaf..Ai na gayamaka Wlh in baka zama Masifan kanka da Gidanka ba Sai kafini zama Abun Tsausayi meya Faru ne Hala..? Abdullahi ya sauke Numfashi da kamar Bazai gayamai ba sai kuma ya fadamai Kadan Daga Cikin Abunda ya Faru Nazifi ya karkace kai kafin yace"Wlh kamin daidai...gwara ka mata haka ai da gangane tasan ai kace mata ta koma Gidan Mama akan Lokaci Salon Raini ne kawai sai an yi mgana su kwashe sukai Gida iyayensu su mara musu Baya Allah dama Gida ka aikata Kila achan tafi gane Kuranta.."Abdullahi yayi ma Nazifi wani kallo kafin yace"Kawai sai na aikata Gida saboda wannan karamin laifin..? Ina fa som matata bawai bana sonta bane kuma Itama tana sona tana kuma min biyayyah daidai gwargwado da kuma Gudun Bacin rai kawai na yarda Kuskure aka samu zan Hora ta kawai da irin Horona ammh ba mganar Turata Gida Mutumina Haba dai Iyayenta ba irin iyayen sakina bane suna da Dattako sosai ba zan iya wani Abun da zan Tozarta musu ya' ba gaskiya.."
Nazifi yace "Ai Shikenan Tunda kace Haka gani nayi Turasu gidan yafi Firgitasu da kuma su Dawo Cikin Hayyacinsu lokaci Daya.."Abdullahi yace'Naki din..? Kai Gida ka Tura sakina Duk da Irin Dibar albarkar Datake maka.? Nazifi yace"Ban taba Tura ta ba ammh zan Turata kwananan wlh.."Abdullahi ya saki Dariya kafin yace"Dan Rainin Hankali...Oh Shine ni kuma da matata bata taba Maidamin mgana sai na Turata gida ko..? Anki din toh.."Sai Nazifi ya maida mganar Dariya Sun Dade suna Hira kafin Nazifi yamai sallama ya tafi.
Da yammah da Abdullahi ya taso Daga wajen aiki Gidan Mama ya wuce yaci Tuwo Dawa miyar kubewa chan yayi sallar mangariba da Isha'i,Har kuma Lokacin Jidda bata Dawo ba Ran Abdullahi ya baci ya Shiga Fada Sosai Mama tana Bashi Hakuri kafin tace"Wlh yayansu na Kira Hauwa"u da kaina Nace mata kace ta Dawo gida sai kanwar uwar ta karbi wayar ta Rokeni na Bari gobe da safe zata Turota yanzu Dare yayi ne kaji yadda mukayi da ita Na dauka Tun safe zata Turota ammh har yanzu Shuru bata Dawo ba.."
Auwal na Zaune yana cin Tuwo yace"Mama bafa zata dawo ba wlh..Dama Yarinyar nan batajin mgana ta samu sake chan bamai gwabamata Dama ai bazata Dawo ba Wawiyar yarinya kawai.."Mariya na zaune tace"Kai ya Auwal kai fa Dan Zugi ne.."Da maficin gabansa ya Jefeta yana Fadin"Kimin Shuru wlh ko nayi kasa Kasa Dake yanzu nan.."Baki ta Tura tana kunkuni Dakatawa Yayi da Cin Abincin yana Fadin''Ammh Mama kina kallonta ko..? Wlh in ta kuskura ta Zageni saina mata Dukan Tsiyan sai ta manta Sunanta karyan Iskanci take ai Duk sune su Jidda marasa kunya.."Mama tace"Kai kuma dan Zafin Rai ba..ke Mariya kar in kara jin Bakinki anan wajem.."Tashi tayi Fuu ta Shige Uwar Dakin Mama Tana Kunkuni Auwal ya Rakata da Harara Abdullahi na Zaune yana Laluban Lambar wayar Mariya wacce Jiddan ta ari wayar Tatafi da ita, Daga ganinsa Ransa a Bace yake ya Hade Girar sama Data kasa Fuskarnan ba Fara"a ko kadan ko Ta kansu Auwal bai bi ba.
Ana Cikin hakane sai ga sallaman Jidda Ta Shigo Dakin Mama da Ledan kaya Riki Riki,Tana sanye da Doguwar Rigar atamfa mai launin ja Harda mayafinta karami ta Sagaloshi ta Wuyanta ta Shigo da Fara"arta tana Fadin"Mama mama..Anty Mariya na Da..."Mganarta ta makalene ganin Abdullahi zaune kusa da Mama sun Hada Ido Hudu Dashi kawai sai Jikinta ya kama Rawa sanin Hali Kauda kanta tayi Gefe daya tana kallon Auwal dake auna mata Harara Mama ta Kalleta tana Fadin"Jidda sai yanzu..? Na dauka tun safe innar taki zata Turoki Ga yayanku nan Tun jiya yake Fada rashin Dawowarki Wlh.."
Jidda Ta Bude baki tana Fadin"Allah mama zan taho Anty Lariyace tace na Tsaya zan karbi sa..."!Ki koma Inda kika Fito sai su Rikeki achan.."Mganar Abdullahi ta katseta wanda ya Fada Cikim kaushi da Fushi Lokaci Daya yana mikewa.
Jin Haka yasa Jidda ta sadda kai kasa Tana Fadin"Don Allah ya Abdullahi kayi Hakuri bazan kara ba.."Wani tsawa ya Dakamata yana Fadin"Yimin Shuru..In kika kara mgana anan wajen sai nazo na Tattaki mara kunya..Tun jiya da kika Fita Daga Gidanan sai yanzu kike Dawowa kuma Saboda Rashin kunya da wani Ficicicin mayafin wanda Dashi da Babu Duk Daya Don kaniyarki Shi kika saba sakawa anan..? Nace shi kika saba sakawa anan gidan..?
Ya karishe Fada Cikin Tsawa Da Sauri Taja baya kafin tace"A"a yaya..Bazan kara ba..'Tafada kamar tayi kuka yatsa ya Nuna ta Dashi kafin yace"Wannan ne na karshe da zan kara zuwa Gidan ace min wai kin tafi wani yawon wofi mara amfani in ma Fitan ta kama Dole akirani awaya a sanar dani in na amince aje in ban amince ba kowacce ta zauna agida bana son Shashanci banza da Yawo mara amfani kinji ko baki ji ba..? Da kai ta amsa kafin tace"Naji yaya.."Bai tsaya wata mgana ba kawai ya Wuce ta gabanta taja baya da Sauri sai da ya saka Takalminsa kana yace"Mama na tafi sai Allah ya kaimu.."
Mama tace"Allah taahemu lafiya ka gaida Hafsah da Megidana.."Bai amsa ba ya Fice Daga Gidan Cikin Fushi Auwal Dake zaune ya Saki Dariyar da Dama yake Riketa Tun dazu Jidda da Hawaye suka kawomata ta kalleshi kafin ta kalli Mama tana Fadin"Mama kinganshi ko..? ta karishe fada kamar zatayi kuka Mama tace"ina Ruwanki kuma Dashi..Kyalesa Hauwa"u na yakinan manta da wannan Babban gwabon.."Tafada tana yafito da Hannu Auwal kuwa sai kara tsintsira Dariya yake mariya na Ciki tana jindu Taki Fitowa Gudun kada Ahada da ita acikin Ranta kuwa Fadi take Anty Hafsah na Hakuri Wlh.
*Assalamu Alaikaum my Follow pipu's Hop kuna Lafiya..? Ya kokari kuma..? Allah ya taimake mu Ameen Ina son Don Allah nayi muku wani karin Bayanine kan Wannan Littafin Dana ke kam Rubuta muku mai Suna Masifaffan Namiji..! Ina so ku Sani Dan adam Tara yake bai Cika goma ba Duk zamowarka gwani akwai inda zaka kuskusre Allah ne kadai ke iya yin Dadai kuma yayi Abun ya zama Daidai akoda yaushe Shi kadai ne baya kuskure ammh mu mutane akoda yaushe Cikin kuskure muke,Toh irin wannan Kuskuran nayi Wajen Da zan Rubuta Shekarun Abdullahi maimakon na Saka 35 sai na saka 32 kumin afuwa Shekarun Abdullahi 35,yayi Aure yana da Shekara 28 ne,Hajara Amira kenan Tana da Shekara 6, ne Yayinda Amir Usman kenan yana da Shekara 3da wasu wattani kenan,a lissafi Suna da Shekara 7 da Aure kenan Tsakaninsa da Hafsah, sai kuskure na Biyu da muka samu Shine wajen da nace Mahaifin Abdullahi ya saki Hajara ta wayar hannu,Toh an samu akasi ne,lokacin wayar Hannu bata Fito ba Shekara Talatin da wani Abu baya Sai mu barshi a Ya Tura mata sakon Sakin ne ta Tarkada har garinsu gusau,Ina Fatan awannan Bayanin nawa kun Fahimce ni..? Ina godiya Sosai Gareku,na Tabbata ba kuna Karatun littafin Janafty da baki bane kawai kuna Hadawa da Duka Zuciyarku Shiyasa kuka gano wannan kuskuran da aka samu,kuma Hakan ya Faru ne saboda karancin Lokacin da nake Dashi,in nayi Typing bana samun Lokaci da zan zauna na Maimaita har nayi Editing dinsa Ballatana in naga kuskure na gyara ammh Insha Allahu zan yi Kokarin na Dinga Bin baya ina Dubawa...Ina Matukar godiya gareku Allah ya bar zumunci Masoyan kwarai..Allah ka barmu da Masoyanmu Duniya da Lahira...Ameen ya Allah...*🙏
*Janafty..*
4/9/21,