Author : Jamilaumar Category : Complete Novels
da Abdullahi ya kafa Dokar Haka ba, sai kawai Zuciyarta ta bata ba lafiya.
Dakinta ta koma,Itama takwanta ita da Noor sai Hudu Saura Tatashi Tayi sallah tatashi Su Amira sukayi sallah sukayi Shirin zuwa islamiya,Ta rakasu Har Kofar gida kana ta Dawo Cikin Gida,Tayi Tunanin ta Kira Abdullahi sai kuma ta Tuna yana Office yana aiki bazata so ta tayar mai da Hankali ba,sai kawai ta Share acikin Ranta kuma Tayi Wani Tunani inda Barkat din Tana so ta san Tana Cikin wani hali ko bata lafiya da Ta Kirata ta sanar da ita Tunda suna Gida Daya amfanin zaman Taren kenan ammh Tunda taki Fitowa bata Bukatar wani ya sani kenan kawai sai ta Fita Batunta ta kama Harkan gabanta
Ganin Har 5pm na yammah Tayi Shuru bata Ji Motsin Barkat ba sai kuma Zuciyarta ta kasa Natsuwa Batare da Tunanin komai ta Isa ga Kofar Dakin Barkat din Tana Doka sallama ammh kuma Shuru ba"a amsa ba,Sai kawai ta Tura labulan Dakin ta Shiga Falon ba kowa Ta kara Rangada Sallama taji ba"a amsa ba Sai Tsoro ya kamata ko Barkat din na Cikin wani Hali da Sauri Tana goye da Noor abayanta ta Tura Kofar Bedroom din ta Shiga Lokaci Daya Tana Kiran Sunan Barkat din.
Abunda ya bata mamaki yasa ta Dakata bata karisa ga Shiga Cikin Bedroom din na Barkat ba ganinta Zaune Gefen gadonta ta Kishingida da Gadonta taci Kwalliyarta Cikin Riga da wando Wadanda suka kamata kanta ba Dankwali tasaka Band ta Daure gashinta kafarta kan Daya tana Taunan Cingam gefe Daya kuma Tana ta latsa wayarta Kamar ma bata ji Hafsah ta Shigo Tana sallama ba, Tare da Kiran Sunanta ba.
Mamaki ya kara kume Hafsah ta Bita da kallo kafin tace"Ikon Allah Barkat lafiya kuwa..?kina ji ina ta sallama baki amsani ba kamar ba yar musulma ba..? Tafada tana kallon Barkat din Wacce tayi kamar bata jita ba Sai Ran Hafsah ya baci ta kada kai Tana Fadin"Allah ya baki Hakuri dana Shigo Miki Daki ..Dama Shuru naji Duk yau baki Fito ba, Sai nayi Tunanin ko lafiya Shine na Shigo na gani Saboda Hakkin zaman tare ammh Alhamdulillah Tunda kina Lafiya.."Daga Haka ta Juya Zata Fice Barkat ta Dago Tana mata wani Wulakantattacen kallo Idanuwanta sun kumbura alamun Tasha kuka Mikewa zaune Tayi Tana Fadin"Ina Jinki Kina Sallama Kawai banga Damar amsawa bane..Mganar kuma Kinjini Shuru ina Abunda ya Dameki ai ba zamanki nake ba balle Fitowata ko Rashinta ta Dameki,mganar kuma zaman tare ke kika sanshi Malama ba Wata Amana Tsakanina da Kishiya Saboda haka karki kara Shigomin Daki Daga yau Kowa Tashi kawai ta Fissheshi Malama.."Tafada tana wani Karkace kai tana Jifan Hafsah da wani kallo na, na Gama Tsanarki.
Hafsah Data Waiwayo Tana kallonta Tunda ta Fara mgana Mamaki ya Cikata ta Bude baki kawai Tana kallonta,Dakyar ta iya Rufe bakinta kafin tace"Ai Shiyasa na Fara baki Hakuri Da Farko..Mganar kuma Ba zamana kike ba Duk bai taso ba Dukkanmu muna karkashin Mutum Daya ne..Dama gani nayi ke keda Girki kuma kinki Fitowa ga yara sun Dawo makaranta Dazu suna Jin yunwa Complex na Hada musu suka Sha suka Tafi islamiya kada su Dawo kuma su sakemin kukan yunwa bana so na Shiga Hakkinki Ranar girkin ki na Shiga Kitchen ina Girkin Hakan ba Dadi Shiyasa na Shigo na gani ko Baki lafiya ne sai na Tambayi Izininki na Girka kodomin yara da kuma Abban Amira da zai Dawo Daga aiki a gajiye yana Bukatar Abinci.."
Har tagama Bayaninta Hararanta Barkat take sai da ta ida kana ta Mike tana Tafa Hannuwanta Lokaci Daya Tana Fadin"Wow..Bravo..Hajiya Hafsah...kinyi iya Tsara kalamai ba Shakka sai dai kuma kin makara bazasu Taba Tasiri a kaina ba Munafuka mai Fuska Biyu,Dama tun Shigowata Gidanan nasan Sai kin kawomin Mtsala azamana da Mijina gashi kuma kin Fara Tunda komai nayi mai baya gani sai ya ambaci Sunanki kamar don ke kadai akayi Shi Bazan Boye miki Na Tsaneki Kuma Allah ya isa Tsakanina Dake Tunda kina son Rabani da Mijina.."Tafada Idanuwanta sun kawo Kwallah baki Hafsah ta Bude tana Bin Barkat da kallo kafin tace"Ban..Bangane ba Ni..."Dillah Rufemin baki Karya nayi Ke ba Munafukar bace..? Har kina wani kokarin cewa baki gane inda na Dosa ba da anyi mgana sai ace ke mai Hakuri Hafsah mai Hakuri Hafsah me kaza..! Kan me nima ai mace ce ki barni nasamu Sakewa mana Nida Mijina Don Allah ki kyalemmu hakanan Bana kaunar ina Tare dashi naji yana Ambatan Sunanki Raina na kuna Kamar zan Mutu nake ji..Na Rokeki ki barni da Mijina Don Allah mganar Girki kuma in kin matsu ki Girki kici Keda ya"yanki kuma In kika Kuskura kika bama Mijina Wlh Allah ya isa ban yafe ba kuma sai Allah ya Kamaki da Cin Amanata Ranar Girkina.."Tafada Lokaci Daya Tana Haki Da Share Zufan Dake Digo mata Daga saman Goshinta.
Harta gama Mganarta Hafsah na Tsaye Tana kallonta Zuciyarta na kuna Idanuwanta Suka Cika da kwallah sai Tayi Saurin Dannewa ta Dago Tana Mirmishin Dayafi kuka Ciwo kafin tace'Naji Duka maganganuki..Sai dai ban isa na Sauya Miki Abunda ke Ranki game Dani ba.Ammh ina so ki sani ko ki yarda ko karki yarda Wlh Tallahi Ni Hafsah da Zuciya Daya Nake Zaune da kowa bama ke ba..Mganar kuma na barki da Mijinki Dama ni Ina Ruwana..? Inace Girki Arabe yake kuma kowa baya Shiga Hakkin kowa..?mganar abinci kuma zan Dafa kodon Ya"yana kuma nayi Miki alkawarin Insha Allahu Bazan Bama Abban Amira ba ballatana Allah ya kamani da laifin Cin Amana Daga karshe ina mai Baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba.."Ta karishe Fada tana jin wani Daci akasan Ranta lokaci Daya ta Juya ta Fita Daga Cikin Bedroom din Barkat din ta Rakata da Dogon Tsaki Lokaci Daya Tana Fadin"Stupit kawai.."Kafin ta koma ta kwanta tana kwafa Tana jin kaso Mafi yawa Daga Cikin bacin Ranta ya Ragu Tunda ta gayama Hafsah Abunda ke Ranta ammh Duk da Haka bata Huce ba tana ji kamar ta kasheta saboda Kishi da Haushi.
Hafsah kuwa koda takai Dakinta bata gani saboda Hawayen Daya wankemata ido kan kujera ta samu ta Zauna tana Kuka,tana Tunanin yau ita Barkat ke Kira Munafuka..me tayi mata..? Bata son komai ba Tsakaninta da Mijinta ba..In Hakane toh sai tace me.? Wani irin Abu ne Abdullahi baya mata Tataba Dora laifin kan wani..? Kodon mai Kishiya bai Mutuwar Allah me yasa take Zarginta..? Ta kasa gane komai sai Tayi kukanta ya isheta kana ta Share Hawayenta Ta kuma yi kokarin Cire Abun Acikin Ranta da Tunanin kirkiro ma kanta aikin Dazatayi wanda zai Dauke mata Hankali.
Wankin Noor da Uniforms dinsu Amira ta fito dashi ta wanke,Ta Share Dakinta Ta gyara Ko"ina Tayi ma Noor wanka ta goyata Gabda mangariba su Amira suka Dawo Daga makaranta Ta umarcesu da suyi alwala suka yi Sallah Tare bayan sun gama Ta Dauko Qur"ani suma tace su Dauko ta Shiga yi musu karatu Noor na Goye abayanta tayi Barci
Sun Dade suna karatun Kafin tace su Maida Qur"anan Su Dauko Littafan Bokonsu su yi Aikin da aka basu,Suka tashi Suka Dauko Ita kuma ta Mike tana Tunanin gwara ta nemi Abunda Zata ci ita da ya"yanta Shayarwa Take tana Bukatar Abinci Sosai Wuni kawai tayi Shan Ruwan Tea,su kansu su Amira yunwa Sukeci Karamin Hijabinta ta Sanya ta Dauki karamar Fitila mai Batir Dayake Sun Dauke Wuta ta Shiga Kitchen tana Goye da Noor ta Fara Jajjaga kayan Miya kafin ta Kunna Gas Dinta Wanda Abdullahi ya gaji ya Siya mata ta Dora Jallop din Taliya.
Ta Zuba Taliyan kenan Taji an kwala Kiran Sallar Isha"i yasa ta koma Daki Tayi sallah taso ta Shinfide Noor Daga Bayanta Ganin tayi Barci Ashe barcinta bai yi Nisa ba ta Farka ta Fara kuka Dole ta zauna ta bata Nono Ta mikama Amira ita,ta koma Kitchen tana Duba Girkin nata,Ita kuma Noor an Tsigeta Daga Nono bata Koshi ba ta Fara Kuka Hafsah kuma na kokarin Sauke Taliyan ta kashe gas ta Zuba musu sai ta Shigo Gabadaya Taji Karan Mashin Din Abdullahi da Shigowarsa.
Da kukan Noor ya Fara Cin karo Tun kafin ya kafe mashin Din ya sauka ya Fara Fadin"Kukan wa nake ji haka..? Noor ce ina Hafsah din take ne kika bar yarinya nata Tsala kuka..? Ya fada yana Sauka Daga kan Mashin Din Lokaci Daya yana Saba karamar jakarsa,Hafsah Data kashe gas ta Leko Daga Kitchen Tana Fadin"Ga ni nan Abban Amira Ina Kitchen ina Kokarin sauke abinci karya Kone..Kuma ma fa yanzu nagama Bata Nono da zan Fito na bama Amira ita ta Riketa Haushin na Cireta anono bata koshi ba yasa kaji tana yanka wannan Ihun kamar wacce ake yankata.."Tafada Tana kallonsa Cikin mamaki Abdullahi yace"Abinci kuma..? Ina ita Barkat Din Da bata Girka ba ko ba ita keda girki ba yau..?
Hafsah Cikin Halin ko In kula ta Juya Zuwa Kicthen din Tana Fadin"ita keda shi mana..Bata Girka bane.."Cikin Kakkausan Murya yace"Saboda mene..? Hafsah ta Fito Dauke da kulan Abinci da Filet Filet na Zubawa Tana Fadin"Bansani ba Abban Amira.."Tafada Tana kokarin Daidaita kanta Ta gabansa ta Wuce tana mai sannu da zuwa Bayanta yabi Zuwa Cikin Daki Acikin Ranshi yana Tunanin Lalle Barkat ta Rainashi ya kuma Zama Dole ya nuna mata kalansa.
Yana Shiga Amir ya taso yana mai oyoyo,Ya daukesa Lokaci Daya ya karisa kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ya zauna Kafin ya Sauke Amir Noor ya karba Hannun Amira yana Lallashinta Lokaci Daya yana Kallon Hafsah wacce ke kokarin Zuba ma su Amira Abinci yace"Kinga Bar Zuba abincinan zo ki karbeta ki bata Nono Tana ta kuka Fa.."Tana Zuba Abincin Tace"Rigimarta ce kawai fa Abban Amira bata da yunwa.."Cikin Daga Murya yace"Wani irin Rigima yarinya na Kuka kina Gayamin Rigima..? Kizo ki Amsheta nace bana son Gaddama Kin sani kuma.."Ya fada muryansa Tana Bayyana yadda Ya Hassala Jin haka yasa Bata kara mgana ba ta Tura ma Su Amira Filet din data Zuba Musu Taliyan Tana Fadin"Oya kuje Tiolet ku wanko Hannuwanku ga abinci kuzo kuci ku kwanta Gobe akwai School."Suka Mike Tare Amira tana Fadin"To Mommy.."kafin su wuce Zuwa Cikin Bedroom Din Abdullahi ya bisu da kallon Sha"awa gefe Daya kuma yana Jinjina Hafsah Domin Bata wasa Wajen Tarbiyansu Shiyasa koda yaushe zaka gansu Cikin Natsuwa da kalama.
Karisowa Tayi kusa dashi ta Zauna ta mika Hannu ya Bata Noor ,Shi ya zage mata Zif din Rigarta ta baya Ta Ciro Nonon ta mika ma Noor ta karba da Sauri ta Fara tsotsa lokaci Daya Tana Sauke ajiyar Zuciya Abdullahi ta kallah ya bankamata Harara yana Fadin"Ji yadda yarinya ke Sauke Numfashin Wahala ammh Ana mgana kina Fadin wai Rigimartace.."Ko mgana Hafsah batamai ba Shima bai Damu ba ya Mike Kawai ya Fice Batare Daya kara mata mgana da kallo Ta Bishi Tana wani Tunani acikinta ranta Su Amira ne suka katseta da suka Dawo Falon.
Afalo ya Iske Barkat tana Zaune tana Kallo ta Dora kafa Daya kan Daya Ta sauya Shiga Tunda yanzu Atamfa ce ajikinta Riga da zani tayi wani Daurin Dankwali na Ture kaga Tsiya,Sallamansa ma Dakyar ta amsa Tunda ya Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa Kafin ya Karisa Cikin bedroom dinta ta Rakashi da Harara.
Yana Shiga Jakarsa kadai ya ijiye ya Sabule kayan Jikinsa ya Fada Tiolet yayi wanka Ya Fito ya Shafa mai ya Fesa Turare ya saka Wata bakar Jallabiya ya Fito Falon Hannunsa Rike da wayarsa Inda ya barta nan ya isketa ammh wannam karon Wayarta na Hannunta tana Dannawa Kanta ya Tsaya Lokaci Daya yana Nazarinta kafin yayi gyaran Murya yana Fadin"Ina Abincina..? Naga har na Fito wanka baki kawomin ba..? Ko sai na Roka..?
Yafada yana mata wani kallon in kikace zaki kawomin wani Raini Zaki gane baki da wayau,Banzar iska tamai ko tama san yana kanta yana mata mgana Ran Abdullahi ya baci Cikin Mamaki yake Binta da kallo kafin ya saka hannu ya Fizge wayar Hannunta yana sakin Huci Jin am Fizge wayar yasa ta Dago a Zafafe Tana kallonshi Cikin Fushi yace"Ke Bada ke nake mgana ba..? Tambayanki nake ina Abincina..?
Kai Tsaye tace"Abinci..? Ta kada kai kafin tace"Ban Girka ba..Kuma ban ga Damar girkawa ba Sai yaya..? Ta fada Lokaci Daya Tana mikewa,Wani Sororo Abdullahi yayi yana kallonta kafin ya nuna kansa yana Fadin"Ni..Ni kike cema Baki Girka ba kuma baki ga Daman girkawa ba Barkat..? Yafada yana Nuna kansa Wani Rausayar dakai Tayi Tana Fadin"Eh kaifa..Ban girka ba nace zan maka karya ne..?Dama na bari ne sai Ranar da na koyi Hakuri da Biyayyah irin na Hafsah sai na Cigaba da girkin..!
Tafada tana wani Girgiza kai Abdullahi da Zuciyarsa ta Fara Tafarfasa yaji Ta kawo mai Wuya Yana Tunanin wani irin Raini ya auro ma kansa,Tunda yake ba Macen da tataba mai irin Wannan Salon Rainin da Barkat tamai,Tuni Idanuwansa Suka Sauya launi Jijiyoyin kansa Suka Tashi Radau Kallonta yayi ido Cikin Ido kafin yace"Kin san kuwa wa kike gayama Mgana Haka..? Nifa Mijinki ne ko kin manta ne..?
Ta Koma ta Zauna Tana Fadin"Nasani mana..Ba Abdullahi bane Mijin Hafsah ba.."Tafada tana Sakarmai ido,Wani Irin Zafi yaji Ransa na masa kamar ya Daga Hannu ya Zabga mata mari sai wata Zuciyar ta kwabeshi,ganin in ya Cigaba da Tsayuwa Wlh sai Barkat taci Ubanta kawai sai ya Wurgamata Wayarta ya kada kai ya Fice ta Rakashi da Mirmishi kafin ta Mike ta Dauki Wayarta Tana Fadin"Dama Ashe ni na bada Dama ake min Abunda aka ga Dama.."
Yana Fita Fuu sai Dakin Hafsah Tana Zaune tana Cin Abinci Noor na kan Cinyarta,su Amira sun Shiga Ciki sun kwanta, ya Fado Dakin Har sai da ta Tsorata Kusa da ita ya zauna kan kujera Yana Kallon Hafsah Wacce ta Dakata da cin Abinci Tana Fadin"Abban Amira lafiya kuwa..? Muryansa Cikin Kaushi yace"Tashi ki Sawo min Abinci.."Kawai ya iya Fada yana Sakin Huci Sama sama Galala ta Bisa da kallo Bata samu Zarafin mgana Ya Daga Murya yana Fadin"Ki tashi ki bani Abinci nace ko..?
Ya fada Cikin Fushi yana Tsareta da ido ajiyar Zuciya ta Sauke Data gano Dalilin Masifar Cikin kwantar dakai Tace"Sai dai kayi Hakuri Abban Amira na Riga nayi alkawarin Bazan baka Abincin nan ba..? Ido ya sakar mata Yana Fadin"What.? Saboda mene..?
Kai Tsaye tace"Saboda bana son Amanar Barkat ta kamani...Tunda ba Ranar girki na bane bani da Hakkin baka abinci."Bata gama mgana ya Mike a Fusace yana Fadin"Wannan ai Zencen banza ne..? Kina matata kuma a kawomin wani iskancin banza acikin Gidana Uban waye kuma yace miki haka.? Ehe nace waye yace zaki ci amanar barkat...? Tunda ita bata Girka ba Hakkinki ne ki Girka ki bama Ya"yana Nima ki Bani Tunda zama na Kike ba zaman wani ba Malama.."Ya Fada yana wani Sakin Nishi na Masifa Kai kawai ta Girgiza Tana Fadin"Kayi Hakuri Abban Amira ban Taba saba Umarninka ba ammh yau zan saba Bazan iya baka abinci ba alhalin Barkat tamin Allah ya isa bata yafemin ba matukar na Baka abinci Ranar girkinta.."
Tafada Cikin kwantar da Murya Sai Abdullahi yaji kamar Jiri na Neman kadashi Saboda kalaman Hafsah Cikin Wani Fushi mai Tsanani yace"Ita tace Haka..? Kai Hafsah ta Sunkuyar kafin ta Ture Filet din gabanta ta Mike Sai da ta Shimfidar da Noor kan kujera ta Dago Tana Fadin"Nidai ina kara baka Hakuri Abb..."Bata idasa ba Taji ya Damki Dankon Hannayenta Da karfi ya Girgizata yana Fadin"Tambayanki nake ki gayamin ita tace haka..? Yafada Cikin Tsanani Fushi sai da Hafsah ta Tsorata Domin Duk Fushin Abdullahi bata taba ganinsa Cikin wannan Fushin ba.
Cikin Rawan Murya tace"E..eh ita tace min haka.."Ido ya Runtse kafin yace"Wani Abu ya Faru bayan Bana nan ko..? Yafada yana kureta da ido Girgizamai kai Tayi Tana Fadin"Bafa Abunda ya Faru Abban Amira.."Karya kike..Wani Abu ya Faru..? Ya katseta Cikin Daka mata Tsawa kafin ya Cigaba da Fadin"Zaki Fadamin Abunda ya Faru ko kema sai Ranki ya baci..?
Yafada yana Sakarmata Jajayen Idanuwansa Numfashi ta Sauke ta karya Wuya tana Fadin"Abban Ami.."Ashe ke ba Wakiliya ta bace in bana gida..? Kice makwafina in bana Gida Hafsah Saboda Haka ki Fadamin Abunda ya Faru yanzu Ina Jiranki.."
Hafsah ta Runtse ido ta Bude Zatayi mgana kawai ya saketa yana Fadin"In baki Fadamin ba.Ban yafe miki ba Hafsah kuma bazan Taba yafe miki ba indai baki Sanar dani Abunda ya Faru ba bayan bana nan.."Yafada yana Kokarin Controlling Din Fushinsa Ido Hafsah ta Zaro Tana Fadin"Baka yafemin ba Abban Amira..?
Cikin kakkausan Murya yace"EH BAN YAFE MIKI BA HAFSAH MATUKAR BAKI SANAR DANI BA.."jin haka yasa Hafsah bata da Zabi Tiryan Tiryan ta Shiga Zayyanamai komai Har karshe ta Karishe da Fadin"Plz Abban Amira karka ce zaka yi wani Abu..Ka bari ka wuce yanzu kana Cikin Fushi ne plz.."Ko Sauraranta bai yi ba ya saka kai zai Fice ta Bishi Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"A"a Abban Amira ina zaka..? In kayi mata wani Zarginta zai Tabbata akaina tace na Hada mata Gulma Na Shiga Tsakaninta da Mijinta Don Allah ka kyaleta Ni Tayi mawa kuma Wlh komai ya wuce..'"
Fizge Hannunsa yayi yana Haki yake Fadin"Wlh karya take Hafsah..Ita Wacece..? Ita din Banza da Wofi Ita Har ta isa ina Auranta Tana Karkashina tace zata zo Gidana ta Raina ni ta kuma Raina min mata..? Me take Takama dashi...? Wlh sai ta gane bata da wayau matukar bazata Darajani ba Kuma bazata Girmamaki kamar yadda Ni da Sauran yan"uwana muke Girmamiki ba Wlh sai dai ta bar Min Gida Bazan Dau iskanci ba Kinjima na Rantse.."Hankalin Hafsah ya Tashi ta Dafe Kirji ko kafin tayi wani yunkuri ya fice ta Bishi da Gudu Tana Fadin"A"a Abban Amira karkayi haka.."
Waigowa yayi yana Fadin"Ki koma Daki Hafsah.."Taki komawa tsawa ya Dakamata wanda Harta Barkat Dake Dakinta sai da tajita Cikin Kakkausan Murya yana Nuna mata Hanyar Dakinta yana Fadin"Ki koma Dakinki ki Zauna...Babu Abunda zaki iya yi, awannan al"amarin saboda Haka Babu Ruwanki.."Daga haka ya Barta nan tsaye ya Banga Labulan Dakin Barkat ya Shiga Cikin Fusata.
Baya Hafsah taja ta Dafe Kirji Tana Fadin"Innalillahi Wa'inna illaihirraju"un.."Domin a yanayin Abdullahi kadai ta Tabbarta da kalamsa Tsoronta kuma Tasan baza"ayi mai kyau ba kasa komawa Daki Tayi Taja ta Tsaya Cikin Zullumi.
Barkat na Tsaye Tun Bayan Jin Tsawan da Abdullahi yayi