Advertisements
Chapter 1 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 38

1 to 3K   out of 113.1K words

πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—




IGIYAR RAYUWA😭




πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Story and written by: Fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:-Gureenjo6763

*Hey readers am here again with another story, hope yhu will like it. Banyi muku alkawarin samu kullum ba sbd yanayin lectures d'ina but zanyi iya kokari don ganin na faranta muku, and I will be considering votes and comments ko da na gaji In har naga comments d'inku ze iya kara min karfin gwiwan yin muku wani page d'in ku biyoni*

'Yar mutan Adamawa

Page➑️1️⃣▢️2️⃣
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Tsugune take a gefen babban kogin da ake kira kogin sarki wanki takeyi a natse tana 'yar wakanta da fillanci kyakyawa ce sossai irin sossai d'innan duk da yadda talauci da babu ya nuna sossai a jikinta hakan be hana kyaunta fitowa ba, sanye take da doguwar rigan material me flowers kanana kanana yellow da baki rigan daga gani zaka san ya dade sbd kodewar da yayi har ya fara fari ta d'aura brown silky hijab d'an daidai da baze wuce gwiwarta ba duk da wanki takeyi hakan be sa ta cire hijabin ba sbd maza dake kai kawo da wasu dake wanka daga bakin gabar kogin gefe da gefenta mata ne manya da kanana wasu na wanki wasu na wanke wanke kaman daga sama taji ance "Adda khairi, Adda khairi" d'aga dara daran fararen sol din idonta tayi ta zubawa yaron dake ihun sunanta wadda baze wuce 5years ba, da gudu ya gangaro bakin ga'bar daga kan tudu yace "Adda khairi Dada d'o nyaune(dada na kira)" a hankali ta bud'e pink well carved and attractive lips d'inta tace "Nabeel ko wad'i an kam a nanata hala?(me yasa kai kam baka jin magana) mi had'ai ma nyaunugo inde am dayinga na?(ban hana ka kiran sunana daga nesa ba?)" tura cute lips dinshi yayi gaba fuskanshi futu futu da kura da alamu wasa yakeyi aka kirashi aka aikeshi kayan jikinshi kod'add'iyar shadda ce blue color irin yadi marasa tsadan nan a cikin masu saukin kud'inma na karshe duk zarenshi ya fiffito a yanayi shagwa'ba yace "wad'u munyal Adda manga(yi hakuri Adda babba)" murmushi tayi hakoranta da suke da d'an girma farare tas suka bayyana tace "daad'i na da kai kenan oya jod'u renu kare d'o ha mi yaha mi wara bo mi viyai a lota(zauna ka kula da kayan nan bari inje In zo kuma bance ka wanke ba) kai ya gyad'a mata ita kuma ta mike, ban san lokacin da na furta 'fa tabarakallahu ahsanul khalikeen' duk da yarinyar da naji an kira khairin ba zata wuce shekaru 17 ba amma Allah ya mata halitta manyan ido gareta farare tas, hancinta me tsawo d'an daidai ba har chan ba bakinta d'an karami ne sossai amma tana da manyan fararen hakora ba irin manya masu munin nan ba a jere suke a kuma had'e gashin giranta a kwance kaman anyi carving Fara ce tas kamanninsu d'aya da Indian actress nan "Drashti dhami, wacce tayi madhubala ta kuma yi geet series" zaka iya cewa 'yan biyu ne abunda zata nunawa khairi to hutu ne yayinda khairi zata nuna mata hips don Allah ya bata bajajjen hips sossai,
a natse ta fara takawa tana haurawa tudu har ta haura ta d'auki hanyar gidansu da tafiya kad'an ne daga bakin kogin sarki, tana cikin tafiya kanta a kasa taji an bangajeta da sauri ta d'ago a kuma zafafe don bata barin ko ta kwana had'a ido sukayi da Hauwa yarinyar da tunda suka taso bata san me ta tare mata ba ita da mahaifiyarta suka d'auki karan tsana suka d'auramusu da family d'inta dukda makwafta ne na sossai har hauwan ta wuce khairi tasa hannu ta fisgo hannunta tare da dawo da ita baya tace "ke hauwa baki ji kin buge ni bane?" Da yake hauwan ba fulani bace wasu kabila ne daga cikin kabilun taraba state, seda hauwan ta dankara mata harara tukun tace "an buge d'in kiyi abunda zakiyi" har khairi ta bud'i baki zatayi magana taji ance "ummul sweetheart wani me kararren kwanan ne ya ta'ba min ke In yi kasa kasa dashi yanzu nan" yana magana ne cikin gadara da murya da ya nuna tsananin dabancinshi baki ne dogo sossai kakkarfa daga shi se shorts da bakar vest jikinshi ko ta Ina yanka ne ga wani tsar'be'biyar tsirarar Adda a hannunshi, shi a dole son unnulkhairi yakeyi tunda ta taso yake kula da ita ba wani shegen da ze ta'bata be rama mata ba se su dada da Abbanta duk da haka ummulkhairi bata ta'ba kula shi ba sbd nasihar Dada da Abba a gareta akan wannan rikakken d'an daban Idi shed'an da ya gagari kowa ciki harda iyayenshi gabad'aya unguwan tsoronshi suke, harara ta zabga mishi dashi da hauwan tukun tayi karamin tsaki tare da ci gaba da tafiya gida d'aya, biyu, uku na hud'un ta shige wadda shine nasu runfar su idi shaid'an da 'yan kungiyanshi na 'yan shila na kafe daga gaban gidansu suna facing juna tsiririyar hanya ne irin na cikin unguwa ya raba tsakaninsu wai yayi hakan ne duk don ya ringa bawa gimbiyartashi kula, madaidaicin gida ne zagaye yake da zana cikinshi shimfid'e da yashi me kyau daga gefe kusa da langalangar kofarsu d'akin bukka ne guda d'aya O kenan, se ginin block me d'akuna biyu daga Chan d'ayan bangaren ba plaster balle penti a jiki zallan blocks dinne se kofa da window na katako d'aya na dada da Abba d'ayan na Ummulkhairi da Nabeelah twin sister din yaron da aka aika kiranta yayinda O d'in ya kasance na Nabeel da twin brother d'in ummulkhairi wato Abulkhairi daga gefen d'akunan block d'in madaidaicin kitchen d'insu da akayi gininshi da jar kasa yake gaba da kitchen din sossai bayi ne da akayishi da langa langa wato zing amma daga gani tsoffi ne don duk jikinsu tsatsa ne duk da gidan talakawa ne amma seda tsabtar su yabani mamaki gidan kal kal dashi ko leda baza ka gani a kasa ba da sallama ummulkhairi ta shigo daga Chan d'akin Abba dada ta amsa tana fitowa da 'yar sandan ta tana cewa "se jotta dadaa am?(se yanzu mama na?)" Khairi tace "Eh dada mi dari be hauwa un ha lawol(na tsaya da hauwa ne a hanya)" dada tace "yau kuma khairiyya ban hanaki biye mata ba? Sam ba halin musulunci bane kiyi kokari ki ringa danne fushinki In ta tsokane ki Dan Allah" da lallami Dada tayiwa khairi magana sbd abu d'aya da ita shine ba'a mata fad'a don Allah ya jarabceta da iska wato aljannu a duk sadda ka d'aga mata murya In basu tashi ba toh tabbas zata kwana biyu a kwance tsabar ciwon kai gwara ka daketa toh baza su tashi ba, baki ta zunburo dukda dadan tasu bata gani tace "ni shikenan In ta tsokane ni bazan amsa ta ba? Allah Dada kin cika sanyi da hakuri" murmushi dadan tayi tana seta inda take jin muryan khairi ta fitowa tayi mata dakuwa tana cewa "ungo naki, Abbanku ya kira akan cefene yace almajirin da ya saba turowa be zo ba ko za'a tura Abul, Abul kuma tunda ya fita da safe be dawo ba shine nace ko zaki ki kar'bo mana?" Cikin ladabi khairi tace "toh Dada bari In chanza kayan nan inzo inje" murmushi dadan tayi tana nufar inda suke ajiye taburma kaman ba makauniya ba da yake ta san kan komai na gidan shekara 18 a cikin gida d'aya ba wasa ba dole ta gane duk wani corner na gidan bayan ta shimfid'a taburma ta zauna daga wurin windownsu khairi bata jima da zama ba khairi ta fito sanye da black hijab kayan de sune bata chanza ba se takalmi da ta d'auko na roba ta saka tana cewa "hato nabeelah bo(Ina nabeela kuma)" Dada tace "o d'ani ha sudu am(tayi bacci a d'akina)" khairi ta dafe kai tana cewa "ooh jotta mo doftatam? Wlh mi yid'a dillugo min tan(ooh yanzu wa ze rakani? Wlh ban son tafiya ni kad'ai)" Dada tace "toh tefu sulaimi le to o wala wad'a ko d'ume se o dofta ma(toh ki nemi sulaimi mana in bata komai se ta raka ki) tana d'an bubbuga kafa ta fice seda taje bakin kofa tukun tace "seto mi warti(se na dawo)" bata jira amsan dada ba ta fice gidan dake gefensu daga hannun damanta ta shige gidansu khairi yafi gidan rufin asiri sossai akan gidan da ta shiga don daga yanayin gidan ma kad'ai zaka tantance "salamu alaikum" wata yarinya da take tsaran khairince ta amsa da "wa'alaikissalam Aminiya sannu da shigowa" murmushi khairi tayi tana duban ummusulaimi tace "yauwa Aminiya Ina ummi" sulaimi tace "ummi taje barka Chan unguwan baraya nima yanzu nake shirin shiga gidanku ki rakani kasuwa" "laaa ai nima shigowa nayi ki rakani kasuwan fad'uwa yazo daidai da zama kenan" inji fad'an khairii "to taso muje yamma nayi amma inason gangarawa bakin kogi na had'awa nabeel kayan wankin da na fara ya dawo da su se mu wuce" sulaimi na sa hijabi ta amsa suka fice ba lefi sulaimin ma kyakyawar bafulatana ce dukda ko kwatan kyaun khairi batayi ba kawaye ne tare suka tashi dukda su khairi sun riga zuwa anguwan amma su sulaimi na zuwa kyakyawar alaka ta shiga tsakaninsu iyayensu suka zama aminai haka yaran ma sulaimi ita kad'ai suka haifa sa'ar khairi da Abul ce, bayan sunje bakin kogi khairi ta had'awa nabeel kayan ya wuce su kuma suka d'auki hanyar da ze kaisu har kasuwa ta lunguna lunguna seda sukayi nisa da tafiya suna 'yar hiransu duk da khairi bata fiya surutu ba sulaimi ce tace "wai nikam me kikama hauwa ne? D'azu naji tana ta zage zage tana kiran sunanki dasu dada" dafe kirji khairi tayi tana cewa "ni 'yar umaru? Ban mata komai ba nikam, hasali ma itace ta neme ni fad'a d'azu na tafi na barsu da idi shed'an" sulaimi tace "hmm to idi shed'an kam ya mata dukan mutuwa" dayake gidansu sulaimi da hauwa a manne yake duk abunda akeyi a cikin na d'aya zakaji inhar aka d'aga murya zaro ido khairi tayi tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun na shiga uku"................






#vote
#share
#comment

'Yar mutan Adamawa



πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—







IGIYAR RAYUWA😭





πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763


'Yar mutan Adamawa

Page➑️3️⃣▢️4️⃣
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

"Thulaimi(sulaimi) ba dukan hauwan da akayi nake tsoro ba thasoba (sbd) ko nima kusa nake da Chatha(chasa) ta thulaimi fad'an Abba ne ban shirya mishi ba Wlh kin than(san) ba son tashin hankali yake ba na tabbatar kuma se Maman hauwa ta kawo kara" khairi tayiwa sulaimi maganan cikin sanyin murya ganin yadda sulaimin ke dariyar rud'ewantan daga farko shiru kawai sulaimin tayi don bata san me zata ce ba hakan yasa khairi ma tayi shiru da bakinta har suka isa kasuwa ta gate d'in baya suka shiga hakan yasa sukayi saurin isa layin 'yan kayan miya daga nesa take hangan malam umaru wato mahaifinsu da suke kira Abba zaune a gaban kayan miyanshi da ba wani yawan kirki ne da su ba, har suka karasa kusa be lura dasu ba seda khairi tace "Salamu alaikum Abba" juyowa yayi yana sakar mata murmushi yace "wa'alaikissalam na'am 'yar Abba kun karasu kenan?" Har kasa suka duka suka gaisheshi tare da mishi sannu da kasuwa d'an ledan dake ganganshi ya d'auka ya mikawa khairi hannu biyu ta sa ta kar'ba tana mishi godiya sallama suka mishi shi kuma yayi musu Allah tsare suka wuce seda suka sayi sakon sulaimi tukun suka juya gida..

Suna isa khairi ta hura murhu ta d'aura musu abincin daren tanayi suna hira da Dada har Abul ya dawo kusan lokaci d'aya suka shigo da Abba khairi ta kawo musu ruwa suna had'a baki da Dada wajen musu sannu da dawowa, abinda na fahimta shine akwai tsantsar kauna da shakuwa a cikin wannan gida suna tattali da kula da juna ba kad'an ba, dab magrib khairi ta gama girki ta fito daga kitchen din tana sharce gumi don duk tayi zufa sbd hayaki sannu sukayi mata Abul da take kira d'an uwa har da mata dariya bata kula shi ba ta d'ibi ruwa ta shige bayi tare da watsawa sauri sauri tana fitowa ana kiran magrib, ta samu ma Abul ya nemo nabeel duk sunyi alwala zasu fice massallaci itama alwalar ta d'aura tare da shigewa d'akinsu ta tada sallah tana idarwa ta fito ta d'auko katuwar taburmansu da ta ji jiki ta shimfid'a a tsakar gidan tare da shiga d'akin Dada ta tada nabeela tana fitowa ta kunna wani fitila me haske da ake makalawa a sama yana anfani da manyan batir a kan taburman ta ajiye tare da kara komawa d'akin Dada ta kwaso qur'anai dasu hadith, zadulmuslim, riyadussaliheen, Arrijalu wannisa'u fil jannah da dai sauransu ta ajiye akan taburman a daidai lokacin su Abba suka shigo akan taburman suka yada zango har nabeela da yanzu ta idar da sallah irin tasu ta yara karatu suka fara Abba ke koya musu dukkansu Dada ya fara yiwa tukun ummulkhairi da Abulkhairi su kuma suka karawa nabeel da nabeela suna gama hadith da sauran littatafan suka bud'e qur'ani me tsarki kowa ya fara inda yake so Dada na zaune tanayi da kai basu suka rufe alqur'anin ba se da sukaji ana kwala kiran sallahn isha adu'a Abul ya musu suka shafa mazan suka nufi massalaci yayin da matan suka yi a kan taburman suna idarwa Khairi ta shiga kitchen ta fiffito musu da abinci da plates, ruwan sha har dana wanke hannu ta Ajiye, su Abba na shigowa suka nufi taburman a natse suka zazzauna tare da wanke hannu suka fara cin abinci wadda ya kasance tuwon masara da aka d'aure da garin alabo se miyan kuka da akayishi da kifi banda, mazan su uku kwanonsu daban haka matan su uku nasu daban gidan Shiru kaman ba mutane har suka gama suka wanke hannu nabeela ta taya khairi tattare kwanukan zuwa kitchen, wai kafin su fito gidan ya kaure da hira nabeel se zubawa Abba surutu yakeyi yayinda Abul ke magana da Dada su khairi ma jona su sukayi yayinda Abul ke tsokanan khairi tana ta shagwa'ba Abba na kar'ba mata (kai readers gaskiya rayuwan gidannan ya burgeni) tsintar muryan Abul nayi yana cewa "In ba tsoro ba er uwa kice Asiya" Da karfi tace "Athiya" dariya suka face dashi kasancewar bata da "sa" duk yadda tayi sede ya fita a "tha" (ba lallaine duk maganan da khairi tayi in rubutashi da 'th' ba, sbd ba kowa ne ze fahimta ba kuma bazan iya dinga rubutawa sau biyu ba)..

Tura baki gaba khairi tayi tana bubbuga kafa tace "Abbana ba ka ganshi ba" wani dariyan suka sa Abba kam murmushi yayi yana cewa "Zo nan 'yar Abba kyaleshi zan rama miki ne" gwalo ta mishi tare da komawa kusa da Abba tana d'aura kanta kan kafanshi, Baammm suka ji an buga kofan gidan a tare suka maida hankali kan kofan lokaci d'aya khairi ta lumshe ido zuciyarta na bugawa alamun mutanenta suna kusa, hauwa ce da mamanta suka shigo a masifance har kan tsakiyar taburman da suke Maman na zuba masifa kaman zata ari baki "matsiyata en iska, en gudun hijira ko kuma ince korarru wai ku har kun isa? Nace kun isa? Kusa d'an isakan saurayin d'anku yima 'yata duka?" Shiru Abba yayi yana kallon khairiyya har ga Allah shi ba mutum ne me son tashin hankali ba haka matarshi be san inda ummul ta d'auko zafin zuciya ba a sanyaye yace "ummulkhairi bata hakuri, Dan Allah Maman hauwa kiyi hakuri hakan baze sake faruwa ba" Abba ya furta Kan ya rufe baki Maman hauwa ta kar'be "baza'ayi ba, baza ayi hakurin ba Wlh se na rama mata ko akan wannan makauniyar nakasashiyar matan nan taka ko kuma kan gantalalliyar 'yarkan....." Abul yayi saurin cewa "dakata Malama ya za'ayi kizo har cikin gidanmu kina zagar mana iyaye toh ya isheki shiru shiru fah ba tsoro bane, wall......." Dada ce tace "Abulkhairi" Da kausasshen murya shiru yayi yana cije le'be duk da ya kasance marar fad'a ga hakuri amma In an kaishi makura shima ba baya ba wurin masifa, wani irin gud'a Maman hauwa ta sauke tana girgiza jiki tace "Ayyyirrriirii yaro man kaza kai baka kai inyi da kai ba haka uwarka sede inyi da uban ka" Abba yayi saurin cewa "dakata dakata talatu shiru shiru fah ba tsoro bane Wlh gudun magana ne ki kiyayi randa zaki kaini bango" be karasa ba ta sa hannu ta bankad'a shi zuwa jikin gini tace "an kaika umaru nace an kaika me zakayi" shiru gidan yayi na mintuna kan naji wani bala'e'en kara da ya sa hanjin cikina motsawa kaman kiftawar ido naga khairi dake kwance a taburma ta lumshe ido da farko kaman bata san abunda ke faruwa ba, ta isa gaban maman hauwa hannun da ta sa ta hankad'e Abba hannun khairi ta rike tare da kafe Maman hauwan da idanunta da suka koma ja tana mata wani irin deadly look wani irin ihu Maman hauwa tayi na azaba tana kiran hannunta hannunta, khairi ta kara murd'awa tana danne hakwaranta da gudu Abul da Abba sukayi kan khairi suna kokarin cire hannun khairi amma ko motsa hannun sun kasa hauwa ma ta karaso da d'ingishi tana ture khairi wani wawan mari me kurmantarwa khairi ta sakewa hauwa da hannun hagunta inda ta ci gaba da murd'a hannun uwar da na damanta, zuwa lokacin duk makwabta na kusa

1 / 38