Advertisements
Chapter 23 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 38

66K to 69K   out of 113.1K words

color ce da ya matukar yi mata kyau dannawa tayi se taga ya kawo haske harda mtn sim a ciki, murmushi tayi a fili tace "thank yhu" tare da d'auko chargarn ta makala ta kuma ajiye kwalin da earphone a kan gado.................

Fita tayi ta haura saman momma tare da knocking kofan daga ciki momma ta amsa tana cewa "har kun dawo khairi?" Khairi tace "Eh mun dawo ya min komai na gode, har uniform kala biyu aka bani" murmushi momma tayi tana mikewa hannunta d'auke da sky blue gyale tana yafawa kan orange and sky blue Swiss lace dake jikinta, tana cewa "muje khairi samun mu dawo da wuri ki d'aura girki" Khairi tace "Toh" tare da yin gaba.................

Musharraf ne ya fito don kaisu momma ta kame a baya khairi ta shiga gaba, ba me magana a motan se khairi dake mishi kwatance har suka isa kofan gidansu, ita da momma ce suka sauka yayinda shi kam ya gyara zamanshi a kan kujerar driver yayi kasa dashi tare da kwanciya, da sallama suka shiga dada dake zaune tsakar gida ta amsa tana cewa "Khairi me ya dawo dake da wuri haka?" Khairi tace "Da momma muke" dada tace "lale maraba sannu da zuwa" sossai momma ke kallon dada tana tunanin inda ta ta'ba ganin fuskan amma ta kasa tunawa hakan yasa ta zauna a kan sallayan da khairi ta shimfid'a mata....................

Zama tayi sossai kan suka gaisa da dada Bayan sun gaisa take sanar da ita kudurinta na son su koma gidanta da zama na har abada zata kula dasu kaman en uwan da suka fito ciki d'aya, tashi d'aya dada taki, ba yadda momma batayi da dada ba amma taki, khairi dake zaune gefe bata ji daadin hakan ba sam, momma ce tace "ki cewa musharraf ya shigo ya gaisheta se mu wuce ko" Khairi ta mike ta fice mintuna biyu ta shigo kan ya shigo daga baya taugunawa yayi har kasa ya gaida ta, ta amsa da fara'a tana mishi godiya don daga jin sunan ta san shine ya sayawa su nabeel kaya kuma shine de surkinta mijin khairi, momma ce ta sanar dashi dada taki su koma gidanshi, cikin hankali da natsuwa ya fara tausar dada inda ya tabbatar mata ya san abinda take tsoro wato wulakanci da tozarci inda yayi alkawarin In har yana da rai duk duniya ba wadda ze wulakantata yana gani be d'au mataki ba, sannan ya tabbatar mata daga kan mommanshi, kannenshi da ershi ba me wani bakin halin da baza ta iya zama dashi ba sossai ya nuna mata illan zamansu anan su kad'ai In khairi tayi aure, jiki a matukar sanyaye dada ta amsa da ta amince zasu zauna tare da su da zuciya d'aya In shaa Allahu..............................











#vote
#share
#comment






'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗







                  IGIYAR RAYUWA😭







                                              🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION (home of peace, charity, honor and super writers)


Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

Page➡️6️⃣5️⃣▶️6️⃣6️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Da tsantsar mamaki da sha'awa take kallonshi a gaskiya ta yabawa kaifin basira da fasahan magananshi sbd sarai ta san Dada In ta kafe a kan abu to fah me tankwarata se Allah haka Abbansu ma duk zuciyar fulani ne dasu, maganan momma ne ya katse mata tunani da kallon da take mishi tace "Khairi tashi muje gobe in Allah ya kaimu se kuyi parking" mikewa khairi tayi dada na ta godiya suka fice...............

Kad'an kad'an momma da musharraf suka dinga hira har suka isa gida, kitchen ta fad'a ta fara girki don ganin rana yayi se kawai tayi musu faten shuwaka da gyad'a ta had'a musu soya beans juice da yaji flavors kala kala a dining ta shirya tana gamawa Amrah da little na shigowa da gudu little taje ta rungumeta sama ta d'aga ta tana dariya tace "pretty sannu da dawowa ya school?" Little ta fara zuba mata surutu akan abinda ya faru a makaranta tana jin labarin little tana magana da Amrah har suka haura inda take gayawa Amrah gobe itama zata fara zuwa school da su in shaa Allah.................

Ihu Amrah ta fara tana tsalle tace "yeeeeeeeh amma naji daadi sossai Allah ya kaimu akwai rocking kafin waec" hararanta khairi tayi tace "ba wani rocking  karatu kawai zanyi malama" waro ido Amrah tayi tare da fasa shiga d'akinsu ta nufo na little da sama nan zasu shiga da sauri khairi ta shiga tana danna kofa tace "ki wuce kije kiyi wanka duk tsamin zufa kike" Amrah na tsaye rike da kwankwaso tace "Lallai ma yarinyar nan amma kin sha ni dayawa ki guji had'uwarmu" murmushi khairi da little sukayi suna tafawa kaman sun yi wani abin kirki, bayi ta shiga da little tayi mata wanka................

A pink towel d'inta ta nad'ota suna fitowa taga mutum zaune bakin gadon little har tsorata tayi kan ta gama gane wanene ajiyar zuciya ta sauke tana ajiye little da niyyan ficewa, cikin husky voice d'inshi yace "zo ki ciro mata kaya" dawowa tayi ta nufi wardrobe d'inta shi kuma ya kamata zuwa kan dressing mirror d'inta ya shafa mata mai tare da murza powder fari ya shafa mata a fuska tare da sa mata lip balm sunayi tana mishi hira murmushi kawai yake sakewa jefi jefi..............

A sace take kallonsu ta bar ma fitar da kayan se kallonsu da take yi kaman tana kallon tv ba karamin burgeta sukayi ba a natse ya taje mata kanta dake tsefe ya shafa mata mai tare da sa mata ruffle ta cikin madubin ya kalli khairi da tun d'azu ya lura da yadda take kallonsu yace "madam muna jira" a kunyace ta fiddo kayan ta miko musu tare da juyawa ta fice cikin sassarfa.................

Ta'be baki yayi yana girgiza kai, tare da sakawa little kayan, kasa suka sauko inda suka samu duk ahalin gidan a kan dining har khairi da momma ta sata zaman dole, sun ma yi nisa a cin abincinsu yayinda khairi ke juya chokalin kawai bayan sun zauna khairi ta mike tayi serving d'insu ta turawa kowa gabanshi a natse ya fara cin abincin ba tare da ya tankawa kowa ba..................

Bayan sun gama momma tayi musu bayanin dawowar su khairi da family d'inta gidan duk cikinsu ba wadda ya nuna 'bacin rai ko a fuska sema farin ciki da suka dinga yi, anan kuma ta sanar musu batun zuwa dukku da zasuyi sbd maganan auren Nuriyyah da Marwan se kuma na Khairi da musharraf tana so su zama danginta kawayenta kuma madogaranta hakan yasa zasu tafi gabad'ayansu tunda kwana biyu kawai zasuyi..................

Tsokana ne fal ran Amrah da Miemie amma musharraf na zaune ba halin yi, se de da ido suke gulman, a bazata musharraf yace "ke tashi kije ki d'auko mun irin ledan d'azu a parlor na" kowaccensu kallonshi take sbd basu san da waccce yakeyi ba, khairi da ta fahimci da ita yakeyi yasa ta mike ta fice yayinda Miemie da Amrah suka kalli juna tare da fashewa da dariya kasa kasa harara ya zabga musu tare da mikewa ya koma parlor ya zauna duk suma parlorn suka koma....................

Mintuna be wuce biyar ba khairi ta dawo da ledojin guda biyu a hannunta har gabanshi taje tace "gashinan" Seda ya gama shan kamshinshi kan ya kar'ba, juyawa tayi d'aki tare da d'auko wayan da ya bata da komai ta fito ta samu su Amrah na murnan nasu murmushi kawai tayi ta nunawa momma, godiya ta tayata murmushi kawai yayi wa momma duk hankalinshi na ga waya..................

Washegari bayan khairi ta zo tayi breakfast da sauri sauri tare da shiryawa cikin uniform da yayi mugun amsanta ta fito a parlor ta tadda Amrah na breakfast zama tayi a kan dining din tana cewa "yi da wuri mu tafi Amrah Dan Allah" kallonta amrah tayi tace "wow uniform nan ya kar'be ki waiiii omoooo wallahi zaki tsone idon mutane yau kinga yadda shape d'inki ya fito? Dama haka kike shiyasa baki ta'ba rabuwa da hijabi? Wowwww amma yaya musharraf ya mo.............." da sauri khairi tace "kayyah Amrah surutunki yayi yawa, In kin koshi ki tashi mu tafi plz" ta'be baki Amrah tayi tana kallonta har lokacin haka khairi ta dinga damunta har seda ta mike suka haura sukayiwa momma sallama kud'i ta bawa khairi tace inji musharraf ta sayi books da pen da de abinda ze taimaka mata a lesson d'in duk kuma za'a samu a school din, godiya sossai tayi kan suka fice....................

A kofan parlor suka gamu dashi a tare suka gaisheshi da lafiya kawai ya amsa su, khairi ce tace "Hamma musharraf na gode sossai" kallonta yayi na fisha tukun ya kauda kai yana nufan kujerun parlorn fita sukayi driver ya ja su suka fice Amrah na mitan itakam suyi suyi waec ta huta da fitan sassafen nan ita bacci baya isanta ga Miemie da Adda nuri ko tashi basu da niyyan yi itace kawai take fama da wani uniform.............

Murmushi kawai Khairi keyi har suka isa, sossai makarantan ya mata daad'i yadda sukayi karatu kaman revision ko wanne malami 40mins ba su suka fito ba se 1:20 sukayi sallah tare da break na 20mins duk wadda ya kalli khairi In har ya san Amrah se ya tambayeta wacece wannnan beautiful girl dinnan se Tace sisternta ce, a haka suka koma suka kuma yin wani 40mins d'in kan aka tashe su, suna fitowa sukayi site d'in nursery school suka d'auki little sukayi gate a nan suka samu driver na jiransu suka shige suka dawo gida....................

Tana sa kai parlorn ta kalli nabeel da nabeela na wasa da mamaki take kallonsu su kuwa da gudu suka rungume Amrah suna gaisheta ko kula khairin ma basuyi ba suka ja little suka fara wasa, d'akin da yake a matsayin nata ta shiga da baki bud'e take kallon d'akin wani babban 6/7 tagani me shegen kyau dukda ba Italian bane na Nigeria ne amma ya had'u se wardrobe dinshi me murfi hud'u daga gefe brown color ne set d'in bed d'in, haka labulayen d'akin ma an sauya zuwa brown, an shimfid'a rug carpet a tsakiyan d'akin shima brown, se wani black mini bed da karamin wardrobe a  gefenshi shima black me murfi d'aya, d'akin se kamshin sabbin furnitures da turaren wuta yakeyi..................

Dada ta hango zaune a bakin gadon rike da sandarta da sauri khairi ta karasa kusa da ita tana kama hannunta tace "Dada yaushe kuka zo? Yaushe kuma aka chanza d'akin nan haka? Na su waye?" Murmushi dada tayi tace "khaih ummulkhairi duk wannan tambayoyi haka wanne zan amsa miki?" Khairi tace "duka" dada tace "kiyi ma surkuwarki godiya khairi, kinga d'akin nan duk da ba gani nakeyi ba amma na san ko yayi kyau, zaki ga wani karamin gado shine na nabeel, nabeela kuma a d'akin zarah zata zauna, sannan wai ya cire su a makarantan gomnati a inda zaki rubuta papper anan zasu ci gaba, ummulkhairi bamu da bakin godiya ga bayin Allahn nan se adu'a  kawai zamu cigaba da binsu dashi Allah ya biyamusu bukatunsu na alkhairi" ................

Kuka kawai khairi ta saka tare da rungume dada tana cewa "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ina d'an uwa? Ina Abba, ku zo kuga burinku, Abba burinka na ganin munyi karatu ko da sau d'aya ne a private school ya cika Abba, burinka na ganin mun zauna a muhalli me kyau ya cika amma baka duniyar, d'an uwa kana Ina da kake tunanin rayuwarmu baza ta sake yin kyau ba sema yafi baya ta'bar'barewa ga haske na shigowa cikinta amma kayi nisa ya Allah in yana raye ya Allah ka bayyana mana shi, In ko ya mutu Allah kaji kanshi ka gafarta mish, ya Allah..........." kuka ne ya sarke ta, haka dada ma sossai sukayi kuka har muryan khairi na dishewa kanta kuma ya fara matsanancin ciwo, fuskanta yayi jajazir abinka da farin mutum.......................

Dada ne ta fara share hawayenta tace "kukan ya isa haka khairi, Allah kuma ya amsa mana adu'arki don darajar Annabin rahama sallalahu alaihi wassalam" karasawa khairi tayi tana me share fuskanta wanka taje tayi tazo ta shirya cikin doguwar rigan atampha simple tasa hijabinta tare da cewa dada "bari na d'aura abincin rana dada" dada tace "Toh khairi" fita khairi tayi a parlor taga little na zaune kasan kafan babanta ta zabga tagumi cike da damuwa...................

'Dago ido tayi se kuwa ya fad'a cikin sexy/oily eyes d'inshi dake lumshewa yake budewa kaman me jin bacci, kauda manyan idanunta da yayi ja sbd kukan da tayi tayi, Chan gefen parlorn ta hangi nabeel da nabeela suna wasa sake kallon little dake zaune shiru tayi, har zata wuce se kuma taga rashin dacewar hakan cikin dashewar murya tace "little pretty wa ya ta'bamin ke" Da sauri ta mike ta nufo ta hawaye na cika idonta tace "cutie ba ke bane na shiga kimin wanka naga kina ta kuka, wa ya ta'baki paapi ya rama miki?" Hawaye ne ya sake cika idon khairi d'ago kai tayi ta saci kallonshi bata hankara ba taji hawaye sun fara zuba kaman panpo da sauri ta wuce kitchen tana rufe fuskanta da hijabi..................

Runtse ido yayi yana jin zuciyarshi na motsawar da ya rasa dalilinshi, me ya sameta? Kukan me takeyi? Duk ya rasa dalili shafa goshinshi yayi tare da fesar da iskan bakinshi waje, tare da sauke idonshi kan little da hawaye ya cika idonta pim, suna had'a ido kuwa suka sauko mikewa yayi ya kama hannunta suka nufi kitchen d'in, a gaban kitchen island suka ganta ta dukar da kanta tana shesheka..................

Kaman daga sama taji ance "dukkan tsanani yana tare da sauki matukar bawa ya dogara da Allah, kin san de matsalarki In kanki ya fara ciwo, ga prettynki nan ki san yadda zakiyi da ita tunda kin san dole damuwar ki ya dameta" be kara ba be rage ba ya juya ya fice se be tafi ba ya jinginu da kofar kitchen d'in, ita kuwa da sauri ta share hawayenta tana dukawa gaban little tace "sorry pretty na sa ki damuwa ko? Na tuna paapi na ne nima" little tace "ya rasu ne koh kaman yadda mamana ta rasu?" Kai khairi ta gyad'a................

Little tace "momma tace in mutum ya rasu adu'a kawai zaka na mishi shi ze nuna kana sonshi ba kuka ba, ki dinga mishi adu'a kinji?" Kai khairi ta kuma gyad'awa cikin rawar tace "Toh pretty"  tafiya ya fara a hankali yana tuna duk wani labari nata da ta bayar yana had'ashi da nashi rayuwar tabbas itama taga jarabawar rayuwa, rayuwa ya bi dasu duk su biyun bisa wani IGIYA me wuyar tsallakewa for the very first time bayan kaddaran rayuwanshi ya fara tausayawa wata mace bayan mommanshi, a fili yace "Toh Ina d'an uwanta ya shige a garinnan?" Taune lips d'inshi yayi yana tuna first promise d'inshi da ta karya....................

A chan kuwa kitchen cikin lokaci kankani khairi ta sake sbd little se kuma tunanin maganganun da ya fad'a mata na dawo mata, ya damu ne da kukanta? me yasa ya za'bi ya mata magana bayan haushin auren chushen da ake shirin mata dashi? Don ta tabbatar baya so, da irin tunanukan ta gama girki, da kyar dada ta yadda ta fito suka had'u gabad'ayansu suka ci................

A washegari bayan sun dawo daga school suka wuce dukku inda gabad'aya family za'a had'u a chan, drivern musharraf ya ja Nuriyyah, dada, nabeel da nabeela a motar miemie, yayinda drivern momma yaja momma, Miemie da Amrah a motar nuriyyah, inda musharraf ya ja motan momma daga shi se khairi da little dake baya, duk wannan tsarin momma ne wadda be so ba amma ba yadda ya iya, zamansu kusa na mugun takura mishi wadda dauriya ce kawai irin nashi, shiru motar ya d'auka se wakan Lost In yhu na Praiz ft sammy ke tashi a hankali shima yana bi kasa kasa.........................






🤧🤧🤧🤒🤭🤐







#vote
#share
#comment







'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗








                 IGIYAR RAYUWA😭







                                               🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

*these page is dedicated to Amina Lawal shahud(Maman heedaya) bani da bakin gode miki sede inyi adu'a Allah ya bar zumunci. Thanks for your support and care Allah yaji kan hamdeeya yasa me ceto ce. Ameen*


Page➡️6️⃣7️⃣▶️6️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

"Nothing I wouldn't do you're me one for two....... it's lonely the bend or crack but it's a whole world with i with you.... yes you underneath the blue light.. silver memories on the skyline... stars will be there to guid us through.. my hands will be there to lead you through.... if they put a brick wall in between us i'am ah be with you down to the pillar....

God's love is real it will free us... got me winning meet me at the temple.. if they put a brick wall in between us i am ah be with you to the pillar God love it real it will free us got me winning meet me at the temple....... nothing can change the way that I feel I will die for yhu.... nothing can change the way that I feel I am lost in you...." abinda yake ta maimaitawa kenan Haka kawai yake tsintan kanshi da kallonta minti minti, tayi luf fuskanta fayau Ba komai d'aya daga cikin dogon rigan da hajiya ruqayya ta bata ta saka, purple me stones sossai white da gyalenshi fuskanta fes Ba komai tana jingine da jikin kujera fuskanta na facing d'inshi.

Sam ba bacci takeyi ba kaman yadda ya zata, sede gabad'aya jikinta a mace yake da farko tunanin yadda en uwanshi zasu kar'beta take sbd taga akwai masu sonshi dayawa a dangi be auresu ba se ya buge da auren 'yar aiki? Me ilimin secondary, ta tabbatar gabad'ayansu sun gama degree ko suna dab da gamawa, sannan kakkaninshi tana tsoron da wani fuska zasu iya ganinsu har su kar'bi aurenta ba tare da 'yan uwan mahaifinta ko guda ba, tunanuka ne fal ranta amma yana fara bin wakar nan da bakinshi se taji wani irin sanyi na shigarta, tunanukan na guduwa se wani

23 / 38