Advertisements
Chapter 13 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   13 / 38

36K to 39K   out of 113.1K words

tayi isha dama tayi magrib gidansu haidar kan suka kwanta sbd sanyin da gari ya d'auka, tsintar kanta tayi da tunanin wadda aka kira da musharraf ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido view din kyawawan lumsassun idanunshi da yake hararanta da shi ya dawo mata tsab kaman wadda ta d'au videon ta ajiye tana kallo a haka har bacci ya d'auke ta..................


*******

Da kyar musharraf ya kai kanshi gida jikinshi na tsananin rawa hakwaranshi na had'ewa duk da zafin da motan ke fitarwa hakan be hana shi jin sanyi ba, horn ya danna malam d'ahe ya zo da gudu ya bud'e mishi kan motan na galau galau haka ya shiga da ita be iya shiga parking lot ba ya Parker ta tsakiyar gida, zama yayi a motan yana kallon ruwan dake zuba har isowarshi gidan..............

Shahada kawai yayi ya bud'e motar ya fita sede ya kasa sauri hakan yasa ruwan ya ci gaba da dukanshi har ya isa d'akinshi zubewa yayi kan gado yana Jan bargo duk da jikinshi dake a jike................

Zaune suke a parlor suna jiran shigowarshi tunda ya danna horn zahra ke tsalle kwana biyu kennan bata sa mahaifinta a ido ba tayi ta kiran wayanshi yaki shiga, ita, momma, Amrah, nuri, miemie, salima se Maryam ne kawai zaune a parlorn yayi nasaran koran Afreen, da Zainab inji ta fad'ar momma...............

Ganin har mintuna 10 sun shige da shigowarshi ne yasa momma mikewa taje ta bud'e kofar parlorn tana duba waje, don In har Musharraf ya shigo gari be ta'ba biyawa wani waje be fara zuwa wajenta ba, sede In ba lafiya ba, yadda taga parking na motar kad'ai ya sanar da ita ba lafiya ba, da sauri ta fita tana kira nuri tare suka fita zuwa part dinshi ko wuta be kunna ba seda suka shiga ne suka kunna................

Suna shiga d'akin tun daga bakin kofa suke iya ganin yadda jikinshi ke rawan sanyi da kuma atishawar da yake ta jerawa da sauri momma ta karasa tana yaye blanket din jikinshi a d'an rud'e tace "Musharraf me ya shigar da kai ruwa bayan ka san yanayinka? Ina shi haidar d'in yake har ka shiga ruwa ba tare da saninshi ba? Musharraf ka fa san yadda ruwa ke wahal da kai?"..................

Shiru yayi nuri ce tace "momma ki sa shi ya cire jikakkun kayan nan sanyi na kara shiganshi da su bari inje In dubo me zan iya bashi da first aid" da yake nuri likita ce, da sauri ta fice momma ta taimaka mishi ya mike da kanta ta ciremai rigan taje drower dinshi ta d'auko mishi sweater riga me had'e da wando na cotton me taushi blue tazo ta mikamai tana cewa "lalla'ba ka tashi ka je ka watsa ruwan zafi zaka rage jin sanyin".............

Da kyar ya mike ya nufi toilet momma ta bishi da towel da kayan, ruwan zafi ta had'a mai tare da ajiye mai kayan da towel din kan mirror stand dake bayin ta fice a d'akinshi ta zauna zaman jiran shi be fito ba har nuri ta shigo hannunta d'auke da tire da d'an madaidaicin flask da cup a kai se wasu magunguna a gefe, ajiyewa tayi akan bedside tana cewa "momma ga wannan se ki bashi in ya fito, bari inje inji da namesyn kin nan kin san yanayinsu d'aya da babanta amma se rikici takeyi wai se ta zo ta ga paapinta"...................

Murmushi momma tayi tana cewa "'yar kwal uba da kin barta ta biyoki In yaso su had'u su kwanta tare" nuri na murmushi ta fice, fitan nuri ba da jimawa ba wayan momma ya d'auki kara haidar ne ke kiranta dama yanzu take tunanin kiranshi taji ya akayi musharraf ya shiga ruwa haka, d'auka tayi suka gaisa ta tambayeshi gajiyar hanya inda yace "gajiya yabi jiki momma, dama musharraf nayi ta kira inji ko ya isa gida lafiya amma baya d'agawa"..................

Momma tace "Ina ko ze d'aga bayan yana fama da ciwon shin nan de, me ya shigar dashi ruwa hk haidar?" Nan haidar ya bata labari ya kara da "gani nan zuwa In ya so se in kwana dashi" momma tace "Allah sarki Allah ya ci gaba da kare mna 'ya'yanmu mata da irin waenchan maza Allah kuma ya saka muku taimakon da kuka mata, sannan ba se ka zo ba kai da kayi tafiya ka dawo matarka na bukatar kulawarka kayi zamanka zan kula da shi"...................

Sallama sukayi bayan haidar ya mishi adu'ar samun lafiya, suna cikin waya da haidar ya fito sanye da kayan sanyin da suka mishi kyau sossai, gado ya hau ya zauna yana kame jikinshi atishawa kam yayi su ba adadi ga muryanshi ya dishe makokoronshi se zafi yake mishi yana jin kaman an shake shi, kaman ze yi kuka yake kallon momma yana jiran tayi mai fad'a se ji yayi tana cewa "sannu ga coffee nuri ta kawo maka ka samu ka sha se ka had'iyi magani"...................

Tsiyaya mishi tayi a cup ta mika mishi kar'ba yayi yana sipping a hankali jikin rau kaman wuta, a zuciyarshi kuwa ba masifan da be yi ba duk ya d'aura laifin kan khairi da ya lakabawa suna da 'kantin ball' 🤣 Wai idonta kaman kantin ball (inji musharraf fah ba ni ba tohm😅) so sunan da yake kiranta kenan a fili kuma yayi tsaki yafi dubu..............

Bayan ya gama shan coffee d'in ya sha maganin tare da sulalewa ya kwanta momma taje wardrobe dinshi ta samo socks ta zo ta saka mishi tare da ja mishi blanket ta rufe shi, kanshi ta dawo tana ta'ba temperature d'in jikinshi a hankali tace "sannu babana Allah ya biyaku taimakon da kukayi, Ina wayanka?" Yace cikin dashewar murya "yana mota" tace "bari inje In d'auko maka zuwa anjima In na tafi kaji jikin ya matsa maka se ka kirani koh?" Shiru yayi ita kuma ta juya ta fice...................

Washegari🌚🌚

Yadda khairi ta saba tashi a kwanakinnan haka ta tashi tayi komai yadda ta saba tayiwa su nabeel wanka suka shirya cikin uniform d'insu na islamiyya ta rakasu har islamiyyan tana dawowa ne ta tsaya gidan Maman hamdeeya suka gaisa tayi mata albishir samun aikinta ta tayata murna sossai............

Bayan khairi ta koma gida ta fara zaman jiran driver jefi jefi suna hira da Dada ta matsu sossai ta ganta gidan tana son zuwa wani government day secondary school da ta gani daga Chan farkon unguwan ta duba me da me zasu bukata na admission din su nabeel amma tana tsoron kar ta tafi driver ya zo...............

Se around 11 sukaji an kwad'a sallama khimar khairi ta d'auka ta sanya tana shewa dada "se na dawo" Dada tace "Allah ya tsare ya bada sa'a" fita khairi tayi ta shiga motar tana gaida drivern din cikin fara'a ya amsa ta kan ya tada motar suka bar unguwan...............

Masha Allah take ta furtawa ganin unguwan da suka shigo gidajen cikinshi masu tsananin kyau da d'auke hankali unguwan shiru sossai, a tsanake drivern ke tafiya har ya iso gidan ya danna horn malam d'ahe ya wangale gate d'in suka shige kan su shiga ma drivern ya tsaya suka gaisa yace mishi kar ya rufe ajiyeta kawai ze yi ya tafi...........

Ai ko yana ajiyeta ya juya d'ago kan da zatayi idonta ya fad'a cikin nashi a tare zuciyarsu ya buga da tsananin karfi da har seda ta hard'e da kayan jikinta ta kusa fad'uwa kan ta d'ago kuma bata ganshi ba, kofar da ta tabbatar shine na asalin cikin gidan ta nufa, a hankali ta fara knocking, ta kusa five minutes a tsaye tukun taji an bud'e.................










#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗







              IGIYAR RAYUWA😭






                                           🎗🎗🎗🎗🎗🎗


Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

            'Yar mutan Adamawa

*~~dedicated to MU KARU DA JUNA group, a gaskiya Ina jin daad'in comments d'inku, bani da abinda zan biyaku dashi tabbas ba don ku ba da na jima da dena rubutu, but yhu always support me kune karfin gwiwana thank yhu so very much for the care and support Allah ya bar kauna~~~*

Page➡️3️⃣8️⃣▶️3️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Wata kyakyawar yarinya da baza ta wuce sa'ansu nabeel bace ta gani tsaye cikin shigan kananan kaya Jeans da pink tshirt, kanta kitson kalba masu kyau an sa mata beats, murmushi ta sakarwa khairin hakan ya sa khairin ma sakar mata murmushi............

"Hey cutie I'm fatima Abubakar Mahmoud but yhu can call me zahra or little, yhu are beautiful" murmushi kawai khairi tayi mata kan tayi magana taji ance "little wanene a kofan?" Matsawa little tayi khairi ta shiga tana karewa parlorn kallo, a kan three seater idonta ya fara sauka, kwance yake rigingine yana kallon sama, fuskanshi ta kalla idonshi lumshe fuskanshi jajazur musamman kumatu da kan hanci, kuma se gyaran murya yakeyi kaman me tsananin mura, kau da kai tayi tana sauke idonta akan momma dake zaune kan one seater tray d'aure akan cinyanta Da wani roba me kyau da tsabta tana yanka fruits...................

Murmushi ta sakarwa khairi dukda bata sheda ta ba da fara'a tace "sannu da zuwa lale" khairi tace "yauwa" tare da sulalewa kasa ta zauna tana karawa da "Ina yini?" Momma tace "Lafiya klau ya gidan naku?" Khairi tace "lafiya" se kuma tayi shiru, atishawar musharraf yafi biyar kan su gama d'an maganan nan hakan yasa hankalinta komawa kanshi a ranta tace bade taimakona da sukayin nan bane ya ja mishi mura haka don taga irunsu basuyi kama da masu shiga ruwa ba.................

Maganan momma ne ya katse ta daga tunanin da ta fad'a inda tace "sede kuma ban sheda ki ba" khairi tace "sabuwar me aikin da Maami ta turo daga Chan gidan su Hamma haidar" don haka taji hafsa na cewa, momma tace "ohh Ohk na gane dama ke ce? But kinyi karama da aiyukan nan zaki iya kuwa?" Cikin ladabi khairi tace "zan iya In shaa Allah hajiya" little dake zaune kasa kusa da khairi ta zura mata ido tace "momma baki tambayi name d'inta ba tana da kyau"................

Momma tace "aiko little, ya sunanki?" Khairi tace "ummulkhairi" momma tace "masha Allah, toh kinji little sunanta Anty ummulkhairi" little ta turo baki gaba tana kad'a kai tace "uhm uhm ni de cutie zan dinga kiranta Anty ummulkhairi yayi yawa" dariya momma da khairi sukayi, kai a kasa khairi tace "yaushe zan fara aikin hajiya? Kuma Ina rokon alfarmar Ina zuwa da safe in koma da yamma"..................

Momma tace "ki dinga kirana momma ohk? Sannan zuwa da dawowan nan ze yiwu? Dukda tsohuwar me aikinmu ma haka takeyi amma abubuwa dayawa se ni ce me yi shiyasa nake son samun wacce zata zauna da mu anan" little tayi tsulum tace "Ayyah ki dinga kwana cutie plz plz plzzzzz" khairi na murmushi tace "kiyi hakuri hajiya hakan baze yiwu ba sbd mahaifiyata na da lalurar ido bata gani kannena kuma sa'annin little pretty ne"......................

Little ta daka tsalle "yeeeeeeeyyyyy cutie am I that pretty???" Kai khairi ta gyad'a mata tana murmushi little zatayi magana kenan suka ji muryanshi da ke shake sbd muran da yakeyi yace "zahra!!!" A tare suka juyo se idonta ya fad'a cikin nashi saurin kau da kai tayi tana lumshe ido ta rasa wani irin abu ne wannan da in suka had'a ido kad'ai se taji wani iri daga yatsan kafanta har kanta ga bugawar zuciya da take fama dashi In har suka kasance cikin inuwa d'aya................

Kallon da ta mishin nan kawai ta tabbatar da zarginta na ta sanadinta mura ya kamashi sossai haka idonshi ya sauya kala sossai haka lips d'inshi sun kara turwa daga light maroon zuwa dark maroon, sanye yake cikin sweater farare riga da wando masu taushi haskensu har d'auke ido yakeyi, ajiyar zuciya ta sauke jin maganan momma tana cewa "ba damuwa khairi zaki iya kina zuwa kina komawa d'in, se ki kiyaye latti sannan albashin dubu ashirin da biyar ne" godiya khairi tayi momma ta kara da...............

"Sannan zaki iya bari se jibi ki fara zuwa, ga wannan ki hau machine se jibin in Allah ya kaimu" godiya sossai khairi tayiwa momma tana kar'ban five hundred da ta bata don hawa abin hawa, mikewa tayi tana cewa "se anjima hajiya" murmushi kawai momma tayi mata tana me ci gaba da aikinta, har ta fita bata sake satan kallon inda yake ba....................

Tana fita suna cin karo da little murmushi ta sakar mata tana cewa "zan tafi little pretty se na zo jibi" little na murmushi tace "Ohk cutie see yhaa" tana d'aga mata hannu da son yarinyar ta wuce, gskiya yarinyar akwai shiga rai, a tsanake ta dinga tattaki har ta samu napep ta shige zuwa government day secondary school dake nan farkon unguwansu..................

A kofar makarantar ya sauketa ta biyashi kud'in shi ta shige, da tambaya  ta karasa office d'in principal bayani ta mishi akan kannenta da take so su fara zuwa karatu anan bayanin abinda zata biya ya mata ta kuwa biya a take don ta fito da gabad'aya kud'in Allah ya taimake ta ma four thousand ya kar'ba tunda primary one duk zasu shiga se kuma ya nemi su zo da tsintsiya, buta, se cup kowa d'ai d'ai godiya ta mishi ta fice..................

Wani napep din ta kara tara ta nufi kasuwa dukda yadda zuciyarta ke bugawa tuna abinda ya faru da ita achan amma haka ta karasa tunda ba wadda ze je musu In ba itan ba, sayayya ta musu da d'an yawa na kayan abinci yadda zasu kwnaa biyu basu nema ba, se en chanji da ta rage na napep din zuwa wajen aiki har yadin uniform da littatafai ta sayawa su nabeel da pencil................

Ta dawo gida around three duk a gajiye da kaya niki niki, da murna su nabeel suka tare ta su suka ringa tayata har ta shigar da komai da ta saya ta sallami me napep din, bayan ta shiga gida ta kimtsa duk abinda ta saya suna hira da Dada tana bata labarin karamcin matar da zatayi aiki da ita....................

Bayan ta gama ta kama nabeela suka shiga gidan Maman hamdeeya "oyoyo Adda khairi, nayi missing dinki d'azun na shiga wurin Dada ai ta cemin kin tafi gidan aiki" khairi na murmushi tace "kede bari gari yayi zafi, amma Alhamdulillah duk Adu'ana Allah ya amsa min nayima su nabeel registration yanzu ma uniform d'insu na kawo dinki inji kud'in kuma"................

Hararanta Maman hamdeeya tayi tana cewa "ko ba kud'in dinki ba, khaih Alhamdulillah na taya murna Allah ya ci gaba da rufa asiri a yau kuwa zan d'inka musu don gobe su fara zuwa"...................

Cikin jin daadi khairi tayi mata godiya, kan ta mike tana cewa "bari inje In d'aura mana abincin dare, kar magrib ya min a kitchen" Maman hamdeeya tace "toh tafi min da hamdeeyan nan plz in tayi kuka se ki dawo da ita samun In yanka abun nan sharp sharp in na gama girkin dare se in zauna In had'a ko ban gama yau bama da asuba zan karasa kan de suyi wanka su shirya.."................

Sa'ban hamdeeya da dama take kan kafanta tayi tana cewa "toh mun gode, se anjima" suka fice suna dariyar Maman hamdeeya dake cewa "kin manta godo ne ba gode ba"...................

************

Bayan tafiyan khairi momma tace tana duban musharraf "babana kaga Allah ya bamu me aiki me hankali da natsuwa ga duk kan alamu yarinyar ta samu tarbiya me kyau", a hankali musharraf ya bud'e lumsassun idanunshi a zuciyarshi yace Lallai momma me kantin ball d'ince me hankali shi kam be gani ba a ganinshi ma she's the craziest person he ever met in his life don wallahi ganin marar hankali yake mata had'uwansu na farko tana aikin gudu a cikin estate da tsakar rana bata kunyan idon jama'a................

Had'uwa na biyu wasu gardawa na shirin keta mata haddi cikin ruwa da kuma magriba In me hankali da tarbiyace wasu iyayen ne zasu bar ersu fita zuwa irin low cost da magriba ko don hadarin da suka gani be isa su ce ta zauna a gida ba..............

Had'uwa na uku daga suka had'a ido mahaukaciyar ta nemi hantsilawa tsabar shirme da shiririta na cinta, sannan the most annoying part shine aikatau da tazo yi shi yana ganin iyaye masu son abin duniya ne ke tura yaransu zuwa aikin bauta a gidan wasu ko lokacin da suke shan wahalan rayuwa be ta'ba yadda momma tayi aikatau ba duk da kuwa ta so yin, Ina babanta In ubanta useless ne irin nashi Ina yayanta In bata da yaya ina en uwanta ko da shike shima nashi en uwan watsar da su sukayi a lokacin da basu da komai...................

Despite the fact that su suka ja musu ko ma menene tunda auren dole sukayiwa mamanshi da babanshi, but duk da haka he see no reason da ze fito da katuwar buduruwa aikatau me yasa baza tayi Sana'a ba and aikataun nan fa gani yake kaman tauye hakki ne tunda ba ta yadda mutum ze had'a karatu da shi.....................

"Musharraf magana nake" boyyayiyar ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "ni de ban gani ba momma, yarinyarn nan bata da hankali, ni de I don't like her" hararanshi momma tayi tace "sannu a Ina ka Santa da ka san bata da hankali? Kuma daga ganin mutum sau d'aya se kace baka sonta ba kyau fa musharraf wai ni me matsalanka da mata ne"..................

'Bata fuska yayi yana pouting mouth yace "toh momma ni me nayi" "laaaaaa paapi kaima kanawa granny shagwa'ba but ni kana hana In maka" little da gangarowanta Kenan ta fad'a on top of her voice, had'e rai musharraf yayi yace "zo" zaro ido tayi tana kallon momma dukda tana jinsu amma shiru tayi tana me ci gaba da aikinta.................

A sanyaye ta karaso don ganin ba dariya a face dinshi seda ta iso gabanshi tukun ya sa hannu ya kama kunneta ya murde, ihu ta tsala tana rike hannunshi cikin dashewar murya yace "Ina wasa dake? Am I your mate?" Da sauri ta girgiza kai hawaye na cika idonta kau da kai yayi yace "and last Friday kinki zuwa school sbd zanzo again yau wednesday amma kinki zuwa school wai don bani da lafiya, zaki sake missing school with no reason?".................

"A'a bazan sake ba I'm sorry paapi" hararanta yayi

13 / 38