Advertisements
Chapter 33 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 38

96K to 99K   out of 113.1K words

samu little kwance tana bacci d'agata yayi zuwa toilet yayi mata wanka nan ta ware ta fara mishi surutu yana amsata har suka gama shiryawa dayake yau yana cikin farin ciki fuskanshi a washe cike da fara'a da annuri, har kan dining ya kaita ya ajiye mata plate d'in Kwai da bread se tea d'inta, se lokacin tace "Ina mommy paapi?" Yace "mommy bata da lafiya tana bacci a room d'ina" fuska ta kwa'be zatayi kuka da sauri yace "karkiyi kuka little taji sauki bacci kawai takeyi" Kai ta gyad'a nan ya dinga mata wasa har ta sake bayan ta gama ya raka ta har mota ya ba driver empty lunch box d'inta da kud'i akan su biya restaurant ya sayata abinda take so na break d'inta.












#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗





               IGIYAR RAYUWA😭






                                               🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

                  'Yar mutan Adamawa

Page➡️9️⃣0️⃣▶️9️⃣1️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Hasken rana da ya fito ne ya fara reflecting idonta hakan yasa ta dole bud'e idon a hankali ya sauka kan agogo dake jikin bangon d'akin da sauri ta mike zaune tana furta "ya subhanallah banyi sallah ba how comes yau na makara haka" nufan sauka daga gadon tayi se taga tray da warmer da flask akan stool dake ajiye inda zata sa kafa ta sauka, murmushi ta sake tuna abinda ya faru da irin soyayyar da musharraf ya nuna mata a daren jiya hannu ta saka ta zare papern da aka d'aura akan trayn rubutunshi dake kwance zarzar kaman computer ne yayi rubutun ta zubawa ido tana karantawa and she can't stop her self from blushing.

Ga abinda yace a paper din "Hey my darling wife
On this super awesome day
Just want to wish you good morning
With lots of kisses for the day
Good morning to you! Tauraruwar zuciyata" Ajiyewa tayi tana jin sonshi na kara samun mazauni a zuciyarta dira tayi a hankali take tafiya zuwa bayi alwala tayi ta fito, hijabin sallahnta da ta shigo dashi jiya ta d'auka ta zura tayi sallahnta ta d'an jima zaune tana istigfari kan ta mike ta cire khimar d'in.

Toilet ta koma ta d'auki sabon brush ta 'bare tare da sa macline tayi ta kuma wanke fuskanta kan ta fito zuwa kan gadon gyara zama tayi, tayi breakfast d'inta cikin kwanciyar hankali tana tunanin ashe musharraf ya iya shiga kitchen ita a ganinta ko kunna gas baze iya ba gashi har unique egg yayi mata fraying ga tea da ya had'a mata, bayan ta gama ta gyara d'akin tare da d'aukan tray d'in ta nufi kasa ba tare da ta sa hijab d'inta ba.

Tun daga saman steps ta hangoshi rike da mop yana moping fari kal d'in tiles dake shimfid'e a parlorn nasu na kasa, waro ido tayi tana saukowa da d'an sauri tace "hamma me kakeyin nan" d'ago ido yayi ya kalleta tare da sakin wani heart melting smile yace "qalbee am moping the floor bcs yhu can't do it today" kitchen ta nufa ta ajiye tray din kan ta dawo ta sa hannu ta kar'be tace "who said that?" Kashe mata ido d'aya yayi tare da d'age gira yace "really, so lafiyanki kalau?" Baki ta tura tana tsoma mop din a ruwan omo tace "good morning" yana kokarin kar'ba yace "morning sunshine, ya jikinki baya miki wani ciwo ko?".

A dabarance tana kokarin kuma kwace mop d'in tace "yes baby" bata hankara ba taji ya d'agata chak zuwa kan kujera ita da mop d'in kan ya zare daga hannunta yace "just chill baby, will do all the house chores" remote ya d'auka ya kunna Tv ya kama mata zee world yace "oya yi kallonki I love yhu" murmushi kawai tayi tana maida kanta tvn da gaske baze barta tayi ba kenan.

Ganin ya shiga kitchen yasa ta guduwa d'akinta ta fad'a wanka tana cikin wanka taji yana kiran sunanta "qalbee, qalbee" watsa ruwa tayi don yaji tana bayi, yajin kuwa memakon ya tafi se ya bud'e bayin ya shige waro ido tayi tana neman d'aukan towel se tsantsi ya d'ibeta tayi baya zata fad'i saurin tareta yayi yana dafe gini don gujewa fad'uwar shima ruwan showern da ta kunna ya ci gaba da zuba a kansu gabad'aya.

Runtse ido tayi shi kuma ya saki murmushi cikin kasa da murya yace "dama me zaki gudu ki boye min? Kin manta ke mallakinace baki da abinda zaki boye min nima haka, mun riga da mun zama d'aya yanzu In har Ina cikin gidan nan duk abinda zakiyi tare zamuyishi, am I clear" murmushi tayi a kunyace tace "yes sir" dariya ya saki jin wai wani sir haka de suka ci gaba da hira kad'an kad'an suna wanka shi yayi mata inda ya nace se tayi mai a dai kunyace ta yi mishi bata karasa bama ta janye towel ta kwasa da gudu tana mishi gwalo, shima dariya ya saki yana cewa "zan kama ki ne qalbee ni zakiyiwa wayo" yana ta sake murmushi har yayi wankanshi ya fito d'aure da babban towel d'inta.

Gaban mirror ya sameta tana shafa mai bayan tayi drying kanta da hand drayer, wardrobe d'inta ya nufa kanshi tsaye ya ciro na biyo da babban akwatinta ya d'ibi kayanta ya cika tap dashi har sleeping wears, kananan kaya, atampha, jallabiyoyi, khimars da veils, tana mai ci gaba da shafa manta tace "Ina zaka kai kayan baby?" Yace "to my room don gaskiya ban son zirga zirgan nan kuma bani da ra'ayin raba room da mata ta shiyasa zan kai miki kayanki chan" Tace "ohk miko min medium size din trolleyn bari In zuba cosmetics" mika mata yayi ta zuba duk cosmetics d'inta Bayan sun gama ya bata wani d'an pingilin riga wai shi zata saka suje room dinsu na sama ta shirya shi bata da wani option se na sakawa iyakarshi cinyarta maroon ne rigan hannunshi na vest gashinta da ta kama a tsakiyar kan se lilo yakeyi fashion ear rings ta saka a kunnenta ta shafa powder da lips stick se kwalli a idonta ba karamin kyau tayi ba.

Se santin kyaunta yakeyi da kanshi ya ajiye mata flat shoe maroon me gashi a ciki sakawa tayi ya janyo babban akwatin ita kuma ta d'auko karamin suka nufi sama ba tare da ya shirya ba suka fara shirya kayan a cikin wardrobe dinshi sawunsu biyu daga sama zuwa kasa kan suka gama tattaro kayanta kab na little kad'ai suka rage.

Sunayi suna hiransu na masoya har suka gangaro kan sharrin da aka mata tana shafa mishi mai ya dube ta yace "kina tunanin waye ya aikata haka? Anty Rabi'ah" Kai tsaye khairi tace "I don't think so baby nafi zargin sufyan dukda ance zato zunubi" Shiru yayi na mintuna kan yace "tabbas shine kad'ai ze iya aikata hakan sbd d'aukar fansar abinda na mishi akanki amma yayi babban kuskure don me raba ni dashi se Allah" marairaicewa tayi tana rike hannunshi tace "baby I have a request plz" Kai tsaye yace "go on qalbee fad'i ko ma menene In be fi karfina bazan ki miki ba" Tace "bana so kayi mishi komai ko ka tabbatar shine, ka kyale shi da halinshi ze girbi abinda ya shuka".

Wani kallo ya mata kan yace "this is impossible, ba ta yadda za'ayi In kyale sufyan wallahi, don ya cutar dani sossai ba kad'an ba ni kad'ai na san halin da na shiga you have no idea also" Shiru tayi ta ci gaba da shafa mishi man har ta gama bata kuma cewa komai ba fuskanta kuwa ba'a sake ba ba'a had'e ba, haka ta nufi wardrobe ta fiddo mishi army green three quarter da sky blue nylon armless shirt seda ta taimaka mishi ya saka ta juya ta nufi ficewa daga d'akin da sauri ya sa hannu ya janyota ta fad'o jikinshi cikin whisper yace "fushi kikayi?".

Tace "nop sbd me zanyi fushi, ni banyi fushi ba" yace "Toh Ina zaki?" Tace "I'm very sure bakayi breakfast ba kalli time gashi na tabbatar little ta kusa dawowa" mikewa yayi tare da ita a jikinshi yace "Ohk muje In tayaki, and kuma tunda bakya so in ma sufyan komai bazan yi ba In shaa Allahu" pecking kumatunshi tayi tace "thanks dear, yanzu muje mu d'aura abincin" kitchen suka shige a tare sukayi girkin rana inda suka girka Tuwo don ta lura yafi so hakan yasa tayi mishi Tuwon alabo(rogo) da miyan d'anyen kifi a dining suka jere suka kuma dawowa kitchen din suka tattare tare, tare da wanke abunda suka 'bata tanayi yana d'aurayewa yana kifawa har suka gama sukayi moping kitchen din duk sunayi suna shan love minti minti zeyi kissing lips d'inta yace "Ina sonki sossai" ko "I love yhu qalbee" a haka suka gama a daidai lokacin little ta shigo da gudu tayi musu oyoyo suka rungumeta a tare, bayan sunyi breaking hug din khairi tace "wanka ko cin abinci pretty?" Little tace "wanka mommy" nan fah musharraf yace shi be yadda ba yunwa yake ji ba yadda suka iya haka suka nufi dinning tayi serving d'insu sukayi bismillah suka fara ci se santi suke zuba mata inda little ta makalawa tuwon suna da tuwon chewing gum shi kuma musharraf yace sede a kira shi manne manne tsabar dankonshi se dariya khairi keyi musu.

TWO MONTHS LATER

Wani irin tsaftatacciyar soyayya wannan familyn suke shimfid'awa a tsakanin junansu kowa na so yaga ya burge d'an uwanshi dukkansu suna gudun 'bacin ran junansu yayinda komai na gidan In har yana nan to ya sabar musu yi a tare ko yaushe tana jikinshi don in yana nan be yadda da zama separate ba tun khairi na damuwa akan tarbiyar little kar ya ta'bo ya nuna mata Ba komai In shaa Allahu, result d'insu na waec da neco duk ya fito khairi ta basu kala don ta samu credits sossai bata da fail ko d'aya hakan yasa yana nema mata University of Abuja dake gwagwalada suka bata bayan tayi jamb ta cinye.

Haka a Gombe ma ya sa an samawa Amrah gombe state university don itama results d'inta sunyi kyau inda take karantan Geology (study of earth shape) yayinda khairi take Anatomy ( study of the structure of human body) don course din na burgeta, sun fara karatu last week inda suka zauna suka tsara time table na yadda zasu ci gaba da rayuwa cikin farin ciki despite ko wannensu na fita kuma yawanci yini sukeyi.

A tsare suka fidda komai nasu dama ya koya mata mota tun wata d'aya da ya wuce kuma ta iya sossai don har tana hawa kan hanya da nashi, a randa zata fara zuwa school a ranar ya bata kyautan mota sabuwa dal Accord maroon color sossai tayi farin ciki ta dinga zuba mishi godiya inda yace be yarda ba In tana so ya amshi godiyarta ta nuna mishi a gado, Ai ko a ranar ta bashi mamaki yayinda sonta da kaunarta suka ninku a zuciyarshi sbd seda ya zauna da ita ya san wacece ita.

Macece me yawan kulawa akan abinda take so da tarairayarshi bata da ganda ko ko na miskala zarratin ga ta da tsananin tsabta da son kamshi ga iya girki Allah ya bata, babban abinda yasa yake kara sonta kuwa yadda take son little ya yi imani ko ita ta tsuguna ta haifeta soyayyar da zata nuna mata kenan, yawancin Friday's zasu kashe awowi suna waya da su momma da kuma su dada inda suke kiranta a wayan inna suyi ta mata tsiya suna shan dariya kan ta mikawa dada tana musu wankin babban bargo, kuma baze hana In an kira next Friday ta fara d'agawa ba.

Sossai momma ke jin daad'in kwanciyar hankalinsu don ko bata gansu ba daga muryoyinsu ta san irin so da kauna da suke wa junansu bare yawanci khairi na turawa Amrah hotunansu a tare In ta matsa mata sede ta gansu a IG lokuta da dama kuma mutane suyi ta santin couples din har hakan ya karawa Amrah yawan followers.

In takaice muku readers a wata biyun nan ko ku aka ce muku ga khairi baza ku ganeta ba hutu ya nuna sossai a jikinta farinta ya kara haskawa tayi kumatu yayinda natsuwa da kwanciyar hankali tsantsa ya nuna a yanayinta ta zama kaman wata matar shugaban kasa komai cikin class take yinshi Haka musharraf ma ya d'an kara kiba yana girma ne amma kyaunshi kaman kara mishi akeyi, in kaji musharraf da khairi sunyi fad'a to akan 'yan matan dake rububinshi ne don ta bashi haushi wani lokacin In ya amsa call dinsu se ta koma gefe ta zauna ta fara mitar.

'Matsalan auren kyakyawa kenan da ma kauye na shiga na samu mummuna daidai ni na aura da ba'a nemi sawa mutum hawan jini ba' nan fah ta tsokono shi haka zasu yini suna fad'a a wasa wasa da tsokanan juna, saura wata uku buki a gidansu bukin marwa da haneefa wadda suka gama shirya abubuwan da zasuyi a group dinsu na WhatsApp sossai suka shaku da 'yan uwanta anan.

Yau da misalin karfe hud'u ta fito daga  lectures kenan ta ji wayanta na kara tana fiddowa taga 'Zauj🔐💝' ne ke yawo a saman iphoneX d'inta da ya chanza mata d'agawa tayi tace "baby" daga 'bangarenshi yace "yes qalbee ya lectures?" Tace "Alhamdulillah ya office ko ka dawo gida?" Yace "nop motana ya samu matsala wallahi yaki tashi, ki biyo ki d'aukeni" murmushi tayi kan tace "ohkey on my way" kashewa yayi a daidai lokacin ta isa mota tayi mata key ta d'auki hanyar office d'insu.

Bayan ta d'aukoshi suka nufo hanyar gida suna d'an hiransu na masoya, da wani irin karfi ta taka Burki a tsakiyar titin inda wani mota yazo ya bugi nata dama gudu takeyi, a tsorace musharraf ya kalleta yace "are yhu alright khairi?" Inaaa bata ji shi hankalinta gabad'aya ya tafi wani 'bangare guda da ta kurawa ido.







Toh readers me kuke gani ya firgita khairi haka?????








#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗





                IGIYAR RAYUWA😭





                                            🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

               'Yar mutan Adamawa

Page➡️9️⃣2️⃣▶️9️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

'Balle murfin motar tayi da sauri tayi d'ayan 'bangaren titin wani matashin saurayi dake tsaye a gaban wani mota dayake traffic ya tsaidasu, be ankara ba kawai se ji yayi an rungumeshi ta baya ko daga Ina, ko ya take, ko a wani hali take In har taga d'an uwanta ba ta gaba ba zata ganeshi.

Tana rungumeshi ta saki kuka da sauri musharraf ya dawo driver sit ya ja motan zuwa gefen hanya kan ya samu ya tsallaka zuwa bangaren da suke yana bawa mutanen da ta tara hakuri, har a lokacin taki sakeshi balle yaga waye se kiciniyar kwacewa yakeyi amma ta rike shi gam, seda musharraf yazo ya janye ta dukda haka taki sakin hannun d'an uwanta, wani babban mutum ne ya bud'e motar da d'an uwa ke tsaye a jiki ya fito dama traffic ne ya tsaidasu a natse yace "lafiya kuwa bayin Allah?" Abulkhairi da ya sawa khairi ido yana ta kallo ne ya juyo yace "Abba nima ban sani ba Haka kawai wannan tazo ta kamani tana kuka" mutumin ze yi magana kenan khairi data ke rike da hannun abulkhairi da d'ayan hannunta, musharraf ya rike d'ayan tace "Dan uwa!!!! Ni ce baka sani ba?" Se ta rushe da kuka.

Mutumin ya kalli musharraf da yayi wani iri sbd ganin yadda matarshi ke kuka yace "bawan Allah mu tsallaka se muyi magana don naga an kusa sake mu" tana rike da Abulkhairi dake ta mata wani irin kallo suka tsallaka mutumin yace "suna na Alhj Abdulrashid hameed ni babban d'an siyasa ne kuma d'an kasuwa, wannan d'ana ne sunanshi "Abdallah" dan Allah ko zaku iya min bayani yadda zan gane ku?".

Khairi tace "wallahi wannan sunanshi ba Abdallah ba, sunanshi Abulkhairi d'an uwa na ne, my twin brother that was lost decades ago, baka ga kaman mu ba?" Ajiyar zuciya mutumin ya sauke kan yace "Toh Alhamdulillah ga kama kam, maganan nan ba na kan titi bane in ba matsala ku bini gidana se muyi maganan cikin natsuwa" har musharraf yace "Toh Alhaji" Khairi tace "a'a baze yiwu ba sede ka bamu address zamu zo da dare sbd yarinyarmu ta taso school tuntuni gashi ba kowa a gidan" cike da wani irin so musharraf ke kallonta duk yadda ta matsu, duk yadda take marmarin ganin d'an uwanta amma sbd baza ta iya barin 'yarshi ita kad'ai ba ta hakura zasu koma gida se daga baya taje wajen d'an uwanta.

Ajiyar zuciya ya sauke kamin ya kalli Abdallah tabbas ba abinda ya banbanta shi da khairi sede kawai don ita mace ta fishi kyau, amma Toh ya akayi be ganeta ba? Kallon khairi yayi kallon d'aya ya gane tashin hankalin da take ciki kawai bata son nunawa ne amma damuwa ya bayyana sossai a fuskanta, maida dubanshi yayi wurin Alhj Abdulrashid yace "ba komai Alhj ka bamu address din after isha prayer zamu zo In shaa Allah" Address din ya basu suka mishi sallama akan se ya gansu idon khairi na kan Abdallah suka wuce shima kur ya mata da ido yana kallo.

Musharraf ne yaja motan hannunshi na cikin nata ba wadda ya iya cewa kowa komai a cikinsu har suka isa gida suka samu little kuwa ta dawo har ta ci abinci ta chanza kaya tana baccinta, samansu suka haura sukayi wanka a tare suka chanza kaya duk ta kasa magana suka kuma gangarowa abincin da tayi tun kan ta fita lectures tuwon semo da miyan d'anyen ku'bewa ta saka musu da zafinshi jau kaman yanzu aka sauke sbd yanayin warmern da ta saka.

Sbd yana bata yana ci hakan yasa ta ci sossai amma ba wai don tana da apatite ba, suna gamawa ana kiran magrib ya mike yayi

33 / 38