Advertisements
Chapter 12 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 38

33K to 36K   out of 113.1K words

zuwa da safe ma ko ran makaranta ne kan su shiga bokon dayake yara ne masu shiga rai har sun saba da islamiyyar kamar sun shekara cikinta, hannun nabeela ya sabe sossai sede be warke ba, daga randa nabeela ta kone kullum kan ta fita se tayi musu abincin rana take fita, tana kuma iyakar kokarinta don ganin batayi magrib a waje ba....................

Yau ma kaman kullum bayan ta gama shiri tayiwa dada sallama suka fito hannunta rike da su nabeel se da suka shiga gidan Maman hamdeeya fishaa kan suka fito suka wuce kasancewar kwana d'aya kenan basu had'u ba, bayan ta ajiye su nabeel ta tari napep ta shige kud'in hannunta saura 300 duk ranta a jagule tana tunanin In bata samu aiki yau ba bata san da wani kud'in zata fita gobe ba, amma bata cire rai ba Allah na nan...............

Cikin mintuna kad'an suka isa low cost cikin d'ari d'ari ta sauka sbd duk cikin unguwannin da take zuwa ba wadda gidajen suka tsoratata kaman waennan ga ko wanni gida da securities, wani gate ta fara knocking gateman din ya fito sanye da uniform yake tambayarta lafiya? Tace "don Allah matar gidan nake son gani" ta san in tace zata dinga fad'awa gate-mans abinda yake tafe da ita zasu dinga mata bukulu ne..................

Kallon sama da kasa ya mata kan ya bata hanya ta shige duk da ya san madam dinshi bata harka da talaka aiko khairi na shiga tana fad'an abinda ya kawo ta matar ta mata korar kare ta had'a harda gateman d'in ta zage tas, a tsorace khairi ta shiga gida na biyu nan ma wulakanci aka mata haka ta dinga yawo duk gidan da ta shiga koranta ake, wasu kam ma har cewa suke ko an aiko ta spying ne, wasu harda barazanar rufe ta a police station sukeyi.......................

A haka har akayi azahar ta samu panpom gefen wani gida tayi alwala tare da komawa gefe ta shimfid'a d'ankwalinta dukda bata san gabas anan ba amma haka tayi sallanta, bayan ta idar ta jima sossai zaune a wurin duk damuwanta na kan rashin samun aikin nan ga kud'in hannunta sun kare ga kayan abincinsu na hanyan karewa, babban damuwanta school tana mugun son su koma makaranta ko shedan gama secondary d'inta ta samu...............

Bayan ta gama sake sakenta ta mike ta ci gaba da tafiya a sad'ad'e har ta samu wani shop sadakarwa tayi ta karasa ta sayi pure bliss da pure water d'aya ta samu wuri ta zauna taci ta sha ruwan kan ta ci gaba da roaming har gab magriba la'asar ma a wani gindin bishiya tayi, ganin magrib ya gabato yasa ta fara neman napep don komawa gida amma ko d'aya bata gani ba ga hadari da ya had'u lokaci d'aya...................

A mugun tsorace take kalle kalle ko gilmawan mutum d'aya babu securities da suke kofan gidaje dayawa ma babu duk sun koma daga ciki tafiya ta fara sauri sauri tana aduar Allah ya sa ta samu ko machine ne, duk hankalinta ya tashi akwai wani gidan da ta wuce d'azu da ko marmarin shiganshi batayi ba sbd yawan securities din da ta gani kofan gidan akwai kaman rumfah haka wurin taje ta tsaya amma ko minti biyu batayi da tsayuwa ba wani katon security ya fito ya koreta..............

Hawaye ta fara ganin iskan ruwa ya taso gadan gadan kana ji ma ruwan na zuwa, ci gaba da sauri tayi batayi aune ba taji an 'barke da ruwa kam kaman da bakin kwarya ci gaba da tafiya a haka tayi ruwan na dukanta, daga nesa Chan ta hangi wasu matasa su kusan biyar suna zuwa zuban ruwan be damesu ba sam se ma wani irin tafiya da sukeyi na kasaita da ji da kud'i dukda In ka zuba musu ido ka lura sossai zaka san a buge suke................

Ci gaba da tafiya khairi tayi kanta a kasa har ta iso kusa da su batayi aune ba taji an chabke hannunta a razane take kallon wadda ya riketan zagayeta sukayi suna sheka dariya d'ayan yace "are yhu seeing this chick komai yaji yau akwai morewa" kokarin fisge hannunta takeyi amma ba rikon wasa ya mata ba a take suka cire mata khimar suka yasar kokuwa suka fara da su amma Ina sun mata yawa kuma aka ce sarkin yawa sun fi sarkin karfi......................

********

"Ni wallahi sam ban so zuwa dukkun nan ba, duk momma ta bi ta matsamin da en uwan mutumin nan" inji fad'ar musharraf kenan yayinda yake driving da motar momma kwanansu biyu dukku wadda momma ce ta sashi dole zuwa duk rabin en uwanta a achan suke kuma en uwantan de sune en uwan mahaifinshi don cousins suke, harara haidar ya sake mishi inda yace.................

"Ko min lalacewan masa de tafi kashin shanu" "mtseww could yhu imagine ni da bana karya ba na son me yinta amma ni ne da karya a office yau Tuesday amma ban koma ba, na fake da wani wai banda lafiya" shiru haidar yayi yana kallon hanya kallonshi musharraf yayi na seconds tukun ya juya kan tukinshi a fili yayi kwafa yana cewa "In miskilanci ne kaima ka san na dame ka na shanye don ma kaine yasa nake maganan".................

Cikin dariya haidar yace "toh musharraf me kake so in ce maka? Na riga da na saba jin wannan mitan a duk sadda na raka ka dukku har muje mu dawo kana mita abinda ban sanka da shi ba" Shiru musharraf ya mishi nan haidar ya dinga magana amma ko ci kanka musharraf ya ki cewa, ganin musharraf d'in ya d'auki hanyar GRA yasa haidar cewa "Kai gidanmu fah zaka kaini In d'auki matata don nayi kewarta".................

Harara musharraf ya sake mishi inda ya juya ya nufi Low cost ba tare da ya ce komai ba, a hankali yake tafiya kaman bayaso sabida karfin ruwan saman dake zuba yana covering view d'inshi hakan ya sa ya kure hasken lights d'in motar yana shawo kwanan street d'in su haidar hasken motarshi ya sauka akan shape d'in jikinta doguwar rigan material dake jikinta fitted one ne hakan ya sa da suka yaga saman rigan be zame ba, runtse idonshi yayi a lokaci d'aya ya bud'e akan black bra d'in dake jikinta ya kamata har tudun breast dinta ana iya gani daga nesa.................

Kallon haidar yayi yaga hankalinshi na kan waya be ma san me ke faruwa ba, takaicin matasan ne ya kamashi me yasa ga mata karuwai dayawa a gari se wacce bata sayar da kanta ba? Rage hasken motan yayi kan yayi kansu da mugun speed da yasa haidar d'agowa hakan yasa ya gane me akeyi, su kuma ganin motar tayo kansu yasa suka arci ta kare ita kuma ta du'ka a wurin tana boye fuskanta a tsakankanin cinyoyinta..................

Wani wawan birki musharraf ya ja a gabanta tare da juya kan motan cikin hanzari shi da haidar suka sauka sukayi kan yaran wani irin duka suka fara musu da ya bani tsoro don daga ganin yaran ba su da wani karfi ajeboters ne, duka sossai suka musu kan suka samu suka tsere, musharraf ya koma mota da sauri yana rawar d'ari don baya shiga ruwa sbd In ya shiga se yayi zazza'bi me zafi da mura kaman baze yi rai ba............

Heater din motar ya kunna yana kau da kai daga kan yarinyar, haidar ne ya karasa kusa da ita ya janyo hijab d'inta dake gefe cikin tausayinta yace "baiwar Allah" kuka takeyi sossai inda jikinta kuma ke tsananin rawa a hankali ta d'ago don ganin waenda suka taimake ta duk da ruwa ake hakan be hana haske tarwal a unguwan ba kasancewar ko wanni gida sun kunna kwayayen fitillunsu, had'a ido sukayi da haidar hannunshi rike da hijab d'inta yana mika mata...................

Kar'ba tayi har yanzu jikinta be bar rawa ba a kuma rud'e take, sa khimar din tayi dukda wuyanshi ya yage sossai haka ta sa tana chukuikuye shi a kirjinta hannunta ya kama shi ko damuwa da ruwan be yi ba shi da yake watanni cikinshi ta Ina ze damu, a hankali ta mike ta bishi don haka kawai taji a jikinta she's safe with them ba abinda ze same ta................

Bayan motar ya bud'e mata ta shiga, ta zauna wani kamshi da dumi da ya buge ta ya sata sauke ajiyar zuciya motar ya d'auki dumi sossai ita bata ta'ba shiga mota me fidda sanyi bama balle zafi, d'aga ido tayi don kallon d'ayan se suka had'a ido ta mirror wani d'an banzan hararan da ya buga mata yasa tayi saurin kau da kanta zuciyarta na bugawa................

Tabbas shine toh me ya kawoshi nan bayan a chan estate ta kalleshi, kau da zancen tayi ta koma tunanin wani hali dada zata shiga In taga har yanzu bata dawo ba ga ruwa anayi tunaninta da kukanta ya yanke ne sadda taji me murmushin iskanci da ta sawa suna da haka wato musharraf na cewa "what are yhu doing? Where are yhu taking her to after the help"................

Haidar yace "haba musharraf are we leaving her at this rain and that street after all that happened to her? I'm taking her to Maami she will know what to do with her" su duk a zatonsu batayi makaranta ba ganin shigan jikinta suna ganin ko tayi ma to irin government dinnan da basa aikata aikin Chas a boko..............


A zuciyarta take magana "Lallai wato sunanshi musharraf kuma be da kirki be da tausayi, tsurewa tayi ganin sun nufi gida me rumfa da aka koreta a cikinshi duk da taji yace ze kaita wurin Maami amma seda taji cikinta ya d'uri ruwa, horn ya buga ba 'bata lokaci wani ya fito ganin motar yasa ya koma da sauri aka wangale gate din suka kutsa kai har gaban entrance na parlorn gidan musharraf ya Parker haidar ya juya ya kalli khairi yace "muje ko" fita tayi shima ya fita da sauri suka haura steps na kofan parlorn shi haidar ya d'auka musharraf dinma ze shigo se gani yayi ya ja motar a guje ya fice daga gidan...................

Girgiza kai kawai yayi yana shiga parlorn da sallama khairi na biye dashi har yanzu kuma tana share hawaye, hajjiya rukayyah ce zaune kan kujerun parlorn a had'e take cikin leshi me tsada da ya amsa sunanshi dukda mijinta baya gari kwalliyan nan de baya barin jikinta murmushi ta sakarwa haidar da ke tsaye.................

Tana nuna mishi set din kujerun ledan dake gefenta ganin jikinshi a jike baza ta yadda ya zauna mata a royal cushion ba, murmushi shima yayi yana zama dama ya sani, a kasan tiles khairi ta zauna tana takure jikinta idon Maami a kanta har tayi sallama da mijinta tukun ta kalli haidar ta kuma kalli khairi ya gane me take nufi hakan ya sa ya bata labarin abinda ya faru................

Ta tausayawa khairi sossai dayake Allah yayi ta mai tausayi da jin kan talakawa tace "en mata ya sunanki?" A hankali khairi tace "ummulkhairi" jijjiga kai Maami tayi ta kuma cewa "ummulkhairi me ya fito dake da dare kuma cikin ruwan nan har mummunan abu ya so samunki ba don Allah ya turo su haidar ba" a natse ta fad'a mata abinda ya fiddo ta.................

Cikin tausayawa Maami ke kallon khairi kan tace "kar ki damu bari In had'a ki da autata kiyi wanka ki chanza kaya ki ci abinci gobe se akai ki gida" tun kan Maami ta karasa khairi ke girgixa kai tace "mahaifiyata makauniyace kannena kuma basu wuce shekara biyar ba na san suna chan hankali tashe bazan iya kwana ba kiyi hakuri hajiya".................

Cikin tausayawa Maami tace "toh za'a maida ki gida amma se kinyi wanka, zaki kuma tafi muku da abinci gobe In shaa Allahu zan tura drivern da ze kaiki yau ya d'aukeki zuwa gidan wata aminiyata dake neman er aiki" cikin tsantsan farin ciki da ya gaza 'boyuwa khairi tayi ta godiya, Hafsat maami ta kira ta had'ata da khairi, hafsa ma tana da kirki kaman en gidansu Cewar khairi dake wanka kenan bayan hafsa ta nuna mata yadda zata yi anfani da duk toiletries d'in....................

Tana fitowa hafsa ta bata doguwar riga da gyalenshi ta saka tayi kyau sossai kuwa komawa parlorn sukayi ta samu Maami ta sa an shirya mata abinci cikin basket bata ga haidar ba don ya jima da shigewa part dinshi dake gidan duk da yana da gidanshi amma zamansu gidan iyayenshi yafi yawa sbd yanayin aikinshi kuma be son dinga barin matarshi gida ita kad'ai da yara...................

Driver Maami ta kira lokacin karfe tara na dare kuma ruwan ya tsaya, ya d'auki basket din khairi ta bi bayanshi kan ta fita Maami ta kirata ta dawo kud'i ta d'auko da d'an yawa ta bata Tace "inji haidar, ga wannan" ta bata wani leda da bata san me a ciki ba godiya sossai tayi kan ta fice ranta kal................











#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa

πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—








IGIYAR RAYUWA😭







πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad: Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

Page➑️3️⃣6️⃣▢️3️⃣7️⃣
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Har kofan gida drivern ya kaita tayi mishi godiya sossai kan ta fice, da sallama ta shiga gidan hakan yasa Dada da ta zuba tagumi sauke nannauyar ajiyar zuciya tana zaune ne kan turmi dukda sanyin da garin ya d'auka ta tabbatar damuwar da mahaifiyarta ta shiga baze fad'u ba a hankali ta kira sunanta "ummulkhairi".......................

A raunane ta amsa sbd tuno abinda ya so faruwa da ita awanni kad'an da suka wuce tabbas da ya farun da bata san wani hali zasu shiga ba ita da waennan en uwa nata, hawayen fuskanta ta share tare da gyaran murya jin dadan ta fara magana cikin sanyi "khairi me ya ajiyeki a waje haka kin san ba magriba kukeyi a waje ba yanzu fah goma saura".................

Bata jira Cewar khairin ba ta kara da "lafiyanki ko? Ba wani abinda ya sameki? Wallahi tun fitanki gabana ke ta aikin fad'uwa" murmushi khairi tayi hawaye na kuma zuba mata ta karasa gaban dadan tana Jan er kujerar tsugunonsu ta zauna kan tace "lafiyata kalau dada kin ga ma albishirinki?" Dada tace "goro" khairi tace "Dada na samu aiki, matar ce ma ta riqeni ganin hadari se da ruwa ya tsaya tukun ta had'ani da drivern ta ya dawo dani gobe ma in shaa Allahu shi ze zo ya d'auke ni"...............

Ta karasa with so much excitement in her voice, ta boyewa mahaifiyarta ibtila'in da yaso afka mata, farin ciki sossai ya bayyana a fuskan dada a fili tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah ya Allah ka ci gaba da rufamana asiri duniya da lahira ba don halinmu ba" cikin murmushi khairi tace "Ameen mamanmu, Ina su nabeel ne ban ji su ba" Dada tace "suna ciki sallah sukeyi tun d'azu suke jiran dawowarki da kyar na sasu yin magrib kin sansu da kafiya Toh isha dinma se yanzu suke mika ta".......................

Khairi ta gyd'a Kai ta kuma cewa "Allah ya sa ba abinda kuka ci don hajiya ta had'oni da abinci don naki ci a chan gidantan harda abu a leda ta ban kinga ko bud'ewa banyi ba" cikin jin daadi ba wai don abincin ba se don jin daadin khairi ta samu uwar d'aki me mutunci don a wannan zamani me mutuncin ne kawai ze iya maka haka, dada tace "aaa harda d'awainiya Toh Allah ya saka, ai ko an gode dama ba wani abinda muka d'aura".............

Khairi tana cikin bud'e coolers din su nabeel suka fito da gudu suna cewa "oyoyo Adda" fasa bud'e flask din khairi tayi tare da taran kannenta cikin murmushi tace "oyoyo chutu'ben dada" (chutu'be means en biyu da fulatanci) rungumesu tayi tana jin kewar kannenta bayan ta sakesu tace "Dada ya kamata mu koma ciki wajen nan akwai sauro ga sanyi".............

Komawa ciki sukayi Allah ya sa akwai wutan nepa tarwal a gidan bayan d'auke ruwa suka dawo dashi, plates khairi ta d'auko musu da serving spoon ta zo ta bud'e coolern fried rice ne had'add'e da pepper chicken se cowslow a gefe da yaji kwai, a lokacin In kaga fuskan waennan familyn zaka tabbatar suna cikin farin ciki saka musu tayi yadda ze ishe su sukayi bismillah suka fara ci a natse.................

Har suka gama ci ba wadda yayi magana a cikinsu daad'in abincin kam ya wuce misali, bayan sun koshi suka ajiye saura a kitchen kan nabeela ta dawo ma khairi ta bud'e ledan aiko designers abaya ne masu kyau guda biyu se turaruka arabian perfumes guda biyu, se kud'in da haidar ya basu 10 thousand...................

cikin jin dad'in karamcin maami da haidar khairin ta d'aurawa Dada kayan akan kafa tatta'bawa dada tayi tana sharara musu adu'a kan ta mayarwa khairi kayan khairi tace "Dada baza ki dau d'aya ba?" Dada tace "a'a ernan rabani ni kam Ina ni Ina kayanku na zamani balle ni da ya kamata in d'au nauyinku bayan kushewar mahaifinku se kece ke d'awainiya dani ni Ina nan bani da anfanin komai"..................

Ta karasa da sanyin murya da alamun abun na damunta, da sauri khairi tace "haba dada me yasa zaki ce haka ke kika fi komai anfani a garemu a yanzu haka dan Allah ki daina daurawa kanki damuwa dama tun asali d'a ne ya kamata ya ji kan iyayenshi bayan ya mallaki hankalin kanshi bare ke da lafiya bata isheki ba" murmushi kawai dada tayi tace "hmmm khairi kenan d'awainiyar ya mace bai barin kan iyayenta har se sun damka ta a hannun mijinta, don ba yadda zanyi ne kawai, ki d'au rigunanki turaren ma ki d'au d'aya kya bar mana d'ayan mu dinga fesawa da kannenki...................

Sannan kud'in ki cire mana na kayan abinci se ki duba makaranta anan kusa na gomnati ki sa kannenki, daga baya ke kuma maga yadda Allah ze yi" khairi tace "Hakan yayi Allah ya shige mana gaba" ta mike ta cire na jikinta wadda hafsat ta bata ta had'a da sauran ta adana kan ta fita tayo alwala tazo

12 / 38