Advertisements
Chapter 34 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   34 / 38

99K to 102K   out of 113.1K words

mata pec tare da cewa "se na dawo" Kai kawai ta gyad'a mishi ya fice ita kuma ta tada little dake kwance kan kujera tace "tashi pretty magrib yayi" tashi tayi tana kaikaya ido tace "yaushe kuka dawo mommy?" Murmushi khairi tayi tace "kina shan baccinki muka dawo, oya an shiga sallah a masallaci tashi kiyi sallah In kin idar ki tabbatar kinyi bitar karatunki Ohk?" Tace "Ohk mommy" ta mike ta shige d'akinta inda khairi ta haura sama.

Se bayan sallahn isha tukuna ya shigo gidan a parlor ya samu little na kallo da gudu taje ta mishi oyoyo don tun safe rabon da su had'u d'aga ta yayi sama ya sauke yace "Ina mommynki?" Tace "mommy na sama tunda ta shiga sallahn magrib bata fito ba" dayake ba kasafai take hawa musu saman ba ko irin baki haka khairi tayi iyakarsu kasa sam bata bari wani ko wata ya haura mata saman miji wadda hakan yasa little ma bata cika hawa ba don In har musharraf baya nan to suna kasa tare har se ya dawo take haurawa.

Sake hannun little yayi kan yace "Ohk yi kallonki bari In dubota" cikin parlorn ta koma shi kuma ya haura d'akinsu ya fara shiga be ganta ba ya tura toilet bata nan, study room/library dinshi ya duba nan ma bata nan, d'akin gym dinshi ya tura nan dinma bata nan kwankwaso ya kama yace "ikon Allah to Ina tayi? Qalbee! Qalbee!! Qalbee!!!" Shiru, kasa ya kara sauka ya tambayi little tace bata ga fitowarta ba kwata kwata.

Saman ya kara komawa ya sake duddubawa a tsakiyar d'akin gym dinshi ya tsaya yana tunanin Ina ta shiga, se ya ji sheshekan kuka kasa kunne yayi tabbas kuka ne kalle kalle ya fara se ya hangi hijab d'inta daga bayan wani gym machine da sauri ya nufi wurin ya duka a gabanta a sanyaye yace "qalbee" fad'awa tayi jikinshi ta kuma sa kuka a d'an rikice yace "menene? Me ya faru kike kuka haka?" Kukanta ta ci gaba da yi Ai ko se ya karasa rud'ewa ya dinga lallashinta da kyar ya samu tayi shiru inda ya tambayi me yasa take kuka haka.

A hankali tace "ban san me ya faru da d'an uwana ba, ban san me ya sameshi ba amma ko me ya sameshi ya kamata ya manta ni? His blood, I really can't believe wai d'an uwa ne ze ce be sanni ba" ta karasa a karye, girgiza kai musharraf yayi kan yace "haba baby yanzu dama don wannan kike kuka? Ai munyi me wuyar tunda mun sameshi kika san ko wani abu ne ya faru dashi da yasa shi manta kowa nashi? Yanzu kinyi sallahn magrib?" Ta gyad'a kai ya kuma cewa "isha fah?" Ta girgiza kai yace "ji idonki fah bana son haka dan Allah, plz karki kara yin irin wannan kukan, se ya zama dole in ya zama dolen ma ki bari se na zo yadda bazan bar tsad'addun hawayenki su zubo a kasa ba, tashi muje kiyi sallah ki shirya mu wuce gidan Alhj Abdulrashid d'in" mikewa tayi yana rike da hannunta har d'aki a gabanshi tayi sallah kan ta d'auko wani Arabian gown ta saka ta yafa gyalen shi kuma ya saka bakin jallabiya suka fito In ka gansu kaman ka sace tsabar kyaun da sukayi.

Har d'akin little tare suka shiga ta saka mata doguwar riga itama suka rike hannunta zuwa mota, da kanshi yayi driving har zuwa wuse zone 3 inda anan ne gidan Alhajin yake, daidai number din house da ya basu a cikin card d'inshi suka tsaya tare da yin horn, me gadin ne ya taso da gudu zuwa inda suke sanye da uniform d'inshi na masu gadi se wasu police dake zaune kofan gidan da alama securities ne, "sannu yalla'bai Kaine wadda kukayi zaku gana da Alhaji bayan isha?" Kai musharraf ya gyad'a mishi ba tare da yayi magana ba, mutumin yace "yace in kazo ka sameshi a annur hospital amenity room 20" nan ma kai musharraf ya gyad'a kan ya karkace ya zaro kud'i ya mikawa mai gadin se godiya yake zubawa har suka wuce.

Da sallama suka shiga room din wasu 'yan mata biyu da zasuyi sa'a da khairi suka fara karo da suna tsaye daga bakin gadon d'aya dake d'akin, d'ayan gadon kuma empty se Alhj Abdulrashid dake zaune akan wani plastic chair, kan gadon kuma Abulkhairi ne kwance yana kallon 'yan matan da alamu wani labari suke mishi don se murmushi yake zubawa, Alhj na ganinsu khairi ya mike har kasa gabad'ayansu suka duka suka gaisheshi ya amsa fuska a sake, 'yan matan da suka rud'e da ganin musharraf suma suka gaidasu suka amsa Kallon khairi d'ayan tayi tace.

"Laaa Abba kaga carbon copy na Abdallah" murmushi Abban yayi kan yace "Nasreen twin sister d'inshi ce" d'ayan tace "wow masha Allah ashe Abdallah ya samu 'yan uwanshi?" Nan Abban ya ba wacce ya kira Afreen labarin yadda suka had'u dasu khairi, khairi kam hankalinta na kan Abulkhairi da shima kallonta yakeyi, runtse ido yayi da karfi jin kanshi na Sara mishi a take rayuwanshi na baya ya fara dawo mishi daki daki har rana yi ta yau yadda ya rike kan yana jujjuyawa yasa khairi cewa "he need a doctor" a rud'e ai ko kaman doctorn na kusa se gashi ya shigo da wata nurse a bayanshi da sauri suka karasa bakin gadon suna cewa su khairi su basu wuri plz.

Fita sukayi suka tsatsaya daga bakin kofan kowa da abinda yake sakawa a ranshi, bayan kaman 30mins Doctor din ya fito ya mikawa Alhj hannu yana cewa "Alhamdulillah patient d'inka ya warke don gabad'aya memory d'inshi ya dawo congratulations" ihu 'yan matan suka sake cikin jin daad'i yayinda khairi ke Allah wadai da d'abi'ar su Alhaj ne kad'ai ke ta godiya  ga Allah.

Komawa d'akin sukayi khairice karshen shigowa aiko yana d'aga ido ya fad'a cikin nata hawaye ne ya fara gangara a idonshi cikin rawan murya yace "'yar uwa!!" Da gudu taje ta fad'a mishi ta fashe da kuka runtse ido musharraf yayi kukanta na yau ya ishe shi haka da ta san yadda yake ji da batayi ba kwata kwata, seda suka yi me isarsu kan suka saki juna little dake rike da hannun musharraf ta sake taje ta kama khairi tace "mom why are yhu crying? Akwai wadda ya dakeki ne?" Kai khairi ta girgiza tace "kukan murna ne pretty na samu d'an uwana see my twin brother" kallonshi tayi tana murmushi tace "hi mommy's twin brother" dariya su Afreen suka saka inda Abul yace "hello twin sister's pretty" dariya suka kuma sawa har khairi empty gado dake d'akin Alhj ya nunawa su khairi suka zauna yayinda Afreen da Nasreen suka zauna a gefen Abul kallonsu Alhj yayi yace.

"Na san kun matsu ku san yadda akayi Abdallah ko ince Abulkhairi sunan da naji kin kirashi dashi ya fad'o hannuna, akwai wani rana wattani dayawa da suka wuce na fito Adamawa zan tafi kano motarmu ta samu matsala kan mu iso gombe dayake mota na bi kuma daga ni se driver na hakan yasa ya nema mana mechanic inda muka jima sossai motar be gyaru ba, da kyar de motar ta tashi a lokacin Yamma likis.

Umarni na ba driver dina akan mu ci gaba da tafiya har muka shigo cikin gombe yayi insisting mu kwana gombe ni kuma naki nace sede mu ci gaba da tafiya, ba yadda ya iya sbd nine sama dashi ba shine sama dani ba a cikin Gombe mukayi magrib da isha kan muka ci gaba da tafiya mun bar gombe Abadan har mun fara nitsawa cikin kauyukan bauchi se muka ga mutum ya fad'o mana from nowhere hakan yasa driver yayi losing control har muka kadeshi inda ya fita hayyacinshi sossai, ba tare da wani tunani ba muka d'auke shi to nearest town inda aka bashi taimakon gaggawa bamu tsaya ba muka ci gaba da tafiya a daren a kano muka kwana inda na kaishi asibiti mu kuma muka kwana a wani hotel.

Kwananmu uku a kano kan ya farfad'o inda ya farfad'o da bacewar kwakwalwa sossai na shiga cikin tashin hankali and I blamed myself hakan yasa guiltiness ya kasa sakeni har se yau, d'aukanshi nayi muka dawo nan Abuja da zama na sa mishi suna Abdallah, kaman yadda kuka sani sunana Alhj Abdulrashid hameed bani da mata ta rasu a wurin haihuwan nasreen inda Afreen ce babba" cike da gamsuwa suka ta mishi godiya.

Inda khairi ta kalli Abul tace "d'an uwa ya akayi daga kaje kasuwa ka sayo mana abun anfani aka tsince ka a hanyar Bauchi?" Runtse ido yayi yana tuna abinda ya faru a hankali ya fara cewa "bayan na fito daga gida na fara takawa a hankali don neman abin hawa ban samu da wuri ba se da nayi nisa da gida se ga wani katuwar jeep baka ta tsaya a gabana ci gaba da tafiya nayi se wani ya fito daga cike ya tare ni inda yace "bawan Allah dan Allah tambaya nake" Kai tsaye nace mishi "Allah yasa na sani tambayana yayi a cikin unguwanmu ko na San wane kaza ni na manta sunan mutumin da ya kira nace ban sanshi ba sbd ni bako ne, ya kuma tambayar ina zanje nace kasuwa yace muje su rage min hanya fir na ki shi kuma ya kafe har yayi nasara ya sakani shiga motan ba don na so ba.

Muna shiga naga manyan maza akallah hud'u na gaban ne yace "aikinka yayi kyau weezy wannan ze yi" kan nayi wani yunkuri sun shafamin wani farin powder, ban tsinci kaina a ko Ina ba se wani katoton d'aki me cike da kayan alatu inda ina farkawa wani babban mutum Alhaji ya shigo ya fara min daad'in baki da nunamin ze bani duk abinda nake so a duniya In har zan amince mishi.

A take na gane manufarshi inda na kafe da yarda na kam baze samu hakan ba, har barazanar kisa da bindiga ya min naki amincewa se adu'a da nake tayi a zuciyana yana fita daga d'akin na bishi a baya inda na maqale Ina karewa babban parlorn kallo waya naga yanayi yana cewa matsalan Ai boka yace se da amincewar yaro za'ayi gashi wannan yaki amincewa.

Banji abinda aka ce mishi a d'ayan bangaren ba se naji yana cewa "Ai yaron na gayamaka kyakyawa ne na karshe ni raina ya biya ko ta karfi zanyi mishi In yaso In nemo na tsafi kuma" dariya ya dingayi bana de jin me ake fad'amishi ban bar adu'ar da nakeyi ba sam don kubuta daga hannunshi d'akin da nake naga ya nufo da sauri na 'buya a Bayan labule ya wuce ba tare da ya bud'e ba ya sa key ya murza yana dariya ya fice a sad'ad'e na dinga bin bayanshi har zuwa wajen katon gidan dake ciki daji, ban tsaya ba na dinga bin jikin gini zuwa bayan gidan na samu da kyar na haye ginin sbd tsawonshi Ina samun fitowa na ranci na kare ba ni na tsaya ba se akan titi gaban wani mota kan In ankara naji motar ta kad'e ni, Toh kunji abinda ya faru".

Kuka khairi ta dingayi yayinda musharraf ke jin zafin kukan nata har ranshi kaman wani punishment takeyi mishi hakan yasa ya had'e rai sossai kaman be ta'ba dariya ba, Abul ne ya kalleshi ya kuma kallon little tukuna ya kalli khairi yace "'yar uwa ya bayan rabuwa kuma? Ina Dada da twins? Ya kukayi rayuwa bayan 'bacewata?" Khairi tana share fuskanta tace "labari ne me tsawo" kallon musharraf tayi ta tabbatar ta 'bata mishi rai da kukan tan nan hakan yasa tace "yanzu dare yayi kuma naga nurse ta kawo takardar sallama kana bada labarin nan, kuje gida muma gida zamu tafi gobe in Allah ya kaimu zamuzo zakaji duk yadda akayi" kai Abul ya gyad'a sallama sukayi musu kan suka fice musharraf na sa'be da little da tayi bacci a kafad'a basu jima da fita ba su Abul dinma suka fito suka wuce gida.









#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗





                  IGIYAR RAYUWA😭





                                              🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

                  'Yar mutan Adamawa

Page➡️9️⃣4️⃣▶️9️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Har suka shigo gida uffan be ce mata ba kuma be sake fuska ba hakan yasa suna shiga d'aki tayi narai narai da fuska tare da kwanciya a gadon bayanshi ta zagaye cikinshi da hannunta duk biyu cikin taushin murya tace "am so sorry dear, plz Kayi hakuri bazan kara ba" lumshe ido yayi yana tunanin anya son yarinyar nan baze yi ajalinshi ba? Juyota yayi ya rike tafin hannunta yace "ni zan rokeki qalbee baki san yadda hawayenki suke da tsada da daraja ba? Zubar dasu kaman wani babban asara ne a gareni plz ki dauri ki dena irin wannan kukan it really hurt here wallahi" ya karasa yana nuna setin zuciyarshi.

Dukar da kai tayi tabbas maganganunshi sun shigeta kuma da yardar Allah bazata sake kuka a gabanshi ba tunda yana damunshi, tsintar muryarshi tayi yana cewa "baza kiyiwa assiddiq d'inki wannan alfarmar ba?" Dayake haka In ta bushi iska take kiranshi kuma sunan na mishi daad'i sossai kasancewar ba wadda ke kiranshi ko da Abubakar d'inshi ne bayan 'yan office d'insu.

Zagaye hannunta tayi ta wuyarshi ta kara tsai tayi brushing lips d'insu kan tace "In shaa Allahu bazan kara kuka haka ba baby" murmushi yayi yana cewa "Ohk baby amma fah kin tada wani fitinar" kashe mishi ido tayi tana jefanshi da wani irin murmushi da shi kad'ai ya san ma'anarshi bata hankara ba se ji kawai tayi ya rabata da kasa zuwa gado, a hankali na fita na ja musu kofa.

Washegari kuwa suka koma gidan Alhj Abdulrashid inda anan ya roki sanin su wanene su, ba tare da wani damuwa ba Abul ya zayyane mishi labarinsu wadda seda sukayi hawaye musamman Afreen da Nasreen da suka kasance masu raunin zuciya, irin kallon da musharraf ke wullo mata ne ya hanata kuka a wannan karon da ta tuna labarinta for the first time in history, bayan Abul ya gama ta basu labarin bayan barin Abul gidan har kawo yau, jinjina kai Abul yakeyi cike da farin ciki wai yau 'yar uwarshi ce tayi aure a garin Abuja tana jin daad'inta cike da soyayyar mijinta gashi tayi wani irin mugun kyau ta kara haske.

Nan musharraf ya roki alfarmar Abul yayi zamanshi dasu Abba In sun tashi komawa Gombe se su tafi gabad'aya suyiwa dada surprise, tambaya Abul yayi "yaushe ne tafiyankun hamma?" Musharraf yace "nan da three months" dukda Abul be so ba sbd kewan dadanshi da kannenshi da yakeji amma ba yadda ya iya musamman da yaji Abba na cewa "hakan shine daidai sbd ko ni zan samu nayi scheduling duk wani aiki nawa" haka suka tsayar kan kowannensu ya wuce abinda ze yi Afreen da Nasreen duk Nile university suke karatu amma different courses.

Bayan wata uku

Khairi ta samu nasarar kare exams d'in first semester cikin nasara don Allah yayita me kwakwalwa hakan yasa exams d'in be yi mata wahala ba, ta 'bangare d'aya kuma soyayyarsu da musharraf se kara gaba yake yi basu ta'ba ji sun gunduri juna ba, dukda zaman yau da kullum ana samun sa'bani amma daga d'aya ya hau d'aya ze sauka se wadda ya hau d'in ya sauko da kanshi tukun su fahimci juna, haka zumuncinsu da su Abba ya kara tsanani In ka gansu kaman wasu family yawanci 'yan matan suna gidan khairi hakan yasa Abul ma nan yake tarewa In Abba ya samu sarari da kanshi yake zuwa ya tattara su amma baze hana a washegari khairi ta gansu ba, little ma ta kare term d'inta itama ta saba sossai dasu Anty Nasreen d'inta, dukda khairi ta lura da take taken Afreen na son musharraf hakan be sa ta chanza mata ko a fuska ba don ta yarda da kanta ta tabbatar ita kad'ai ce a birnin zuciyar mijinta dukda shi musharraf d'in ba kowa ke ganin fuska a wurinshi ba halin shin nan na nan yadda yake treating su Amrah haka yake yiwa su Nasreen.

A washegari zasu bar Abuja to gombe Abba yayi musu komai na flight da zasu bi dukkansu har 'ya'yanshi don yana so da kanshi ya damka Abul a hannun mahaifiyarshi gashi kuma yana son yaron har ranshi, zaune suke akan gado shi yana daga bakin gadon kafafunshi na zube a kasa system ne akan desk dake gabanshi yana dannawa gefen system d'in hot coffee ne yana sipping daga shi se wani gutun three quarter milk in kuka ga yadda ya kara wani irin haske da murjewa se kunyi mamaki.

Khairi na kwance daga bayanshi daga ita se a wani 'bingilelen riga nylon pink me hannun vest gashinta a sake bata saka mishi ribbon ba ko de tace ta saka musharraf ya cire fuskanta d'auke da kwalliya sossai wadda har seda nayi mamaki (a su khairi an waye😜) kunnenta sanye da fashion pink video call takeyi da Amrah da miemie se surutu suke zubawa ba ma su san musharraf na gefenta ba se tsokananta suke.

Amrah tace "irin wannan kyaun haka khairi ko hammanmu ya miki ajiya ne" hararar ta tayi tace "wallahi ki kiyayi bakinki na gaya miki ba wani ajiya" suka saka dariya Miemie tace "seriously Khairi kinga wani irin fresh da kikayi sa'banin Adda nuri da ciki ke wahalar da ita ba kaman farkon aurenta ba itama baki ga yadda ta zama ba amma yanzu se kashi bata iya cin komai" Khairi ta waro ido tare da yin fuskan tausayi tace.

"Dama haka cikin yake? Da gaske mutum baya iya cin komai?" Amrah na dariya tace "matsoraciya khairi ke damuwanki kar babynmu ya hanaki d'urin da kika saba ko" harara ta wurga mata "ban son tsiya dama chan ci ne dani?" Miemie tayi saurin cewa "a'a kede yanzu me albishir d'in?" Ta san karamin aikin khairin ne ta kashe wayanta kan ta fad'a musu albishir

34 / 38