Advertisements
Chapter 10 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 38

27K to 30K   out of 113.1K words

fari kal din vest dinta na bayyana, se straight skirt brown me tsagu har cinya se turban brown, seda ya kare mata kallo daga sama har kasa kan yaja tsiririn tsaki ya bud'e gaba ya shige ko sannu da zuwanta be amsa ba...................

A ranshi yake tunanin yanzu wannan ce ze aura? Gsky ya cire ta lissafi Allah yayishi me tsananin kishi shi kallon tsirara ma yake mata don ba maraba a fili ya saki tsaki, tunda suka gaisa da drivern momma be kara magana ba har suka isa gida ko gaisuwan Afreen d'in be amsa ba haka duk surutun da zahra keyi be tanka ta ba dama ta saba....................

Ana parking be jira komai ba ya sauka ya nufi main parlor yana ganin yadda Afreen ta bishi da ido kaman zata cinye shi, da gudu zahra ta zo ta rike hannunshi suka karasa tare, tare da barin Afreen da dakon akwati. "Salamu alaikum my momma I miss y............" maganan ne ya makale ganin Maryam, salima da Zainab baje a parlorn ko wacce taci ado kaman masu zuwa gasan kyau...............

Ba laifi dukkansu kuma kyawawa ne farare sossai irin farin gomben nan, amma duk cikinsu ba wacce ke da ki'ba ko dirin kirki, Zainab sanye da riga me had'e da wando na atampha ta cakara d'auri a gaban goshi tana zaune kan two seater hannunta rike da waya kirar iPhone X, se salima dake kwance kan doguwar kujera sanye da wando jeans pink da pink shirt d'an karami ba d'ankwali kanta se gashinta da ta raba gida biyu ta kamasu da manyan ribbons................

Se Maryam da yayiwa lakabi da er rawan kai ko ya ce mata kaza kanki da motsi tsaye gaban tv hannunta rike da remote tana chanza channel sanye take da straight gown da yabi jikinta ya fidda karamin shape dinta black hannunshi na vest, fuskanta kam mad'au yaji makeup kaman ba gobe se gashinta da tayi parking tsakiyar ka yana lilo....................

Ganinshi ya sasu tasowa da gudu kowacce na niyyar rungume shi, ganin da gaske fah suke yasa shi daka musu tsawa "what nonsense!!!!!" Birki ko wacce ta ja tana shagwa'be fuska, Zainab tace "sannu da zuwa sweet bro" a nyamutse yake kallonsu d'aya bayan d'aya akan salima ya tsaida idanunshi don a ganinshi ta fi su hankali yace "Ina momma?" A yangance cikin murmushi ganin duk cikinsu ita yayi wa magana tace "tana upstairs hamma" ba tare da ya tanka ba ya haura hannunshi rike da na zahra ya san ba me mishi wannan abu se momma yanzu ita momma cikin waennan taga matar aure?..................

******

"Dada Ina ganin zan nemi aikin aikatau sbd mu tsira da mutuncin mu" 'bata fuska dada tayi tare da cewa "inaaa khairi bazan yadda ba, ba abinda ya kai aikatau kaskanci ba wai don aikin ba a'a irin masu kud'inmu na yanzu rabi da kwatansu en wulakanci ne, ba zan juri kije inda za'a na wulakanta ki ba, ga kuma yanayin jikinki wani abin ya faru wadda ba shine ba bazan ta'ba jin daad'i ba".................

Ajiyar zuciya khairi ta sauke tare da yin shiru tana zurfafa tunaninta kan maganan Dada ta san da gaskiyanta amma zamansu hakan ba ze ta'ba yiwuwa ba, "Dada kiyi hkr bamu da wani option bayan wannan In d'an kayan abincinmu ya kare ina kike tunanin zamu samu kud'in wasu? Sannan Dada Ina da burin ci gaba da karatu na da na kanne na, kaman yadda mahaifinmu yaci buri kan rasuwarshi, Dada na yi miki alkawari zan kula ba zan ta'ba bari wani abu ya kai ga zuciyata bama balle ya 'batan rai har wani abu ya faru, ki ci gaba da min adu'a in had'u da mutanen kirki waenda bazan ta'ba kuka da su ba".....................

Dada tace "shikenan khairi Allah ya za'ba mana abinda ya fi alkhairi" karamin murmushi khairi tayi tare da sa'ba hamdeeya dake bacci kan cinyanta a kafad'a tace "Ameen dada bari In shiga wurin maman hamdeeya" kai kawai dada ta gyad'a, khairi ta fice, da sallama ta shiga gidan ganin maman hamdeeya tayi kan keke tana d'inkin uniform da yafi kama da na islamiyya gefenta kuma nabeel da nabeela ne zaune suna cin d'an wake..................

Da murmushi khairi ta karasa tana cewa "eyye autocin dada d'an wake ake ci?" Nabeel yace "eh Adda khairi ke ma ki zo ki ci baki ji daad'in da yayi ba Ammi ce ta mana" Ammi suke kiran maman hamdeeya jin haka hamdeeyan ke cewa kuma sossai take jin daad'in hakan, khairi tace "toh shine ko tayi babu" nabeela zatayi magana kenan maman hamdeeya tace "Ke ni kyale min yara su ci abinci kin wani zo kin fitine su"..................

Dariya Khairi ta kwashe dashi tare da Cewa "Lallai ma wato haka kikace? Kar ki yi wasa yanzu su jefa ki rana In de su nabeel ne" murmushi kawai maman hamdeeya tayi tana kallon hamdeeya dake hannunta tace "wai wani wankan kika kuma mata? Ai dole ta shantake tata bacci taji ruwan zafi, in kuwa ta hana mu bacci da dare ta katanga zan jefo miki ita"..............

Murmushi kawai khairi tayi tare da karasawa parlor ta kwantar da ita, ta kuma fitowa ta ja kujera zata zauna kenan maman hamdeeya tace "karki zauna karasa kitchen ki d'ibo d'an wake" nufar hanyar kitchen d'in tayi tana cewa "aiko ci zan yi ba wani fulaku dan yana cikin favorites d'ina" murmushi kawai maman hamdeeya tayi bayan ta d'ibo ta zo ta zauna inda tayi niyyan zama tun farko ta fara ci.....................

Bayan su nabeel sun gama sun wanke hannunsu ne maman hamdeeya tace "twins ku d'auki cooler d'in chan ku kaima dada d'an waken ta ne" d'auka nabeela tayi suka fice bayan fitansu khairi ta kalli uniform d'in da maman hamdeeya ke d'inkawa tare da cewa "wannan fah?" Maman hamdeeya tace "uniform d'in su twins ne na islamiyya" murmushi khairi tayi cikin jin Son matar tace "kin ko gama mana komai mun gode" hararanta maman hamdeeya tayi inda ita kuma ta saki murmushi...................

"Yauwa maman hamdeeya ya kike ganin aikatau a garin nan ana saurin samu?" Da mamaki maman hamdeeya ke kallon khairi tace "ba de aikatau zakiyi ba?" Cikin murmushi khairi tace "wallahi dariya kuke ban ke da dada wai nafi karfin aikatau ne? Ni wace? Ko kin manta rayuwan yau da gobe ga masu sana'a da aikin gomnatin ma ya bare mu? Ba bu ta yadda za'ayi mu zauna haka maman hamdeeya" ta kara da maganganun da tayiwa dada.................

Seda tayi shiru tukun maman hamdeeya tace "hkne khairi kinyi tunani me kyau wai nake gani da de irin sana'un hannun nan kuka rike amma se kuma na tuna ba ku da jaari tabbas da Ina da kud'in kirki da ba abinda ze hana In baki jari duk da ba ko yaushe ake samun ciniki a sana'an hannun ba" khairi ta kara da "kuma bukatun mu ya wuce nan maman hamdeeya ko mai lalla'bawan mu baze ishemu ba"..................

D'an shiru maman hamdeeya tayi na mintuna tukun tace "ga shi kuma ban san wata dake aikin d'iban masu aikatau a garin nan ba" murmushi khairi tayi tace "ai alkhairunki yawa gareshi wadda kikayi a baya ma Allah ya biyaki, abinda nake bukata kawai ki fad'a min unguwannin masu kud'i na garin nan ni kuma In shaa Allahu zan bi gida gida da izinin Allah kuma zan samu"....................

Ba tare da maman hamdeeya ta so ba tace "toh yaushe zaki fara?" Khairi tace "gobe in Allah ya kaimu" "Toh Allah ya kaimu" cewar maman handeeya, sun d'an ta'ba hira tukun khairi ta wuce da albishir wa dada akan gobe su Nabeel zasu fara zuwa islamiyya dake nan cikin unguwan sun daga kasa ba wani nisan kirki.................

*******

Da sallama ya kutsa kai cikin d'akin na mahaifiyarshi dake tashin kamshin turarukan wutan ta masu tsananin kamshi, amsa sallamanshi tayi fuskanta cike da murmushi a gaban gadonta ya karasa ya duka tare da cewa "Barka da gida momma mun same ku lafiya?" "Lafiya klau son ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" d'an shiru sukayi kan tace "tashi muje ka ci abinci" cikin 'bata fuska yace................

"Momma dan Allah me ya kawo waennan yaran?" Itama 'bata fuska tayi tace "Ina ruwanka? Wurinka aka gaya maka suka zo? Sannan ni da kaina na kira iyayensu suka turominsu ba zuwan banza sukayi ba, kuma maganan da mukayi da kai d'in nan kar ka zata wasa nake maka wannan karon Musharraf ka fita idona" runtse idanunshi yayi tare da bud'esu lokaci d'aya ya watsa mata su a take sun sauya kala kau da idonta tayi tana ta'be baki................

Tana jin tausayinshi har ranta sede ta tabbatar In ba nuna mishi 'bacin ranta take ba baze ta'ba d'aukan maganan serious ba, tana mugun son ganinshi cikin kwanciyan hankali irin na ko wanni na miji dake sa'anninshi, duk da be ji daad'in yadda momman tayi mishi ba amma ya ya iya? Basar da maganan yayi inda yace "Ina su Amrah?" Momma tace "suna school nuri na wurin aikinta" kallon zahra yayi se yanzu ya tuna yau Friday a kausashe yace................

"Me ya hana ki zuwa school?" Dukar da kai tayi cikin rashin gaskiya ta san yau da kyar In bata zanu wurin paapinta ba bata gama tunani ba taji ya daka mata tsawa "ba da ke nake ba?" Kame kame ta fara momma tace "ka ganta nan ba yadda banyi da ita ba ta tafi taki wai sbd zaka zo baza ta je makaranta ba" Da gudu zahra ta koma bayan momma ta san a nan ne kad'ai bazai bita ya buga ba, aiko be ce komai ba ya mike ya fice..........

Ko kallon su salima dake zazzaune be yi ba ya fice zuwa site d'inshi yana shiga ya fad'a gado tare da runtse ido hannunshi dafe da goshinshi, ya kusa shafe sa'a a haka kan ya karkata ya zaro wayanshi daga aljihu wani contact ya danna da na ga an rubuta haidar, cikin sa'a numbern ya shiga ba kaman yadda yayi ta gwadawa last two weeks a kai akai baya shiga ba............

A speaker ya sa hakan yasa ana d'agawa naji na d'ayan 'bangaren yace "Shege d'an iska se yau ka tuna dani?" Had'a girar sama da ta kasa musharraf yayi yace "zan ci ubanka haidar Ina wasa da kai? Ko ni sa'anka ne?" Dariya haidar din ya fashe dashi sossai seda ya tsagaita tukun yace "sannu gembo uwar son girma sati d'ayan da ka bani ne kake ganinshi da wani yawa ko?"................

"Mtseww ko minti d'aya ne girma de girma ne, in ba iskanci ba ba tun last two weeks ka ce min zaka hawo land ba?" Cewar Musharraf, cikin muryan zolaya haidar yace "hmm ka san abinka da me mata Ina dawowa ta kwace wayan ta kashe hutuna na one month ne so ta d'auka wa kanta ni na two weeks" tsaki me karfi musharraf ya ja hakan ya sa haidar kwashe Wa da dariya...............

Ze yi magana kenan yaji musharraf ya kashe wayan, se da yayi kira kusan uku kan musharraf ya d'aga haidar yace "daga magana......" kan ya karasa musharraf ya katse shi "ban son iskanci ka san ni fad'i." haidar yace "tukuna kana Ina ne?" Musharraf yace "gombe" haidar yace "Ohk gani nan zuwa amma se matata ta cika min....." Kit ya ji an kashe wayan hakan ya sa shi fashewa da dariya yana mamakin hali irin na musharraf duk da ba sanin yau ya mishi ba amma kullum da sabon halin da ze ganshi dashi, mikewa yayi yana d'aukar keyn motanshi a gurguje ya fice bayan yayi kissing chicks na matarshi, cikin farin ciki ta mishi Allah tsare...........








Afuwan🙏🙏




#share
#comment
#vote




'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗







                  IGIYAR RAYUWA😭






                                            🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

            'Yar mutan Adamawa

*An kar'bo daga baban musa Allah ya yarda dashi yace: manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace "mumini ga mumini kaman gini ne saashi yana karfafa saashi" Bukhari ya rawaito*

Page➡️3️⃣0️⃣▶️3️⃣1️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Kusan mintuna 20 da gama wayansu yaji an turo kofa an shigo ko be d'ago ba ya san haidar ne, yana nan yadda yake d'azu a kwance rigingine banbancin kawai yanzu akwai taba a hannunshi yana zuka, haidar Abokinshi tun na yaranta Haka iyayensu mata da mazan abokanaine sanadin mahaifinshi momma ta san mahaifiyar haidar sede zumuncin iyayensu maza ya gama ta'bar'barewa ne sadda mahaifinshi ya shayar da su ruwan mamaki da har abada baza su manta ba, sati guda musharraf ya ba haidar banbancinsu kuwa haidar su biyu kawai iyayensu suka haifa daga shi se kanwanrshi Hafsa sa'ar miemie ita ma de tana jerin masu son Musharraf amma har ita be bata fuska ba duk kuwa yadda suke da yayanta.............

Haidar na da mata d'aya Islam da 'ya'yansu biyu Abdallah da Abubakar wadda ya ci sunan musharraf suna kiranshi Mu'allim, haidar sojan ruwa ne in an turashi aiki se yayi 5months,6 ko ma shekara kan ya waiwayo gida.............

Yana karasowa ya sa hannu ya fisge taban yana hararan musharraf yace "har yaushe? Baka san ba kyau ga lafiyarka ba? Me ya sa baza ka maida qur'ani abokin debe kawarka ba se taba abinda da kafi tsana" harara musharraf ya banka mishi yana cewa............

"Kaga kar ka fara daga zuwa? Ai ba gidanka na je nake sha ba a cikin gidana nake, d'an iskan banza kawai" yana maganan ne yana kokarin fisge taban shi daga hannun haidar da gudu haidar yayi kofa ya tsaya tare da danne taban a jikin gini a take ya mutu..........

"Me yasa zaka kashe min kayana? Ai naga ba haramun bane daga kai har momma kun sani gaba da maganan taban nan don ma na dena shan sauran kayan maye!!!" Kallonshi haidar ke yi cike da tausayawa ya san adu'a da tsantsar tsayawa ta mahaifiyarshi ya sa ya dena shan kayan maye da har so yayi ya zama addicted to drug Allah ya takaita musu............

A hankali yace "toh Lafiyar jikinka fah?" Tsaki musharraf yaja yana zama a bakin gadon yace "Afuwan doctor Haidar bazan kara ba" dariya haidar yayi ganin yadda musharraf din yayi magana kaman da gaske shi din doctor ne, girgiza kai kawai yayi tare da karasawa ya zauna ganganshi yace "naga kaman kana cikin damuwa lafiya kuwa?"...........

Ajiyar zuciya musharraf ya sauke a sanyaye yace "ba lafiya ba haidar wai fah aure momma ke son nayi nan da wata biyar kuma tsakaninta da Allah wannan karon, wallahi Ina cikin damuwa bayan duk abinda surrayah tayi min na kuma yarda da wata mace?............

Har na bata amanar kaina, 'yata, dukiyata da family na? Never haidar an shaa ni sau d'aya na kuma warke" haidar ya dube shi da damuwa "Musharraf se aka ce ma duk mata halinsu d'aya? Ka gwada ka gani in shaa Allahu Allah baze kara had'aka da irin surayyah ba, kuma na tabbatar kaima kanka kana da bukata, a yadda na sanka musharraf baza ka ta'ba zama har karshen rayuwanka ba mace ba sede In harkar zina zaka fad'a wadda bama fata, sannan ka dubi little tana da bukatar uwa kusa da ita ka kara duba lamarin ni de Ina bin bayan momma ko dole ne se mun maka d'an iska In ka ga dama ka tasata a gaba ka ta kallo kaman hoto"...........

Murmushi ne ya kubcewa musharraf haidar d'an iska ne komai seriousness dinka se ya kawo maka barkwanci kaman ba soja ba, "ni de ban shirya wani aure yanzu ba in ba so kuke mu koma gidan jiya ba" girgiza kai kawai haidar yayi sanin halin abokin nashi In ya kafe twankarashi se Allah se kuma momma.............

Kallon time yayi a agogon dake d'aure tsintsiyar hannunshi kan ya d'ago ya dubi musharraf "tashi ka shirya time na juma'a ya karato" ba tare da ya tanka ba ya mike ya nufi toilet yana 'balle Buttons din rigarshi..........

Haidar ganin zaman da yayi ze sa shi fad'awa duniyar tunanin qaddara irin ta musharraf yasa shi jawo system din musharraf ya kunna ya san baze rasa American film din kallo ba don ya San musharraf mayen American films ne..........

Ilai kuwa ya samu the state union yayi playing tare da fara kallo, har musharraf yayi wanka ya fito ya fara shiri cikin dark green shadda da yaji guga se sheki yakeyi tare da kafa hula a kanshi me adon green takalmanshi sau ciki black ya fiddo tare da d'aura wristwatch d'inshi na gucci me tsada, collection na turarukanshi ya feshe jikinshi dashi............

Yana jin yunwa amma mayun nan yake tunani In har ya je parlorn Chan se sun mamayeshi sun sa ranshi 'baci ba gaira ba dalili, kiran numbern Amrah yayi ya san zuwa yanzu ta dawo ita ko nuri, ringing d'aya ta d'aga don ta sanshi sarai ta bari ya katse bata d'aga ba ta shiga uku............

"Salamu alaikum" cikin kasa da murya don shi ba ma'abocin d'aga murya bane mussaman in yana waya ko namiji haka yake waya da shi "wa'alaikissalam kin dawo?" Da sauri ta amsa "Eh hamma" "ohk kawo Min abinci" kit ya kashe wayanshi............

Kusan 15mins suna zaune yana danna waya haidar na kallo, sallama yaji daga parlor daga jin muryan ya san ba na Amrah bane wato don tsabar iskanci da reni ya sata aiki ita kuma ta aiko wata hmmm Allah had'a idonta da nashi, don tsabar rashin kunya zainab dinma bata jira amsa sallaman ba ta kusto kanta cikin d'akin da idonshi ta fara cin karo yana aiko mata da sakon harara...........

Ita har ga Allah tana son idanunshin nan mussaman In yana harara kyau idon keyi na fitar hankali, murmushi ta sakar mishi tare da nufar gefenshi ta ajiye tire din hannunta tare da d'aukan plate da niyyar serving d'inshi............

Cikin husky voice dinshi ya fara magana kaman ba da kowa yakeyi ba yace "mutum naci naci se kace talauci ban san ko ana so dole ba, ni kam ma Allah ya sawwaka In auri sa'ata" haidar dake kallo dariya ke cinshi be so yayi zainab ta kara kuluwa don ya san ta kulu, sa'arshi fa bayan ya san nuri ma ta girmeta da wattani dariyan da yake dannewa ne ta kwace lokcin da musharraf ya ce "baaa de ni

10 / 38