Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
sallamoni..............
Bayan mun dawo ne na samu ganinshi sossai na mishi fad'a da nasiha yace baze sake ba, a haka a haka na yi renon cikin nuriyyah har na haifeta tun daga sanda musharraf ya d'aga ma mahaifinshi hannun kaina be sake dukana a gabanshi ba sede yayi min hukunci a lokacin kwanciyar aure, abinda ya matukar bani mamaki kuwa shine ganin sa'banin yadda na gani a lokacin haihuwan musharraf.......................
Allah ya d'auramishi son nuriyyah tun daga randa ya d'aura ido a kanta hakan yasa ta samu gatan suna sossai daga wurinshi har su yaya nasir suka zata ya sauya haline amma hausawa suka ce hali zanen dutse yana nan da kayanshi, seda nuriyyah ta shekara biyu tukun muka koma Abuja inda ya ci gaba da shaye shayenshi wadda da bayayi a gombe, ko da yanayin kuwa be ta'ba shigowa gida a buge ba....................
Sam jituwa be ta'ba shiga tsakaninsu da musharraf ba nayi iya yina da kokarina don ganin musharraf be tsani mahaifinshi ba amma ban ci nasara ba ganin abun na shirin kwa'bewa yasa na yi enrolling musharraf a boarding school don tun kafin mu dawo mahaifinshi ya dena biya mishi kud'in makaranta wai ba yadda za'ayi yana wahala da yaro bayan ci da sha ya kuma biya mishi kud'in makaranta amma yazo yana mishi rashin kunya ba....................
Sam musharraf be so ba da kyar na samu na shawo kanshi ya yarda don shi gani yake In baya nan babanshi ze samu damar ci gaba da dukana yadda yake so, shekaran nuriyyah hud'u na haifi miemie wacce asalin sunanta Aslamiyya muke ce mata miemie, seda mukayi rikici sossai kan ya yarda da sunan don seda na had'a shi da yaya Ahmad abunda ya mugun bashi mamaki kenan don be zata zan iya ba, shekarar miemie be cika biyu ba na samu cikin Amrah..................
A lokacin musharraf ya gama secondary school yayi jamb ya kuwa ci, sossai aikina ya taimakeni don tun dawowarmu Abuja na koma, da kud'ad'ena da nake tarawa na samu yi mishi chukuchukun samun University of Abuja, yanzu muna cin albarkacin son da yake yiwa nuriyyah yana saya mana kayan abinci, ya saya a makaranta me tsadar gaske, duk da rayuwan aurenmu be koma kaman na mutane ba amma ya bar dukana sbd nuriyyah tace bata so..................
Shekarar musharraf 24 ya gama jami'a har service inda ya karanci accounting a lokacin na samu kawata hajjiya ruqayyah wacce tun zuwanmu Abuja muke mutunci sossai amma kawancen be yi karfi ba sbd ban bada fuska ba, sede 'ya'yanmu musharraf da haidar da suke abokai, itace ta kar'bi takardun musharraf ita da mijinta suka mishi hanyar samun aiki a CBN...................
Shekarar nuriyyah 15, yayinda miemie take 11 se Amrah 9, a lokacin kuma musharraf ya fara matsanancin ciwon ciki kullum muna hanyar asibiti Zaki sha mamaki kuwa In na ce miki har lokacin basa ga maciji da mahaifinshi ba irin nasiha da wa'azin da banyiwa musharraf ba amma ya riga da rike shi a rai, dayake zaman mu rabi gombe rabi Abuja yasa su nuriyyah suka saba da en gomben sossai, naji mamaki sossai da likita yace wai musharraf na da karfin sha'awa hakan yasa maniyyi ke taruwa mishi a mara wadda yake haddasa mishi ciwon ciki me tsanani.....................
A tsakankanin ne komawa gombe ya kamamu, sabon gida muka koma me d'auke da part biyu manya a d'aya na gaban muka zauna, sam hankalina be kama da barin musharraf shi kad'ai a Abuja ba dukda na yarda da tarbiyar shi amma shed'an tana tsoron sharrinshi, Kiran musharraf nayi a waya nace In yana da buduruwa tayiwa su yaya nasir magana a tura gidansu.................
Ce min yayi be dashi ya bani dama in za'ba mishi duk wacce naga tayimin, Anty Aisha na samu mukayi maganan inda ta ta had'amu da surayyah yarinya me hankali da natsuwa er gidan manya ba wai kud'i ba a'a Addini da tarbiyyah, a lokaci kankani aka yi komai aka gama mamaji yace tunda site biyu ne damu ta zauna a d'ayan kan musharraf yayi gini, sam musharraf be so ba amma ba yadda ya iya, shi abinda baya so shine anfani da komai na babanshi...................
Se ranan d'aurin aure musharraf ya zo, don gudun idon mutane yasa mahmoud had'a musu dinner na manya da yara a tsare yayi komai kuma naji daad'in hakan da kyar na shawo kan musharraf yaje, abinda na lura da shi sosssi a wurin dinner shine kallon da Mahmoud ke yiwa surrayah har abun yaso tsorata ni, amma ganin mun had'a ido se ya wayance be kuma sake kallonta ba......................
Abuja suka wuce a chan suka ci gaba da zama har surrayah tayi nasarar sa musharraf fara sonta da kyakyawar d'abiyanta, duk hutu in ya samu gombe suke dawowa muyi tare, har ta samu cikin Zarah, Ashe musharraf da haidar suna business wadda ban sani ba seda ya saya gidan da muke cikin nan a yanzu haka....................
Seda ya kawo ni gidan kan yace "surprise momma, ga gidanmu" harararshi nayi nace "stop kidding me" musharraf na murmushi yace "wallahi da gaske momma, muna business na shigo da motoci da haidar wadda muka had'a share, ban fad'a miki bane kawai sbd Ina son yi miki surprise ki san d'anki ya girma" dariya nayi sossai cikin farin ciki na sawa business d'in albarka...................
Bayan haihuwan zarah da kwana arba'in cib cib wani ranar alhamis da tashin hankali ya shigo rayuwarmu me tsanani don ba wadda be azabtu da wannan ibtila'i ba a family d'inmu, tun bayan haihuwan zarah da musharraf ya koma be dawo ba se ranan dayake a gida surrayah tayi wanka wata dattijuwa iyayenta suka turomata ta taya ta zama itama dattijuwar ranan ta tafi.................
Part dina straight musharraf ya sauka bayan isowarsu da murna na tareshi yadda na saba, mun d'an jima kan yace bari yaje yayi wanka a part dinshi ya dawo yana fita da kamar five minutes naga musharraf ya shigo a tsanin rud'e jikinshi na mugun rawa idanunshi sun kad'a zazur har hawaye na zuba a rud'e na mike nace "Lafiya musharraf?" Be iya amsa ni ba se part d'inshi da yake ta nuna min da hannu.................
Da sauri na bi shi tun daga parlor nake jin gurnani da nishi irin na masu yin sex a hankali na d'aga labulen d'akin tashin hankalin da na shiga ba a kwatantawa khairi kin san kuwa abinda na gani? Bata jira amsar khairi ba tace mijina da surkata tsirara kwance a kan gado turmi da ta'barya suna aikata mash'a a razane khairi ke kallon momma da kuka ya sarke ta seda ta samu tayi tukun taji nauyin zuciyarta ya ragu har seda ta saka khairi kuka dama tun daga farkon labarin take share hawaye...................
Ci gaba momma tayi da, yanke jiki nayi na fad'i ashe a daidai lokacin musharraf ya je kitchen ya d'auko wuka da niyyar da'bawa mahaifinshi duk da ya lura da had'in kan matar akeyi amma yafi ganin bakin mahaifinshi a kanta, Allah ya sa yana shigowa baban ya lura dashi da sauri ya mike ganin wukar da musharraf ya kawo setinshi hannu biyu yasa ya damki hannun musharraf dake rike da wukan a take suka fara kokawa hannun mahmoud ne a sama shiyasa ya zama kaman shi ke controlling juyawar wukan....................
Ganin musharraf na shirin fin karfinshi ne yasa ya saita surrayah dake kwance a sandare ta kasa komai ya ja musharraf da karfi wukan ya da'bu a cikinta be shiga sossai ba amma ba karamin azaba taji ba da ya sata sandara ihu, da sauri mahmoud ya saki wukan ya d'ibi kayanshi yayi bayi da gudu tare da danna sakata, bayan ya sa kaya ne ya kira police yake ce musu wai d'anshi ya kashe matarshi yana shirin kasheshi suyi sauri su zo...................
Shi musharraf tunda wukar ta sauka cikin surrayah ya daskare a wurin idonshi har lokacin be bar zubar da hawaye ba don ba karamin so yakeyiwa surrayah ba, a hankali ya sabule hannunshi daga kan wukan yana juyawa zuwa kan sofan dake d'akin ya zauna a tsananin rude ya ma kasa tuna ni Ina kwance a sume a d'akin, ita kuma surrayah ganin jini na zuba sossai yasa tayi kokarin tashi tana dafa gado hannunta ne ya gauce se jinta tayi a kasa tayi rub da ciki wukar ya gama shiga cikinta wani ihu da ta tsala seda ya tsorata musharraf da gudu ya taho ya juyata a lokacin polisawa suka cika d'akin suna saita musharraf da bindiga shi kuma se kallon surrayah yake cikin tsananin takaici da haushinta wa ya san ko tun yaushe ta fara mu'amala da mahaifinshi...................,,,
Kamashi akayi se a lokacin mahmoud ya fito yana ganina a sume ya fara ihun karya yana cewa "bade ya kashemin mata ba ko?" Police mace ce ta ta'ba wuyan Momma tace "bata mutu ba suma ce kawai" ruwa aka saka man na farfad'o kenan naga d'ana sanye da ankwa har biyu a hannunshi a gaba suka saka shi Ina ta ihu da cewar baze aikata haka ba suka kamashi suka tafi dashi.......................
In takaice miki gwagwarmaya sossai akayi a court wadda duk sheda ta nuna musharraf ne ya aikata komai kuma karya yake da yace ya samu mahaifinshi da matarshi turmi da ta'barya, da na so 'boyewa amma ganin ana shirin halaka min yasa na mike nayi shedar nima da nake matarshi na gani ido da ido rudewa kam su dadda sun yi shi wadda yayi sanadiyar kamuwarsu da hawan jini, mamaji kam har ciwon zuciya...................
Mutane wasu sun yarda wasu basu yarda, a take don ba sheda ga sawun hannun musharraf d'in jikin wukan aka yanke mishi hukuncin zama a gidan yari na har abada, a nan na yanke jiki na fad'i, da sauri aka d'aukeni zuwa asibiti jini yayi mugun hawa ba kad'an ba, su dadda da suma suke fama da jikinsu ne suka ci gaba da bani baki amma inaa d'ana namijin kwaya d'aya jal shine aka yaankewa zaman gidan kaso da har abada? Kuka sa me sauti bayan sati biyu aka sallamenu bamu zarce ko Ina ba dukku don na tsani zama da mahmoud a lokacin na san ko mutuwa yakeyi yana farfad'owa bazan ta'ba komawa gidanshi ba..................
Family meeting aka had'a inda anan na cire kunya na bada labari yadda Yaya mahmoud ya kuntata min ya azabtar dani, ya kuma zalunceni, ba wadda be yi kuka ba dadda kam har seda ta wanka min mari kan ta yake jiki ta fad'i mamaji ma ciwon zuciyarshi ta tashi a tare aka had'asu zuwa asibiti..........................
*kuyi hakuri plz saboda rashin wuta ne yasa kuka jini shiru shekaran jiya da jiya*
#vote
#share
#comment
**Not edited
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️6️⃣1️⃣▶️6️⃣2️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
In kika ce tashin hankali kin rage a abinda na shiga ko ince muka shiga gabad'aya family, mamaji kaman baze rayu ba ko da suka yi niyyar tsinewa Mahmoud Bappa da diddi ne sukayi tsayin daka wajen hanasu inda suka nuna musu ko basu tsine mishi ba abinda de ya shukan nan shi ze gir'ba sun amince baza su tsinemai ba amma kar ya sake tako kafanshi inda suke har abada In kuwa yazo to tabbas tsinuwa ce tsakaninsu, ba yadda su hamma nasir basuyi ba ganin an ku'buto da musharraf amma abin yaci tura abinda yaso haukatar dani kenan..................
Dadda da ta tashi yimin fad'a har kaman zata bugeni akan yadda na boye rayuwar aurena, se kuma suka d'aurawa kansu laifin suna rayuwa with that guiltiness, khairi In nace miki na zauna na natsu karya nake yi, tunda aka kai musharraf prison ban kara bacci da dare ba, kullum a tsaye nake a gaban ubangiji abinci se anyi da gaske nake ci su miemie kam ma ko kallonsu bana yi dukda basu san me ake ciki ba wacce ta fahimta ma nuriyyah ce haka In Ina kuka zata zo ta sani a gaba muyi tare...................
Da nasiha da adu'o'i da komai aka samu na d'an sake har muke zuwa prison ziyartar musharraf randa na fara zuwa halin da na tadda musharraf ya kusa yin ajalina, a buge ba yadda yake rungume shi nayi ina kuka kaman raina ze fita hakan yasa shima fara hawaye, inda da kyar na samu yayi min magana ya tabbatar min tunda abin ya faru kuka ma be samu yi ba se yanzu, a sanyaye na ce "musharraf me ya kaika fara shaye shaye da hankali da iliminka?" A yanayi na marar hankali yace "Toh me kike so inyi momma? Anan fa zan kare rayuwana sanadiyar sharrin mahaifina, na san yaushe zan mutu? Na san iyakar shekarun da zanyi a duniya? Momma dan Allah ki barni kawai abin nan yana rage min damuwa kaman yadda na ciki suka fad'a"......................
Ina girgiza kai nace "Inaa musharraf ka fawallawa Allah lamuranka shine kad'ai me iya rage maka damuwa ba shaye shaye ba, musharraf ba tarbiyarka ba kenan amma ban ga laifinka ba duk na mahaifinka ne" yana kallona da idonshi da suka rine da kayan maye yace "Ina rokon ki abu biyu a duniya momma, ki kularmin da little sossai momma ki kuma kwantar da hankalinki wurin tarbiyar su nuri kar laifin ubansu ya shafesu, sannan abu na biyu shine dan girman Allah karki komawa auren mahmoud don Allah" Ina gyad'a kai nace "naji musharraf naji, zanyi duk abinda kace" ya kuma cewa "sannan alfarma nake so kiyi min na komawa gidana na nan garin da zama, ki kula da su little a wurin ki ci gaba da sana'anki"...............
Nan ma kai na gyad'a mishi yana baya baya yace "and kiyi hakuri ganina ze dinga d'aga miki hankali hakan yasa na yanke shawaran bazan kara fitowa ba daga yau, am sorry" Ina ta kiranshi amma ko waiwayowa be yi ba ya wuce su hamma ne suka kama ni muka tafi, haka na dinga zama da kewan d'ana da kyar na samu na shawo kan su diddi suka barni na dawo cikin gombe da zama, anan na ci gaba da business Ina ci gaba da kula da su miemie, a lokacin ne kuma su hajjiya ruqayya suka dawo gombe, sossai ita da mijinta sukayi mana jaje, se kuma daga lokacin kawancenmu yayi karfi....................
Kullum In naje prison musharraf baya fita haka kuma bana kin zuwa ko letter in bayar akai mishi, sannan mahaifinshi ban kara ganinshi ba, kowani karshen wata se su hamma nasir da Ahmad se sun turo mana kayan abinci da kuma kud'i haka taheer ma, a lokacin ma anyi auren Rabi'ah har ta haifi afreen................
Bayan three years
Se bayan three years aka chanza mana sabon governor a gombe state inda yayiwa duk en prison afuwa wadda de ba'a saka mishi baza'a ta'ba sake shi ba a file se Allah ya taimakemu musharraf baya ciki, nuriyyah na zaune tana kallon Network news kawai taga an sanar da sake en prison da sabon governor ya bada umarnin ayi da gargad'i me tsanani In kuwa suka kuma aikata laifinsu toh za'a dawwamar dasu a prison din.................
Da gudu nuriyyah ta haura ta sameni tana kuka tana dariya hannuna ta kama cikin tsantsar farin ciki tama rasa me zata ce se tsalle take a d'an rude nace "lafiya kuwa nuri?" Tace "momma zo ki ga, zo ki gani" mikewa nayi ganin yadda take ja na, har gaban tv ta tsayar dani a lokacin ake maimaita kanun labarai, Ina gani na sulale nayi sujada ina mai mika godiyata ga Allah se kuma kukan murna ya biyo baya, su hamma Ahmad ne suka kirani suna tambayana ko na ga news cikin kuka nake ta gyad'a kai suka ce In jira suna zuwa....................
Cikin 30mins suka zo da matansu mu matan kam se kuka mukeyi hajiya ruqayyah ma tazo da mijinta wadda ya kasance a da abokin mahmoud amma tunda abunnan ya faru ya fita hanyanshi, a tare muka dunguma zuwa prison at last after good three years zan sa d'ana a ido, ashe he will be free one day, Ashe Ubangiji na ya amshi adu'o'i na, a bakin kofa muka tsaya jira har ya fito kasa karasawa wurinshi nayi se kuka................
Da kanshi ya karaso ya rungume ni, yayi baki sede ba rama a jikinshi se ma wasu packs da suka fito rad'a rad'a a cikinshi don ba riga ya fito, daga ka ganshi zaka san ya zama tantiri d'an shaye shaye, bakinshi yayi maroon duk da dayawa na cewa kyau ya karamishi, duk en uwa ma rungume shi suka dinga yi d'aya bayan d'aya, a lokacin mamaji ya kira yace mu wuce dukku..................
Ina rike da hannun musharraf kaman wadda aka ce ze gudu ko wani abun ze sameshi In ban rike shi ba muka koma gida, su little zamu d'auka se mu wuce dukkun mun kuwa samu sun taso daga school gabad'aya motan da muke suka shiga kasancewarshi babban sienna ne, kallon kallo little da musharraf suka tsaya yi Bayan nuriyyah ta rungumeshi ta sake miemie da Amrah da basu ganeshi sossai ba seda nuriyyah tace "Hamma musharraf" kan suka rungumeshi suma Amrah na cewa "Ina ka tafi ka barmu hamma, tun tafiyanka ba me kaimu shopping ba me saya mana chocolate and rest and kullum se miemie ta bugeni bayan ka hanata" ture ta yayi daga jikinshi ba tare da ya ce komai ba.................
Anan na lura da sabon miskilancin da ya koyo wadda da ba halinshi bane kuma na lura duk en uwana su taheer da su hamma nasir da kyar yayi musu murmushi, abin yaso sani kuka don ba haka yake ba yana da son mutune mussaman ma kannenshi duk da na san son sun a jininshi yake amma miskilancin da ya koyo baze sa ya nuna musu ba, tapping laps dina da yayi shi ya dawo dani daga tunanin da na tafi tare da maida idona kanshi....................
Little ya nuna min tukun ya nuna kanshi, alamun yana tambayana ershi ce? Kai na gyad'a mishi se naga murmushi a fuskanshi yana kallonta yace "hi little" kallona tayi nace "your paapi" Ai da gudu ta rungumeshi dama ta saba ganinshi a hoto kuma kullum se tayi