Advertisements
Chapter 16 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   16 / 38

45K to 48K   out of 113.1K words

yayinda khairi ke murmushi, shagwa'be fuska Amrah tayi tace "au ni ba kawar ki bace?" Khairi tace "babba ma kuwa" nabeel yace "but Adda sulaimi min andi"(Adda sulaimi muka sani)"............

Har khairi zatace bata jin fulatanci se ta tuna jiya taji little nayi, Amrah tace "ha toi Adda sulaimi mai woni?"(a Ina Adda sulaimin take?) nabeela tace "ha jalingo"(a jalingo) Amrah tace "Toh kunga wadda yake nan dashi akeyi nice a nan sulaimi a jalingo" zasu sake d'auko wani maganan khairi tace "kinga Adda Amrah muje ki gaida dada dare nayi kar momma tayi fad'an kun zauna"............

Karasawa wurin Dada sukayi a cikin d'aki da tun d'azu take jinsu kasa Amrah ta duka tace "'yan nyalli jam na dada?"(mun yini lafiya dada?) dada tace "jam noi shomri noi saare"(lafiya ya gajiya ya aiki?) Amrah tace "jam wala ko d'ume"(lafiya kalau ba komai)...............

Tana mamakin me yasa ta amsa mata bata kallonta se wani direction d'in bata gama tunanin ba idonta ya fad'a kan sandar dada da take anfani dashi wani tausayinsu ne ya rufeta don ta tabbatar Dada bata gani gashi bata ga alamun akwai wani namiji a gidan ba don d'akin dai kwaya d'aya dashi ake anfani d'akin zaure a rufe............

Duk tana Chan duniyar tunani little suka gaisa da dada, har seda khairi tace "Adda Amrah lafiya?" Firgigit tayi tana cewa "lafiya Adda khairi, dada ba kinga khairi ba na hana ta ce min Anty ta dawo Adda bayan kuma ta girme ni" ta karasa da tura baki kaman tana gaban momma.............

Dariya sauran yaran sukayi har khairi dada kuma tana murmushi tace "Toh khairi kinji bata son Adda ko Anty ki ce mata Amrahn ta" Amrah tayi saurin cewa "yauwa dadanmu" tana yiwa khairi gwalo dariya suka sake yi...........

Khairi ta mike tace "bari In kawo muku ruwa" Amrah tayi saurin cewa "Ke yi zaman ki, tafiya zamuyi mun bar baba Adamu a waje yana jiranmu oya little lets go"..........

Sallama sukayiwa Dada tana ci musu albarka, har mota nabeel da nabeela da kuma khairi suka raka su, suna d'aga musu hannu har suka tafi...........

Da hira suka shigo parlorn se kuma sukayi shiru ganin musharraf zaune kusa da momma yana shan coffee, little ce ta karasa tana hawa jikinshi tace "I miss yhu paapi" yana gyaramata zama yace "ba wani ba kin samu wata Chan kin manta da ni ba" little ta shagwa'be fuska tace "waye kuma wata Chan paapi" har ze kira sunan khairi se kuma ya Basar yace "you better start saying sorry"............

Tace "sorry paapi" yace "Ohk then" hiransu momma ne ya d'auke mishi hankali duk da sam be yi kaman yana jinsu ba inda Miemie ke cewa "Ina kuka je ba ni?" Amrah  tace "Ina zaki sani kin shiga d'akin Adda nuri maula" hararanta mimie tayi tana nuna musharraf da baki wato ba don shi ba da ta gane.............

Momma tace "kun dawo?" Amrah tace "Eh momma baki ga gidansu ba abin tausayi amma they live happily na lura ba wani namiji babba a gidan ga mamansu makauniya siblings dinta kuma sa'annin little ne" momma tace "Ayyah" Miemie tace "Allah sarki next time in za'a kaita nima zani" Amrah tace "Ohk" mikewa musharraf yayi yana cewa "good night momma" momma tace "Allah tashemu Lafiya da zarahn zaku kwana?" Yace "Yeah amma Amrah kiyi mata wanka ki sa mata nightwear se ki kawota".........

Tsalle little ta dinga yi don tana mugun son kwana da shi shikuma ba ko yaushe yake yadda ta kwanan ba, fita yayi yana amsa seda safen miemie...........

Yana kwance yayi zurfi cikin tunani wadda ban san na me ba se ga little ta shigo ta kwanto jikinshi tana bashi labarinsu cutie be hana ta ba sam sema hankalinshi da ya bayar kanta dukda ba amsa ta yakeyi ba, a haka ta gaji tayi bacci............

Washegari

Bayan sun gama breakfast yam and sous se tea da khairi tayi musu da misalin karfe 9:30 ya fiddo akwatinshi aka sa a mota, sanye yake da well ironed three pieces suit navy blue da ya matukar amsarshi, yayi kyau sossai har ya gaji yana shigowa parlorn kamshinshi ya bule ko Ina.........

D'akin momma yaje tayi mishi adu'a suka fito tare da su Amrah little se shagwa'be fuska takeyi alamun kuka don wannan karon ya d'an jima, sun fita daga parlorn har sunje wurin mota yace "opps Ina zuwa" ya juya ya koma parlorn direct kitchen ya shiga tana tsaye tana chopping carrot kawai taga mutum a kanta, sake gaisheshi tayi duk da ta gaidashi da Safe amsawa yayi, yana nufan fridge ruwa ya d'auka dukda ya san akwai ruwa a fridge din parlor amma haka kawai ya tsinci kanshi a kitchen, bayan ya d'auko ruwan ya 'balle murfin ya kafa a baki dukda sanyinshi be cire ba seda yayi rabi kan ya juya ya fice...........

Yana fita ya samu haidar ya zo gaisawa sukayi kan ya shiga mota shima rakiyar mota uku suka mishi har airport, seda sukaga departing d'insu kan suka dawo............

One month later

Zuwa yanzu khairi ta saba sossai da gidan aikinta da ma mutanen gidan gabd'aya sossai suke kawance da Amrah har ta san labarinsu bayan alkawarin baza ta gayawa kowa ba, khairi na iya kokarinta ganin bata wuce matsayinta ba, sun saba sossai da little In baka sani ba se ka d'auka mamanta ce..............

Tunda musharraf ya bar Gombe almost month kenan be sake zuwa ba sede suyi waya da 'yan gidan yana Chan yana rayuwan da ya saba na kad'aici se shan taba iyakarshi da mutanen office d'insu gaisuwa se kuma In aiki me muhimmaci ya had'aku daga mazan har matan, har gwara mazan ma da mata kam, me makon abun ya ragu amma se karuwa yake..........

Rayuwa tayiwa su khairi daadi don zuwa yanzu ba abinda suka nema suka rasa albashinta na farko da ta d'auka last week ta saya musu duk abinda zasu bukata har kayan sawa ta kara musu kad'an, sauran kud'in da ba wani yawa ta cire kud'in napep dukda momma na yawan bata kud'in napep amma ba kullum ba gwara ta dinga rikewa In an batan ma se ta ajiye na wurinta sauran kud'in sukayi savings...........

Matsalan da ta fara fuskanta na d'aya a gombe wadda ya girgiza ta shine cewa da mijin Maman hamdeeya yayi yana sonta, a wata ranan laraba ta fita don zuwa gidansu musharraf ya tare ta a daidai kofan gidan shi, inda ya furta mata shi de yana sonta kuma soyayya ta aure, bata tsaya kulashi ba ta tare napep ta wuce ranan ta wuni jimami da tsoro tana tsoron kar Maman hamdeeya taji don bata san ya zatayi ba............

Yanzu sati biyu kenan rabonta da shiga gidan kuma ta kasa fad'awa dada, har yau da ya kasance Friday kuma a ranan musharraf ze zo don momma ta fad'a mata tun jiya da ta shirya yau akwai aiki sossai a gidan..........








#vote
#share
#comment






'Yar mutan Adamawa

🎗🎗🎗🎗🎗








                 IGIYAR RAYUWA😭







                                        🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

     'Yar mutan Adamawa

*Alhamdulillah Ala kulli haalin, thanks for your prayers🙏*

Page➡️4️⃣6️⃣▶️4️⃣7️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Tunda garin Allah ya waye take jin gabanta na fad'uwa kaman yadda yake mata de in jikinta ze tashi ko kuma mutanenta suna kusa, kaman ta ki zuwa wurin aikin amma In ta tuna momma tace akwai ayyuka dayawa yau sbd dawowan musharraf se jikinta yayi sanyi bata so su sha wahala.............

Dada ta fad'awa bayan sun gama breakfast dada tace "ki yawaita azkar a zuciyarki kuma ki kiyaye duk abinda kika san ze ja miki 'bacin rai, Allah ya tsare de kar suyi miki sanadiyar aikin nan" khairi tace "Ameen" a sanyaye ta gama duk abinda zatayi suka sallami dada suka fito ta ajiye su nabeel makaranta ta wuce GRA............

Yanzu sunyi time table sbd saukaka mata base ta dinga tambaya ba musamman breakfast, yau Irish potato za'aci da kwai se black tea duk me so se ya zuba madara da bournvita, aikinta ta fara cikin natsuwa tunda kitchen din a goge a share ta sameshi, kan lokaci ta gama ayyukanta tare da shiryasu kan dining, ta dawo kitchen ta wanke duk abinda ta 'bata ta kuma share kan gas d'in.................

Bayan ta gama ta koma d'aki taje ta kwanta har wa yau zuciyarta be dena bugawa ba, adu'a kawai takeyi a cikin ranta, ta jima sossai a haka ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba, tana jin muryoyin su momma a parlor amma ta kasa tashi ta fita, tanaji momma ta turo Miemie ta dubo ta ko lafiya, har Miemie ta shigo bata iya ta tashi ba seda ta jijjigata tukun ta bud'e ido Miemie tace "khairi, khairi tashi momma na magana" ta juya ta fita, a hankali ta mike ta sa khimar dinta ta fito..................

Har kasa ta duka tace "Ina kwana momma?" Momma tace "Lafiya klau ya gajiyar aiki? Da su dada?" Khairi tace "duk Lafiya klau Alhamdulillah" gaisawa sukayi da nuri tukun Miemie, Amrah da little kam sun tafi school, salima da maryam kam sun jima da komawa gidajen iyayensu, khairi tace "me dame za'ayi momma?" Momma tace "eh toh zakiyi pepper soup na kifi, se tuwon semonvita da miyan ku'bewa d'anye, se zobo da fruit salad" kai khairi ta gyad'a tace "bari na fara wasu abubuwan yanzu kar lokaci ya kure" da toh momma ta amsa tana cewa "nuri da Miemie ma zasu shigo su tayaki"..................

Tashi sukayi suka rankaya kitchen din gabad'aya ko wacce ta fara aiki, cikin lokaci kankani suka gama, nuri na kallon khairi tace "Ke kuwa khairi lafiyanki kuwa yau? Na ganki duk wani iri" khairi ta d'anyi murmushi tace "lafiya klau Adda kawai kaina ke d'an ciwo amma na san zuwa anjima ze yi sauki" miemie tace "subhanallah sorry bari In kar'bo miki magani wurin momma"....................

Ficewa tayi Ba'a jima ba ta dawo da panadol biyu a hannunta nuri ta miko musu ruwa ba yadda ta iya haka ta kar'ba ta sha, karasa had'a zobon dake gabanta tayi tana jin miemie da bata dad'e da fita parlorn ba na cewa "Adda nuri har sun shigo gombe fah, inaga tafiyar asuba sukayi amma wannan karon sunyi sauri yanzu 12 fah" nuri dake kitchen din bata ce komai ba se had'a fruit salad d'inta da ta ci gaba................

Khairi kuwa jin sun shigo se kawai ta juye zobon a wani plastic robber me d'an girma ta d'auka ta sa a deep freezer wai don ya d'an yi sanyi kan ya karaso, nuri kuma ta zuba fruit salad din a jug ta saka mishi kankara ta had'a akan tray da cups ta fitar zuwa dining, wanke wanke khairi tayi tare da share kitchen din ta goge ya fita kal kaman ba'ayi aiki a ciki ba...................

Tana shiga d'aki taji shigowarsu parlor, shi da Amrah da little sun had'u a gate ne se kawai suka shigo tare, momma dake zaune a parlor ne tayi mishi sannu da zuwa, samun wuri yayi kasan kafanta ya zauna yana cewa "mun sameku lafiya" se da gabanta ya fad'i jin muryanshi, ba abinda ya sauya a ciki yana tashi cikin sanyi da amo..................

Momma tace "Lafiya klau Alhamdulillah ya hanya? Ya kuma wurin aikin naku?" Yace "Alhamdulillah" yana shafa cikinshi yace "momma am starving Allah ko breakfast banyi ba" waro ido momma tayi tace "me kakeyi haka ya hanaka karyawa" murmushi me d'an sauti ya saki yace "kawai momma, nayi kewarku" murmushi itama tayi kan tace "oya muje ka ci abinci se kayi wanka kayi shirin juma'a gabad'aya" mikewa yayi suka nufi dining, Little da ta haura bata ga khairi a saman ba ta gangaro tace "momma Ina Adda khairi I want to eat with paapi, tazo ta min wanka da wuri"..................

Dariya momma tayi tace "Toh sannu mamanta, duba d'akin ta kanta ke ciwo In baza ta iya ba ki zo nuri ta miki ko miemie" d'akin ta nufa tana kwala kiran "cutie cutie" har ta shige mikewa khairi dake kwance tayi tare da zama tace "wannan irin kira haka pretty?" Tura baki gaba tayi tace "Toh ba ke bane cutie kinki kizo ki min oyoyo yadda kika saba ba"..............

Khairi tace "ohh sorry dear baki ji momma tace headache na damuna ba? muje In miki wankan anan tunda akwai kayanki koh? samu ki ci abinci da paapinki kan ya gama" da gudu ta nufi toilet dama daga ita se pant ta gangaro, towel d'inta khairi ta d'auka tare da binta bayin tana murmushi, wanka tayi mata suka fito se surutu take zuba mata amma khairi ta kasa magana se uhm ko uhm uhm, ciwon kanta ya fara yawa ga faduwar gaba dake ta kara damunta.................

A Haka ta shirya little cikin short gown dinta blue me kyau tare da gyara mata parking din kanta don kanta a tsefe yake tayi mata parking din gefe tare da bud'e jakanta ta fiddo powder, ita ba gwanar kwalliya bace amma tana yawan sayan powder da lip glose se kajal, tana ma saka su jankanta ne sbd nabeela idonta idon kayan kwalliya se ta 'bata mata su..................

Shafawa little tayi tare da saka mata kajal da man baki tayi kyau kuwa sossai, da gudu ta fita ta kuwa samu paapin na jiranta be fara ci ba, zama tayi tana kallon momma, Amrah, miemie da nuri da suka kusa cinye nasu, ta'be baki tayi tana cewa "ba kunki jirana ba to de paapi na ya jirani" momma tace "ku ta dama daga ke har paapin naki mu de baza mu zauna da yunwa don ke ba da In kin zaunan ma ba cin kirki zakiyi ba".................

Dariya su Amrah sukayi musharraf na murmushi yace "khaih momma, kin de ki jiranta don bakya so tazo ta ci dayawa ta fiki kiba da tsai" momma na murmushi tace "wa wannan d'in? Tab ai wannan da take kaman bebin robannan ko rabin kiba na bazata yi ba bare tsaho" tura baki gaba little tayi tare da raurau da ido da sauri musharraf yace  "oya open ur mouth in baki kiyi maza maza ki ci kifi momma kiba da tsai" Ai ko da sauri ta bud'e bakin hakan yasa su kwashewa da dariya banda musharraf da murmushi kawai ya saki..................

Ita ala dole ita so take tafi momma kiba da tsaho, khairi dake jinsu daga d'aki ta saki murmushi hawaye na gangaro mata tana tuna lokacin da suke happy family, Ashe dama yana wasa da dariya da family dinshi? Da sauri ta mike tana cewa "subhanallah" shap ta mance da zobo bata kai musu ba, d'aukan khimar dinta tayi ta saka tare da fitowa, Amrah na hanganta tace "Tbest yanzu nake ta sauri In gama In zo In d'ura miki naki, tunda naji momma na cewa kina headache na san baza ki wani ci abincin rana ba"..................

Murmushi kawai khairi tayi tana jin idanunshi a kanta Ai ko hakan ne kallonta yayi na akallah 30 seconds kan ya d'auke kanshi, da sauri ta shige kitchen tana sauke ajiyar zuciya, robbern ta d'auka ta fito zuciyarta na tsananta bugawa kanta kaman ze tsage sauri takeyi ta ajiye musu ta koma d'aki duk abinda ze sameta ma gwara tana d'aki bata hankara ba tayi missing step na haurawa wurin dining kuma skirt ne a jikinta hakan yasa ta hantsila robbern ya kubce mata..................

Se jikin musharraf gashi farin tshirt ne jikinshi da farin Jeans a take suka rine da sauri ya mike yana furta "subhanallah, ya Salam" ya karasa a hankali yana lumshe ido don cooling temper dinshi, ganin ta sulale ta duka wurin tare da rufe ido yasa haushi ya kamashi a lokaci d'aya ya daka mata tsawa "Ke wace irin mahaukaciya wawiyar yarinya ce da zaki watsa wa mutum abu a jiki kuma ki ki ce mishi komai??? I hate nonsense wallahi, useless human being" duk en dining din mikewa sukayi tun sanda zobon ya zubewa musharraf din a jiki................

Momma zatayi magana kenan taga Khairi ta mike ta tsaya tare da bud'e idanunta da suka rine ta kafe musharraf da shi, fuskantan nan kaman bata ta'ba dariya ba, little ce ta nufe ta tana cewa "sorry cutie paapi ne ya 'bata miki rai ko?" Wani irin turewa da tayiwa little seda duk suka tsorata ba don musharraf yayi saurin tare ta ba da tayi mummunan fad'uwa a tsorace ta fashe da kuka tana kallon khairi da har yanzu musharraf take kallo.....................

Nuri musharraf ya mikawa little cikin kasa da murya yace "ku tafi parlorna kuyi kallo" kar'ban ta tayi jikinta na rawa, binta da ido yayi jikinshi na sanyi har suka fita daga parlorn, runtse ido yayi yana jin tsanan mahaifinshi na kara ninkuwa mai, a kullum In yaga nuri se ya tausaya mata in ya tuna wai banzan halin mahaifinsu ya ja mata aljannu, da basa mata da wasa in sun tashi don ma yanzu sunyi sauki sossai don magungunan ya dinga nema mata kasashe kasashe.....................

A hankali ya bud'e idonshi dake lumshe ya d'aura akan na khairi da har yanzu kallonshi takeyi ko kifta ido babu, tun daga kallon farko da ya mata ya san ba ita ba ce sbd yana da tabbacin baza ta ta'ba iya juran kallon cikin kwayar idonshi na fiye da minti d'aya ba, hakan yasa ya saci kallon nuri ganin hannunta na rawa yasa ya tabbatarwa kanshi zargin da yake hakan ne yasa ya tura nuri part dinshi don kar nata ma su tashi....................

Tunaninshi ya katse ne ganin ta nufo shi cikin zafin nama ya rike hannayenta da take shirin shako shi dasu kokuwa suka fara, ganin tana shirin fin karfinshi ne yasa ya sa duk karfinshi ya ja ta tsakiyar parlorn tare da tad'iye kafanta yayi saurin sa hannunshi a kwankwasonta a tare sukayi kasa, se shi ya sauka da guiwanshi d'aya ita kuma ta sauko kan kafan, d'ayan kafan yasa ya danne ta tare da, danne hannayenta da duk hannunshi biyu don ya lura ba karamin karfi ne da aljanin jikintan ba..................

Kallon momma dake kallonsu cikin tausayawa yayi yace "momma a d'auko hayakin nuriyyah plz ayi sauri" ya kalli Amrah dake hawaye yace "yi sauri ban ruwa kad'an a cup" da sauri ta nufi kitchen momma ma ta nufi sama, adu'o'i ya ci gaba da mata kan saukowan momma, yanayi yana

16 / 38