Advertisements
Chapter 20 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 38

57K to 60K   out of 113.1K words

na iya d'auke ni In fad'i, ana cikin haka mukayi hutu yayi daidai da bukin taheer hakan yasa mamaji cewa dole se munje haka muka tattara muka nufi gombe bayan uban kashedin da nasha a wurin mahmoud kuma naji don sossai na tsorata da lamarinshi kwata kwata be da tausayi da imani don da cikin ma haka yake duka na yayi ta naushin cikin hakan ze barni da azaba, ban ta'ba tsammanin musharraf ze zo duniya da rai ba.........................





*kuyi hakuri plz na jina da kukayi shiru jiya ba lallai gobe ma ku jini ba sbd younger brother na ba lafiya anyi admitting d'inshi kuma ni ke zama dashi, plz kuyi mishi adu'a bcos he need it*








#vote
#share
#comment




'Yar mutan Adamawa


๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—







ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย ย  IGIYAR RAYUWA๐Ÿ˜ญ







ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย ย  ๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo


ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย ย  'Yar mutan Adamawa

Pageโžก๏ธ5๏ธโƒฃ7๏ธโƒฃโ–ถ๏ธ5๏ธโƒฃ8๏ธโƒฃ
๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Ba irin tambayar da su dadda basu min ba ganin irin karewar da nayi kaman kud'in guxuri amma na ki fad'a musu shi ne ma yace musu Ai basu ga yadda nayi jiki ba farkon auren kawai yanzu cikin nan ne, ba yadda suka iya haka suka bar zancen ba wai don sun yarda ba, har kunyan shiga mutane nake ji don duk wadda ya ganni se ya tanka..................

A haka aka gama buki muka koma Abuja zama nake na hakuri da juriya har na haifi musharraf wadda tsananin rabo ne ya ajiye cikin, na shaa wahala sossai lokacin sbd nayi labour ba me taimakona da kyar na fito tsakar gidan, mai gadi na ganina yaje da gudu ya kira mahmoud seda ya 'bata lokaci sossai kan ya fito se juyi nake kaman bazan rayu ba, da ya fi to d'inma a kaina ya tsaya yana min kallon banza ganin zan iya mutuwa su dadda su tuhumeshi yasa ya d'aukeni ya wurga mota tare da figar motar zuwa asibiti......................

Naquda me wahala nayi kan na haifo shi a lokacin ya kira gida ya sanar musu inda mamaji ya bashi umarnin maza ya biyamin kud'in flight in koma gida kar ya yarda yace mota zanbi, ba don ya so ba Se don ba yadda ya iya haka ya biya yazo ya bani ticket a wulakance ko fuskan musharraf be gani ba, da kanshi ya kaini airport wai baya so inje inyi missing flight in ja mishi asara, bayan mun isa airport kan na fita a motar nace "baka mishi hud'uba ba" wata uwar harara ya zabga min a zafafe yace "baki da uba ne? Ke kar ki yarda, don't you dare try me a airport nan, bayan duk asaran kud'i da nayi da wadda zanyi dole In kun je gida se kin nemi kakaba min banzan d'ankin nan to wallahi ki kiyayi biyan bashi na".................

A hankali nace "ni de d'ana ba banza bane" waro ido yayi kan yayi wani yunkuri na fita daga motan da sauri, kwafa yayi tare da juya motarshi ya fice, trolley na naja rungume da d'a na da tambaya har na gane yadda ake komai a airport se kuma karance karance a haka har na shiga jirgi na zauna a sit d'ina da karanbani na d'aura belt don ban ta'ba ba................

A jirgin na taune dabinon dake jaka na na saka mishi a baki tare da zuba mishi ruwan zamzam, hud'uba nayi mishi da sunan baba na, don na gane baki da uban nan da yace min yana nufin kar In saka mishi sunan babanshi, bayan na isa hamma Nasir da matarshi Anty Aisha suka zo suka d'aukeni bamu ma shiga cikin gari ba muka wuce dukku, Anty Aisha rungume da musharraf, ni kuma Ina rike da marwan lokacin yana da kwana hamsin a duniya.....................

Bayan mun isa naga suna ta fiddo kayayyaki daga motansu anan na ganeย  sun yi min duk wani necessary sayyaya daga gombe, sossai su mamaji sukayi murnan ganin musharraf se tabarakallah masha Allah suke cewa, a part din dadda (mahaifiyar mahmoud) na sauka, ranan suna suka tambayeshi sunan yaro yace yana jin kunyan fad'a a tambayeni tsabar iya lauyanci, ba kunya nace "Da sunan bappa ya mishi hud'uba" don bazan bari mamaji ya sa sunanshi ba In je In shiga uku na ni kad'ai, sossai kuwa sukayi farin ciki da sunan, ranan suna mamaji ya bada shanu aka yanka, bappa kuma ya yanka mishi raguna biyu basu ma bi ta kan mahmoud ba da be zo ba be kuma kawo kudin rago ba sun ajiye hakan as kunya bayan kuma yi d'inne bazeyi ba............

Bayan kwana arba'in sossai nayi kyau nayi bulbulbul har bana so ace yau zan koma Abuja duk da sossai dadda ta fahimci be damu da ni da musharraf ba gashi tunda nazo bata ta'ba gani nayi waya da shi ba, randa na cika kwana arba'in na tafi gombe sati biyu kwarara nayi, sati na farko gidan yaya Nasir, kwana biyu gidan yaya Ahmad shima lokacin matarshi na da tsohon cikin sufyan..............

Sauran kwanakin kuma gidan taheer nayi su kan na tarkata na koma dukku a lokacin dadda ta kira mahmoud ta ci mishi mutumci daidai gwargwado don tunda na zo Gombe mahmoud be zo ba har yau, dadda ta kuma jaddada mishi bazan koma ba har se ya zo In kuma yaga baze iya ba Toh yayi ta zama shi kad'ai yana fakewa da aiki.............

Ba yadda ya iya haka yazo ya d'aukemu su yaya Nasir suka kaimu har airport ran nan a had'e sbd fad'an da iyayenshi suka mishi a kaina, Ai ko isarmu bada jimawa ba ya min dukan da ba gaira ba dalili ya kuma biya bukatarshi da ni a wulakance............

Renon musharraf na cigaba da yi har ya kai shiga makaranta na saka shi a makarantan da nake koyarwa duk waennan shekaru mahaifinshi be kashe ko naira biyar akan komai nashi ba, idan ya shigo site dinmu musharraf na nufanshi ze hankad'e shi wani lokacin har ciwo yakeji tun yana zuwa wurinshi har ya daina, abu na farko da na lura musharraf na da shi kenan zuciya yana d'an shekara uku idan har mahaifinshi ya bugeni haka ze zauna yayi ta kuka kaman ze had'iyi rai inyi lallashin duniyan nan baze ta'ba shiru ba ban san ashe tsanan mahaifinshi na ginuwa a zuciyarshi bane............

Rayuwa na gurguwa dayake albashina me tsoka ne hakan yasa ba abinda muka nema muka rasa da d'ana improvement da na samu kuma shine cire damuwar mahmoud a zuciyana tun wani mahaukacin hawan jinin da nayi kaman ba zan rayu ba, gashi ba wadda ya sani a gida..........

Daga lokacin na cirewa zuciyata damuwanshi hakan yasa na d'anyi kyau dukda raman na nan se kuma haskena ya dawo, In kuma kinga munzo nan gombe to babban abu za'ayi se muyi shekara bamu je ba, a haka musharraf ya shekara bakwai In kin ganshi zaki rantse d'an shekara sha uku ne sbd tsawo da Allah ya bashi zaki sha mamaki In na ce miki bayan musharraf na d'auki ciki sau hud'u, biyu suka zube sbd duka sauran biyun kuma sbd rough sex ko ince miki raping.............

Kuma har yau ban ta'ba fad'an halin da nake ciki ba, haka musharraf sbd Allah yayishi ba me son magana ba kuma sam baya shiga harkar da bata shafe shi ba yasa be fad'awa su dadda ba ko a hira kuwa, a tsakanin ne aiki ya dawo da mahmoud gombe wani abinsu na siyasa da ban sani ba kuma 4years ze yi achan hakan yasa muka tarkato muka dawo sam ban so dawowarmu ba sbd tonuwar asiri ne a garemu, gashi ajiye aikana nayi, abinda yafi damuna kenan Ina zan samu kudin da zanyi enrolling musharraf makaranta? Kuma Ina zan samu kud'in da zan ci damu?.................

Bayan munyi settling a gidanshi dake gefen government house, naje gidan yaya Nasir da siyasa nace mishi Ina so in fara business kaman ya san kud'i nake nema a lokacin ya min transfern 200k sossai na mishi godiya haka mukayi da yaya Ahmad ma, shima 100k ya bani tare da sanya albarka business na fara na manyan leshuka da atamphopi, veils, shoes se perfumes irin na harkan manya de.................

Matan su yaya ahmad ne suka dinga had'ani da manya sossai harka ya bud'e har na samu shigarda musharraf makaranta a lokacin yana primary four, na kuma yi mana sayayyar kayan abinci, a kwana a tashi har mukayi shekara a Gombe business kawai na sa a gaba se kula da tilon d'ana, wata ranan alhamis muna zaune a parlor ni da musharraf Ina koya mishi assignment muka ji an turo kofa a tare muka d'aga kai ganin babanshi ne yasa suka ci gaba da abinda sukeyi.................

Toh kullum ya dawo se ta mishi sannu da zuwa amma be ta'ba amsawa ba tun tanayi ta zo ta gaji ta daina, dayake gidan sun nan se an shiga main parlor ake shiga part part na gidan wadda guda biyu ne se boysquaters, Ashe yaji haushin banzan da mukayi dashi a tsawace yace "Kai wawa marar anfani, baka ganni bane da baza ka min sannu da dawowa ba In ita uwarka taki min din ni ba ubanta bane, kai baza ka min ba Ina ubanka?" Shiru musharraf yayi.................

Yana matsowa yace "Kai don uwarka wannan ba magana nake maka ba?" Musharraf yace "bade uwata ba" cikin gunguni wani wawan mari ya sauke mishi da sauri ya nufi wurin tv ya fisgo wayar Av ya dawo Ina ta zungurin musharraf ya gudu amma wawan zuciyarshi ya hanashi tashi yana zuwa ya rufeshi da duka tunda musharraf ya nad'e kafafuwanshi ya d'aura kanshi a kai be kara motsi ba kaman itace ake duka..................

Abinka da uwa se na kasa jurewa na san tunda musharraf yayi haka baze ta'ba gudu ba kuma baze yi ihu ba, hakan yasa na rike Av Ina cewa "kayi hakuri yaya mahmoud" mari ya saukemin tare da komawa kaina ya fara duka yana yi yana masifa "duk ke ce me hure mishi kunne gaki uwar banza me koya mishi tarbiyar banza aka gaya muku da maganarku da rashinshi wani abu ze karamin ne, en iska kashin tsiya".................

Ya d'aga ze kai kenan yaji an rike Avn yana juyowa yaji saukan mari yaya Nasir ne da matarshi se d'ansu mari ya kife Mahmoud dashi hagu da dama yace "mahmoud irin tarbiyar da aka bamu kenan? Ko bare ce zaka sa ta gaba kana wannan dukan a gaban d'anta balle er uwarka? Me ta maka haka? Yarinya me hankali da natsuwa" mikewa musharraf yayi da gudu ya fad'a jikin uncle dinshi, kirjinshi se tashi yake yana sauka shi ba kuka ba shi ba shiru ba yace.................

"Uncle ka gayamishi ya fita harkar uwata da ni tunda baya karinmu da komai, uncle kullum mutumin Chan se ya duki momma bayan bata mishi komai, momma na ke saya mana kayan abinci, momma ne ke biyamin kud'in makaranta duk abinda nake so ita ke saya min ta kuma saya ma kanta to me yasa ze zo yayi ta dukanta?" Da matukar mamaki yaya nasir ke kallona ya kuma kalli mahmoud..................

Dukawa yayi yana kallon jikin musharraf da yayi rud'u rud'u da duka yace "son kayi kuka, kaji In kayi zuciyarka ze yi sanyi irin haka na sawa mutum ciwon zuciya, kaji yi kuka" kuka ya fashe dashi sossai yayi kuka, seda hawaye ya cika idon yaya nasir da matarshi, samun wuri yayi ya zauna muma muka zazzauna a hankali yace "Fatima gayamin rayuwarki na aure daga farko har yau" Shiru nayi, be ce komai ba ya fiddo waya yayi kira "duk inda kake ka zo gidan mahmoud yanzu yanzu it's urgent plz" Shiru muka zauna se kallon mu yakeyi ya kalleni ya kuma kalli mahmoud...................

Ba'afi fives minutes ba akayi sallama Ahmad ne ya shigo zama yayi yana cewa "lafiya?" Hamma Nasir yace "ba lafiya ba" ya kalleni "ke fatima, kalleni Ina wasa dake??" Girgiza kai nayi yace "bani labarin rayuwan aurenki daga farko har yanzu" a hankali na fara bashi labari jin ba wasa a lamarinshi kallona suka dingayi kaman tv har na gama a tare suka maida idonsu kan mahmoud...............

Baki ya bud'e da niyyar maganan a tare suka sauke mishi mari d'aya haggu d'aya dama, Yaya Ahmad yana hawaye yace "irin tarbiyar da dadda da diddi suka mana kenan? Mahmoud me yasa zaka ci amanar aure ka san kuwa illar dukan mata matan ma matarka?" Yaya nasir kam kasa magana yayi, da kyar yayi mishi nasiha me ratsa jiki, Ahmad kam fad'a sossai yayi mishi kuma da zaran ya bud'e baki da niyar magana se ya d'auke shi da Mari a karshe yace mamaji ze fad'awa......................

A hankali nace "kuyi hakuri hamma Dan Allah karka fad'a musu baza su ji daad'i ba kuma ka san mamaji nada hawan jini plz kar wani abu ya sameshi" yace "naji Amma In yana so muyi Shiru se ya sayo kayan abinci ya cika store sannan ko marinki yayi ki fad'a min wallahi zaka sha mamaki na banza marar tunani" juyawa yayi ya fara tafiya har ya kai bakin kofa yace "sannan ka cire musharraf a makarantar da ta sa shi da kud'inta ka maida shi wadda yafi tsada a gombe, zan zo gobe da rana inga bakayi abinda nace ba zaka sha mamaki na mahmoud" ya juya yayi tafiyarshi..................

Fad'a sossai da nasiha yaya nasir ya kara mishi don ya san yafi jin tsoro da kuma maganan Ahmad ya san dole yayi abinda yace, kaman kuwa nasihar ta shigeshi a washegarin yayi duk abinda yaya Ahmad yace kuma da gaske yazo ya gani sossai ya ja mishi layi ya mishi tijarar da ya bani tsoro don beda fad'a sam, Ashe jiyan ma don ganin yaya nasir ne....................

Ai kuwa sossai maganan yaya Ahmad ya shigeshi, ya ajiye mana kayan abinci sossai ya kuma sauyawa musharraf makaranta, kuma be sake min ko kallon banza ba, ba lefi kuma In yazo karban hakkinshi ba ya mata ta karfi, a haka na samu cikin nuriyyah, ranan na tashi da laulayi sossai Ina kwance zazza'bi ne ke damuna, dama tunda ya sayo kayan abinci dashi nake girki kuma yana ci.................

So ya fito se be samu breakfast d'inshi ba, a zafafe ya shigo d'akina ina kwance cikin bargo ya janye bargon tare da cewa "ke!! Me kike nufi? In sayo kayan abinci kuma baza ki girkamin In ci ba? Ai ko baki isa ba karkiga kaman don na sararamiki kwana biyu ki zata tsoron su hamma nake wallahi yanzu se in tattakaki" a hankali nace "kayi hakuri bana jin daad'i ne" ban rufe baki ba ya janyoni kasa "ba ruwana da rashin jin daad'inki ki wuce ki samamin abinda zanci" kasa mikewa nayi yace "taurin kai ko? Ohk" belt na jikinshi ya zare ya fara dukana.................

Kaman daga sama mukaji musharraf yace "baba me tayi maka kake dukanta? wallahi ka kara dukanta se na rama mata da tsantar mamaki babanshi ke kallonshi jin furucin da ya fito daga bakinshi kan ya d'auke shi da mari, ganin ko gizau be yi ba sema kafa mishi ido da yayi yana kallonshi juyawa yayi ya fice a fusace kama ni yayi na mike ya taimaka min zuwa kan gado zan mishi magana akan abinda yayi yanzu se kawai ya juya da sauri ya fice.......................








*thanks for your prayers ya samu sauki sossai Alhamdulillah*











#vote
#share
#comment









'Yar mutan Adamawa


๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—








IGIYAR RAYUWA๐Ÿ˜ญ






๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Story and written by: fateemah Muhammad gurin

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

*This page is dedicated to yhu mama on this your special day, Ina rokon Allah ya karo miki shekaru masu albarka, ya biya miki dukkanin bukatunki na duniya da lahira, Allah ka bata tsawon kwanan da zamu faranta mata kamar yadda ta faranta mana kuma take kai. Yhu the best woman I've ever met and strong lady I've ever known. I love yhu so very much mama*


Pageโžก๏ธ5๏ธโƒฃ9๏ธโƒฃโ–ถ๏ธ6๏ธโƒฃ0๏ธโƒฃ
๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Musharraf ne ya kula da ni a ranan, dukkanmu da ni dashi tea muka yini sha sbd be iya girki ba ni kuma bazan iya ba, da dare mahmoud ya dawo ganin ba abinci a dining yasa ya nufi d'akina da belt a hannu Ina kwance cikin burgo ya yaye blanket d'in ya fara dukana, bai hankara ba kawai yaji saukan kwalba a keyanshi a matukar razane ya juya da tsantsar mamaki yana kallon d'anshi d'an shekara tara wai yana dukanshi..........................

Kwalban pepsin dake hannunshi ya bi da ido, belt mahmoud ya zuba mishi shi kuma ya d'aga kwalban da niyyar sake kwad'a mishi a firgice nace "innalillahi wainna ilaihi rajiun Abubakar!! Me zan gani haka? Me kakeyi" na karasa maganar cikin d'aukewar hankali ban kara sanin inda kaina yake ba se na ganni asibiti su hamma Ahmad suna tsatsaye kaina sannu suka dinga min...............

A kasalance na amsa Ina dudduba inda zanga musharraf baya d'akin, yaya Ahmad yace "sannu fatima, dukanki ya sakeyi ne? Musharraf ya kira mu da gaggawa wai yazo ya ajiyeku a asibiti yayi tafiyarshi" girgiza kai nayi nace "a'a hamma be dakeni ba ban da lafiya ne, Ina musharraf d'in?" Yaya Nasir yace "yana waje yaki ce mana komai" ajiyar zuciya ta sauke tana runtse ido, doctor Aslam ne ya shigo yana kallon su hamma Nasir yace "congrats tana d'auke da cikin wata biyu" cikin jin daad'i sukayiwa Allah godiya...................

Nan suka tambayeshi yaushe ne sallama, yace za'a iya sallamanta zuwa gobe da safe, godiya suka mishi ya fice a take suka kira su dadda suka fad'a musu suma sunyi farin ciki sossai da sukaji da laulayi kuwa suka ce zasu bani dattijuwar me aikinsu ta kwana mini biyu, Ai ko washegari aka sallameni na samu ma mai aikin ta iso na bata d'aki cikin part d'ina tunda aka kaini asibiti musharraf be yarda mun had'a ido ba har aka

20 / 38