Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
ya san yanayi ba wani irin tashin hankalin da baze iya kwatantawa ba yake ji, a haka suka shiga mota haidar na tambarshi ko lafiya amma ya kasa amsawa da kyar ya samu "Innalillahi wainna ilaihi rajiun" ya kubce daga bakinshi kan ya runtse ido hawaye ya fara gangarowa daga cikin kurmin idonshi.
2503 words
🤦♀️gosh nayi typing dayawa har hannuna na ciwo gaskiya harda na gobe😅 but idan naji ra'ayinku akan page din nan watakila ku samu gobe in Allah ya kaimu, me kuke tunanin musharraf ya gani ko ya karanta har ya shiga cikin wannan tashin hankalin?
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️8️⃣3️⃣▶️8️⃣4️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Gida haidar ya nufa dashi ganin yadda jikinshi ke rawa hawaye kuma yaki dena gangara daga fuskanshi, be ta'ba tunanin shi rago ne ba se yau ya kasa zuciyarshi ya kasa aminta da abinda ya gani sede ga sheda, suna isowa ya fad'a d'akinshi tare da datsewa don be son kallon fuskan kowa daga bakin kofan ya tsuguna tare da cire hulanshi ya tusa hannu cikin gashin kanshi duk jijiyoyin jikinshi a tashe yau ba don yayiwa momma alkawarin baze kara shan abun maye ba da ya sha giya, tuna akwai taba a d'akin yasa ya nufi wardrobe ya d'auko tare da cire babbar riganshi ya jefar anan ya zube ya kunna taban se kuma ya kasa sha, jefarwa yayinda karfi yana me naushin iska toilet ya fad'a ya sakarwa kanshi shower ba tare da ya cire kayan jikinshi ba.
Ya kusan minti talatin tsaye a wurin zuciyarshi be yi sanyi ba ji yake kaman an saka zuciyar a tukubar tsire tsabar Azaban zafin da yake mishi, why? Why? Why khair yake ta nanatawa da kyar ya samu yayi wanka zazzafan zazza'bi na rufeshi sbd abinda ya dami zuciyarshi da kuma ruwan sanyin da ya zubawa kanshi na about 30 minutes, a bayin ya kwa'be kayanshi tare da fitowa d'aure da towel ya zube kan gado yana lullu'buwa jikinshi kaman wuta.
Cikin tashin hankali haidar ke ta zarya a kofan d'akin don bugawar duniya musharraf ya ki bud'e mishi about 2hours kenan da shigowarsu tare ya barshi don yana tunanin yana son samun space in ya ware se ya dawo yaji abinda ke faruwa, amma har anyi hotuna mutane duk sun watse an koma gombe don shiryawa dinner yanzu a gidan daga momma se su dadda da su uncle Ahmad, momma ma ta shirya zata wuce kenan ita da hajiya ruqayyah.
Da sauri haidar ya fita ya tare ta yana cewa "momma, maami akwai matsala" Da mamaki suke kallonshi a tare sukace "matsalan me? Ina musharraf?" Shiru yayi na mintuna kan ya fad'a musu abinda ke faruwa momma da tun d'azu take fad'an kin zuwan musharraf a d'auki hotuna kuma tayi ta kiran layinshi be d'aga ba, a rude tayi d'akin suka rufa mata baya itama maganan duniya musharraf be bud'e ba.
Su bappa ta kira a lokacin har hawaye ya fara zarya idanunta me musharraf ya gani haka? Da spare key din part d'in mamaji yazo lokacin duk waenda suka saura a gidan sun cika kofan, bud'ewa uncle Ahmad da ya kar'bi key din yayi a tare suka fad'a d'akin cikin wani hali suka samu musharraf da yasa momma kusan fad'uwa yana kwance ne kawai shi da gawa ba maraba kuka ta saka tana sulalewa kasa, dadda ce ta kamata haidar ya karasa da gudu ya ta'ba pulse dinshi yaji yana har'bawa a hankali ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "he's alive we just need a doctor" uncle nasir yace "saka mishi kaya Aliyu se mu wuce cikin gombe kawai" nan suka fita dadda na rike da momma da ta kasa dena kuka se kace an ce mata musharraf din ya mutu.
Cikin lokaci kankani sukayi asibiti dashi inda suka bar mamaji, diddi da dadda a gidan, uncle Ahmad, uncle nasir, hajiya ruqayyah, bappa, momma se haidar ne suka wuce dashi, cikin hanzari akayi emergency dashi Doctor Aslam da wasu doctors din suka fad'a d'akin, sunanan zaune kusan hour uku a lokacin har magrib ya gabato doctors basu fito ba, uncle Ahmad ne ya d'aga waya ya kira marwan kai tsaye yace mishi "a fasa dinner din nan musharraf na asibiti ba lafiya" cikin damuwa yake tambayar me ya sameshi uncle Ahmad ya sanar dashi doctors basu fito ba har yanzu.
Abunka da gidan buki nan take maganan ya bazu ba dinner amma ance za'a kai amare gidansu a daren sbd musharraf ba lafiya shiyasa ba za ayi dinner ba, mutane dayawa sunji haushin hakan amma ya suka iya, khairi kwance a d'aki dada na zaune gefenta tana mata er nasiha da kad'an kad'an akan zaman aure don su se gobe zasu wuce Abuja a tsarin da sukayi tun farko don a Abuja aka shirya duk wani kayan d'akinta sbd musharraf be da wani gida anan part d'inshi kuma yayi karami amma In sun zo nan zasu dinga sauka.
Amrah ce ta fad'o d'akin ko sallama babu tace "Khairi musharraf ba lafiya yana asibiti" a zabure ta mike ta zauna tana dafe kirji tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun me ya sameshi? Amrah me ke damunshi?" Amrah tace cikin damuwa har yanzu doctors basu fito ba almost 3 hours kenan a sume aka sameshi a d'akinshi na chan dukku" hawaye ne ya fara gangarowa khairi me ya sameshi har haka bayan basu wuci awa shidda da magana dashi ba wayanta ta d'auko ta kunna fuskan hotonshi ne sanye da kayan daurin auren na d'azu yana gyara babbar riganshi aka d'auka fuskanshi cike da murmushi.
Kuka ne ya kwace mata tana ji dada na ta mishi adu'ar samun lafiya, Khairi tace "Dan Allah dada Ina son zuwa na dubashi" dada tace "Ashe baki da kunya? Kina Amaryan ko fah gidanshi ba'a kaiki ba, bama haka ba ga en buki ba wadda ya tafi" kuka me sauti khairi ta sake tare da komawa ta kwanta tana nan kwance har su Amrah suka tafi kai nuriyyah din momma tace kar suje asibitin su raka yarsu ta kuma wakilta hajjiya ruqayyah tazo tayi mata fad'a dukda gidansu Marwan da gidansu duk abu d'aya ne yayisu amma seda hajiya ruqayyah tayi mata fad'a sossai kaman yadda momma zata mata kan aka tafi da ita se kuka take gidan duk an tafi kai nuriyyah yayinda waenda suka rakata In sun ajiyeta zasu raka maryam daga chan su dunguma raka zainab.
Bayan sun tafi ne hajiya ruqayyah ta shiga wurin dada, tana d'aura idonta akanta seda jiri ya so yarda ita wacece wannan haka me tsananin kama da innanta kukan da khairi keyi ne yaja hankalinta tayi sallama a sanyaye dada ta amsa hajiya ruqayyah de ta rud'e hakan yasa ta d'aga waya ta kira innanta tace "inna naga wani abun alajabi a gidan hajiya fatima" daga d'aya bangaren aka ce "ke kam ko yaushe zaki girma oho ruqayyah, wani irin abun alajabi ne da ze sa ki kirani a waya kina fad'amin" hajjiya ruqayyah tayi murmushi kan tace "naga me kama dake wallahi har muryanku iri d'aya" Da sauri Hajiyar dake zaune a wani tangamemen parlor ta mike tace "da gaske ruqayyah kar ki saka min ran ganin indo ko danginta In zo In samu ba haka bane" hajiya ruqayyah tace "nima wallahi ban tabbatarba amma gamu nan zuwa" ta fad'a tana kashe wayan.
Kallon khairi tayi tace "ummulkhairi tashi dan Allah ki bani Aron dadanki muje innanmu ta ganta wallahi suna tsananin kama" Khairi tace "ba komai Maami muje In raka ku" kallon dada tayi tace "dada itace hajiya ruqayyah da nake baki labari maami" godiya dada zata fara mata dukda maganganun da taji matar tayi ya matukar d'aga mata hankali da sauri tace "ba yanzu ba Dan Allah muje na san inna na chan tana zullumi" kama dada tayi da kanta suka fice khairi na binsu a baya har motan hajiya ruqayya driver yaja.
Wani unguwa da khairi bata ta'ba shiga ba suka shiga tare da horn a kofar wani katon gida, gateman dinne ya leko ganin motan gidan hajiya ruqayyah yasa ya koma ya bud'e suka shigo masha Allah gidan babba ne sossai gidan sama guda biyu suna facing juna se wani karamin part flat dake tsakiyarsu daga baya akwai wani flat din bayanshi wadda suna bangan kwanonshi, a parking lot driver yayi parking suka fito gidan shimfide da interlocks ga flowers ko ta Ina.
Karamin flat dinnan hajiya ruqayya ta nufa dasu tare da tura kofan babban parlorn da sallama, da mamaki khairi ke kallon farar bafullatanan dake zaune sanye da glass a idonta gefenta sanda ne me kyau da alamu shi ke taimaka mata wurin tafiya tana d'aura ido akan dada ta mike har gabanta hajiya ruqayyah takai dada tace "kin ganta inna baki ga kamanku ba?" Kuka inna ta fara tana rike hannun dada Haka kawai dada taji matar ta shiga ranta irin sossai din nan.
Musamman yadda ta rike hannunta take kuka dukda ba kallon matar take ba bayan tayi kukanta ma ishi kan ta zauna tana zaunar da dada gefenta khairi ma zama tayi inna tace "gayamini wacece ke? Me sunan mahaifinki da mahaifiyarki? Daga Ina kike haka kikayi kama da kanwata sossai?" Dada batayi musu ba ta bata labarinta inda ta fad'amata sunan mahaifinta bata san sunan mahaifiyarta ba sede ta fad'a mata kauyen da aka aurota.
Cikin farin ciki inna tace "ke 'yar indo ce wallahi don Ali gamji mahaifinmu yaba aurenta tana da shekaru sha hud'u, kuma fulani me yawo ne sossai da shanukanshi, na d'auka har abada bazan ga jininta ba, Alhamdulillah Allah yaji kanta ya gafart mata" kallon hajiya ruqayyah tayi ta tambayeta "ke ruqayyah Ina kika samo su?" Nan hajiya ruqayya ta bata labarinsu inda momma ta bata, seda tayi hawaye ta kama khairi ta rungume murnan da khairi da dada suka shiga ba kad'an ba dukda dare yayi kusan goma hajiya ruqayyah ta kira momma ta fad'a mata Ashe su khairi en uwansu ne iyayensu mata uwarsu d'aya ubansu d'aya gashi yanzu ta kawo ta wurinta, dukda tashin hankalin da momma ke ciki hakan be hana ta nuna jin daadinta ba sossai tace a bata dada, ta taya ta murna khairi kam dama duk murnan da takeyi zuciyarta a chunkushe yake da rashin sanin halin da mijinta ke ciki, tana ji hajiya ruqayya ta tambayi ya jikinshi momma tace "hmmm gashinande har yanzu be farfad'o ba doctors din sun fita amma ba wadda yace mana komai" Adu'a hajiya ruqayya tayi mishi kan ta mikawa inna tayi mishi adu'a itama yayinda momma ta tayata murna don duk wadda ke tare da inna se ya san labarin indo.
Inda inna ta roka su khairi su kwana wurinta zuwa gobe se ta kawo mata khairi ta d'auki nabeel da nabeela da dada, dukda momma bata so haka ba taso ta zauna da su dada har mutuwa ya raba amma ya ta iya jini yafi gaban komai aka ce blood is ticker than water kuma ta san dadan ma zata fi son zama da en uwanta da "Toh inna" kawai momma ta amsa tare da musu seda safe.
Khairi kam hawaye ta dinga sharewa a fakaice ita kam tana son ganin mijinta wallahi inna dake ba masu aikinta umarnin abubuwan da zasu kawowa su khairi ce ta lura cikin masifa irin ta tsufa tace "eyeeeee kunga marar kunya, 'yar zamani yanzu akan wanchan sarkin had'e ran kike kuka? Mutum kullum fuska kaman an aiko mai sakon mutuwa ko kyauta aka bani shi bazan kar'ba ba sema In kai kasuwa amma shine kike 'bata hawayenki?" Shiru khairi tayi tana tura baki murmushi hajiya ruqayyah tayi kan tace "daughter rakani mota In tafi gida" mikewa khairi tayi ta raka ta.
A hanya hajiya ruqayya tace "ba kuka zaki dinga yi mishi ba ki mishi adu'a in shaa Allahu ze samu lafiya and I promise yhu gobe before eight zanzo mu tafi tare sannan karki damu da inna fah In tana miki irin maganganun d'azu a wasa takeyi kuma dama kullum In musharraf ya rako haidar wurinta se sunyi fad'a" murmushi khairi tayi tace "Toh Maami" kallon two storing buildings din dake gidan tayi tace "ga gidan uncles dinki guda biyu yayyuna kenan da safe duk zaki gansu" Kai khairi ta gyad'a Bayan sun isa mota tayiwa maamin seda safe kan ta koma.
Nan inna ta dinga hidima dasu ina za'a d'aga ina za'a saka, har seda dada ta hanata da kyar ta barsu ta je ta kwanta, suma kwanciya sukayi a katon d'akin da ta saukesu me kama da aljannan duniya don ba abunda babu a d'akin, bayan dada tayi bacci ta dinga kiran layin musharraf amma a kashe haka ta tasa hotunanshi na wayanta tana kallo da taga baze anfaneta ba kawai ta mike ta fara kai kukanta ga Allah har seda taji bacci ya kamata sossai kan ta kwanta bayan tayi adu'an bacci.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️8️⃣5️⃣▶️8️⃣6️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Washegari bayan sunyi sallahn asuba inna ta shigo suka bude shafin hirar indo da dada, ta bata labarin lokacin da aka aurar da indon ita bata sani ba tayi aure anan cikin gombe zuwa billiri kawai tayi ta samu an aurar da kanwarta tayi bakin ciki sossai gashi iyayensu su biyu suka haifa, a lokacin ta haifi 'ya'yanta duka uku Muddasir, Muzzammil, da ruqayyah, bayan auren indon da shekara biyu Allah ya kar'bi ran iyayensu sanadin gobara yanzu en uwa ne kawai a 'billiri 'ya'yan muddasir bakwai yayinda muzzammil ke da shida dukkanninsu mata bibbiyu suke da se 'ya'yan ruqayyah biyu.
Misalin karfe takwas part d'in inna ya cika da jikokinta a lokacin ta saka dada da khairi sunyi wanka da breakfast duk wadda ya shigo zatayimishi bayanin dada da khairi kuma se aka ci sa'an basu da wulakanci kwata kwata familyn da murna suke taran su en matan suka ja khairi zuwa cikin gida duk da yadda take suku suku sbd bata san halin da musharraf yake ciki ba.
Suna zaune a d'akin en matan da ke part d'in uncle muddasir da suke cewa dad shima sun gaisa da khairi a lokacin da suke shigowa be santa ba kuma yaran basu fad'a mishi wacece ba, hira sukeyi amma gabad'aya hankalinta baya tare dasu su shidda ne en matan duk kuma sa'annin ta ne hafsat da taci sunan inna, Asiya, fatima, firdausi, Asma'au se hauwa, hira sukeyi kaman ba 'yan kishiyoyi kuma ubbanninsu daban daban ba hakan ya tabbatarwa khairi tarbiya da had'in kan dake gidan ganin taki sakewa se kawai suka koma hiran su ya sa su ci gaba da hiransu su ya su akan waliman da zasuyi na kammala secondary, wani karamin yaro ne ya shigo da gudu yana cewa "Adda Asma'u wai kizo inji Anty Ruqayyah" kan Asma'u ta mike khairi ta mike hauwa tace "har mun gama hiran kenan?" Khairi tace "A'a In na dawo zamu ci gaba, fita zamu yi da Maami" Firdausi tace "Toh se kun dawo" sauran ma suka ce se ta dawo da asma'u suka fice zuwa part d'in inna tana kara yi mata bayanin yaran gidan amma jinta kawai khairi ke yi bata fahimta.
Suna shiga ta duka har kasa ta gaida Maami cikin fara'a ta amsa tana tambayarta ya bakunta murmushi kawai tayi tana kallon hafsan maamin da suka rungume juna da Asma'u tana saketa itama tayi hugging dinta tana cewa "welcome to the family sis" murmushi kawai khairi tayi tare da zama kusa da inna, Maami ta kalli khairi tace "kinga nace zanzo 8 gashi har 8 ya wuce, tashi muje na cewa hajiya fatima Ina zuwa" mikewa khairi tayi da sauri dama da hijab a jikinta inna tace "er kusun uwa daad'i miji".
Kai ta dukar tana cewa "dada mun tafi" dada tace "ki gaisheshi da jiki ki kuma gaida mommanku" bata amsa ba sbd masifar inna se ma ficewa da tayi Maami ta bi bayanta tana cewa "se mun dawo" bayan fitansu Asma'u tace "yanzu inna khairi na da aure?" Inna tace "Eh mana ita kuma aka gayamiki kaman waenchan dalotayen yayyunkun nan ne da zasu ce se sun gama makarantar jami'a kan suyi aure, Toh da aurenta jiya da safe aka d'aura mata aure".
Asma'u tace "Kai inna tambaya fah d'aya na miki amma kin ban amsa uku, Toh me yasa ba'a kaita gidanta ba ta Kwana a gidan nan?" Hararanta inna tayi tace "ban sani ba" Hafsa tace "kyale innan nan muje zan fad'a miki" fita sukayi hafsa na mata bayanin abinda yasa ba'a kaita ba.
Da sallama hajiya ruqayyah ta tura d'akin asibitin khairi na biye da ita a baya momma ce kad'ai a d'akin tana zaune kan kujera shi kuma yana kwance sambal akan gado daga shi se dongon wando baki, fatanshi yayi fari sossai fuskanshi fayau idonshi a lumshe kaman me bacci amma sam ba baccin yake ba duniyar tunani ya fad'a me yayiwa ubangiji da ya tsinci kanshi a wannan rayuwa, da sauri kuma yayi istigfari ko ya yayi da idonshi hoton da aka turomishi yaki barin idonshi sam.
A jikinshi yaji zuwanta wurin me makon yaji sauki se yaji wani irin haushinta na mamaye zuciyarshi yana jin muryanta kuma a lokacin da take gaida dada se yaji kaman ya had'iyi zuciya ya mutu ya rasa me yasa sonta yaki ko da raguwa a zuciyarshi kaman yadda ya tsani surraya lokaci guda, wani kunyan momma taji tana ji dukda sabon dake tsakaninsu, bayan sun gama gaisawa ne hajiya ruqayyah tace "ya mai jikin dai har yanzu be farka ba?".
Momma tace "da sauki kuma tun tsakar dare ya farka amma wallahi ba yadda banyi ba ya gayamin me ya sameshi me ke damunshi yaki fad'a min komai bayan