Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
ba me tsada bane amma d'an uwanta ya fidda d'inki a wurin A shape gown yayi mata da yaji pattern na kayan daga sama har wurin cikinta daga wurin kuma har kasan rigan stones ne baja baja dayake atamphar sea blue ce me adon orange a jiki se ta yafa orange gyale na wani dogon riganta cikin wadda hajiya ruqayyah ta bata, orange flat shoe ta zurawa kafanta wadda na Adda nuri ce ta bata kyauta yau da safennan da Amrah take had'a mata kayan da zata saka suka rasa takalmi.
Fuskanta fayau ba d'igon komai a hakan kuma tayi matukar kyau kaman a sace, dayake kanta ba d'ankwali se gyalen ya zauna sossai akan silk long hair d'inta irin na fulani da baya kitsuwa ta dad'i, sallama sukayi da diddi inda suna fitowa suka gamu da su bappa sallama suka musu suma suna ci musu albarka suka wuce ta so su shiga suyi sallama da dadda amma tana tsoro tunda shi uban gayyan ko part d'in be kalla ba.
Suna shiga ya tada motar tana ji sadda yayi adu'ar shiga abin hawa da na matafiya hakan ya tuna mata itama tayi, a natse yake driving motan shiru sbd ba abinda ke kunne hankalinta gabad'aya ta mayar kan hanya tana kallon wurare wani irin murd'awa da taji maranta yayi ya sata ambaton "innalillahi wainna ilaihi rajiun" Da sauri ya kalleta da kyar ya iya cewa "are yhu okey?" Kai ta gyad'a mishi yace "words" tace "am fyn" dafe maran tayi tana tunanin rabonta da period tun last three months.
Dama haka yake mata inda aka cewa Abbanta aljannunta ne ke mata wasa da period don idan watanta yayi se tayi ta ciwon mara amma ba jini, tun suna neman magani har suka hakura, idan ta shafe wata biyu wata uku batayi ba baze ce ga randa ze zo ba amma In ya tashi zuwa kaman zata mutu da ciwon mara har karin ruwa ake mata, ajiyar zuciya ta sauke tana adu'ar Allah ya sa kar ya fi karfinta kan su isa, jujjuya kai ta fara hannunta na kan maranta gani take kaman ba driving yake yi ba gashi tana mugun rushing Allah yasa kar ta 'bata mishi mota kan su isa.
Duk abinda takeyi hankalinshi na kanta kuma ya fahimci abunda ke damunta amma se yayi kaman be san halin da take ciki ba, se ma cd da ya saka a motar ya kunna wakar All ever need na Austine mahone, ya fara bi a hankali, kasa jurewa tayi yasa ta fara mutsu mutsu hawaye suka fara tsere a saman fuskanta jujjuya kai kawai take tana ambaton sunan Allah, dukda cikin zuciyarshi cike yake fal da tausayinta hakan be sa ya tsaya ba don be san me ze mata ba.
Wayanshi ya d'auka ganin sun shiga wani d'an kauye ya kira Amrah don ya san itama tana wannan ciwon dukda be kai ko kwatan na khairi ba kuma yana ganin maganin da take sha amma be san sunan ba, tana d'auka ya tambaye ta maganin Mp fad'a mishi tayi ba tare da wani dogon nazari ba, fita yayi ya tambaya ko akwai chemist anan aka nuna mishi wani d'an karamin chemist zuwa yayi ya saya tare da dawowa motan da sauri fuskanshi na nuna damuwar halin da take ciki.
Ruwa ya d'auka tare da 'ballan maganin ya bata da kyar ta sha se aikin kuka takeyi ajiyar zuciya ya sauke tare da tada motar da hannu d'aya d'ayan hannun kuma ya sashi cikin nata yana matsawa a hankali, dayake ya kwantar mata da kujeran hakan ya sata kwanciya ta dukunkune tana cin azabar period pain, a haka bacci ya kwashe ta tana jin yadda d'umin hanunshi ke ratsa ta suna shigowa cikin gombe tana farkawa a gigice tare kokarin bud'e kofa.
Da sauri ya parker motar be gama tsayawa ba ta sauka da gudu ta fara sheka amai goran ruwa ya d'auka tare da fitowa yana mai tsananin tausaya mata yazo ya riketa, ko gyale babu a kanta tsabar ciwo bata san ta jefar da shi ba, tana gama aman taji kafanta ya kasa tsayuwa sbd ciwon da sukeyi wani murd'awan da cikin ya kumayi yasa ta saki kara tare da sulalewa ta zube a jikinshi a sume, a matukar rud'e yake jijjigata ganin da gaske suman tayi yasashi d'aukarta da gudu zuwa mota zagayawa yayi ya shige tare da figan motan zuwa FMC duk wadda ya ganshi kaucewa yake sbd irin gudun da yakeyi cikin lokaci kalilan ya isa inda ya fita da sauri ya d'auketa yana kiran doctor da gudu nurses suka kawo gadon marasa lafiya suka kar'beta tare da yin emergency da ita, dafe kanshi yayi yana kiran sunan Allah.
*kuyi hakuri na rashin jina Kwana biyu idon ne ya karye 👓 ba kuma zan iya typing ba shi ba amma an gyara zaku ci gaba da jina In shaa Allahu kaman ko yaushe*
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
Page➡️7️⃣3️⃣▶️7️⃣4️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Bayan kaman 40mins doctor Aslam ya fito yana kallon musharraf yace "muje office" bin bayanshi yayi zuwa office Bayan sun zauna yace "dr ya jikin nata?" Doctor yace "da sauki sossai tana bacci ne yanzu haka sbd alluran da aka mata" fuskanshi d'auke da damuwa yace "Amma ba yadda za'ayi a cire mata ciwon gabd'aya Ina nufin next month kar tayi haka?" Doctor Aslam yace "itama sistern ka ce?" Dayake Doctor Aslam ya san en gidansu gabad'aya, har ze ce er aiki se yaji bakinshi ya furta "wacce zan aura" murmushi dr yayi yace "masha Allah, ciwon mara na period pain ba yadda zamu yi mu cire mata se Allahn da ya d'aura mata, wasu matan suna denawa ne daga sun yi aure wasu kuma har se sun haihu yayinda wasu har abada, yanzu de mun yi mata allurai da karin ruwa ruwan na karewa zaku iya tafiya".
Godiya ya mishi tare da amsan bill d'insu ya fita, biya yaje yayi kan ya dawo d'akin da aka kwantar da ita dayake sun san en gidansu duk amenity ake kwantar da su hakan yasa da ya shigo da khairi aka bata amenity, a bakin gadon ya zauna yana kallon fuskanta da yayi fayau farinta ya fito sossai, baccinta ya mishi kyau sossai musamman yadda idonta da bakinta suka bud'e kad'an.
Seda ya gama morewa kallonta kan ya koma kan plastic chair ya kishingid'a tare da lumshe ido yana tuna randa sonta ya fara shiga zuciyarshi, be san taya ba be san ta Ina ba kuma be san yadda akayi ya karya alkawarin da ya d'aukarwa kanshi da zuciyarshi na hana kanshi son wata 'ya mace ba, be san yadda akayi ta kakkarya duk wani takunkumi da kwado da ya sawa zuciyarshi ba ta shige tun kallo na biyu da ya mata randa ake shirin keta mata haddi, tunda kuwa yaji labarinta se yaji kaman ninka mishi sonta da tausayinta akayi yana sonta har be san iya adadi ba.
Yana kaunarta da dukkan zuciyarshi, babban abinda yasa ta zama numfashinshi kuwa shine yadda take matukar son little tabbas duk wadda yaso little to shi ya so, abinda ya hanashi bud'e mata zuciyarshi kuwa shine yana tsoron sabarwa kanshi rayuwa da ita da soyayyar ta tazo tayi betraying d'inshi irin surrayah, gwara ya zauna be d'and'ani zakin soyayyarta ba zuwa ya gama yarda da ita 💯% karan wayanshi ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya fad'a a hankali ya bud'e idonshi dake lumshe ya sauke su akanta gashinta me taushin bala'i dake baje akan pillown da take don tuni tayi wulli da ribbon da kuma gyalen ta, wayanshi ya zaro daga pocket d'inshi yana kallon caller id d'in ganin "first love" yasa shi d'auka tare da karawa a kunne yace "hello" momma daga 'bangarenta tace "lafiya son naga baku iso ba har yanzu" idonshi na kanta yace "yarinyar nan ce ba lafiya tana FMC" momma tace "subhanallah me ke damunta haka?" Yace "period pain, ku taho yanzu am on my way too sbd flight d'ina 1 ne and yanzu 12".
Da Toh kawai momma ta amsa tana kashe wayan, mikewa yayi ya karasa bakin gadon yasa hannu ya mayar mata da gashin goshinta dake yawo a fuskanta, cameran wayanshi ya shiga yayi mata pics sossai kan yayi pecking goshinta ya juya kenan yaji an riko hannunshi a hankali ya juyo se yaga duk cikin bacci ne sabule hannunshi yayi ya juya ya fice cikin takunshin nan me sace zuciyar mata.
A parking lot yayi parking tare da fita straight wurin su momma dake shirin fita asibiti ya tsaya da ita da Amrah ganinsu ne yasa drivern tsayar da motan tare da sauke glass, momma tace "har ka dawo?" Kai ya gyad'a mata tace "Toh Allah ya tsare ya bada sa'a, a de dinga kiyayewa zamu yi waya kan ka tashi don na san ba asibitin zaka koma ba" kwa'be fuska yayi ya ki magana se kallonta da yakeyi.
Dafe kai tayi tace "yanzu kai yaro ne musharraf, da kullum se na maka nasiha kan ka tafi? Kuma se na ga tafiyarka?" Kuma 'bata fuska yayi yana kallon driver da Amrah ganin hankalinsu baya kanshi yasa yayi mata alamun plz da lips d'inshi, fita tayi tana cewa Amrah "kira nuriyyah a waya ku tafi in ya tafi zan zo, Miemie kuma ta kula da yaran nan da dada" a waya Amrah ta kira nuri yayinda momma ta bi Bayan musharraf zuwa part d'inshi, a parlor suka zauna tayi mishi nasiha sossai kamar yadda ta sabar mishi tun farkon samun aikinshi bayan ta gama ya mike yaje ya d'auko briefcase dinshi da ya zuba muhimman abubuwanshi sharp sharp.
Be yi sallama da little ba don ya san kuka zatayi kuma gashi khairi bata gida bare ta sata yin shiru da sauri idan su Amrah ne har ya isa Abuja tana kuka, dada ya shiga ya sallama itama adu'a ta mishi ya fito gudu gudu zuwa mota inda momma da driver ke jiranshi duk yadda momma ta so mishi maganan khairi sharewa yayi ya dinga basar da maganan har suka isa Airport har ciki ta raka shi tukun sukayi sallama ta wuce asibiti.
Bayan sati biyu
Rayuwa yayiwa su khairi daad'i sossai suke samun kulawa daga wurin su momma har momma ta samu wata me aiki yanzu ba abinda khairi take se in ita ta sa kanta da kanta, karatu kawai suka dukufa dayi ita da Amrah, wanchan sati momma tayi musu sayayyar kayan sawa sossai musamman dada, da su nabeel itakam har kayan kwalliya dukda ba kwalliyan take yi ba, su nabeel ma sun koma school d'insu duk tare suke zuwa kuma suke dawowa dukda ba koyaushe suke fita da sassafe ba.
Bata ta'ba waya da Hamma musharraf ba sede taji suna waya da en uwanshi har nabeel da nabeela suna waya su kam ma kullum a wayan little se dada ma sun ta'ba waya sau biyu, hakan kuwa sam be mata daad'i ta rasa dalili, sam kaman yau da ya kasance juma'a tana gyarawa momma d'aki taji wayan momman na ringing d'agawa tayi se taga "Son" a fuskan wayan hakan yasa ta San musharraf ne amma kuma momma bata nan ta fita ta mance wayan, share wayan tayi ya kira kusan sau hud'u kan ta d'auka ta 'bangaren shi yace cikin shagwa'ba "tun d'azu nake ta kira kinki d'auka motherrr" cikin daburcewa khairi tace "ba ita bace hamma" lumshe ido yayi yana jin wani natsuwa na shigarshi.
Yayi kewarta da muryanta sossai amma haka yake hana kanshi kiranta, a sanyaye yace "Toh wace ce?" Tura baki tayi a zuciyarta tace Lallai ma mutumin nan wato muryanta ne ze ce be sani ba a fili tace "ummulkhairi" Shiru yayi na mintuna kan yace cikin husky voice d'inshi "baki iya gaisuwa ba kenan" Da sauri tace "Ina kwana Hamma musharraf?" Yace "bazan amsan ba seda na roka?" Be jira cewarta ba yace "Ina momma?" Tace "ta fita ta manta wayanta a gida".
Shiru yayi na mintuna kan taji kit ya kashe wayan, ta'be baki tayi tare da ajiye wa ta ci gaba da gyaran d'akin bayan ta gama ta sauka zuwa d'akinsu a bakin gado ta zauna dada na garden da su nabeel da Miemie. Wayanta ta d'auko se taga text message ya shigo.
"There has never been and will never be a time when God will desert you. Place all your fears in him" ta karanta text d'in ya kai sau biyar ta rasa wa ke tura mata wannan message d'in yau na biyu kenan, last friday ma taga wani shigen wannan wadda aka rubuta "Fasten your seat beats, your life is soon landing in Happyland!".
Ta rasa wa yake turo mata wannan messages d'in ta kuma kira numbern sau biyu ba'a d'aga ba, ya akayi wannan ya san tana cikin damuwa? Duk da damuwan a da ne yanzu damuwarta d'aya, yaushe d'an uwanta ze dawo? Tana son sanin wani hali yake ciki In ma mutuwa yayi tana son sani sbd ta ci gaba da mishi adu'ar samun rahamar Allah.
Bayan dawowar momma ta sanar da ita Hamma ya kira kuma ta d'aga da Toh momma ta amsa mata Bayan ta haura da mintuna talatin ta fito take ce musu next week Friday musharraf ze zo tsalle su little suka dinga yi cike da jin daad'i itama sossai hakan ya mata daad'i a zuciyarta sbd tayi matukar kewanshi musamman ma kamshinshi me tafiya da zuciyarta amma tuna ko tambayanta be ta'ba yi ba In suna waya da en gidan, kuma ya tafi ya barta a asibiti amma ko ya jiki ya ki mata dukda bata kwana ba ma a ranar aka sallameta.
Ta 'bangaren musharraf kuwa a daddafe yayi sati biyun nan, zuciyarshi cike yake da sonta da kewarta da ya mugun bashi mamaki sam be zata ze yi kewarta haka ba, seda yaji muryanta me makon kewar ta ragu se kuma tayi mugun karuwa shi da yayi niyyan se lokacin aurensu ze d'auki hutu ya dawo amma se gashi yana shirin dawowa be kai ko wata da tafiya ba, system d'inshi dake sleep ya ta'ba se ga kyakyawar hoton ta ya bayyana kwance akan gadon asibiti wadda ya mata a ranar da ze taho, arrow key ya danna se ya tafi next tana tsaye tana serving abinci duk hankalinta na kan abinda takeyi, dannawa ya kuma yi se ga wani hotonta tsaye a kitchen tana girki wadda gefenta d'aya kawai ake iya gani tayi kyau sossi a hoton haka ya ci gaba da tafiya hotunanta kala kala duk kuwa bata sani ba amma sunyi masifar kyau.
Juma'a
Yau sun tashi da aiki sossai sbd dawowar shi yayinda suka riga suka fara waec tun last monday, yau basu da paper hakan yasa basu je makaranta ba inda nuriyyah ta tafi wurin aikinta Miemie kuma na school, daga ita se Amrah da momma se kuma sabuwar me aikinsu ce a kitchen d'in se aiki sukeyi suna hira lokaci lokaci har suka gama, pounded yam da egusi soup se waina da Miyar taushe da yaji tantakwashi se pepper soup na cow-tail da yaji cloves da garlic, daga karshe khairi ta mishi zobo, indo suka barwa wanke wanke da sharan kitchen din suka fice kowa ya fad'a wanka sbd huce gajiyar girki.
Bayan khairi ta fito daga wanka ta duba cikin kayanta ta zaro wani material d'inta me kaman atampha da akayimishi d'inkin fitted gown, sawa tayi a jikinta tare da shafa oil d'inta a hannu ta shafe bayan kunnenta da gefen wuyanta haka kawai ta tsinci kanta da shafa powder da red lipstick a bakinta tare da sa kwalli a idonta tayi kyau sossai kuwa abin ka da wacce bata saba kwalliya ba.
A parlor ta bar dada hakan yasa tayi komai cikin natsuwa amma kuma se ta kasa fita kunya sossai ya rufeta hakan yasa ta hau gado tayi kwanciyarta tare da ba kofa baya, tana nan kwance taji shigowarshi parlorn Amrah na mishi sannu da zuwa kin fita tayi tana ji suka gaisa da dada da kuma momma, momma tayi mishi iso zuwa dining tare da bud'e mishi kulolin pounded yam da egusi soup ya za'ba ta saka mishi tare da tsiyaya mishi zo'bo.
A natse ya fara ci, yana sa Loma d'aya a bakinshi ya san miyan nan ita tayishi haka zo'bon ma yana kur'ba ya san hannunta ne haka ya ci gaba da ci cikin natsuwa yana jin daad'in girkintan yana kuma mamakin me ya hanata fitowa yi mishi sannu da zuwa ya tabbatar In har tana d'akin chan to taji zuwanshi.
Har ya gama ci bata fito ba, hakan yasa ya mike ya fice daga parlorn zuwa part d'inshi yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya zuciyarshi fal tunaninta dukda suna gida d'aya, Bayan ya gama shiryawa ya fita zuwa garden a hankali yake zagayawa yana shakan sansayyar kamshin flowers da na kasa da garden d'in ke yi kaman ance kalli chan se ya ganta tana tunkaro inda yake tana tafiya tana lullumshe ido da alamu weathern na mata daad'i, ajiyar zuciya me karfi ya sauke yana me kara kallon fuskanta da ya mishi kyau fiye da kullum da sauri ya 'buya a bayan mango three dake gefenshi ganin zata bud'e ido Ai kuwa bata lura dashi ba tazo zata wuce wurin kenan taji an fisgo hannunta tare da juyata ya manna ta da jikin bishiyar hannunshi d'aya yasa ya zagaye cikinta yayin da d'ayan hannun ke kan bakinta da ke shirin tsala ihu.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763