Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
musharraf baya ta'ba boyemin komai" ta karasa da damuwa tuna irin damuwar da take hangowa a kwayar idonshi, hajiya ruqayyah tace "ki kwantar da hankalinki aminiya in shaa Allahu ze samu sauki kuma wtkl be son fad'amiki matsalarshi ne sbd kuna asibiti" momma tace "hmmm toh Allah yasa" ita kam khairi tsaye tayi tana mamakin me ya sameshi kuma me ke damunshi da har ya shigar dashi wannan hali.
Maganan momma ne ya dawo da ita daga tunaninta inda take cewa "daughter ki zauna dashi bari muje da hajiya ruqayyah gida sbd bakin da na tara" Khairi tace "toh momma" gyalenta ta yafa tana mikewa, hajiya ruqayyah ma ta mike a tare suka fita Bayan ta kalli fuskan musharraf tace "mun tafi" don ta san idonshi biyu ne kawai yasa ya amsa ta kasan makoshi, bayan fitansu khairi ta karasa bakin gadon ta zauna cikin kasa da murya tace "baby ya jiki?".
Shiru yayi kaman be ji ba ta kuma cewa "sannu hamma kayi breakfast?" Nan ma Shiru yayi a take hankalin khairi ya fara tashi bata daddara ba tace "Hamma musharraf" tsaki yaja yana juya kwanciyanshi tare da bata keya hawaye ne ya cika idonta se jin saukowansu tayi akan kuncinta komawa d'aya 'bangaren tayi tace "Hamma laifi nayi maka ne? Plz in wani abu na yi maka da ba daidai ba ka fad'amin In baka hakuri ba wai kayi fushi da ni ba" nan ma Shiru yayi d'an Shiru tayi tana tuna ko tayi mishi wani laifi da bata sani ba da sauri tace "ko don ban zo ba se yau?" Bata jira cewarshi ba ta kara da.
"Ka san mun sami en uwanmu? Ashe mahaifiyar maamin haidar Addan mahaifiyar dada ce" tsaki yayi tare da bud'e jajayen idanunshi yana kokarin mikewa yana taune lips hannu ta sa da niyyan taimaka mishi da sauri ya matsa yana cewa "don't yhu dare touch me" yayi maganan cikin danne hakwara da alamu controlling kanshi yake kokarin yi.
Baya ta matsa tana kallonshi, zama yayi tare da jingina bayanshi da pillow wuri d'aya ya kafawa ido yana ji a jikinshi kuka take ko be kalleta ba, wani abu yake ji ba daidai ba a zuciyarshi tuna irin wahalhalun da tasha ya fara daga farko har karshe to me ze jefata aikata zina da irin wannan rayuwar da tayi, ko de sbd ta taimaka musu da abinda zasu ci ko kuma samun wurin zama?.
Jin an turo kofan yasa shi kallon wurin se yaga haidar ne ya shigo, murmushi haidar ya sake ganin abokinshi zaune da alamu lafiya ya fara samuwa, yana zama yace "dude how far" yayi maganan yana mika mishi hannu kashewa sukayi amma fuskan musharraf ba ko d'igon fara'a yace "not too far friend" se a lokacin haidar yaga khairi cikin sake fuska yace "aa aa aa Amarya da kanta ce nan ai ban lura dake ba" a fakaice ta share hwayen fuskanta tana murmushi tace "Ina kwana?".
Yace "lafiya kalau sister ya gajiyan buki?" Tace "Lafiya kalau, Ina Anty hanan" yace "tana gida se anjima tace zata shigo, welcome home dear Maami ta ban labari" murmushi kawai tayi, kallon musharraf yayi da ya kara had'e rai yace "ka kula min da kanwa na gayamaka da tun kafin bukin na sani ma da ban baka ba se kayi biyayya" Kau da maganan musharraf yayi da cewa "Ina wayata?" Hannu haidar yasa a aljihu ya d'auko mishi tare da mika mishi kar'ba yayi yana kunnawa don kashe yake.
Sam be da shakku akan haidar ya san be bud'e wayan bama balle yayi bincike har yaga abinda be son kowa ya sani kuma ya gani, hira haidar da khairi da ta koma ta zauna akan plastic chair suka ci gaba dayi dukda hankalinta dake a tashe amma bata son kowa ya sani tana ganin karamin sa'banine kuma zasu shirya bata so ace daga aure har sun fara samun matsala da shi har mutane su sani.
Tambayoyi haidar ya dinga mata akan rayuwansu na da tana bashi amsa, har hiran randa aka so mata fyad'e seda ya tambaya da kuma ranar da kare ya bita a Arabian estate, bashi labari tayi a tsanake abinda ya kaita anan yake ce mata "Ai ranan na kama mijinkin nan ya rakani gidan sister dina, au sister dinmu dani da ke 'yar uncle mudasir babba dake aure achan Adda fadeelah" Da mamaki tace "inda kuke zaunen shine kofan gidanta?" Yace "Eh kin shiga ne?" Tace "eh matar na da kirki sossai ba kad'an ba" ta bashi labarin yadda sukayi da ita yana murmushi yace "ai haka take da kirki wallahi ta jima da aure amma Allah be bata haihuwa ba har yau" Tace "Allah sarki Allah ya bata" yace "Ameen".
Su Amrah ne suka shigo gabad'ayansu harda nabeel da nabeela da gudu sukayi kanta suka rungumeta tana dariya Tace "chutu'be" suka had'a baki wurin cewa "Adda khairi good morning" Tace "morning how are yhu? Ina pretty?" Nabeel yace "tana zuwa da Adda Miemie, Adda Ina kuka tafi ke da dada?" Khairi tace "wurin innan dada kakanku kenan" nabeela tace "dama dada nada mama?" Ta fad'a cikin waro ido Haidar ya lakaci hancinta yace "wa ye kika ta'ba ji ya fad'o daga sama" dariya sukayi kan suka gaishe shi ya amsa a lokacin Miemie sun shigo Amrah kuma na gaisawa da khairi wurinshi su nabeel suka koma suna tambayanshi me ke damun shi khairi ta zata suma baze amsa musu ba se kuwa ta ga akasin haka cikin sake fuska ya amsa su, haka da su Amrah da miemie ya amsa musu fuskan ba laifi.
Har cewa Amrah yayi ta sa mai abinci, da sauri khairi ta kalleshi amma ko 'bangarenta be kalla ba haka Amrah ta sa mishi breakfast yaci kaman baya so bayan ya gama wai ze yi wanka haidar ya taimaka mishi ya raka shi toilet din ya dawo, haka tana ji tana gani suka wuce ta gefenta kaman be santa ba, wayanta ta d'auka ta duba last chats d'insu zallan soyayya ne haka msg na karshe da ya turo mata shine na d'aurin aurensu Toh me ta mishi?.
Sossai ta tsinci kanta a matsanancin damuwa to ba wai ya santa bane a matsayin mace bare tace dama chan jikinta yake so ya kuma samu ze mata abinda ya ga dama, Ashe ya manta be d'auki kayan da su Amrah suka kawo mishi ba hakan yasa yayi magana daga chan akan haidar ya miko mai, haidar kuma se ya mikawa khairi yace "sister bashi" kar'ba tayi ta mike ta nufi cikin bayin knocking tayi se yace "come in" duk a zatonshi haidar ne, ita kuma batayi magana ba ta tura kofan ta shiga.
'Dago kan da zaiyi kenan se suka had'a ido d'an fara'an da ya saura a fuskanshi ya had'iye tare da had'e rai kaman an aiko mai da sakon mutuwa hawaye ne ya fara zuba a idonta daman kukan na kusa cikin kasa da murya tace "Don girman Allah hamma ka fad'a min laifin da na maka In baka hakuri wallahi ban san me nayi maka ba, fushinka na azabtar dani ka sabar min da kulawa da soyayyarka a kullum me yasa zaka gujeni yanzu?".
Kayanshi ya fisge ya fara sakawa kallon shi takeyi daga shi se towel a kwankwaso ginennen jikinshin nan ya fito sossai ba kaman a kaya ba kaman d'aura mishi akayi, ganin yana shirin cire towel din yasa tayi saurin juyawa se akan idonshi tsaki yaja a fili yace "kaman da gaske" yana sa buttons din farin riganshi da ya d'aura akan Ac Milan trouser black and red yace "I really hate yhu ummulkhair, yhu deceived me and my family and ki jira sakayya wallahi kin cuci zuciyata cuta mafi muni a duniya da ba wadda ya ta'ba yi min irinshi amma Ba komai yadda kika tsara haka za'a ci gaba da tafiya" murmushin takaici yayi kan ya furta "green snake under green grass" ya juya ya nufi fita amma jikinshi da ba karfi yasa yayi tagal tagal kaman ze fad'i da sauri ta tare shi dukda idan da faduwan zeyi sede su fad'i dukkansu don bata da wannan karfi na taranshi, da sauri ya sa hannu ya turata har ta buge da jikin gini kan ya ja tsaki ya fice a hankali.
kuka ta sake tana tana dafe goshinta da tafin hannunta ba wai kukan bugewa da tayi takeyi ba kuka take akan maganganun da ya gama fad'a mata me tayi da zafi haka innalillahi wainna ilaihi rajiun ta dinga maimaitawa tana kuka da kyar ta samu kukan ya tsaya ta wanke fuskanta ta fito kallo d'aya ya mata ya d'auke kai, haidar ne ya tambayi me ya sameta tace kwaro ne ya fad'a idonta, haka tayi yinin ranar sukuku a asibiti a gida kuwa har dada da inna sunje wurin momma dasu Alhj mudan da Alhj muzammil godiya sossai sukayiwa momma inda tasa aka had'a kayan nabeel da nabeela da kuma na dada khairi kam nan zata ci gaba da zama har se mijinta yaji sauki su wuce Abuja.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️8️⃣7️⃣▶️8️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Two weeks later
Rayuwa yaci gaba da tafiya wa khairi a birkice sbd bata san laifinta ba ake hukuntata hakan kuwa yafi komai mata ciwo musamman In ta tuna irin soyayyarsu me kashe zuciya da irin kulawar da yayi alkawarin nuna mata bayan aurensu amma gashi yanzu kwana goma sha biyu da samun Lafiyanshi.
Sunyi kwana biyu a gida tare da su momma kan ya shirya da niyyar komawa Abuja inda yace ze barta nan, nan fah momma da bata gane mishi ba kwata kwata a kwanankin tace be isa ba kaman yadda suka tsara da matarshi da little zasu tafi a sata a makaranta achan haka khairin ma results dinsu na fita ze nemar mata admission a chan.
A haka be so ba suka taho Abujan a maimakon jirgin da yayi niyyar bi ya fasa suka tafi a mota, tunda suka je a kwana goman da sukayi zatayi girki ta jera a dining amma ko kallon arean dining din baya yi, haka ze wuce sama dama d'akin kasa ya bata ya kuma ce kar ta kuskura ta hau mishi samanshi ko da bakin wasa.
Da little kad'ai yake d'an sakewa har ya ja ta saman wani lokacin har kwana takeyi amma khairi bata ta'ba hawa ba, yaron dake gyara mishi tun kan zuwanta shi ya ci gaba da gyara mishi abun na damunta ba kad'an kad'an ba amma ba yadda ta iya be bata fuskan tambayanshi laifinta ba bare ta kare kanta.
Kaman yau Bayan ta gama shirya little da sabon uniform d'inta na Hempstead da aka maida ta ta fara daga primary one, janta tayi zuwa kan dining tare da zuba mata irish and egg se tea da tayi musu ta fara ci ita kuma ta koma kitchen ta had'a mata lunchbox dinta, ta fito dashi ta ajiye a gefen jakanta dake d'aure saman dining se surutu take zuba mata amma da kyar take amsawa sbd yanzu magana ma na neman gagaranta, takun saukowanshi ta fara ji ko bata juyo ba kamshinshi da ya bule parlorn ya tabbatar mata da ya had'u yadda ya saba cikin suit dinshi na office.
A hankali ta juyo ta kalleshi aiko a shirye yake cikin 3 pieces suit d'inshi brown da farin shirt se brown necktie hannunshi rike da black brief case dinshi fuskan nan a matukar had'e kaman kullum tun dawowarsu maroon lips dinshi a cikin bakinshi yana d'an tsotsa ya karasa dining din gaban 'yarshi ya tsuguna yayinda ko matan bata ishe shi kallo ba.
Little tace "good morning paapi" yana d'an sake fuska yace "morning sweetheart how was your night?" Tace "fantastic paapi, mom tace kullum In zanyi bacci se nayi alwala In kuma yi adu'a shed'an baze zo kusa da ni ba and she's right I'm always sleeping good with no dreams and shetan around me".
Satan kallon khairi yayi se yaga kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta kallon seconds yayi mata ya fahimci raman da ya bayyana a jikinta fatanta da yayi wani irin kyau da yalki sbd gyaran da aka mata na buki se d'aukar ido yake lumshe ido yayi yana tuna laifinta ya gama yanke shawaran abinda ze yi kuma In shaa Allahu ze sanar da ita a yau ba se gobe ba, kallon little yayi yace "that's good but she's not your mom, your real mom is already gone".
Da sauri khairi ta kalleshi hawaye na cika idonta little tace "but paapi yhu told me that she's my mom and haka granny ta fad'amin that's why muke rayuwa gida d'aya a tare but meyasa yanzu zaka ce she's not?" Had'e rai yayi yace "na riga na fad'amiki am off to work" hanyar waje yayi khairi tabi bayanshi da sauri har seda suka fito kofan parlorn kan ta sha gabanshi dayake gidan ba daga kana fita bane zaka hango masu gadi, drivers da me bawa flowers ruwa kofan main parlorn a corner yake.
"Ina kwana" ta furta a sanyaye muryanta na cracking Shiru yayi yana kallon fuskanta yana mamakin irin son da yake wa yarinyar nan but she end up disappointing him ya rasa me yasa sonta ya ki barin zuciyarshi se ma tausayinta da ya fara ji a kwanan nan, ganin be amsa ta ba yasa tace "bakayi breakfast ba zaka fita?" Kaman ba ze yi magana ba amma ganin yadda tayi maganan a gajiye ga hawaye dake gangara daga fuskanta yasa shi cewa "am full" tare da ra'bawa gefenta ya fice daga gidan.
A wurin ta zauna tare da had'e kai da gwiwa hawaye na zuba a fuskanta sossai fin na farko, fitowar little tana kiran "Mommy, mommy, cutie" yasa khairi d'agowa ta share hawayen fuskanta tace "pretty har kin fito? Kin koshi kam" little tace "yes mommy" Khairi tace "Toh baby kije driver na jiranki banda rashin ji da tsokana plz always what?" Little tayi saurin cewa "listen to ur teachers" murmushi sukayi wa juna kan ta wuce tana cewa "bye bye mommy" Khairi tace "bye dear" da gudu tayi hanyar waje khairi kuma ta koma.
Shara tayi da moping na just kasa ta d'aura abincin rana don gama ayyukanta da wuri take jollof rice da yaji veggies tayi da salad ta zuba a wormers d'inta masu rike zafi sossai ta shirya su a dining area tare da rufe kan da wani farin abin saki kitchen ta koma ta gyara ta wanke abinda ta 'bata seda ta tabbatar komai tsab a gidan se kamshi dake tashi kan ta rufe kofan parlornta ta shige room dinsu da little tayi kwanciyarta sossai ta yabawa hajiya ruqayya da taimakon da tayi musu, taimako zata ce don lokacin da tayi mata kayan d'aki bata san su en uwa bane, kayan kasan nan gabad'aya itace tayi dukda one bedroom ta shirya saura two bed rooms din Ba komai ciki amma kujerunta na parlor da suka kasance Ash and black masu kyau ne sossai haka kayan kitchen komai me ma'ana ta saya mata kuma sun kara mata kayan kitchen sossai ma kan dawowarsu suka kuma yi alkawarin shirya mata sauran rooms din kasan.
Wayanta ta d'auka tare da bud'e data family group da aka sata ta shiga taga se hira ake tsakanin juna dukda bata san wasu dayawa ba amma ta san en mata shidan nan da Hafsat din hajiya ruqayya da kuma haidar akwai Adda Fadeelah, Adda haneefa, Hamma Bashir, hamma faisal, Adda Marwa se hamma jamal, se yaron cikinsu wadda ze yi sa'a da su nabeel me suna Isma'il suna kiranshi Ameer.
Hira suka fara janta dashi ganinta online Ai ko ta biye musu suka dinga hira ta lura familyn akwai respect amma ba wani nuna isa da iko sbd yaran suna hira da yayyun kaman abokai har hotonta su Hamma Jamal suka ce se ta turo musu sun gani don su suna karatu ne a india, haka ta tashi ta gyara d'ankwalin atamphar jikinta ta yafa tare da d'aukan hoto ta tura musu aiko suka dinga santin kyaunta tana musu dariya.
Adda haneefa tace "Amma da kina da babban yaya ba abinda ze hanani makale mishi ya aureni sbd na san shima ze yi kyau" Hamma bashir yace "kinga kuwa twins?" Tace "su kuma su waye" hasiya tace "sibling d'inta nabeel da nabeela" Maryam ta turo hotonsu tace "kin gansu" wow wow Adda marwa tace kan suka fara muhawara akan wa ya fi kyau tsakanin khairi da twins.
Tuna d'an uwanta tayi se taji hawaye da yana nan da yanzu shima yana cikin wannan group suna shan dariya dukda su maryam d'inma kyawawa ne sossai kuma farare amma se wani santin kyaunsu suke dukda ta san bata fi su kyau ba, cewa tayi "nima ina da twin brother" kowa ya fara jefo mata tambaya Ina yake me yasa basu ganshi ba waye waye, basu labarin 'bacewarshi tayi nan kowa ya fara turo sad faces da sorry masu adu'ar Allah ya bayyana shi nayi, godiya tayi musu.
Adda Fadeelah ce tace "d'an Allah khairi kiyi mana voice note din labarinku muna son ji" dukda bata so ba amma ta san bazata iya cewa bazatayi ba nan de tayi musu voice note na about an hour, dukda ma tayi briefing kuma bata fad'i wasu abubuwan ba, kowa seda yayi voice matan kam ba wacce batayi hawaye ba haka de suka ci gaba da hira suna tsinewa hauwa da mamanta daga baya kuma suka saki zancen suka koma hiran bukin Adda haneefa da Adda marwanatu da za'a yi nan da five months.
Abinda kenan ya debewa khairi kewa tana jin daadin kasancewarta da family d'inta, ta yaba sossai da hankalin Adda Fadeelah tunda taje gidanta ta gani tana son yin wani important magana da ita akan matsalanta da musharraf bata son yi da Amrah sbd kanwarshi ce kuma tana ganin itama batayi hankalin fahimtar abinda yake faruwa ba har ta bata shawara hakan yasa ta d'auki numbern Adda Fadeelah