Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
ta had'a na kayanta zuwa d'akin sulaimi...........
Duk da shi talaka ne futuk amma yana da wadatar zuciya bade a rasa abinda za'a sa a baki a gidan na kwana ukun nan kam safe,rana, dare. Abunda ke d'aga mishi hankali shine In aka wuce haka be san ta inda ze ciyar dasu ba, Ya nemi jin me ya faru gidan Malam umar ya kasance a kulle Maman sulaimi tace bata sani ba Wlh taji de kukan dada se ta fita ta samu yayan babansu khairi na ta watsar da kayakinsu shine na nemi yara suka tattaro zuwa nan, muna shigowa kenan kuma kuka shigo..............
Sauke ajiyar zuciya yayi inda ya kudurta a ranshi ana sadakar uku ze zaunar da Dada ta fad'a me ya faru me kuma yasa hamma habu ze koresu a gidan da yake na mijinta?............
Yauma Alkali ne ya kawo masa/waina da kunu ba'a wani 'bata lokaci ba akayi ma mamaci adu'o'i aka ci aka sha kowa ya watse yana me bin Abba da adua, har cikin gida baba yayiwa alkali iso inda ya kara yiwa su dada ta'aziyya su kuma suka mishi godiya sossai akan hidiman da yayi dasu..............
Bayan tafiyanshi ne baba ya kira Maman sulaimi, Abul, se khairi suka zauna daga tsakiyar gida, inda baba ya kalli dada dake sanye da khimar dogo har kasa, a natse yace "Maman nabeel ya kamata mu san me ya faru bayan tafiyar mu koto, me yasa hamma habu ya watso muku da kaya waje bayan gidan ya kasance mallakinku?"...........
Runtse ido dada tayi, idon da In ka gani zaka rantse ba makauniya bace In har ba fad'a maka akayi ba, a sanyaye tace "hmmm ban san me kaddara ta tanadar mana a gaba ba amma Ina matukar tsoro da shakkar abinda ze biyo baya muddin burin Hamma habu ya tabbata, mawiyacin hali da suka sa mu, da kuma tagayyar da rayuwanmu da sukayi be ishe su ba har se sunzo neman wani abin kuma a garemu a daidai lokacin da d'an uwansu ke halin mutuwa ko rayuwa.....".......
Hawayen idonta ne suka zubo a kan kuncinta, khairi ce ta sa hannu ta goge mata, da dishashiyar muryarta da sam baya fita sossai tsaban kara da takeyi idan aljanunta sun tashi da kuma kukan da take sha bayan sun tafi, a kwanakin nan baza ta iya lissafa sau nawa sukazo ba duk ta rame se ido da tsiririn hancinta ake gani............
Tace "Dada ba tun yau ba muke rokon ku ku fad'a mana tarihin rayuwanku da abinda yasa 'yan uwanku gabad'aya basa sonku, sau d'aya kachal muka je 'baba gaasa' amma mun fuskanci wulakancin da bamu kara marmarin zuwa koda ta arean ba, me kukayi musu da zafi haka da har d'an uwansu na jini ze fad'i ya rasu ba wadda yazo ta'aziyya ko zaman makoki? Dan Allah ki daure ki fad'a mana su wanene ku"...........
Ajiyar zuciya Dada ta sauke seda ta nisa tukun ta fara magana "Kamar yadda kuka sani sunana safiyya Ali gamji Ni haifeffiyar cikin kauyen 'baba gaasa' ne dake chan bayan 'Abbare' karkashin karamar hukumar 'Lau' na nan cikin Taraba state......
Mu fulanin Chan ne dagani har mahaifinku sede iyayenmu mata ba daga Chan suke ba, ni mahaifiyata er wani kauye ne dake chan cikin gombe wadda ban san suna ko d'aya daga cikin 'yan uwanta ba, ban ma san karan kanta mahaifiyar tawa ba, kasancewar ta mutu a lokacin da take haihuwana.................
Na taso gaban kishiyarta Ummi itace mace ta farko a wurin mahaifina kan mahaifiyata kamar yadda mahaifiyata taci wahala da azaba haka nima naci fiye da nata, duk wani aiki da wahalan aikin gida ni nake yinshi tun ban mallaki hankalin kaina ba, ba tare da sanin mahaifina ba, Yana tsananin so na kasancewata 'ya mace d'aya tilo a gareshi, Ummi 'ya'yanta hud'u maza da hamma bawuro, Hamma sharif, Hamma hamid se kanina Amadu...........
Duk wani wahalan da nake ci a wurin Ummi sam mahaifina be sani ba don shi ba mazauni bane ko yaushe yana yawo daji daji da shanukanshi, idan ya dawo kuwa na san ko na fad'a mishi ba yadda ze yi ba sbd fuska biyu Ummi ke da shi tana nunamin tsantsar kulawa idan yana nan amma daga ya tafi duk wani abinda na saba yi da tayi yana nan se ta fanshe shi a jikina.................
Baffa se ya kwashe wata kan yake zuwa wani lokacin ma fin haka..........
Kamar yadda nake er uba a cikin en uwa na haka mahaifinku ma yake d'an uba a cikin gidansu, mahaifinshi shine jauron kauyen mu, jauro umaru, sunanshi mahaifinku ya ci mutum me mutunci, da tsan tsan karamci kowa ya shedi kyawawan halayenshi, tsab halayenshi mahaifinku ya kwaso ga kuma an haife shi da ciwon zuciya, shi yasa mahaifinshi ke tsananin son shi magaji ake kiranshi, mahaifinshi ya ke kiranshi da hakan har gabad'aya kowa ya kama...............
Yana da sanyin hali da hakuri amma In ranshi ya 'baci to fah ba zaman lafiya haka yake, ko kwatan wahalan da nake sha a wurin Ummi ba ya sha a wurin Mama goggo sbd kasancewar shi namiji me tsananin zafin zuciya da taurin rai har shakkanshi yayyunshi sukeyi, shine d'a na uku a wurin jauro umaru, iya ballo, hamma habu se mahifinku, Babangida, bamanga da autansu Isma'il..............
Duk cikinsu ba wadda yayi karatun boko se mahaifinku sbd a lokacin da makarantan boko ya shigo cikin lau mama Goggo tace sam 'ya'yanta baza suyi karatu yahudawa ba duk yadda jauro umaru ya juya ta taki sam hakan yasa ya kyaleta ya tura umaru kad'ai se ya kasance umaru ya kuma finsu natsuwa da hankali gashi ya san wurare da dama a cikin gari don har cikin jalingo yana shigowa.............
Hakan ya kara mishi tsana a cikin en uwanshi, Sam be damu ba kuma be da alamun damuwa abunda ya sani de shine ba wadda ze dake shi ya bari ko kuwa ya zage shi, tun bai yi wayau ba mamanshi ta rasu itama er wani kauye ne dake chan cikin Adamawa.................
Mafari.....
"Ke! Ke!! Safiya tashi ki je ki d'ibo min ruwa kan In tattaka ki" a natse na mike bakina d'auke da adu'ar tashi daga bacci kiran farko naji akeyi a massallacin dake kusa damu, ban damu ba sbd na saba tashi a irin wannan lokutan sede Ummi bata ta'ba aikata rafi war haka ba se gari yayi haske................
A tsorace na fito na d'auki tulun da na saba d'iban ruwa na fita sam garin ba haske ba alaman sa a sad'ad'e nake tafiya motsi kad'an se in firgita In juya, a haka har na karasa bakin rafi da bismillah na d'ibi ruwana na kuma d'aura a kaina ina juyowa naga mutane tsatsaye a kaina a firgice na sake tulun ya fad'i ya fashe duk da duhu ne hakan be hana ni sheda d'an uwana dake cikin matasan dake tsayen ba da kuma d'an jauro, habu ba ..................
Baki na rawa nace "Hamma bawuro" wani irin dariya suka saka seda sukayi me isansu tukun Hamma bawuro ya dubi habu yace "dama na maka alkawarin cikawar burinka gashi na cika saura ka kashe kishirwanka" kwalalo ido nayi waje Ina kallonshi tare da son fahimtan me yake nufi ban gama tunani ba naga habu yayo kaina.............
Baya baya na farayi har na isa bakin gaa'bar rafin ban hankara ba naji hannun habu a kugu na, a lokacin ban wuce shekaru 15 ba ihu na sandara ko Allah ze sa wani ya jini amma kaman a banza don na tabbatar ba wadda ze zo ta wuraren a irin lokacin da karfi na buge hannun habun Ina hararanshi wani murmushi ya sake a lokaci d'aya ya sa hannu ya janyoni jikinshi tare da matse ni................
Da iya kacin karfina na sa hannu Ina kokarin raba jikina da nashi inaa karfi ba d'aya ba ganin yana kokarin raba ni da kayana yasa na gantsara mishi cizo me shiga jiki a tamanin ya sake ni yana ihu da mugun gudu na bar wurin inda su Hamma bawuro da sauran abokanshi suka rufa min baya..................
Gudu nake da iyakacin karfina Ina a taimake ni amma ko tsuntsu be bayyana ba, maimakon nayi cikin gari se kuma na nausa daji nayi gudu sossai har numfashi na na shirin d'aukewa naji an janyoni da karfi cikin wasu ciyayi masu tsai na bud'e baki da niyyan ihu se ji nayi an danne min baki tare da jin wani sautin shiiii alamun inyi shiru.................
Shirun kuwa nayi ba wani jimawa naji su hamma bawuro sun iso suna ta dube dube sun jima suna dubani ganin basu ganni ba yasa suka juya suka tafi suna cizon yatsa, se da ya tabbatar sun tafi tukun ya mike ya fito nima fitowa nayi a lokacin gari ya fara haske hakan yasa muke kallon fuskokin juna da kyau..............
"Me ya fito dake gida da asubahin farkon nan?" Shiru nayi tabbas na ganeshi umaru ne d'an gidan jauro wadda en matan kauyen ke rububinshi amma ni kam bamu ta'ba magana ba kallo ma sede In hange shi daga nesa, ganin bani da niyyan amsa mishi yasa ya soma tafiya ai da gudu nabi bayanshi muna tafiya a tare har muka shigo cikin kauyen namu...............
"Ke er wani gida ne?" A sanyaye nace "Aliyu gamji" gyad'a kai yayi don ya kasance ba mai yawan magana ba 'kamar yadda ummulkhairi kike' har kofan gida ya rakoni na shige Ina waiwayonshi, Ina shiga Ummi ta fara surfamin bala'i Ina ruwan da ta aikeni me kuma ya zaunar dani har yanzu, a sanyaye na sanar da ita abinda ya faru maimakon ta ji tausayina se ta rufe ni da duka wai zanma d'an ta sharri............
Seda ta tabbatar na daku tukun ta bani wani tulun na je na debo ruwa a lokacin en mata dayawa sun fito d'iban ruwa hakan yasa ban damu ba, Ina dawowa na yi mana abin kari na share gida, nayi mata wanke wanke da wankinta tukun ta d'auramin tallahn nono zuwa cikin abbare ta kuma tabbatar mum da kar In sake in dawo ban sayar ba don wallahi In na dawo da ko guda ne se ta yanka ni............
Haka na d'auka na fice jiki a sanyaye da kafa na dinga bi har na isa cikin Abbare zuwa kasuwansu, bani da kawa ko d'aya haka nake rayuwa na ni kad'ai.......
Ashe lokacin da naga umarun nan mahaifinsu ne ba lafiya da dare ya shigo garin shine mahaifinshi ya aikeshi tsinko mishi ganyayyakin magani da shi kad'ai ya sansu cikin yaranshi kasancewa da jauron suke fita dajin.............
A bakin en matan kauyenmu naji ban ma san jauro Umaru ba lafiya ba se a lokacin, haka na zauna jugum Ina tunanin taimako na da umaru yayi ba ni na sayar da nonon nan ba se bayan magriba lokacin ba er kauyenmu ko d'aya a wurin a tsorace na d'auki kwaryata na d'aura a kai tare da nausa dajin da zai kaini baba gaasa cikin sauki..........
Nayi nisa sossai da tafiya dukda a tsorace nake haka na dinga ambaton adu'ar da ya zo bakina, kaman daga sama naga mutane biyu a gabana 'Hamma bawuro da habu' a tsorace nake kallonsu Ina ja baya su kuma se dariya suke, cikin zafin nama habu yasa hannu ya parke rigan sakin da ke jikina ihu na sandara Ina me kakkare jikina da tafukan hannuna...........
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Ihun da na sandara shi ya janyo hankalin umaru da ya idar da sallahn magrib kenan yana shirin kora shanukanshi da na mahaifinshi zuwa gida, da sauri yayo inda muke yana isowa ba tare da wata wata ba ya saukewa bawuro sandan goran hannunshi a kai a take ya sheme, duk da sarai ya gane wanshi ne a kaina ba tare da wani tunani ba shima ya sauke mishi a take ya baje shima.................
Da sauri ya kama hannuna ya d'aga ni tsaye tare da d'aukan kwaryan nono na fito me daad'i yayi wa shanukanshi a take suka iso inda muke, duka muka nufi cikin gari, tunda muka fara tafiya nake kuka kaman raina ze fita, yanzu su habu baza su tausayawa maraici na ba? Sannan hamma bawuro kaman ba d'an uwa na ba!! Shine wai ze rako a lalatamin rayuwa..............
Tsoro sossai ya kamani tunda na san ko na fad'awa ummi ba yarda zatayi ba, kuma baze hana gobe ta kara d'auramin tallah ba, gashi ba.... "Ke!! Da Allah ki rufewa mutane baki, akwai wadda ya aike ki ne? In ba rashin hankali ba kina mace me ze kawo ki cikin dajin nan da irin wannan lokaci?".................
Kafin na bashi amsa naji wani abu me tsananin zafi ya ciji kafana ihu na sandara tare da zamewa na zauna a kasan da sauri ya haska torchin da ke hannunshi se yaga katuwar kunama ce da sauri ya take ta, tare da dukawa a lokaci d'aya ya zame d'ankwalin kaina tulin gashin kaina ya bayyana, yaga d'ankwalin biyu yayi inda ya kama kafan ya d'aure da karfi................
Cikin azama ya fara dube dube yana haske hasken torchi har ya samu ganyen da yake nema, ni kam se kuka nake da duwatsu biyu ya samu ya markad'e ganyen tare da sawa a daidai inda kunaman ya sareni, kara na sake Ina me rike hannayenshi a hankali yace "sannu" kai kawai na gyad'a ruwan hannunshi ya mika min na kafa bakin goran a bakina ban sauke ba seda na shanye wasu hawayen na gangaromin.................
"Lallaba ki tashi mu shiga cikin gari dare na yi kar hankalin iyayenki ya tsahi" a sanyaye nace "ko da zan kwna a dajin nan banda wadda hankalinshi ze tashi saboda ni.." da mamaki yake kallo na a hankali yace "sbd me??" Haka kawai naji na fara bashi labarin rayuwana daga farko har kawo yau, na kara da "har yanzu kana ganin laifina don na shigo cikin daji da dare??" Na karasa Ina me kallon cikin kwayar idonshi da suka chanza kala sbd tausayi..............
Da sauri ya kauda kanshi yana me runtse ido ba tare da yace komai ba ya kama hannuna muka mike ba wani nisa ne tsakaninmu da cikin gari ba don haka nan da nan muka isa, har kofan gida ya rakani tare da mikamin kwarya na se da ya ga shiga na tukun ya juya ya fice..............
Ba wani fargaba na shiga don na san ko damuwa da abinda yasa nayi dare ummi bazatayi ba, ai ko hakan ta kasance Ina mika mata kwarya da kud'inta ta soke a zaninta ba sannu bare na gode ba me yasa kikayi dare haka? A sanyaye na wuce d'akina Ina kallon wuyan rigana dake a yage.................
Tabbas da mamana na nan na san cikin tashin hankali zata rikeni tace me ya samu rigana ya yage haka? Me yasa nayi dare a waje? In ban sayar ba bazan dawo tun ido na ganin ido ba? Wani matsanancin kuka ne ya kwace min, kwanciya nayi akan er taburman kaba na Ina rerawa a haka bacci ya d'auke ni dukda tsananin yunwan da nake ji..............
Kaman jiya yau ma da asubar fari ta tasheni tare da bani tulu na tafi d'iban ruwa, Ina fitowa bakin kofan gidanmu na ganshi tsaye hard'e da hannu kasancewar akwai farin wata sossai yasa na kalli murmushin da yake aika min, nima murmushin na sakar mishi tare da karasawa wurinshi nace "en ummi jam?"(mun tashi lafiya?) yace "jam noi kusd'e ma mai?(lafiya ya kafan kin)............
Murmushi kawai nayi muka kama hanyar rafi jefi jefi muna hira har muka isa na d'ibo ruwa da sauri ya kar'ba min muka kamo hanyar dawowa seda ya ga shiga na gida tukun ya juya ya tafi, haka lokacin tallah na nayi ya zo Ina fita muka gamu har Abbare ya rakani ya juyo da misalin biyar na yamma ya koma seda ya jira na sayar gabad'aya ya sani a gaba muka nufo hanyar kauyenmu...................
Wasa wasa shakuwa me karfi ta shiga tsakaninmu kusan satinmu uku kenan da muke tare In har zan fito daga gida Toh shi ze rakani duk inda zani abunku da karamin kauye nan da nan gulamanmu ta bazo masu zagi nayi masu jin haushina 'en mata' na ji, da maganan yazo kunnen ummi dukan mutuwa tayi min tace in rabu da magaji ko ta d'aura min sharrin da har na mutu bazan manta ba..................
Ban ji magananta ba sbd ni ya ke taimaka ba ni ke taimakarshi ba, da kariyan Allah da kuma shi kad'ai na dogara, na de fad'amishi be ce min komai ba akai se in yi hakuri wata rana se labari, a na haka kwatsam mahaifinshi ya fad'i ya rasu bayan jinyar da ya sha, sossai na tausayawa umaru don kaman ze yi hauka sbd mutuwar ba karamin shiganshi tayi ba....................
Har gidansu naje nayi mishi ta'aziyya a sace na d'auki abinci na na fita da shi tare da tilasta mishi yaci ya kuwa ci dukda ba mai yawa bane, seda safe na mishi Ina shirin fita mama goggo na shigowa da tsantsar mamaki take kallonmu da alamun zargi, wani murmushi tayi kan ta juya ta fice da sauri nima na fice.............
A washegarin na fita d'ibo ruwa har nayi nisa da tafiya naji ance "yau kuma ba jira ne?" Da sauri na juyo murmushi na kwace min ashe ze zo dukda a jiya mahaifinshi ya rasu saurin gimtse fuska na nayi nace "me ya fito da kai yanzu kai da kake fama da rashi?" A sanyaye yace "safiyya kenan se kace ba musulmi ba? Baffa ya riga ya rasu baze ta'ba dawowa ba adu'a kawai zamu ci gaba da yi mai shine gatan da zamu mishi yanzu"....................
Kai na gyad'a muka ci gaba da tafiya muna hira, a hanyar mu ta dawowa lokacin gari yayi shaa, kaman ance ya waiga se yaga hannuna da gefen fuska na duk sunyi rad'a rad'a kaman wadda cinnaku suka kwana cizo, a firgice ya rikemin hannu yana cewa "safiyya d'ume un d'o"(safiyya me wannan?) karamin murmushi nayi ina sauke ajiyar zuciya nace..............
"Nima ban sani ba wasu abu ne kaman qwari kaman cinnaku suke fitowa a d'akina ko na binne wurin se sun tono