Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
aka ce daga d'ayan bangaren ba se momma da tace "Toh gashinan de musharraf ne Wlh ba lafiya muna asibiti" Shiru tayi kan tace "Eh amma da sauki sossai, Ohk toh se kinzo"...............
Bayan ta kashe ta kuma yin wani kiran "hello taheer ya kk?, ya su takwara na? Eh dazu da mukayi waya da yaya Ahmad ya fad'amin.......... Ohk toh dama musharraf ne ba lafiya yana nan FMC......... wlh hawan jinin de........ Ohk toh se ka zo se da safe"..............
Zatayi wani kiran taji an rike hannunta d'ago kai tayi tana kallon musharraf tace "lafiya de ko?" 'Bata fuska yayi yace "momma dan Allah de wayan ya isa, na san yanzu gobe d'akin nan ze koma kaman kasuwa wlh kuma kin san bana son hayaniya" waro ido tayi tana cewa "don baka son hayaniya se bazan fad'awa dangi ba? Yanzu dakata bari inyi waya da hajiya ruqayyah se muyi wata magana tunda na ga kaji sauki"....................
Yana saurarenta har ta gama waya da hajiya ruqayyan ita ma rashin lafiyanshi ta fad'awa kan ta kalleshi tace "An kawo tambayan Saliman Yaya Ahmad" karamin murmushi yayi a zuciyarshi yace ta gaji da jiran gawon shanu kenan, a fili kuma se yace "Allah sanya alheri" momma tace "Ameen amma yaushe rabonka da gidan yayyun mahaifinka da kannena?" Yana 'bata fuska yace "momma In na zo ba lokaci kema kin sani, last zuwana ma seda na shiga time din aikina da kika sani zuwa dukku wurin grannys" momma tace "wannan ba hujja bace dukkansu cikin gombe suke ba wani gari ba balle kace akwai tafiya me yawa tsakani wallahi ka gyara halinka musharraf"...................
Zamewa yayi ya kwanta yana dafe kai, tace "Toh ba wannan ba ma, musharraf Da gaske nake har zuciyata Ina maka kwad'ayin auren khairi, In har kana son farin ciki na da kwanciyar hankalina toh ka aureta" Shiru yayi na mintuna tukun ya sauke ajiyar zuciya kan yace "In haka kike so momma so let it be, Allah ya sanya alheri" murmushi tayi tana jin son d'an nata har cikin ranta duk abinda tace take so ko da baya so haka ze yi shi..................
Maganan da take son mishi na gaba shine na shan taba amma tafi son se an sallameshi sun koma gida tukuna, abinci ta di'ba taci suna hira jefi jefi har ta gama, bargo ta d'auko ta lullu'ba mishi, ta kuma shimfid'a wani akan sallaya ta jefa pillow ta kwanta tana rufuwa da hijab dinta, cikin tausayawa yake kallonta Eyyah uwa de ko ya take bata gajiya da d'awainiyar yaronta tun daga yarantan shi har girmanshi yanzu dubi a kasa zata kwanta da girmantan nan bayan shi yana kwance akan gado...........................
Washegari
Kamar yadda khairi ta saba da wuri ta tafi wurin aikinta, duk basu tashi ba, ta fere dankali ta soya da kwai, ta dafa black tea da yaji kayan kamshi, ta san dole akai na asibiti hakan yasa bata jira tashin su nuri ba ta shirya a basket ta fito ta ba driver ya tafi dashi, sauran ta shirya a dining, ta gyara kitchen din, bata jira komai ba ta d'aura abincin rana, dambun shinkafa tayi da sous na hanta, se tayi pepper soup na kayan ciki da fruit salad.......................
Lokacin da ta gama 11 yayi, tana fitowa parlor su nuriyya na saukowa duk a shirye suka sauko har little sun shirya ta cikin duguwar rigan atampha orange da black se white hijab da white shoe tayi kyau sossai, da murmushi ta musu barka da safiya suna nufan dining suna kuma gaisawa, Amrah na tambayar khairi ya su nabeel da dada, tana amsawa da suna lafiya..................
Little da ke rike da hannunta ne tace "cutie I want to see them plz come with them 2morrow" nuri tace "gaskiya nima Ina son ganin twins din nan da su miemie suka dameni da kyaunsu" khairi tace "Adda Ai suna zuwa islamiyya ne shiyasa ban ta'ba zuwa dasu ba" little tace "plz plz plz cutie su hakura da na gobe kawai su zo mu yini plzzzzzzz" Amrah tace "yes plz Tbest" miemie tace "please" nuriyyah ma tace "plz Adda khairi" a tare suka sa dariya har khairin tana girgiza kai tace "Toh shikenan zan zo dasu In Allah ya kaimu" "yeeeaahaahhahhhhhh💃💃" little ta dinga rawa da tsalle...................
Khairi ta ja kujera ta d'auke ta ta d'aura ta akai tana cewa "oya ci abinci tukun ki tsayawa mutane da rawan" wani dariyan sukayi tana kallonsu tace "Toh yanzu Anties breakfast zaku ci ko lunch?" Miemie tace "khaih kar de har kin gama lunch?" Khairi ta gyad'a kai tana murmushi nuri tace "weldon khairi na asibiti fah?" Khairi tace "tun 8 na bada driver ya kai musu" nuri tace "masha Allah sannu da kokari" murmushi kawai khairi tayi......................
Amrah tace "nide chips zanci se in mun dawo hospital se inci lunch ko kuma inyi achan don na san su Anty rabi'ah zasu kai abinci" miemie tace "nima" little ma tace "me too, Anty Amrah who's at hospital? Naji kince su sauban zasu je" nuri tace "just eat bana son surutu and sauban ba uncle dinki bane kike kiranshi gatsau haka?" Pouting lips tayi tana cewa "but Anty nuri we are mates, same class and everything be yi babba ba like yhu and uncle marwan" dariya su Amrah sukayi miemie tace "se yayi girma kaman mu kenan zaki kirashi uncle" little tace "yes, sauban, Anwar and sudais are not my uncles" tana 'bata fuska tace "no way".................
Amrah na dariya tace "yes way, sbd kannen paapi dinki ne kap d'insu yhu better start calling them uncles na gayamiki" kara tura bakin tayi wai tayi fushi a haka har suka gama cin abinci suna sauka daga dining din da niyyan tafiya momma na shigowa, da gudu little taje ta rungumeta tana cewa "oyoyo granny" momma tace "oyoyo namesy how was ur night?"....................
Tana kwa'ba fuska tace "hectic, I didn't see you and my paapi" momma tace "Eyyah sorry, yanzu kuje ku ganshi I will be on my way too" little na tsalle ta fice, gaida momma duk sukayi suna tambayar ya jikin nashi tace "yayi sauki Alhamdulillah, jinin ya sauka kila a sallameshi da dare ko gobe muran ne de se a hankali ze sakeshi" ajiyar zuciya suka sauke, nuri tace "ba abinda za'a iya yi akan kidneyn yanzu?" Momma tace "babu munyi magana da doctor Aslam da safen nan yace ba wai ya kamu da wani ciwo bane yana barazana ne sbd baki da yayi" Amra tace "Toh Allah bashi lafiya"................,,
Suka ce "Ameen" miemie tace "Toh da wa kika barshi?" Momma tace "wai Ai family sun cika d'akin pim, kuje nima wanka kawai zanyi in tafi, nuri kije d'akinshi ki d'auka mishi kananan kaya da sponge da soap ku tafin mishi dashi, basket nan fah?" Nuri tace "Ohk, lunch dinshi ne ciki" momma tace "sannu khairi, har kin gama kenan?" Khairi ta gyad'a kai kanta kasa, momma tace "to ki bi su kuje, nima yanzu zan biyo ku" tace "toh momma" dama da hijab dinta jikinta, so fita kawai sukayi momma ta haura sama....................
Little ta shiga motan nuriyyah, yayinda Amrah da khairi suka shiga motan da Musharraf ya ba miemie na zuwa makaranta, seda suka jira nuri taje part din musharraf ta dawo kan suka jera suka fita a tare, bayan sun isa suka nufi d'akin little da nuri ne gaba se miemie tukun Amrah da khairi a baya, da sallama nuri ta tura d'akin da gudu little tayi kan gadon ganin paapinta, d'aga ta yayi zuwa kan gadon tana cewa "me ke damunka paapi kake kwance a hospital?".....................
Yace "ba gaisuwa?" Tace "good morning paapi?" Yace "morning" yana d'ago kai se idonshi ya fad'a cikin nata da ta shigo a karshe da sauri ta dukar da kai tana jin jikinta ya d'au rawa, mutane ne a d'akin akallah sun kusa 30 yara da kanana kamshi ko ta Ina na turaruka daban daban, gaban gadon ta nufa da basket din abincin rana a hannunta kafanta har rawa yake jin yadda ido ke yawo a kanta...................
Kusan kowa kallonta yake a d'akin ganin bakuwar fuska har kasa ta duka,
Ta gaida wasu manya da ta gani su uku zazzaune akan plastic chair, da fara'a suka amsa mata, bayan ta ajiye basket din ta d'an saci kallonshi da sauri ta kawar da kai ganin shima kallonta yake, cikin kasa da murya tace "Ina kwana? Ya jiki?" A hankali shima cikin dashewar murya yace "Alhamdulillah"......................
Kan darduma ta karasa da ta ga mata hud'u zaune suna hira, a kasa ta duka ta gaishesu suma suka amsa mata ba laifi, baza ido tayi a d'akin tana duba inda zata tsaya don tuni su Amrah ko wacce ta samu abokiyar hira bayan sun gaggaisa da uncles d'insu da Anties d'insu, wasu matasa biyu kyawawa idonta ya fad'a kai suma ita suke kallo gaishesu tayi, d'ayan ya amsa da d'an murmushi d'ayan kuma ba walwala ya amsa yana mai da kai kan wayanshi........................
Kusa da Amrah taje ta tsaya tana lura da yadda d'ayan saurayin ke kare mata kallo up and down, ganin kallon yayi yawa kuma en matan gefen Amrah na ta yatsina fuska yasa khairi ta nufi kofa, yana magana da little amma yana lura da irin kallon da sufyan ke bin khairi dashi, ganin ta fice daga d'akin yasa ya sauke ajiyar zuciya, yana mai me da hankali kan little, Amrah kuma ganin khairi ta fita se taji ba daad'i hakan yasa ta bi bayanta.................
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
*wannan page d'in naki ne Sadiya (Maman khalil) ina jin daad'in comments dinki sossai, irin sossai d'innan plz keep it up dear, Allah ya bar kauna*
Page➡️5️⃣4️⃣▶️5️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Dube dube Amrah ta fara bayan fitanta Chan ta hange ta zaune kan wani dakali daga bayan d'akin ta zabga tagumi, karasawa tayi ta zare tagumin hakan yasa khairi d'agowa tana kallonta..........
Murmushi sukayiwa juna kan khairi ta d'an matsa Amrah ta zauna, bayan ta zauna tace "family sun cika d'akin" khairi tace "Ai kam duk ban san su ba gwara su Anty salima" Amrah tace "eh su da iyayensu ne, bari nayi miki bayani dalla dalla kan ki shigo daga ciki" hararanta khairi tayi tace "Toh wa ya gaya miki zan amince balle har in shigo daga cikin?" Amrah na dariya tace "har se an fad'a!! Lallai ni kam har na hango wani boyayyen sirri" waro ido khairi tayi tace "wani sirri?" Amrah ta fashe da dariya tana cewa "na san baza ki ki bane kawai amma ba wani sirri" a tsarge khairi ke kallon Amrah kar de har ta har'bo jirginta............
Ganin tana shirin tona asirin kanta yasa tayi saurin cewa "uhm Ina jinki suwaye da waye a d'akin?" Amrah tace "Duk waennan family da kika gani Alhaji Mahmoud dukku shine tushensu da shi da matarshi hajja marwa wadda yanzu duk sun rigamu gidan gaskiya, Allah ya bashi 'ya'ya guda biyu rak a duniya kuma duk maza da kakanmu ta wurin uwa da kakanmu ta wurin uba, Alhaji Adam wadda shine mahaifin Abbanmu se Alhaji Abubakar wadda shi ya haifi su momma.......................
Alhaji Abubakar da Alhaji Adam sun taso kaman en biyu sabida ba wani tazara bane tsakaninsu sannan komansu d'aya, da yake mahaifinsu sana'ar saida dabbobi yake hakan yasa suma suka tsunduma sana'ar mahaifin nasu inda sukayi shura a ciki har ya kai ga sunyi suna a dukku da ma gombe gabad'aya, a yawace yawancen da sukeyi na safarar dabbobi ne suka had'u da Aslamiyya da kanwarta shuwa a garin chad suma ya da kanwa ne iyayensu sun mutu sakamakon harin da aka kaiwa kauyensu...................
A wurin saida sauran dabbobinsu don tseratar da rayuwansu suka gamu inda Adam ya nemi su zo su koma tare don sossai ya tausaya musu jin labarinsu, tare suka dawo Nigeria inda hajja marwa ta tarbe su hannu biyu take basu kulawa sossai jin labarinsu haka Alhj Mahmoud ma duk wani kulawan da uba ze bawa d'anshi yana basu daidai gwargwado a lokacin Aslamiyya na da shekaru sha bakwai yayinda shuwa ke da shekaru sha biyu a duniya......................
Inda Adam ke da 26, Abubakar kuma 24 wasa wasa soyayya me tsanani ya shiga tsakanin Adam da Aslamiyya sossai Alhj mahmoud yaji daadin haka ba'a 'bata dogon lokaci ba akayi musu aure, anan cikin dukku suka gina gidan irin na zamani babban gida ne me part uku, Adam a d'aya Abubakar a d'aya In yayi aure se na tsakiyar na iyayensu, da kyar suka shawo kan Alhj mahmoud ya yarda suka koma gidan gabad'aya...................
Alhj mahmoud yaga ranar haihuwa sossai don a lokacin ba abinda yakeyi na aiki haka hajja marwa en aiki baja Baja, a hk suka ci gaba da rayuwa cikin tsantsar kwanciyan hankali don basu da wani damuwa, har Allah ya azurta Adam da samun d'a na farko, Alhaji Nasir shine wadda kika gani daga daman ya musharraf sanye da fararen kayan nan In kin lura duk ya fi su tsufa, bayan shekara biyu da haihuwarshi suka sake samun wani d'a namijin shine Alhj Ahmad shima yana nan ciki da sky blue shadda...............
Bayan haihuwan Ahmad ne hankalinsu Alhj mahmoud ya fara tashi akan rashin auren Abubakar yayi mishi magana ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, amma amsan d'aya ne a kara mishi lokaci, ba irin lokacin da bai d'ibar mai ba amma ba mata, da ya gaji kawai se ya had'a aurenshi da marwa a lokacin ta gama secondary anan cikin dukku.....................
Zama suke kaman ba auren had'i ba don iya gwargwado suna kula da junansu, Allah be basu rabo ba seda suka shekara biyar da aure a lokacin, yayyunsu sun sake samun karuwa inda suka haifi mahaifinmu Senator mahmoud Adam, sossai farin ciki ya cika wannan familyn don sun damu sossai da rashin haihuwan nasu akan lokaci.....................
Sossai cikin yaga gata ba na wasa ba, har ya kai lokacin haihuwa inda suka samu 'ya mace taci suna 'fatima' momman mu, bayan haihuwanta da shekara biyu suka haifi uncle taheer shima yana cikin room din sanye da black gezner, bayan shekara biyu suka kuma haifan Anty Rabiah, ita ma tana d'akin, tun daga kan babanmu su Alhj Adam basu kara samun wani haihuwan ba....................
Nasir, Ahmad, da mahmoud a ABU zaria sukayi karatu inda Nasir ya karanta business yayinda Ahmad ya karanci Education se mahmoud da ya karanta political science, sossai suka dawo da nasara mai yawa, a wurin bautan kasa suka had'u da matarshi Aisha a jihar bauchi inda suka kulla soyayyarsu mai tsabta, haka Ahmad ma ya samu matarshi zulaiha a nan cikin dukku dayake shi anan yayi service suna gamawa service aka sha buki na ji da fad'a inda duk suka samu gida a cikin Gombe.................
Haka Allah ya basu Aiki cikin sauki basu wani sha wahala ba, sbd kyaun results d'insu, a nan Gombe state university uncle Ahmad ya samu karantarwa yayinda Uncle Nasir ya samu aiki a wani textile company, Bayan aurensu ne suka tashi da mummunar rashi na Alhaj Mahmoud Dukku, sossai suka jimanta rasuwar don tabbas sunyi rashi babba, bayan rasuwanshi da wattani biyu hajja marwa matarshi ta bishi tashin hankalin da suka shiga ba'a magana amma se suka fawallawa Allah......................
Abbanmu kuma ya tsunduma siyasa kuma be da niyyar aure sossai ya kashe kud'in mamaji (Alhj Adam) akan siyasan har ya samu nasarar samun kujeran chairman a haka ya dinga taka matsayi har ya zama ministern man petur na kasa a lokacin ran mamaji ya kai makura wurin 'baci da rashin aurenshi hakan yasa sukayi shawara da bappa (Abubakar) akan su aura mishi fatima wato momma................
A lokacin ta kusa kammala karatunta na NCE anan gombe tana zama gidan Uncle Nasir sam bata ce komai ba sbd ta kasance mai biyayya da ladabi ga hakuri da Allah ya zuba mata, a fili mahmoud ya dinga nuna kiyayyar shi ga auren har barazana ya dinga yiwa momma daga baya da yaga an fi karfinshi sai kawai yayi shiru amma da mummunar kuduri a ranshi game da momma duk da ba kyau ta rasa ba ba komai ba don duk cikinmu tafi kowa d'ibo kamannin shuwa arab dukda suma sauran suna da kyau kuma farare amma se Abbanmu ya fita chocolate color, Kinga Adda nuriyyah colornshi ta d'auko................."
Bazan iya baki labarin zaman auren da momma tayi ba wannan kam se ita ko yaya musharraf haka kuma bazan iya gayamiki takamamman laifin Abba ba..... sbd....." kuka ne ya sarke ta ta kasa karasa maganan, side hug khairi tayi mata tana bubbuga dantsen hannunta, seda tayi kuka akallah na two mins kan tayi shiru tana share hawayen fuskanta tare da karamin murmushi tace ....................
"Yaran Uncle Nasir da Anty Aisha hud'u hamma marwan wadda shine ze auri Adda nuri, se Maryam wacce kin Santa, se salim da muke sa'anni se autansu sudais sa'an Little, duk tazara mai yawa ne tsakaninsu don Anty Aisha In ta haihu se tayi planning na akallah shekaru hud'u kan ta cire. Se Uncle Ahmad babban d'anshi ya sufyan, salima itama kin santa se Rufaida, zainab waenda kusan kanmu d'aya autansu shine Ibrahim wadda yanzu yake 12years old................
Se Kanin momma Uncle taheer da matarshi hajiya Asiya 'ya'yansu hud'u Zainab wacce kin san ta se Farida da fatima da suke en biyu kuma sa'anninmu se auta Anwar sa'an little. Se er autansu momma Anty Rabi'ah mijinta uncle Isma'il 'ya'yansu biyu Afreen da itama sa'ar mu ce se sauban sa'an little" Ajiyar zuciya ta sauke tare da karawa da "Toh kinji familyn Marigayi Alhj Mahmoud dukku"..............
Murmushi khairi tayi tace "masha Allah what a huge family!! Allah ya kara had'e kanku" Amrah zata amsa kenan taji miemie tace "eyeeeh ku kuma nan kuka zo kuka 'boye kuna ta gulma momma na Chan ta damu ya Musharraf na ta cigiyarku" waro ido sukayi a tare suka ce "ya musharraf???" Dariya miemie ta fashe dashi harda kama ciki tace "irin wannan tsurewar? Ko de baku da gaskiya ne" harara Amrah ta banka mata tana mikewa...................
Khairi ma mikewa tayi zuciyarta na luguden bugawa a tare suka nufi d'akin, Ashe bayan