Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
khairi acham ha d'o min d'o fija be hamdeeya"(Eyyah dan Allah Adda khairi ki barni a nan muna wasa da hamdeeya) ta'be baki khairi tayi kan ta juya ta fice seda ta je ta saya itacen tukun ta juyo gida tana shiga ta tura nabeel gidan maman hamdeeya don ta san baza ta ta'ba cutar da su ba.............,..
Girki ta d'aura inda tayi musu tuwon masara da miyar busashiyar kubewa tana yi suna er hira da Dada, anan take fad'a mata yadda sukayi da maman hamdeeya akan Sana'an da za suyi ilai kuwa ta aminta da hakan tace se gobe khairi ta koma kasuwa tayo sayyayan da sauran kud'in hannunta, da Toh kawai ta amsa, seda ta ga magrib ya gabato tukun ta shiga ta taho da su nabeela sukayi sallah sukayi karatun da suka saba tun suna happy family seda sukayi isha tukun suka baje abincinsu suka ci suka koshi kan hira ya biyo baya................
****
Zaune take kan d'an sallayanta sanye da hijab d'an karami fari sol hannunta a sama tana adu'a hawaye na zuba daga idonta, turo kofa akayi aka shigo da sallama, da tsantsan mamaki momma ke kallon zahra da take ta kuka tana motsa baki, da sauri ta karasa ta zauna kusa da ita jin hakan yasa ta shafa adu'anta tare da fad'awa jikin momma ta kuma fashewa da kuka..............
A natse momma ke shafa bayanta cikin rarrashi tace "me nene damuwanki takwara? Me akayi miki? Wa ya 'bata miki rai?" Zahra tace "granny mommy na na tuna friends d'ina ko wacce tazo mommy tayi min kaza tayi min kaza, mommy kaza amma ni kam se de granny, paapi ko Anties" ta karasa da wani hawayen.............
Momma ta share mata cikin tausayawa tace "zahra kwata kwata shekarunki nawa da zaki zauna kina wannan tunani? Yarinya dake? Ba na ce miki maman ki ta rasu ba? Toh me ya kamata kiyi mata? Zahra tace "adu'a nake mata don akwai hadisin da akayimana a school an ce
"عن ابي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم 'إذا مات ابن ادم انقطع عمله الا من ثلاث، صدقة خارية أو علم ينتفع به أو ولد صا لح يدعو له"
"An kar'bo daga baban huraira Allah ya yarda dashi yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace 'idan mutum ya mutu dukkanin ayyukanshi sun yanke se guda uku 'Sadaka mai gudana' 'ko ilimi wadda ake anfani dashi' 'ko d'a na gari wadda ke mishi adu'a" granny ina mata adu'a kullum kuma Ina son Allah ya bani kud'i masu yawa don na yi mata sadakatul jariya malam yace sune rijiya, bohol, massalatai, bishiyu ko qur'anan da ake karatu da su a massalaci................
Karkata fuska tayi a shagwa'be tace "na sha yiwa paapi magana tunda yana da kud'i ya bani in mata ko yayi mata amma kullum sede ya had'e rai, ko ya daka min tsawa, granny shima In mishi adu'ar rage fushi?" Ta karasa da iyakar gaskiyarta duk da hawaye ya gangaro daga idon momma amma seda tayi murmushi tana sharewa ta gyad'a kai...............
Sossai take mamakin wayau da Allah yayiwa zahra da kaifin basiranta ko da shike d'an na gada yafi d'an na koya halinsu d'aya da Musharraf yana karami, lallashin zahran tayi har bacci ya sureta kan ta mike ta fito, tana shiga room d'inta ta d'auki wayanta ta danna kiran musharraf bayan sun gaisa tace cikin kakkausan murya "na baka nan da wata biyar ka fidda mata cikin waenda suke binka da sunan soyayya gasu dayawa cikin dangi da waje In ba haka ba kuma na aura maka wacce raina yaso" bata jira cewarshi ba ta kashe waynta tana runtse ido ta san ta saka shi a mawuyacin hali amma ba yadda ta iya, dolene ya samawa zahra farin ciki ya kuma samwa kanshi natsuwa ba duka aka taru aka zama d'aya ba.................
*barkanmu da sallah en uwa, fatan anyi sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Ameen *
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️2️⃣6️⃣▶️2️⃣7️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Wayan ya jima sakale a kunnenshi bayan ta kashe kan ya sabule ta a hankali ta fad'i kan katifan gadon da yake kai ba tare da ya bud'e idonshi dake lumshe ba ya dafe kanshi da hannunshi, cikin tsananin tashin hankali yake murza goshinshi da hannunshi dake kai.............
Aure fah Aure kuma? Yanzu? Daga muryan momma ya fahimci wannan karon da gaske takeyi, gaskiya be shirya ba, ya gama aure, ya rufe babin mace a rayuwanshi ya gama yarda da mata a duniyan nan, hawaye ne ya cika idanunshi, a fili yace "Surayyah baki min adalci ba, bakiyiwa kanki adalci ba, Allah ya Allah" gam ya runtse idonshi yana kokarin hana hawayen idonshi gangarowa.................
Hannunshi ya mika bedside drawer ya janyo kwalin Aspen tare da liter ya kunna ya fara sha ba ji ba gani, yana tuna masu sonshin maryam, salima, zainab, Afreen. Shi duk cikinsu ba wacce tayi mishi dabiunsu duk na en boko ne ba na kad'an kad'an ba ze iya rantsewa ko za'a shakuresu baza su ta'ba karanta maka fiye da izu biyu na qur'ani ba da ka ko da qur'anin, Lallai yana cikin tsaka mai wuya................
****
Washegari da sassafe khairi ta tashi dama akwai sauran tuwon jiya da miya, dumame tayi musu me daadi tana saukewa ta d'aura ruwan wanka ta fito ta fara shara tana gamawa ta juye ruwan ta taso nabeel da nabeela tayi musu wanka kan tayi nata ta kuma surkawa Dada ta kai mata, seda ta taimaka mata ta shiga tukun ta dawo ta shirya cikin wani atampha ganta/maso da shima yaji jiki ja da green d'inkin riga da skirt seda hawaye ya zubo mata tuna wadda ya mata d'inkin (Abulkhairi)................
Ta d'aura d'ankwalin a kanta lokacin har su nabeel sun shirya cikin kod'add'iyar shaddansu iri d'aya, abinci ta shigo musu da shi tare da ajiye roban yaji a gefen nata da na Dada don dukkansu masu son yaji ne, su nabeel sun jima da fara cin abinci kan Dada ta fito ita ma atampha marar tsadar kudi ta saka riga da zani be wani kod'e sossai ba zama tayi, suka fara cin abinci da bismillah suna gamawa bayan sun wanke hannu sun shaa ruwa khairi ta dubi Dada tace.....................
"Dada Ina ga ya kamata mu koma makaranta, su nabeela kam ma boko da islamiyya ya kamata mu mayar da su" ajiyar zuciya Dada ta sauke tace "toh khairi In kin je kin sayo abinda ya sawwaka na sana'a In kud'in ya saura se mu duba maakarantun a cikin unguwan nan don bana so kuyi nisa".................
Murmushi khairi tayi cikin jin daadi tace "ze yi ma Dada makarantun gomnati ba a Biyan wasu abin kirki haka islamiyya ma be wuce kud'in laraba ba" Kai Dada ta gyad'a tsam khairi ta mike ta d'auki roba hijab d'inta red color ta sanya tare da zura roba silifas d'inta tana duban Dada tace "na tafi kasuwan Dada" dada tace "zaki gane ko? In fa baki gane ba ki dawo fah" Kai khairi ta gyad'a se kace dada na kallonta, ta fice Dada na binta da adu'ar tsari.....................
A natse take tafiya har ta samu napep ta tsare ta hau ya kaita har bakin kasuwa ya ajiye, 200 ta mika mishi ya zaro chanji ya bata se bata had'a cikin kud'in hannunta ba ta soke shi cikin d'ankwalinta don ta san halinta In chanji sukayi yawa a hannunta zubewa suke, straight ta nufi layin masu sayar da abubuwan da ta zo saya don bata manta ba, ita da wuya tazo wuri sau d'aya ta manta...................
Taje ta saya kuka, daddawa, da kubewa duk na 2/200 ta d'ago hannunta tana zarar masa kenan taji an wabce kud'in gabad'aya tare da artawa a guje, ido ta zaro waje tare da bin bayan saurayin tana ihun a taimaketa kud'inta duk cikin masu sayar da abu a layin ba wadda ya motsa don sun san in ana irin wannan abun kace zakayi taimako kaima yasheka za'ayi.........................
Se daidai kun matasa dake tsaye ne suka bishi da niyyan kamashi amma ko sama ko kasa an nemeshi an rasa, hannu khairi ta sa akai tana ambaton sunan Allah hawayen idonta kuma yaki tsayawa, ganin da gaske bashi ba labarinshi yasa ta sulale kasa dabas ta fashe da kuka bilhakki, sossai tayi kuka har mutane dayawa suka tausaya mata amma ba me cire naira biyar d'inshi ya bata sbd wannan rayuwa kowa kanshi ya sani..................
Wasu sede suce "se hakuri yarinya ze biyaki a inda ba kud'i" bata kula kowa ba tayi kukanta ta gaji tukun ta mike ta nufi me kayan daddawa da ta fara saya dama ta riga ta mika mishi 1000 yana ganin tana share hawayenta yace "yarinya In sa miki a leda?" Bata kula shi ba se fisge dubu d'ayanta da tayi, ta juya a fusace tana jin yana dariya yana cewa "ba ni na kar zomon ba ko rataya ba'a bani ba ehe" wani sabon hawaye ne ya gangaro mata jin makwabtanshi sun kwace da dariya.................
Sauri sauri ta isa bakin hanya ta tsare napep ta fad'a mishi unguwansu tare da shigewa, tana jin zafi a zuciyanta gwara zafin kwace kud'inta da zafin abinda en kasuwancan sukayi mata, ta tsani wulakanci tana da tsan tsan riko duk da tana da saurin yafiya adu'a ta ringa musu Allah ya had'asu da ibtila'i fiye da nata da na en uwanta, kukanta ta dinga yi har suka iso....................
Da kud'in cikin d'ankwalin ta ta biyashi tana ji yana cewa "malama rayuwan yanzun se hakuri fah" bata kula shi ba ta fad'a gidansu da gudu ta zube jikin dada tare da kuma sa kuka In ta tuna shine last kobonsu ashe gwara ma da Allah ya sa ta sayi d'an kayan abinci wadda In har ya kare bata san inda zasu samu kud'in sayan wasu ba...................
Cikin tashin hankali Dada ke shafa fuskanta da ya kumbura suntum tsabar kukan da ta ci take cewa "me ya faru khairi?" Shiru khairi tayi har dada bata san sadda ta dakawa khairi tsawa ba "nace me ya sameki ummulkhairi?" Ta karasa da hawaye a fuskanta hannunta kuma na rike gam da ita cikin kuka khairi tace "Dada an kwace kud'in gabad'aya dada, wani marar imani dada ya wabce kud'in yayi tafiyanshi".....................
Salati Dada ta saki tana tafa hannu sam batayi wani kukan ba, se cewa da tayi "khairi kukan ya isa haka Allahn da ya bamu wanchan d'in yana sane da mu kuma bakin da Allah ya tsaga baya hanashi abinda ze Sa a ciki sede In ya rena"..................
Shiru khairi tayi tana ajiyar zuciya a lokaci d'aya ta sulale ta kwantar da jikinta kan taburma tare da d'aura kanta kan kafan Dada tana sauke ajiyar zuciya inda hannun Dadan ke kanta tana shafawa bata wani jima ba bacci ya sureta.................
*****
"Hajiya zulai barka da yammaci ya gd ya yaran?" Banji abinda aka ce daga d'ayan 'bangaren ba nade ga momma na murmushi cikin dariya tace "aiko kaman kin sani daughter nake son ki turomin tyi min kwana biyu" banji mai aka kuma cewa ba, se godiya da momma tayi tare da kashe wayan..............
Hajiya Aisha ta kira yadda sukayi da hajiya zulai haka sukayi da hajiya Aisha, haka ma hajiya rabi da hajiya Asiya, tana gamawa ta saki murmushi a fili tace "wannan karon kam sede ka fashe musharraf dear" ya ce mata ze zo ran Friday gobe kenan shi yasa ta jaji'bo mishi gayyan en mata masu tsananin sonshi inda biyu suke 'ya'yan yayyun mahaifinshi biyun kuma 'ya'yan kannenta....................
Har gwara 'yayan kannentan ma yana basu fuska sabanin yaran yayyun mahaifinshi da yake jin haushinsu ba wai tsana ba, maryam er hajiya zulai da Alhj nasir Adam ne wa ga mahaifinshi, se salima er hajiya Aisha da Alhj Ahmad Adam shima wa ga mahaifinshi, se Zainab tahir Abubakar er kaninta se Afreen Isma'il er kanwanta....................
Mayen son Musharraf ke kad'asu amma be ta'ba basu fuska ba se tsan tsan wulakanci da yake zuba musu ba ji ba gani, mikewa tayi ta nufi kasa don bada sakon abinda za'a sayo mata wadda zata girkawa d'an nata sbd jirgi ze biyo wannan karon kuma shigowar safe...................
******
Bayan ta tashi daga bacci ne take tambayar dada Ina su nabeela bata gansu ba, Dada tace "suna gidan maman hamdeeya" cikin fad'a khairi tace "haba dada ya za'ayi su tafi su barki ke kad'ai bayan baki gama sanin gidan ba In wani abu for god sake ya sameki fa?" Murmushi dada tayi tana cewa "kar ki d'auko wani hali da ba naki ba ki yafawa kanki ummul ki sawa zuciyarki salama komai ya faru da ke damu yana cikin igiyar kaddaranmu da se yanzu muka iso cikinta....................
Mu godewa Allah wasu tasu IGIYAR RAYUWAN ta ninke namu ta shanye ki yawaita istigfari hailala, da salati zakiji sauki, sannan yanzu ba inda ban sani a gidan nan ba gidan da ba wani girma yake dashi ba kuma akallah yau kwana na biyar cikinta taya za'ayi bazan san ko Ina ba!!!!".....................
Shiru khairi tayi kanta kasa gaskiya ba wacce ta kai mahaifiya a rayuwa duk da ba kallonta take ba amma ta fahimci halin da take son jefa kanta, mikewa tayi tana cewa "Toh na gode dada bari In d'aura mana abincin rana In na gama se in dubo su" murmushi kawai dada tayi, a natse ta hura wuta ta d'aura musu shinkafa da mai da yaji..................
Tanayi suna hira jefi jefi da dada har ta gama ta kwashe musu a d'an kulansu tare da d'aurawa kan karamin tiren silvernsu ta sa cokula ta ajiye kan tabarman da dada take duk da rana tsaka ne amma garin sam ba rana se duhu kaman hadari ruwan se yawo yake a sama, fita tayi ta shiga gidan maman hamdeeya daga bakin kofa ta fara jin kamshi na tashi kasancewar maman hamdeeya na sana'an turaruka humras, collecture, turarukan wuta da na tsuguno hakan yasa kana doso cikin gidan kamshi ze bule ka.................
A lokaci d'aya kuma ita tela ce, da sallama khairi ta shiga da gudu yaran suka zo suka rungumeta 'nabeel, nabeela da hamdeeya' se kawai ta suri hamdeeya ta fara juyi da ita se wangale hakori take, da murmushi maman hamdeeya dake had'a turarukanta a kan varender ta tare ta "barka da shigowa uwar alkhairi idonki kenan?".................
Khairi na kokarin zama gefenta bayan ta ajiye hamdeeya sun ci gaba da wasan su tace "hmmm kede bari maman hamdeeya wani ibtila'in ne ya sake sauko mana d'an kud'in da ya saura mana duniya wani ya kwace" salallami maman hamdeeya ta fara tana tafa hannu inda take tambayar khairi garin yaya hakan ya faru? Tsab khairi ta bata labari har da abinda sukayi niyyan yi da sauran kud'in wato komawa school da islamiyya...............,
Zagin da maman hamdeeya ta yiwa wancan saurayin ko kud'inta ne albarka, "dan Allah khairi ki ban labarin rayuwanki?" Khairi tace "yau kuwa don na yarda dake d'ari bisa d'ari baza ki ta'ba cutar da mu ba, amma bari inje In ba su dada abinci, Ina zuwa" ta mike ta sa su nabeel a gaba suka fice hannunta d'auke da hamdeeya...............
Bayan sun gama cin abinci sauran da ke cikin kula ta kullawa mai da yaji ta bawa nabeel suka fice zuwa gidan maman hamdeeya kaman yadda suka zo Dada kam ma bacci tace zatayi, da murna maman hamdeeya ta karbi abincin ta fara ci inda take cewa khairi "kaman Kin san wannan shine favorite na" murmushi kawai khairi tayi, bayan maman hamdeeya ta gama cin abincinta ta sha ruwa ta fuskanci khairi tace.................
"Ina jinki" a natse khairi ta fara bata labarin rayuwansu idonta na kan su nabeel tun daga kan labarin iyayensu zuwa nasu bata boye mata komai ba, da mamakin khairi se gani tayi maman hamdeeya na kuka tsakaninta da Allah share hawayen idonta khairi tayi tana murmushi me ciwo da kyar ta samu maman hamdeeya tayi shiru a hankali tace "da d'an sana'an da nakeyi nayi alkawari daga yau na d'auki nauyin karatun islamiyyan su nabeel har su gama" cikin tsantsan farin ciki khairi ta rungumeta dama karatun addinin shine yafi damunta...................
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gureen
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️2️⃣8️⃣▶️2️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Washegari
Misalin karfe 10 na safe jirginshi yayi landing a birnin gombe, bayan ya gama checking ya janyo brown medium size trolley d'inshi tafiya yake cikin izza da tsantsar takama daga nesa In ka hangeshi zaka san lallai gayen ma'abocin gym ne don yadda kayan da yasaka suka mugun fidda yanayin jikinshi................
sanye yake da farin long sleeve shirt masu buttons da black crazy jeans amma ba irin crazy me munin nan ba, rigan sossai ya kamashi ya 'balle buttons biyu na sama, kanshi da ya sha gyara se kyalli yake daga nesa, tun fitowanshi ya sheda motar mommanshi sede ya tamke fuskan nan tamau sbd ba ita bace yake hange...................
Da gudu zahra ta taho ta rumgume shi dukawa yayi ya d'aga ta sama yana juyi da ita duk hankalin en matan wurin ya karkata gareshi wasu na kallonshi da tsantsan burgewa wasu kuma na kallonshi da tsantsar so dariyan da yakeyiwa ershi ya mugun tafiya dasu, yana sauke zahra ya kama hannunta suka karaso jikin motan yana karewa Afreen dake tsaye jikin motan kallo...................
Sanye take da long sleeve peach color shirt me buttons kaman na maza ta kama kasan ta d'aureshi a cikinta har