Advertisements
Chapter 25 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 38

72K to 75K   out of 113.1K words

uhm Rabi’ah uhm uhm wani irin seducing? Kina da hankali kuwa In ma seduction d’in ne se a cikin gidansu” bappa ne ya kalli momma da wani irin haushin rabiah ke cinta yace “ban gane me take nufi ba Fatima wani irin asiri tayi muku?” Mamaji ne yace “a bar maganan nan se gobe yanzu dare yayi” kallon sufyan da musharraf yayi yace “In har na isa daku ban son ko kallon banza ya kara shiga tsakaninku har zuwa In yanke hukunci” juyawa yayi ya fice dadda ta bi bayanshi, bappa ma ya shige part d’insu diddi ta bishi, Marwan ma ya kama sufyan suka wuce, nan fah maganganu suka fara tashi dukda basa son d’aga murya sbd musharraf dake tsaye sun tabbatar ranshi a ‘bace yake yau dinnan...............

ganinta a duke tana kuka yasa wani irin tausayinta da ya ninka na da kamashi, wurinta ya nufa tare da kamo kafad’anta ta mike hannunta ya kama tare da janta zuwa part din momma, Amrah da Miemie ne sukayi ihu tare da tafawa nuriyyah kam se murmushi, momma ma murmushi tayi farin cikin furucin musharraf na d’azu na kamata dukda haushin Rabi’ah da ta Shaka yau, sannan bata wani damu sossai da dukan da musharraf yayiwa sufyan ba ko kuma tace fad’a don shima musharraf d’in kasan idonshi ya tara jini............

A take en parlorn suka watse ko wacce da abinda take cewa mussaman hajjiya Zulai mahaifiyar sufyan harda habaici ta jefawa momma, girgiza kai kawai momma tayi tana shigewa part d’inta su nuriyyah suka rufa mata baya, suna shiga d’akin ya kaita har gaban gadonta tare da zaunar da ita ya duka a gabanta yana rike hannunta yace “me ya had’aku?” A dabarance ta zame hannunta tare da goge fuskanta, tana kokarin hana kuka kwace mata tace “wallahi sako na gani a wayana” ta d’auko wayan ta mika mishi amsa yayi ya karanta ta d’aura da, “duk zatona kai ne hakan yasa na fita, Ina fita ya fara yi min wasu maganganun da ban gane kai ba, shine nace mishi zan tafi ina kokarin wucewa ne ya riko hannuna kai kuma se ka sh.....”.

Kuka ta sakar mishi tana tuna abinda Anty Rabi’ah tace ‘wai seducing sufyan’ Allah ya sawwaka mata and har zuciyarta bata ji daad’in kalman asirin da ta ambace su dashi ba, ya Allah wannan wani irin masifa ne kuma ke shirin kunnu musu? Anya amincewa auren nan da tayi ba wani igiya take kuma kokarin kullawa wanchan rayuwan da suke gudu ba? Lallausar tafin hannunshi da taji akan kumatunta ne ya sata dawowa tunaninta..............

A hankali yake share mata tears d’in idonshi na kan yatsun hannun sufyan da ya fito tas akan fuskanta taune lip d’inshi na kasa yayi yana sauke ajiyar zuciya, a hankali kuma ya maida idonshi cikin nata wani irin abu da be ta’ba gani ba a rayuwanshi ya gani suna fita daga cikin idanunta zuwa nashi itama cikin kwayar idonshi take kallo cikin d’aukewar tunani, a chan cikin wata duniya ta tsinci kanta me cike da furanni na soyayya😁😁 (toh fah anzo wajen).

Da sauri ta d’auke kanta tuna wadda ke tsugune a gabanta wani irin kunya na rufeta murmushi ya saki, a fili yace “kunya na kar’banki khairrr” ya wani ja khairr d’in In a unique way da ya sata murmusawa tana boye fuskanta, mikewa yayi yace “se da safe habeebty” Tace “Allah tashemu lafiya hamma, plz ka shafa ointment a kasan idon kan nan kan ka kwanta” Kai ya gyad’a mata yana ficewa daga d’akin a parlor ya ga su nuriyyah har little suna kallon tv, be kula kowaccensu ba ya fice, da gudu Amrah da Miemie suka shiga d’akin, har suna buge juna.

Turus sukayi suna kallon gadon khairin don kwance take taja borgo zuwa kirjinta tare da juya musu baya, Amrah tace “Eyyeh soyayya manya, ke Miemie kina ganin wani irin love? Wato har ya rarrashi abunshi tayi bacci ba tare da d’igon damuwa ba” Miemie tace “hmmm kede bari, amma wannan soyayyar na san ko lokacin maman little iyaka. Hamma musharraf da ke nuna baya so shine har da tada jijiyoyin wuya ‘ummulkhairi matar da zan aura kuma yarinyar da nake so da kauna’” wani irin dariya Amrah ta sa ganin yadda Miemie ke magana wai tana koikoyon Hamma musharraf.............

Khairi na jinsu har suka gama tsiyansu Miemie ta shige bayi yayinda Amrah ta koma parlor, sossai take dariyar shirmen su Amrah tana kuma tuna kalmomin Hamma musharraf na d’azu, wani irin sanyin daad’i taji yana shigarta In kuwa ta tuna yadda ya ambaci sunanta se taji duk tsikar jikinta sun tashi, dukda zuciyarta na cike da damuwa amma d’an farin cikin da ta samu daga gareshi ya danne damuwar ya hanashi tasiri akanta har bacci ya kwasheta a haka............

Washegari

Da misalin karfe goma aka had’u a babban parlorn mamaji, kallon momma mamaji yayi yace “Da me kike tafe kika ce?” Momma tace “yarinyar da musharraf yake so kuma ze aura ita da familyn ta, mamaji inda hali so nake su zama cikin ahalinmu su kasance en uwa a garemu don basu da kowa” dadda tace “haba fatima don basu da kowa se su zama d’aya daga cikin ahalinmu? Inaaa baki san yadda duniya ta koma ba ko? Sannan a gaskiya bazamu aurawa musharraf ita ba, ba tare da en uwan mahaifinta ko danginta bayan uwa ba” Hajiya zulai tace “Ai ko da danginta baza mu yarda da auren ba don alamu sun nuna raba kan en uwa zatayi tun kafin ta shigo tunda gashi har ta had’a musharraf da sufyan fad’a”..............

D’aya bayan d’aya mamaji ke kallonsu ba tare da yace komai ba, har seda sukayi shiru tukun ya murmusa yace “ummulkhairi kaman haka naji musharraf ya anbata jiya ko?” Kai khairi ta gyad’a yace “Ina son sanin su waye ku? Da wani mugun nufi kuka shigo cikinmu?” Idon musharraf dake lumshe ya bud’e yana kallonta itama kallonshi tayi ya gyad’a mata kai cike da bata kwarin gwiwa.

A hankali ta fara bada labarin rayuwanta tun daga kan na iyayenta har ita duk parlorn anyi tsit ana jinta da kallonta har ta gama da kuka sossai a muryanta ta d’aura da “bamu da wani mugun nufi akanku sbd ban ta’ba zama da d’an uwana musulmi da zuciya fiye da d’aya ba, na tabbatar haka sauran ahalina” ta kai karshen maganan da sa bayan hannunta ta goge hawayenta, dada ma hawaye take, hajiya Aisha da mijinta uncle Nasir, diddi, salima, farida, fatima, da bappa se da sukayi hawaye tsabar tausayi da wannan ahali suka basu, Sauran en parlorn duk ta’be baki sukayi suna juya keya alamun basu yarda da labarin ba, mamaji kam cikin jimami yake kallon khairi da tunanuka fal ranshi, wadda shi kad’ai yasan abinda yake kullawa..............

Bayan shirun mintuna fiye da biyar yace “a haka kike so musharraf ya aureta?” Ya karasa yana kallon momma, Musharraf dake jin zafin kukan da khairi takeyi yayi saurin kallon mamaji, yana shirin magana yaji momma tace “Eh” cikin bada umarni yace “ban yarda ya aureta ba!!!!” ..














#vote
#share
#comment









‘Yar mutan Adamawa

🎗🎗🎗🎗🎗








                IGIYAR RAYUWA😭







                                             🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)


Story and written by: fateemah Muhammad gurin

Wattpad:- Gureenjo6763


Page➡️7️⃣1️⃣▶️7️⃣2️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

"What!!!" Exclaimed musharraf with a mouth open agape, kallonshi momma tayi da alamun gargad'i hakan yasa yaja bakinshi ya yi shiru, cikin sanyin murya momma tace "ko sbd me yasa mamaji?" Mamaji yace "duk cikin zuriyarmu bamu da wata ko wani me aljannu baza mu fara daga kanta ya zamana gaado ba, don mu yarda da aurensu ba danginta Ba komai bane sbd ko iyayenku a haka muka auro su".

Kai dadda ta dukar cike da kunya shap ta manta da su a ya aka auresu take kokarin aibanta wasu sbd rashin dangi, murmushi momma tayi me cike da manufa tace "Ai ko inde haka ne marwan baze iya auren Nuriyyah ba" da mamaki suke kallonta bappa ne ya iya cewa "ko sabi da me fatima?" Kai tsaye tace "sbd itama aljannun ne da ita, am sorry to say mamaji masu aljannun ba mutane bane? Ko akwai wadda ya ke d'aurawa bawa bayan Allah? Tuni ne kawai nake muku na san kun sani Allah ne ke qadarta wa bawa abu a yadda yaso, na boye muku nuriyyah na da aljannu ne sbd kwanciyar hankalinku.

Sbd In har kuka san dalilin samuwarsu a jikinta zaku ci gaba da d'aurawa kanku laifin komai ne" dadda tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun, menene dalilin samuwarsun?" Musharraf yace "duk wani banzan aiki na ubanmu wadda ya shafi sihiri zuwa wurin boka don cin za'be, sun za'be ta ne sbd yafi sonta akan duk mu 'ya'yanshi a rayuwanshi" salati en parlorn suka d'auka dadda kam fashewa da kuka tayi tana Allah wadai da d'a irin mahmoud.

Mamaji ma shi kad'ai ya san halin da yake ciki, Bappa ne ya dinga musu nasiha cikin ilimi da fasaha ya nuna musu kar su karaya suce zasu tsine mai su ci gaba da adu'a shine ze taimaka mishi koda Hakki ze tashi kamashi ze zo mishi da sauki, da kyar mamaji ya nitsar da kanshi tare da mai da kwallan idonshi yace "tun yaushe take fama da su? Kun yi magani?" Momma tace "tun shekara d'aya da rabi da ya wuce, Musharraf ya taka rawan gani sossai akan maganninta I cannot ask the better for them bcos he's the best brother ever, ya tsaya sossai duk inda yaji wani malami ya kaita har abin yayi sauki ba kaman da da zatayi sati bata san waye kanta ba hallitarta duk se ya sauya ni kad'ai na san irin tashin hankalin da na shiga mah......" kuka ne ya kwacewa momma tuna irin wahalan da nuriyyah ta sha a tsakankanin kan tayi sauki.

Duk parlorn nuriyyah suka zuba wa ido cike da tausayawa hakan ya sata fashewa da kuka, duk yadda mamaji yayi kokarin maida hawayen idonshi hakan ya gagara se da suka zubo, bappa ma seda yayi hawaye yana godiya ga Allah da kaddarar ta, yana mata adu'ar samun aljannah sbd hakan don tayi matukar kokari wurin cinye jarrabawarta.

Musharraf da idonshi ke kan khairi ganin zata fara wani kukan yasa ya had'e rai ya zaro mata ido tare da girgiza kai, baki ta turo tana dukar da kanta a lokaci d'aya tana kokarin mayar da hawayen tunda yace baya so su zubo, maganan mamaji ne ya katse musu tunanukan da suka fad'a da kuma kukan da wasu daga cikin en matan ke yi, "Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani irin wannan d'a, Fatima, Musharraf, nuriyyah bani da bakin baku hakuri amma Ina neman wa kaina da matata yafiyar ku, sbd duk mu ne silar komai da bamu nemi Abubakar da maganan son had'a fatima da mahmoud ba da hakan be faru ba don Allah Ku yafe mana kar hakkinku ya hana mu kwanciyar kabari".

Momma tace "Wallahi ni ban rike ku ba mamaji na d'auke shi matsayin kaddara, da IGIYAR RAYUWA na baya kulle da na mahmoud da hakan bata faru ba, so ni kam na yafe muku" Nuriyyah tace "mamaji baka min komai ba ni kam wallahi na yafewa kowa amma banda Abba" Shiru duk sukayi suna jiran jin ta bakin musharraf amma gayen nan yayi shiru abinshi kaman be san dashi ake yi ba, kuma yaki kallon bangaren momma.

Khairi ce ta kalleshi for the first time tayi niyyar bashi hakuri da sa baki a cikin harkanshi ita bata ga laifin su mamaji ba bare yace baze yafe musu ba, d'ago kai tayi se taga yana kallon ta hakan yasa ta shagwa'be fuska tare da karkatar da kai alamun plz yayi magana, juya idanunshi yayi kan ya fiddo maroon lips d'inshi da ke cikin bakinshi yana tsotsa yace "Allah ya yafemana" murmushi tayi tare da kauda kanta daga kanshi se taga idon momma akansu a kunyace ta dukar da kanta.

Tabbas khairi alkhairice a garemu taci sunanta, taga alamun musharraf ya fad'a cikin kogin Sonta da kaunarta wadda hakan ze sa ta iya tankwarashi duk da a hakan ma ta san ze iya yiwuwa wani lokacin kuma baze yi ba, maganan mamaji ne ya katseta inda yace "shikenan In Allah ya kaimu goben se a yi komai na auren a saka date da komai" murmushi momma ta sake tana kallon musharraf amma shikam kaman be san me ake cewa ba don fuskan nan ba ko d'igon fara'a a de sake yake amma ba fara'a sam be nuna ba, Hajjiya Rabi'ah ce tace "haba mamaji ya za'ayi gida be koshi ba a bawa waje, yara en matan nan ba wacce bata son musharraf amma ya dinga zuba musu wulakanci kaman ba gobe yanzu kuma se ya d'auko wata bare marar tushe yace ita ze aura? Er aiki ce fah, Ina had'i biri......"

"Dakata Rabi'ah ban cike da halin iskanci, tun jiya da na miki maganan abinda nake son yi kike share ni da jefa min habaici, wai me ke damunki ne? Ina da er uwa amma bazamu ta'ba muyi maganan sirrin junanmu ba sbd baki so, na barki kuma yanzu ince ga wacce nake so kuma d'ana yake so a matsayin suruka kice bata yi miki ba? Ke zaki zauna mishi da ita? Ko ko auren dole za'ayiwa musharraf d'in?" A hasale momma ta karasa maganan don bata manta bakaken maganganun da ta dinga fad'a mata jiya ba kawai don ta zauna da ita da diddi ta fad'a musu manufarta akan su khairi da dada.

Diddi ce tace "baki da hankali Rabi'ah, ban kuma san yaushe zakiyi hankali ba, yau da hannunmu khairi ta fara sauka ko fatima da musharraf basu yarda ba se na aura mishi ita, ki natsu ki san me kikeyi er uwarkice" cike da haushi take hararan khairi Bappa ma fad'a ya mata, ganin kusan 12 yasa mamaji cewa "maganan karshe kan watsewarmu musharraf da girmanku me ya had'aka fad'a da d'an uwanka yanzu fisabilillahi kalli fuskanshi" kallon fisha yayiwa mamaji kan ya maida kanshi kan khairi yace "fad'a musu abinda ya faru" bayani tayi musu inda anan take babanshi Alhj Ahmad da tunda yayi opening prayer be sake cewa komai ba, ya rufeshi da fad'a sossai ya mishi fad'a Alhj Nasir ma yayi mishi nasiha tare da had'ewa da yaran gabad'aya ya musu nasiha sossai kuma ya tabbatarwa en matan Afreen, Zainab, sulaimi, maryam akan tare za'a had'a aurensu da khairi da nuriyyah don haka ko wacce ta turo maneminta auren baze wuce 2months ba.

Daga nan bayan an rufe taro da adu'a aka wuce dining, khairi ta kama dada suka nufi hanyar fita har sun kai kofa musharraf yace "ke!! Ina zaki bayan kina ga abinci za'a ci?" Juyowa tayi ta kalleshi ya nuna mata dining da kanshi juyowa sukayi suka dawo kowa yayi serving kanshi Ina khairi ta sa ma dada ta tura mata rice and stew ta sa mata tare da d'aura mata hannu akan chokalin, "saka min abinda zaki ci" kallonshi tayi kaman ba da ita yake magana ba kama ma bashi yayi ba.

Tuwon semo miyan kubewa ta saka mishi ta tura mishi tare da d'iba itama ta fara ci a hankali su maryam dake dab da ita ne suke ta mita da masifa ta ya za'a had'a aurensu da wannan shashashar talakar tsab take jinsu amma ko a fuska bata wani ci na kirki ba ta mike ganin dada ma ta ajiye chokalin yasa ta kamata suka mike, diddi dake chan gefen bappa tace "bade har kun koshi ba me kuka ci?" Da fulatanci tayi maganan kan khairi ta bada amsa hajiya zulai tace "hmmm ba'a saba bane babu a house" hajiya rabiah tace "a toh Kin san irin haka in anci dayawa ciki rud'ewa yake" momma ce ta buga table d'in tare da cewa "enough, kar ku kaini makura wallahi akan cin mutuncin khairi da iyayenta ba abinda bazan iya yi ba" Hamma Ahmad ne yace "ku kiyaye don kun min farin sani be game ni naci mutuncin kowaccenku ba, zulaikha na sake ganin kin zagi yarinyar nan se ranki yayi mugun 'baci try me and see" shiru sukayi girgiza kai mamaji yayi yana kallon su dada da har sun fice ma, murmushi musharraf yayi haka yake so mommanshi ta koma baya son sanyinta nan, ya kuma lura akan khairi se ta fi haka masifancewa murmushi yayi yana me ci gaba da cin abincinshi.

Washegari da safe mazan suka zauna a take akayi komai har sadaki mazan suka bayar amma de ba'a fad'i kud'ad'en ba, na marwan da musharraf akayi na sauran se next week, kwana biyun da khairi tayi taga wulakanci kala kala cikin familyn masu sonta kad'an ne, daga familyn su musharraf se diddi, mamaji, bappa se su uncle Ahmad da nasir, se surkuwar nuriyyah matar uncle nasir hajiya Aisha amma banda yaranta marwan ne ma ba ruwanshi sufyan kuwa In har sun had'u kallon banza ke had'asu dadda ta biyewa hud'ubar su Anty Rabi'ah da Anty zulai ta tsani khairi ba gaira ba dalili.

Hakan yasa khairi ta auri zaman d'aki karfi da yaji taki fita ko dining ne, sbd hakurinta kad'an ne ba don ma halin rayuwa ba a cikinsu akwai wacce zata mata kallon banza ta Kyale, Toh yanzu ma tana kin fitan ne sbd maganin kar ayi kar a fara, kuma tunda akayi meeting na safe a washegarin da suka zo bata kara sa musharraf a idonta ba. A yau zasu koma ta gama had'a kayanta gabad'aya haka ta had'a nasu nabeel ta kai har motan da suka zo dashi don yadda aka zo haka za'a koma.

Da d'ad'aya da d'add'aya duk kowa ya wuce saura su kad'ai ita da shi don little ma su momma ta bi, tana zaune tana jiranshi suna hira da diddi, kamshinshi ne ya fara sanar da ita isowarshi kan bayyanar shi da sallama a bakinshi, kallon seconds sukayiwa juna kan suka d'auke kai, sanye yake cikin Ash suit ya sha polished cover shoe gashinshi da ya sha gyara se sheki yakeyi yayi kyau har ya gaji.

Ita kuma tana sanye da doguwar rigar atampha duk da

25 / 38