Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
yhu are the most beautiful African girl that I've ever met, Wallahi Ina sonki" and khairi can stop her self from blushing daad'i take ji har cikin ranta.
Tace "ba wannan ba yaushe zaka dawo?" Yace "au ina sonki ba important magana bane? And kuma baki amsa min bafa!!" Ya karasa da karkata wuya gefe, murmushi ta saki har yana kallon fararen hakwaranta da dimple dinta da ya lotsa, tace "ohk Ina sonka nima" lumshe ido yayi yana jin daad'in words din har cikin ranshi, kallonta da yakeyi yanzu ji yake wani abu na yawo cikin jikinshi, wani mutuwa jikinshi keyi a duk sadda ya ji sassayar muryarta, a hankali yace "randa zakuyi kamu ko menene zan dawo" juya ido tayi da sauri ya kawar da kanshi da ta san yadda yakeji In ta juya idanuntan nan da bata mishi ba, bata ce komai ba ya san bata ji daad'in randa ze dawon ba.
"Momma zata tafi Abu Dhabi jibi da safe don miki sayayyar kayan aurenki ko zakuje tare zaki fi za'ban abinda kike so?" Tun kan ya karasa take girgiza kai dama ya san baza ta yadda ba sbd kunya ya gwadata ne kawai, cewa tayi "a'a wallahi duk abinda ta sayo Ina so, na San ta fini ma sanin abinda ze min kyau" kan yayi magana yaga little ta fad'a kanta cikin murna tsayawa yayi kallonsu khairi da bata san murnan da little ke yi ba tace "little pretty me muka samu ne?".
Little tace "cutie granny tace daga next two weeks zaki zama mommy na?" Satan kallon musharraf tayi hakan yasa little juyowa ihu tayi ganin paapinta tace "Paaaapiiii is it real that cutie will be my mommy?" Musharraf yace "yes dear ai kina so ta zama koh?" Cikin murna tace "of course yes paapi, I really love her" haka suka ci gaba da hira cikin son juna musamman little da murnanta ya kasa boyuwa kusan one hour sukayi suna shan hira kan sukayi sallama.
Da dare suka koma gidan maami, kaman yadda ya fad'a jibin momma ta tafi Dubai kwananta hud'u ta dawo da set d'in akwati guda masu tsananin kyau kaya kam har da kyar ake rufewa, a ranan aka kuma kawo na nuriyyah ita ma set ne me kyau, shirye shiryen buki ya kamkama Inda Za'ayi lalle day ranan Wednesday a gidan uncle nasir aka had'u gabad'aya hajiya yasmeen da ta kware a lalle da kwalliya ne ta chancharawa amare nuriyyah da Khairi da wasu manya har momma, don gabad'aya matan familyn suka had'u, masu lalle kusan hud'u amma na hajiya yasmeen yafi had'uwa, ba abinda ke tashi a gidan se kid'a cikin wakokin hausa yara se chashewa suke, su Amrah kaman za'a karya kwankwaso, wai juyawan da zanyi se naga en mukaru da juna group mota guda wai sun zo lalle.
Kama baki nayi ina kallonsu ko wa ya gayyato su oho, su maman khalil, Aisha lawal shahud, Zainab Ads, hauwa Adam(jiddo), Nagarta, Smeenerl, salmerhalee, Maijidda, salmer Auwal, saadah Sanusi da queen mai makon su je yin abinda ya kawosu se na hange su gaban dj mace da aka kawo se rawa suke harda kwaso shoki Maman heedaya na tsaye gefe tana d'aukansu video tana dariya sbd ta samu na status da turawa a Mukaru da Juna, ganin za'a gama lalle banda ita yasa ta zame taje ta zauna aka chanchara mata nata tanayiwa su maman khalil dariya don ganin sun kusa rasawa da kyar suka shawo kan hajiya Yasmeen tayi musu Bayan sun gama tikan rawansu amma be kai na maman heedaya kyau ba haka suka tafi da haushi.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️8️⃣1️⃣▶️8️⃣2️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Buki fah yayi buki ko wani gida mutane ne fal washegari da ya kasance bridal shower da safe suka tattara gabad'aya se dukku, dada kam kin zuwa tayi ba yadda momma batayi ba taje tace bazata ba ai suma dawowa zasuyi zuwa jibi, hakan yasa momma ta zuba akwatunan auren khairi da nuriyyah d'akinta ta rufe da key tare da kiran mai aikinta akan ta dinga kwana a gidan da dada har su dawo don har su nabeela da nabeel za'a tafi.
Gabad'aya amaren da kawaye a part din momma na wurinsu dadda suka sauka duk a takure khairi take sbd bakaken magana da harara da su maryam da kawayensu ke jefanta, ganin Haka yasa nuriyyah ta jata da kawayenta zuwa d'aya room din su Amrah ma da Miemie nan suka koma, anan suka shantake suna ta hira tana mamakin karamci irin na su nuriyyah mamaki sam yaki sakinta ganin kawayen nuriyyah ne zasu zauna a matsayin kawayenta su da suka fita class da wayewa don daga en jami'a se wacce ta gama, Amrah da Miemie suna cikin kawayenta don abinda kawaye zasuyi anfani dashi duk sun d'inka.
Da yamma aka gayyaci kwararriyar decorator d'innan Muhsina maikano tayi decorating gabad'aya gidan da mutanenta mussaman inda za'ayi bridal shower din, shima taron ba maza, inda musamman chief cook din nan saadah sanusi tazo ta baje fasaharta tayi girki kala kala, momma uwar ango da amare biyu gabad'aya a busy take na saukar da mutanenta masu zuwa wasu tun daga Abuja waenda sukayi koyarwa tare, wasu mutanenta na nan gombe donma hajiya ruqayyah na taimaka mata.
Wow wow masha Allah shine abinda na furta ganin amaren nan da sukayi matukar tafiya da imanina dukkansu Allah ya zuba musu kyau ko wacce da kyaun da Allah yayita don Allah be hallici mummuna ba, amma kyaun khairi na daban ne, gabad'aya amaren anko sukayi haka kawayensu ba'a banbanta na wace da wace ba sanye suke cikin purple bridal gown me bits da kwalliyan pink, ko wacce an saka bata band daga kafad'a zuwa gefen kunkurunta light pink inda akayi rubutu da dark pink aka rubuta "Bride to be" sossai sukayi kyau sbd purple din ya kar'bi fararen fatansu, hajiya Yasmeen ta baje fasaharta wurin kyalliya da d'aurin khairi da nuriyyah wani d'an banzan hill suka saka pink da pose pink da suka rike a hannunsu a jere reras suka fito suka nufi filin bayan gidan da akayi decorating dj mace da aka d'auko ta sake musu waka me sanyi da taushi.
Nan fah taro ya fara tafiya yadda ya kamata amare kowacce ta samu gifts daidai gwargwado akayi hotuna da videos aka ci abinci daga karshe aka sake kid'a aka chashe, en Mukaru da juna ne gaba wurin rawa da suka ci ankon peach da orange se kace an gayyacesu, se na Queen bee da suka sha ankon light blue da dark blue, Chan na hango en Annur writers Association na chacewa daga baya se ga en Wattpad da nasu ankon red suka baje tasu basirar rawar su didi ta (haneefah muhammad Gurin) har kwankwasonta ya kusa karyewa, su Aisha Gurin duk miskilancinta da kunyarta seda ta zage ta kwashi shoki harda su zanku da gwara gwara.
Khairi de taga mutanen da ta rasa daga Ina kuma ba laifi sun sata nishad'i da farin ciki sossai, bayan taro ya watse ta kar'bi wayan Amrah ta tura duk hotunanta dake ciki tare da kunna data ganinshi online yasa tace "baby" ko seconds biyar be yi ba yace "qalbee ya gajiyan buki? Na san an gajiyarmin dake dayawa" murmushi ta turamishi kan tace "wallahi akwai gajiya Sweetheart ka samu tahowa ne?" Yace "Eh muna ma gida d'aya and I wanna see yhu right now" tura mishi emojin juya ido tayi da na shagwa'ba tace "akwai fah mutane dayawa a gidan nan taya zanyi in fita Inzo wurinka?".
Yace "plzzz I wanna see yhu" ya tura mata emojin plzzz, batayi reply ba se tunanin fita da take ganin bata ce komai ba yasa yace "shikenan tunda baza ki fitoba, turomin pics din bridal shower dinku I know yhu looked perfectly good and the most beautiful bride of this century🥰" murmushi tayi tare da tura mishi "tnx love an am sorry" yace "no I understand ai an kusa kai mini ke gabad'aya mu rayu har abada yadda ba wadda ze min katanga da ke".
Murmushi tayi tare da tura mishi pics din aiko ya dinka tura mata emojis din love da sauransu dariya ta dinga yi ita kad'ai, su Miemie na kallonta da mamaki juya ido tayi tace "what" waro ido sukayi Amrah tace "eyee soyayya daad'i" Miemie tace "Allah samu a danshinku" dariya kawai tayi tare da cewa "Ina son yayankun nan sossai gaskiya and he loves me equally" shewa suka sake da sauran kawayen nuriyyah suna cikin wannan maganan ne Anty Rabi'ah ta shigo da wasu cousins dinsu ta bangaren uba tare da nunata tace "kun ganta nan, itace Adda fatima ke wani tada jijiyoyin wuya an zageta, gida be koshi ba an d'auka an ba na waje, na wajen ma marar asali da gata".
D'aya daga cikinsu tace "ikon Allah gashi ba kyau tafi en familyn nan ba Ba komai ba, watakil da boka aka had'a" khairi da kanta ke kasa ko d'agowa ta kasa ranta ke wani irin tafasa kanta ya fara saarwa cikin kasa da murya tace 'not now plz' d'aya daga cikinsu tana kallon Rabi'ah tace "kuma kikace mahaukaciya ce ko? Amma haukan tashi tashi?" Ba kunya Anty Rabi'ah tace "Eh wallahi, ita kad'ai aka gani fah da uwarsu se en biyun da na nuna muku, gashi uwarsu nakasashiya wa ya sani ko a yawon maula ta samosu duka".
Jikin khairi ne ya fara 'bari fuskanta yayi jajazir idonta a lumshe tana jin yadda kanta keyi kaman ana daddatsawa da arda ko wani makami, sama sama ta fara jin maganganunsu, da sauri miemie taja nuriyyah suka fice daga d'akin zuwa part din diddi, Amrah kuma ta d'aga waya ta kira musharraf yana d'agawa tace "Hamma kazo akwai matsala, khairi ce" bata rufe baki ba ya dira daga kan gadonshi tare da ficewa zuwa part din dadda.
Basu ankara ba basu ji tasowarta ba se ji sukayi an had'a kawunansu an gwara, ihu suka tsala tare da zubewa don ba karya sun bugu, a rud'e Anty Rabi'ah tayi kofa bata karasa ba khairi ta rikota ta shake wuyanta kam duk abinda takeyi idonta na rufe, ihu Anty Rabi'ah ta dinga yi na neman taimako gani take kan azo cecenta ta mutu don ba karamin shaka aka mata ba, a take mutane suka fara taruwa don ganin abinda ke faruwa, musharraf da ya iso ne ya tsaya kallonsu shi ya rasa me ke damun mata wallahi ya tabbatar cikinsun nan baza'a rasa masu shi ba amma sun iya taruwa ganin gulma, mamaji, bappa, uncle nasir, da uncle Ahmad ne suka shigo suka korasu kan musharraf ya shiga cikin d'akin ta'be baki yayi yana gyara tsayuwa tare da tura hannuwa cikin aljuhu ya zuba masu oily eyes dinshi yana kallo.
Mamaji da be shigo ba yacewa su unlce Ahmad "na San Musharraf ze iya kula da matarshi don haka muje In baku wani hayaki kowa ya samu kasko a je babban kitchen a d'ibi wuta a yiwa gidan gabad'aya hayaki sbd na tabbatar baza ta gaza yin kara ba kuma bamu san adadin masu shi ba" ficewa sukayi da sauri don cika umarni bayan ya bawa kowa kullin hayakin yana da burin sama ma khairi da nuriyyah inganttaciyar magani in Shaa Allah.
Tsabar irin mugunta na musharraf seda yaga pendonshi ta kusa mutuwa tukun ya zare hannu a aljuhu yaje ya fara kokarin janye khairin da kyar shima ya samu janyeta tare da sanyata jikinshi ya matse don kar ta fisge tayi wani wurin, Adu'o'i ya fara tofa mata da alamu aljannin ba me wani fitina bane, cikin lokaci kankani ya tafi, tuna abinda ya faru yasa ta saka fuskanta cikin broad-chest dinshi ta fara kuka, bayanta ya dinga shafawa a hankali har ta tsagaita kukan tukun ya d'ago ta direct toilet ya shiga da ita ya sa hannu ya wanke mata face d'inta kan suka fito lokacin kusan 11 hakan yasa ya karasa da ita bakin gado ta kwanta ya lullu'bamata bargo tare da zama gefenta ya rike mata hannu.
Ba abinda yace mata itama haka har bacci ya d'auketa gyara mata blanket din yayi kan ya fice, direct zuwa parlorn diddi don duba lafiyar nuriyyah, Anty Rabi'ah ya fara tozali da se kuka take fuskanta yayi jazir idanunta sunyi zuru zuru, fad'a su mamaji suke mata akan abinda ta aikata, don miemie na shigowa da nuriyyah ta fad'awa su momma abinda ke faruwa daga ita har mahaifiyarsu cewa sukayi baza su ba a kasheta.
Bayan su mamaji sun gama hayaka ko ina shine suka zo nan din don sunga shigan Rabi'ah part din tana layi hannunta dafe da wuyanta, anan ne suka ji abunda ta aikata shine suke mata fad'a, bappa kam zagin cin mutunci ya mata har kaman ze mareta uncle nasir ne yayi ta basu hakuri har suka hakura, musharraf dake zaune gefe idonshi lumshe yana jin zagin da cin mutuncin da tayiwa hasken rayuwanshi yana tunanin da ya barta ma da khairin ya rufe kofar da key yayi tafiyarshi da keyn, kash wallahi yaji haushi.
Ita kam Anty Rabi'ah ba alamun nadama sema wani tukukin bakin cikin da takeji da aurenta da 'ya'yanta a zauna ana mata wannan rashin mutuncin sbd matar d'an yayarta duk waenda suke parlorn ji take kaman ta rufesu da duka har iyayen nata ko da tana buduruwa bazata iya tuna fad'an su bappa da diddi akanta ba sbd sanyinsu da hakurinsu amma gashi tsofe tsofe da ita an zauna ana yi mata fad'a kan wannan shegiyar da tunanuka fal ranta aka tashi taron.
Washegari khairi ta tashi fes ba wadda yayi mata maganan abinda ya faru jiya se ma hakurin da momma ta bata murmushi kawai tayi, da yammacin ranan sukayi walima inda manyan malamai da aka gayyato wasu tun daga kano sukazo suka baje fasaharsu a kan zaman aure da bautar da ke ciki, amare sun sha kyau cikin lafayarsu maroon me tsananin kyau da tsada, su hassana s Fagge na hango an natsu ana jin wa'azi, daga gaba gaba na hangi Anty wasia(ummu rijaal) itama zaune tana jin wa'azi da er joter d'inta tana jotting abubuwa masu anfani da ake fad'a, Chan na hango kawata sadiya muhammad sanye da orange lafayarta itama an natsu ana jin wa'azin.
Fatima Usman hadeija aka had'a da snacks da za'a ci a waliman inda tayisu masu shegen daad'i su samosa, spring roll, fish roll, fish pie, donuts da meat pie se drinks su aka ci a waliman, washegari da safe bayan an sauko juma'a aka d'aura aurensu d'aya bayan d'aya a babban masallacin juma'an dake cikin garin dukku inda suka ga ruwan mahalarta wannan aure motoci kaman zasu fasa dukku sbd mutane to auren mutane biyar kuma ba laifi 'ya'yan masu harka da masu akwai.
Kwance take kan gado su Amrah da Miemie da wasu kawayen nurriyah cike da d'akin suna shan kwalliya sbd hoton da zasuyi kan wucewa gombe a ranar gabanta se fad'uwa yake da ta rasa dalili sanye take da tun kayan baccin safe ko wanka batayi ba bare maganan kwalliya, kaman a cikin dodon kunnenta takeji yadda masu busa algaita ke ta busawa maroka kuma nata shelan an d'aura an d'aura.
Tsaban gulma irin ta maroka na fad'i ba'a tambayeka ba suka dinga fad'an sadakin kowa, na nurriyah da aka fara d'aurawa dubu d'ari biyu, se na maryam dubu d'ari da hamsin, na zainab dubu d'ari, suna jira suji na khairi dubu hamsin se suka ji, "me gayya me aiki wato me kankat Alhaji Abubakar mahmoud Adam ya biya sadakin matarshi ummulkhairi farouq umar akan tsadadden set na gwal da kud'insu suka haura dubu d'ari shidda da hamsin" gud'a su Amrah da kawayen nuriyyah suka sake, momma kam seda tayi hawaye tsabar farin cikin abinda musharraf ya aikata don ko ita bata san sadakin da yayi niyyar badawa ba, hajiya ruqayyah kam seda ta tattaka don turawa Anty Rabi'ah da hajiya zulai dake zaune bakin ciki sadakin erta me uwa da uba da gata be kai ko rabin na wacce suke kira marar asali ba.
Shigowar text taji a wayanta a yayinda hawaye ke kwaranya daga ramin idonta zuwa kyakywar fuskarta, bata ta'ba tunanin zatayi aure me mutunci da daraja irin wadda tayi ba su momma sun gama musu komai, yayinda musharraf ya tabbata numfashinta, farin cikinta, sanyin idaniyarta ya kankaro mata daraja da ta tabbatar a fad'in family d'inta da nashi da kyar a samu wacce aka bada sadakinta da gold, karanta sakon tayi kasan makoshinta ga abinda sakon ke cewa "Alhamdulillah, finally Mrs Abubakar mahmoud Adam" kuka me sauti ta fashe dashi.
Su Amrah suka rufeta suna mata wakar ta zama d'auko riga, ta zama d'auko hula, ta zama d'auko kwano ta zama ta zama d'auko wando, wani kukan ta kara sakewa, bayan duk an wawatse zaune yake da dakakkiyar Farar Australian geztner da yaji d'inkin er ciki da babbar riga sabuwa gal har d'aukan ido yake kanshi sanye da hula zanna masu zare dark blue takalmin cover dake kafanshi ma dark blue hannunshi sanye da wata arniyar agogo ta kampanin Gucci golden se zoben zinari dake yatsarshi na tsakiya yayi kyau har ya gaji duk yadda ya motsa se kaji fitinannen kamshishi na tashi, wayan hannunshi yake kallo bayan ya tura mata sako datanshi dake kunne yake kokarin kashewa sbd sakkonin taya murna suke ta rige rigen shigowa, magana yake da haidar fuskanshi washe da fara'a kaman ba musharraf ba kowa ya ganshi ya san yau ranar farin ciki ne a gareshi.
Mistakenly hannunshi ya danna wani sako da number ne kad'ai har ze fita se kuma ya tsaya karantawa, a take ya mike, waro gabad'aya idonshi yayi kan wayan zuciyarshi na dukan tara tara ba ma uku uku ba, wani irin jiri ne ya d'ibe shi ba don haidar yayi saurin rikeshi ba da ya zube kasa Allah yasa ba mutane dayawa a wurin duk an tattafi, hannunshi haidar ya kama zuwa mota binshi kawai yake ba don