Advertisements
Chapter 2 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 38

3K to 6K   out of 113.1K words

sun shigo mazan suka taru suna kokarin cire hannun Maman hauwa a cikin na khairi amma abun ya ci tura da sauri Abba ya nufi kitchen ya d'auki cup tare da kanfatan ruwa a randar kasarsu wasu adu'o'i yayi da sauri da sauri ya tofa tare da zuwa ya watsawa khairi a fuska wani irin ihu ta sake tare da sulalewa kasa ta sume nan kukan Maman hauwa ya cika gidan ita da 'yarta tana ta fad'in "ta karyani shikenan ta nakastani kaman uwarta" nace(Lallai matan nan wato bakin nan be mutu ba) wasu daga cikin waenda suka shigo ne suka fice da ita, yayinda gidan ya saura daga su Abba se sulaimi da iyayenta, wasu adu'o'in Abba ya karatofawa a same ruwa tare da watsawa khairi a hankali ta motsa tana dafe kanta da take jin kaman ze rabe sheshekar kukan mahaifiyanta da kannenta yasa ta fashe da kuka itama dukda bata san me y faru ba amma tasan abun beyi kyauba, sulaimi ce ta kamata zuwa kan taburma inda Abul ya kama hannun Dada ya zaunar da ita yana share mata hawaye Abba kuma na lallashin su nabeel, seda iyayen sulaimi suka ga gidan ya d'an natsu tukun suka saka 'yarsu a gaba suka fice suna adu'ar Allah ya kiyaye gaba, sossai khairi tayi kuka inda take ta maganganu tana neman yafiyar iyayenta musamman dada da ta sa kuka anan ne take fad'an "wlh Abba ban mata komai ba haka ban saka idi shed'an bugunta ba Wlh banda masaniyar hakan ze faru da data bangajeni ban tanka mata ba da shiru nayi kaichona...." Abba ne ya katse ta "kul uwar alkhairi yi shiru abinki ba laifinki tun kafin a haifeku take nuna mana wannan hali, ta musgunawa mahaifiyarku ba kad'an ba" Abul yace "Abbanmu me kuka mata?" Shiru Abba yayi kaman baze yi magana ba kuma se yace "talatu tazo ta same mu a unguwan nan da farko a mutunce muka kar'beta duk da bamu san inda ta fito ba hakan be hana mu bata kulawa ba ganin babban ciki a jikinta kuma tana halin neman taimako ni nayiwa Bala dillali magana ya bata gidan da taken nan haya da yake da d'an kud'inta ta zo shawarana ta tambaya na sana'an da zatayi inda na bata shawaran yin abincin sayarwa a bakin kasuwa wadda har yanzu shine sana'anta bayan kwana biyu da ta d'an natsu se ta tareni da wani magana wai In ta haihu na yarda na aureta tunda matata makauniya ce, sam na nuna mata bana sonta ta nemi wani namijin tun Ina mata yadda zata fahimta taki har taja na fara wulakantata ana haka ta haifi 'yarta mace har nan ta zo ta roki mamanku wai inje In ma 'yarta hud'uba da sunan da yamin mamanku bata damu ba kasancewar bata san abunda ya faru tsakanina da ita ba, ta tursasani naje nama hauwa hud'uba da suna hauwa, bayan haihuwan hauwa ta ci gaba da bina ni kuma naci gaba da wulakantata har ya kai na kai karanta fadan sarki inda ya ce ta fita harkana don ta matsamin har kasuwa take bina daga lokacinfa ta d'auki tsana ta daura mana da mahaifiyarku ko motsin kirki bamu da daman yi shine har ya gangaro kanku, kun ji fah"..........








#vote
#comment
#share


'Yar mutan Adamawa



πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—






IGIYAR RAYUWA😭




πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Written & story by: fateemah Muhammad Gurin


'Yar mutan Adamawa

Page➑️5️⃣▢️6️⃣
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Tsaye yake gaban balcony d'inshi idonshi na kan rana da yake shirin fad'uwa a lokaci d'aya hannunshi rike da karan sigari (taba) yana busawa kare mishi kallo na tsaya yi kai gaskiya gayen had'add'e ne sossai akallah zeyi 34 sanye yake da dark blue jeans da wani yellow riga me kaman sweater da gashi gashi a jikinshi long sleeve me had'e da hula igiyan hulan sun sauko gefe da gefe har kan faffad'an kirjinshi, kyakyawar kafanshi fari tas me d'aukan hankali sanye da yellow normal flat shoe na maza na companin Gucci, a natse na kai idona kan fuskanshi Ina kare mishi kallo, yana da round face me d'an fad'i tare da kananan ido da ya had'u da tsiriryar hancinshi zuwa kan lips dinshi masu fad'i kad'an red ko kuma ince maroon kasancewar shi me shan taba lips dinshi yayi baki kad'an se ya had'u da red lips dinshi ya bada wani color me d'aukan hankali, abinda yafi d'auke hankalin mata kai harda wasu mazan a fuskanshi shine kwantaccen bakin sajenshi da ya mugun kawata fuskanshi gashin kanshi kaman wadda akayi coiling tsaban yauki da murdewa wadda ya zo har kan goshinshi kai masha Allah, duk da idonshi fad'uwar rana yake kallo amma tunaninshi ba nan yake ba yayi zurfi cikin tunanin bakar rayuwanshi na baya me cike da duhu da tsananin kalubale tabbas his father is the villain of his story a take madaidaitan idanunshi da ake referring as kanana sbd kankancesu da yake yi suka koma red a fili ya furta "A bad egg" meaning worthless person, kara zukan taban da ya rike da hannun hagu yayi cikin kwarewa har seda karan ya kare jefarwa yayi a kasa yana shirin kunna wani kenan wayanshi dake cikin pocket dinshi ya fara ringing, kaman baze fiddo ba yana yatsuna fuska ya fiddo yana kallon fuskan screen din wayan nashi da ya kasance Samsung galaxy latest one d'in, 'My little' ya gani karamin murmushi da bai gama maye fuskanshi ba yayi tare da d'auka ya kara a kunnenshi cikin murya irinta yara yaji tana cewa "Afternoon paaapi" yace "Afternoon sweetheart how are yhu?" Daga d'ayan bangaren tace "I'm Fyn paapi, paapi I mistakenly broke my laptop" yace "Ohk baby uncle murtala will fix it for yhu, where is my momma?" He guess tana juya manyan idonta masu kama da balls da ta d'auko daga mahaifiyarta, sunan kawai da ya kira na 'mahaifiyarta' da yayi guessing a zuciyarshi yasa yaji ranshi yayi matukar 'baci d'an fara'an da yake kan fuskanshi duk ya 'bace a sama sama yaji tana cewa "she's at her sitting room lemme take the phone to her" a kasalance yace "no baby I will call her later, bye take care" ya kashe wayan yana sauke nannauyar ajiyar zuciya juyawa yayi zuwa cikin bedroom dinshi anan ya cire kaya daga shi se boxers, cikin tafiya ta cikakkun maza da suka sha gwagwarmayan rayuwa ya nufi bayi tare da tara ruwa a jacuzzi ya shige ciki tare da lumshe ido yana tuna bakin azabar da ya sha a rayuwanshi......

**
Safa da marwa kawai take tana tunanin hukuncin da zata d'auka akan malam umar sanda da familynshi idonta ta maida kan hannunta da yau kwana biyu kenan da aka gyara gurdewan wrist din amma maimakon ya sa'be se kara kumbura yake yi, kaman yadda suka sa ta wahala se ta d'an d'ana musu bakar azaba rayuwa tabbas akanta zasu san kaidin mace da ake cewa ko shed'an tsoronshi yake murmushin mugunta tayi da ta tuna abunda ya rabo ta da garinsu wani d'an banzan munafurci ta had'a har yakai aka yi rashe rashen rai Allah ya taimake ta tana da ciki da an Kone ta manyan sukace a barta albarkacin cikin jikinta taje amma kar ta sake shigowa cikin garin ko da bakin wasa shinefa ta shigo cikin garin jalingo, wani murmushin tayi tace a fili "zaka San ka sa mahaukaciyar 'yarka gurd'ani, bazan bari na warke ba a yau zan aikata abunda na kudurta akanka, se kayi zaman gidan kaso na shekaru kan ka fito kuma iyalanka sun tagayyara" wayanta ta fidda ta kira wasu 'yan iskan 'yan tasha tace su sameta da dare akwai haaja..

Tsaye take a jikin ginin kitchen d'insu ta jingina kanta da jikin gini gabad'aya jikinta a sanyaye da fad'uwar gaba da take fama dashi tunda garin Allah ya waye, Abba dake zaune kan taburma kusa da Dada ne ya kalleta, da yake yau ya dawo da wuri tun 4 ya shigo gidan suna ta shan hira abinsu Abul na zaune gefensu kan turmi yayinda nabeel da nabeela ke wasa a tsakar gidan duk rabin wasan fad'a ne, Abba na shirin magana kenan nabeel ya kwasa da gudu zuwa kanta yana Jan hannunta yace "Adda khairi Ina ni kika ce In na iya karatu zaki ba biyar In saya sweet?" Nabeela ma tazo da gudu ta taho ta rike d'ayan hannun tana cewa "A'a Adda khairi Ina ni kikace zaki bawa? Ai kince nafishi iya karatu koh" da Lafiya klau ne zatayi murmushi tace 'eh duk wadda ya iya karatu shi zan siyama sweet banda me kan kifi' Ai kuwa se su hau musu da bitar karatunsu duk da take musu, Amma yau se ta daga musu tsawa "dallah ku kyaleni haba!!!" A tsorace suka matsa suna kallonta Abul yace "er uwa??" Da tsantsan mamaki a muryanshi don ko mutanenta suna kusa ne tana fama da ciwon kai da bugun zuciya lalla'basu takeyi su kyaleta ba tsawa haka ba yayinda mutanentan karan kansu suke tsananin son kannen nasu, kuka ta fashe dashi harda shesheka se duk sukayi shiru suka zuba mata ido Abba da kanshi ya tashi yaje ya kamo hannunta ya karaso da ita kan taburman seda ta zauna tukun ya zauna yana zama ta fad'a jikinshi ta kuma fashewa da wani kukan da yafi na da, Dada tace "Eyyah bongel am me ke damunki ne haka? Tunda garin Allah ya waye na lura bakya cikin natsuwa da farin ciki sam me aka miki?" Cikin kuka tace "Dada nima ba za'bina bane d'aga muku hankali Wlh ban san me ke damuna ba ga gabana dake ta fad'uwa" Abba yace "In shaa Allahu alkhairi ne ki dinga maimaita la ilaha illalahu wahdahu la sharika lahu lahulmulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumitu wa huwa ala kulli shai'in qadeer, zaki ji sauki In shaa Allah" Kai ta ringa gyad'awa tana ci gaba da shesheka Abul yayi shiru ya zuba mata ido, suna zaune shiru shiru duk jikinsu a mace har aka kira magrib suka mike kowa yayi alwala ya gabatar da sallah sukayi duk activities d'insu da suka saba bayan sunci abinci Abba ya mike yace "bari inje In zo" duk suka had'a baki wurin cewa "A dawo lafiya Abbanmu" yana fita Maman hauwa dake tsaye ta daka tsalle har da fame ciwonta amma bata damu ba dama da suka fito sallahn magrib ta aiki wani yaro ya kai mishi papper da ya kunshi rubutun sarki na son ganinshi bayan isha don shine limamin babban massallacin sarki dake cikin unguwan sarki unguwansu kenan na nan cikin jalingo, tana ta Allah Allah kar ya lura ba stamp na sarki Ai kuwa be luran ba ya fito don zuwa, ta had'a baki da wani dogari da yake cikin masu gadin gate akan idan yazo yace sarki ya ce ya zauna ya jirashi zuwa In ta kirashi se ya kuma cewa, sarki ya ce yayi hakuri ze sake nemanshi. Maman hauwa na shiga gida ta samu kujera ta zauna tana kallon samarin nan su biyu tace "kuje kuyi aikinku, ki tabbatar yayi kaman fyad'e aka mata" Kai suka gyad'a suka shige d'akinta suka hau kan 'yarta na cikinta tsabar bakar zuciya da hassada ne ko me zan kira wannan tana ji tana gani wasu suka hau kan 'yarta duk don bakantawa wasu bayin Allahn da ko mummunan zato basa d'aurawa a kanta, dama chan 'yarta bata da budurci sbd business takeyi da ita sossai amma yau ta ce wa samarin nan su mata kaca kaca se tayi kaman fyad'e aka mata...

Malam Umar sanda ganin ya dad'e sarki be aiko ayi kiranshi ba yasa ya mike ya sake samun wannan dogarin ya tambayeshi hakuri dogarin ya bashi akan sarki abubuwa sun had'u mishi ze neme shi, godiya mal umar yayi tare da ficewa shapp ya manta hanky d'inshi da ya shimfid'a ya zauna akan dakalin kofan sarkin yayi gaba abunshi, nan dogarin da suka had'a baki ya kirata ya fad'a mata Ai kuwa tayi murna tace ya kawo mata dama ta samu takalminshi sawu d'aya zata had'a.. yana shiga gida ya samu har yara sunyi bacci seda suka ga shiganshi tukun ummulkhairi ta d'auki nabeela yayinda Abulkhairi ya d'auki nabeel sukayiwa juna se da safe suka shige d'akunansu don dare yayi.....

Washegari - wadda sukayiwa lakabi da bakar rana.

Bayan sun dawo sallahn asuba Abba ya shiga wanka yayinda Abul ya d'auki tsintsiya ya fara share musu tsakar gidan inda Khairi na kitchen tana shirin abun breakfast d'insu, bayan Abba ya fito ya shige d'aki don shiryawa zuwa kasuwa wani irin banko kofa akayi da yasa khairi fitowa da gudu Abul ma da yanzu shiganshi bayi don yin wanka ya fito da sauri Abba ma da sauri yasa riga ya fito dogarawa ne da polisawa a tare inda suna ganin Abba suka kamashi police d'aya ya rige kugunshi d'aya kuma ya kama hannunshi ya sa mishi handcuff cikin rawan murya khairi tace "bayin Allah lafiya me yayi muku?" Ta karasa tana kallon Abba da yayi mutuwan tsaye hawaye na zuba a idonta kaman panpo wani daga cikin dogarayen ne yace "kana nan kaman mutumin Allah limamin massallaci dakai da aikata aika aika irin haka, munafukin Allah ai Allah ba Azzalumin bawanshi bane kaima Kana da 'ya buduruwa" Abul yace "me yayi na wannan cin fuska haka?" Abba dake ta kallon Dada da tafito tana dogara sanda har bugewa take tsaban rud'ewa, a matukar firgice ya juyo jin wani dogari yace "fyad'e yayiwa 'yar mutane" a tare sukace "me??????"😳







#vote
#share
#comment




'Yar mutan Adamawa


πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—







IGIYAR RAYUWA😭





πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

Story & Written by: fateemah Muhammad Gurin

'Yar mutan Adamawa

Page➑️7️⃣▢️8️⃣
πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—

A kullum mahaifiya itace jigo a kan ko wani hali d'a ze shiga tana tsayama d'a akan ko wani kaddara ze fuskanceshi tabbas ya yarda da kalman nan na 'behind every successful man their must be a woman' in ba don mahaifiyarshi ba be ta'ba tunani ko zato ze zo inda yake yanzu ba, ta tsaya tsayin daka akanshi da rayuwanshi, ya ginu ne bisa kalaman nan guda uku "hakuri, kaddara, jarabawa" ya ga jarabawa iya jarabawa amma da ya kasance me hakuri da yarda da kaddara se hakan ya zame mishi nasara a rayuwa..

Maganan momma ne ya dake shi da kalaman da ba sabo bane a gareshi ya saba jinsu kullum In har yana tare da ita ko ze yi waya da ita "babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da kaddarar Allah, wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne kuma abinda be so faruwansa ba to haqiqa ba zai faru ba, Allah ya rantse cewa hakuri Alheri ne ga masu yinsa a inda yake cewa 'kuma Lallai idan kukayi hakuri toh babu shakkah shine mafi alheri ga masu hakuri' Musharraf ka sani masu haquri ne kawai ake cikawa ladar su ba da lissafi ba, toh kai me yasa bazakayi haquri ka rungumi kaddaranka da jarabawar da Allah ya saukar maka a rayuwa ba? Shekaru Akallah 4 ba wasa bane sam kaki bari komai ya wuce a rayuwanka? Ya ci ace yanzu ka manta da duk wani rayuwan mu na baya, ka samu mace ta gari ka aura itace zata zama fitila me haske rayuwanka da ta jima cikin duhu, Ina maka adu'a a kullum randa na gaji kuwa sede kaji an d'aura maka aure na gaji da wannan halin naka" karyewa muryanta yayi alamun kuka na shirin kubce mata, idonshi dake runtse ya bud'e sunyi ja kaman an zuba mishi yaji yana jin tsananin ciwo da zafi a zuciyarshi cikin sanyin murya yace "kiyi hakuri momma" karamin murmushi tayi daga 'bangarenta tace "nayi Musharraf" ajiyar zuciya ya sauke shi de bayan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi da suke ciki d'ayaΒ  se 'yarshi ba macen ko namijin da ze kara yarda dashi a duniyannan kuma har yanzu ta'bon zuciyarshi d'anye ne sam be shirya wani aure yanzu ba ko nan gaba sbd ya gama sarewa da al'amarin mata, "Allah ya maka albarka ya za'ba maka mata ta gari" a sanyaye yace "Ameen Ina su Miemie?" Tace "sun shiga school Amrah nada lectures so ta raka ta" "uhm" kawai yace sun d'an ta'ba hira tukun sukayi sallama yana jinshi wasai..........


***

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun" Da Abul ke ta nanatawa ne ya dawo da ummulkhairi daga suman tsayen da tayi, idonta ta kai inda dogarayen suke tare da polisawan da suka sama Abbanta ankwa, wayam taga wurin ba kowa alamun sun tafi dashi tana daskare a wurin wani irin kuka ta fashe dashi tana d'aura hannu akai a rud'e tayi hanyar kofa da gudu riketa Abul yayi hawaye na gangaro mishi fisfisgewa ta fara tana cewa "Abba! Abba!! Abbaaaaa!!!! D'an uwa sakeni sakeni kana ga zasu tafi da Abbanmu Wlh karya ce karya sukeyi Abba baze ta'ba aikata zina ba a rayuwanshi balle yayi wa wata 'ya mace fin karfi wacce irin shafin kaddara ce ta bud'e mana waiii hande 'yan boni(yau mun shiga uku)" ta karasa da wani irin kuka tana d'aura kanta kan kafad'an d'an uwanta shima hawaye kawai yakeyi yana tuna hukuncin fyad'e tabbas ya san Abbansu bazai aikata mummunan aikin nan ba amma ya san duniya da sharrin mutane ze sa a d'aureshi a matsayin mai laifi toh ma wacece yarinyar? Me shedansu? duk be sani ba, idonshi ne ya sauka akan Dada

2 / 38