Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
magananshi inaga duhun da yayi da kuma gashin dake kanshi da ya tara kaman ba Indiye don har bayan wuyanshi ya sauko se kuma lips dinshi da suka koma maroon yasa ta kasa ganeshi, nan ta dinga zuba mishi surutu wani ya amsa wani yayi murmushi har muka isa.....................
Abu na gaba da na lura ya shafawa kakkanninshi ta wurin uba laifin ubannashi don da In munje dukku wurinsu yake fara sauka suyi wasa da dariya kan ya wuce part dinmu amma wannan Karo ko kallon part d'insu be yi ba ya wuce namu, da suka had'u ma da kyar ya gaishesu suna mishi wasa ma ko murmushi be d'aura a fuskanshi ba balle magana, har kuka sukayi sbd hakan, sossai na mishi fad'a amma ba abinda ya sauya..............
Da iyayena kawai yake d'an wasan jika da kaka, kwana biyu mukayi muka dawo cike da alhinin sabon halin musharraf en uwan mahaifinshi da suka fito ciki d'aya ma ba magana yake musu ba bayan gaisuwa, muna dawowa kuma ya ci gaba da shaye shayenshi sossai fah kaman ba gobe sossai na tsorata na kira en uwana muka zauna hamma Nasir, Ahmad se Tahir da Rabi'ah sossai muka tattauna inda taheer ya bada shawaran kaishi gidan tauri................
Tashi d'aya na ki, hamma Ahmad ne yace akwai doctorn da ya sani yana treating irin abun ze tuntu'beshi yaji, sannan dole se mun dage da adu'a kuma tunda yana so na sossai duk duniya ba wadda ze girmama magananshi se ni, In dinga nuna mishi tsanata ga kayan maye sannan wa'azuzzukan da sukayi magana akan shaye shaye ki nema mishi caset din yana ji..................
Sossai na aminta da shawaran yaya Ahmad inda daga nan muka dage ana treating dinshi ina nuna mishi 'bacin raina ga wa'azi da dama ya sani amma yake takewa cikin wattanni uku mukayi nasarar sashi dena shaye shaye, se taba kawai da har yanzu be dena sha ba wadda muke fata ya dena,Β a bayan hakan ya koma aiki ta hanyar mahaifin amininshi haidar wadda lokacin da shima yaji labarin an sakeshi ba karamin kuka yayi ba, Ashe kuma duk shekarun nan yana ci gaba da kula da business d'insu Inda yake wa musharraf savings din nashi share d'in account daban da ya bud'e mai da ya bashi atm card din, ba karamin murna mukayi ba gabad'aya har musharraf a lokaci d'aya ya mana hidima mai yawa har chanjin furnitures da sa na d'akinshi, motoci biyu da ya saya bayan tsohon nashi..................
Abuja ya koma da zama sede yana yawan zuwa weekend anan cikin nasara ya koma aiki don ana yawan tura shi assignment kasashen waje da haka yayi ta samun karin matsayi har zuwa yanzu ya kaini makka a first year dinshi na komawa aiki haka In an bashi assignment zuwa wani kasa se ya za'bi kanwanshi d'aya su tafi tunda d'awainiyar ba kanshi yake ba, Toh kinji khairi wannan ne tarihin musharraf kinji sanadiyar tsana da wulakancin da musharraf ke yiwa mata bayan ni kannenshi, ershi da mamana....................
Kinji sanadiyar da yasa ya dena sakewa en uwana mussaman waenda suke ciki d'aya da Mahmoud...........
*********
Kuka kam khairi tayishi ba kad'an ba, wani irin imani ne ya shige ta ashe nata rayuwan nafila ne da nasu sossai tausayin musharraf ya shigeta sam kuma bata ga laifinshi na tsanan mata da yayi ba kuma bata ga laifinshi na maganganun da yake yiwa mahaifinshi ba.................
A hankali tace "na Amince momma zan yi iya kokarina In shaa Allahu wurin ganin hamma musharraf ya koma rayuwanshi irin na da me cike da tausayi da son mutane, haka kuma In shaa Allahu baza ki sameni da halin cin amana irin na surrayah ba" hawaye momma ta share tana murmushi lokaci d'aya cike da jin daad'in kalaman khairi tace "na gode khairi, na gode" mikewa momma tayi ganin har magrib ya kusa basu yi la'asar ba ta fita tana istigfari Allah ya taimaka tacewa su Amrah suyi girkin dare.................
Bayan tayi sallahn la'asar ta fito da azkar a bakinta na tuban rashin sallan la'asar a kan lokaci se lokacin take tunanin inda su nabeela suka shiga, a gaban wani door size enlargement d'inshi dake parlorn ta tsaya tana kare mishi kallo, sossai ya had'u a hoton sanye yake da three pieces suit dark blue da ya matukar fito da haskenshi, hoton tana ga ya jima don red lips ne dashi a cikin hoton se kuma kanshi a aske cikin askin low-cut gashin ya fara fita amma be cika kan ba................
Yana murmushi ne farin hakwaranshi sun fito reras se daga tsakiya wushiryanshi ya nuna sossai haka dimple dinshi ya lotsa kuma a d'an d'osane yake akan irin kujera mararΒ baya me juyawan nan, a zuciyanta tace 'masha Allah he's so handsome kai more than handsome ma and at the picture he looks so young, adoring, charming, and sexy at the-same time' kusa da kunnenta taji muryanshi yana cewa cikin sanyi "ya dai en mata? Irin wannan kallo haka" zaro ido tayi tana juyowa murmushi ya sakar mata don ba karamin dariya ta bashi ba ganin yadda ta kwalalo ido kaman ze fad'o, kan ya wuceta yana barinta da tsananin kunya da kamshin turarukanshi.................
Tana nan tsaye kaman statue taji su little sun rungumeta suna ihu maida idonta kansu tayi tana murmushi tace "oyoyo Ina kuka shige ne?" A tare suka ce "wurin wasan yara and shopping" nabeela tace "mun sha wani abu mai daad'i Adda khairi ashe shine ice cream inji paapi" nabeel yace "paapi ya sayamana five five pairs of English wears kin gansu" little tace "cutie look at my new teddy bear" nabeela tace "and mine too" nabeel yace "look here Adda khairi my new aeroplane zan d'aukeki a ciki phewwwwwwww to makkah" murmushi sossai takeyi ta rasa maganan wa zata amsa se kawai ta duka tana dudduba abinda suka sawo tana murmushi d'ago idon da zatayi ya fad'a cikin nashi yana jingine da bakin kitchen hannunshi rike da table water na faro, shima su yake kallo da murmushi a fuskanshi don sossai suka burgeshi dama yaran sunyi enlightening mood dinshi ganin sun had'a ido yasa ya d'aga mata gira d'aya asking what the look for, da sauri ta kauda kai tana murmushi..................
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
πππππ
IGIYAR RAYUWAπ
πππππ
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Pageβ‘οΈ6οΈβ£3οΈβ£βΆοΈ6οΈβ£4οΈβ£
ππππππππ
Bata kara kallon inda yake ba ta ja su d'akinta suna ci gaba mata da surutu, harhad'a komai nasu takeyi cikin sauri don kar magrib ya musu a waje bayan ta gama suka fito zuwa parlorn ba kowa hakan yasa ta ja su zuwa d'akin momma sallama sukayi mata ta kira driver akan khairi na fitowa ya kaisu gida, bayan sun fito ta shiga d'akin su Amrah ta musu sallama haka ma nuriyyah..................
Suna fita bayan sun shiga mota little ta sa kuka da mamaki khairi ke kallonta kan ta bud'e ta fito ta duka a kusa da ita tace "little pretty me yasa kike kuka haka?" Tana tura baki tace "I want to go with yhu plzz" khairi tace "sorry pretty ki zauna a gida kinji, ai gobe ma zan zo" tana kallonsu nabeela da suma sukayi raurau da ido tace "but ai bada su zaki zo ba" ba lallashin da khairi bata yiwa little ba amma tace ita kam se ta bi su..................
Tunda suka fara yana tsaye jikin windown parlornshi yana kallonsu yana murmushi da be san dalili ba, ganin taki hakura ne yasa ya had'e rai tare da fitowa ya tsaya a bakin kofa ya ce "little" juyawa tayi tana kallonshi kan ta fara tafiya zuwa wurinshi hannunta ya kama ba tare da yacewa khairi komai ba ya juya suka shige part d'inshi, ajiyar zuciya ta sauke kan ta shiga mota suka wuce......................
Suna isa gida ana kiran magrib, hakan yasa sukayi alwala kawai kan suka shige d'aki sbd hadarin da ya had'e sama ga kuma sauro, bayan sunyi sallahn magrib dada tace "khairi Maman hamdiyya na nemanki tace dan Allah In kin dawo In ce ki shiga" mikewa khairi tayi tana tunanin ko lafiya? Ba tare da ta tsaya karatun bayan magrib ba tace "bari inje inji menene dada" da Toh dada ta amsa ta kan ta fice....................
Da sallama ta shiga gidan Maman hamdeeya dake tattare tattare tana murmushi tace "ke wallahi khairi kirkinki yayi yawa tun yaushe rabon da ki shigo gidan nan?" Khairi tace "afuwan Maman hamdeeya wallahi abubuwa ne suka had'e min gashi ba lokaci ba gashi na shigo ba" Maman hamdeeya tace "dama ke kullum akan bada hakuri kike daga kinyi laifi" murmushi kawai tayi a lokacin Maman hamdeeya ta gama tattare abunda ya sawwa ka tayi mata iso zuwa d'akinta...................
Bayan sun zauna ta matsa ta kama hannunta tace "Alfarma muke roko a wurinki khairi, Dan Allah kiyi hakuri ki amince da bukatarmu na auren baban hamdeeya" da sauri khairi ta zame hannunta tana mata wani kallo na baki da lafiya kan tace "Maman hamdeeya??? Wani irin magana ne wannan anya kuwa kina cikin hankalinki?" Maman hamdeeya na murmushi tace "Lafiya ta kalau khairi kawai de ina son hakan ne don haka ya bukata sannan ni wallahi er uwa na d'aukeki ki amince da auren nan yadda zamu cigaba da rayuwa tare cikin kwanciyar hankali" khairi ta had'e rai kan tace "bana sonshi" Maman hamdeeya ta waro ido tana cewa "ba kunya khairi a gabana kike cewa baki son mijina?".....................
Khairi tace "Au Ashe da kunya, shi be ji kunyar sanar dake yana so na ba? Abarma wannan maganan plz ni na samu wadda nake so yake sona aurenmu kawai nake jira" bata jira amsan Maman hamdeeya ba ta mike ta fito tana kiranta amma ko waiwayowa batayi ba ta tafi bayan ta koma gida ta d'an ta'ba karatu kad'an se kuma aka kira isha mikewa sukayi suka gabatar kan khairi ta saka musu abinci suka ci.....................
Bayan sun gama su nabeel sun kwanta khairi tace "Dada Ina da muhimmiyar magana dake" Dada tace "Ina jinki khairi" khairi tace "Dada........ na samu wadda nake so ne, and kuma yace ba maganar 'bata lokaci yana so ayi aure cikin lokaci kankani" Dada kallon setin da muryan khairi ke fitowa baki sake tayi a hankali tace "aure? Khairi kin san kuwa me kike cewa?" Khairi tace "na sani momma, yana sona haka mahaifiyarshi na sona, haka en uwanshi kinga ba dalilin kin yin auren, In fa kin amince kenan, amma kan amincewarki Ina so in baki labarin waennan ahali inda zaki yanke hukunci ko In shiga cikinsu ko kar na shiga" Shiru d'akin ya d'auka se muryan khairi da ke fita cikin kuka da tausayawa don In itane kam Allah ta tuba baza ta iya jurewa ba, da kullum tana cikin kuka sbd ba karya Allah ya jarabce su....................
Dada ma seda tayi hawaye, tana mamakin wani irin juriya da hakuri ne ga wannan mata, tabbas momma da ahalinta sunga jarrabawa, a hankali tace "yana sonki khairi?" Khairi cikin hawaye don se yanzu labarin ya gama game ta tace "Eh dada" dada ta kuma cewa "kina sonshi?" Khairi ta kuma cewa "sossai dada" ta furta idonta a runtse................
Tana ji dada tace "Toh shikenan khairi Allah ya tabbatar da alkhairi, amma kin fad'a musu wacece ke?" Khairi ta kuma cewa "Eh" dada tace "toh Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" Khairi tace "Ameen" kwanciya sukayi don dare yayi kowa da tunanin da yakeyi a ranshi..................
Washegari tayi duk house chores d'inta kan ta fito dada na mata adu'ar sa'a se kuma fad'an kare mutuncinta, ta rasa dalilin tashinta cikin farin ciki yau, bayan ta isa direct kitchen ta nufa ta fara aikinta cikin tsanaki tanayi tana er wakanta da fillanci har ta gama ta shirya akan dining tana sauka daga wurin taci karo da su miemie da saukowarsu kenan gaisawa sukayi cikin fara'a Amrah na tambayarta Ina su nabeel tace sun tafi makaranta................
Amrah tace "wai kin karyane?" "Eh wallahi na karya a gida, bari In karasa aikin nan In zo" wanke wanke tayi ta fito ta samu momma ma ta fito har kasa ta duka ta gaisheta amsawa tayi cikin fara'a tana tambayarta dada, tace dada na nan lafiya, momma tace "dama akwai maganan da nake so muyi yanzu ki shirya ku fita da Amrah Musharraf ze kaiku makarantansu yayi miki registern waec da neco, sbd kinga ba halin ci gaba da karatu mussamanma In anyi auren, zaki dinga zuwa lesson da Amrah na two weeks kan fara paper"....................
Cikin farin ciki khairi tace "na gode momma" momma tayi murmushi kawai ta kuma cewa "In kun dawo Ina so in d'aukeki zuwa gidanku Dan magana da dada" Khairi tace "Toh" tare da mikewa ta shige d'aki, tana shiga ta daka tsalle cikin murna dama tana da burin ci gaba da karatu a rayuwanta gashi burinta na shirin cika ba abinda zata d'auka don hijabinta na jikinta dama ba cirewa take ba, fitowa tayi cikin zumud'i................
Se kuma ta d'an dakata hanganshi da tayi akan dining yana karyawa hannunshi rike da waya yana dannawa at same time, a tsakiyar parlorn kuma Nuriyyah ce da miemie da Amrah, nuriyyah sanye da kayan bautar kasanta se after dress baki da ta d'aura a saman, kanta sanye da half hijab fari, Miemie ce tsaye a gabanta tana mata magiyar dan Allah ta bata aron phone d'inta ta yi kira don wayanta ya fad'a ruwa ta gayawa Hamma musharraf kuma be ce komai ba...............
Bata sa ran samu nan kusa ba don Amrah ma tun kan ya koma wanchan karo wayanta ya Sami matsala shikam little ce ma ta yar, kuma ta fad'a mishi amma har yanzu fin wata be saya mata ba, harara nuriyyah ta sakar mata kan tace "bazan bayar ba fa gwara kin nemi me baki, kinga ma tafiyata" juyawa tayi ta fice tana mata gwalo, Amrah dake zaune tana ta aikin dariya ta watsawa harara kan ta wuce sama fuuu kaman guguwa...............
Musharraf dake zaune dining khairi ta kallah wadda yayi tamkar be san da wanzuwarsu a parlorn ba se ma harkan gabanshi da yake ran nan had'e kaman be ta'ba dariya ba, wurin Amrah ta nufa tare da zama a kasa Amrah tace "TBest ban son gulma fah da fulako me na zama a kasa bayan ga kujeru" harara ta bankawa Amrah akan lips d'inta tace "Ina ruwanki" waro ido Amrah tayi tace "eyeeeh ashe, na manta gwaninta be kar'bi kare ba" Shiru khairi tayi mata idonta na kan tv da ake maimaicin tarkon kauna a arewa 24......................
Itama Amrahn shi take kallo jikinta sanye da uniform tunda ta shiga ss3 zuwa makarantan se a hankali balle kuma da suka fara lessons kawai se kusan past 10 take tafiya ta dawo 2, mikewa musharraf yayi yana gyara rigan half jumpha na getzner dake jikinshi maroon color, kallon Rolex watch silver dake d'aure a tsintsiyar hannunshi dake cike da gargasa yayi kan ya zaro tissue ya goge bakinshi tare da saukowa daga kan dining d'in kallon Amrah yayi da kai ya mata alamar su tafi..................
Ta'ba khairi Amrah tayi tace "ke tashi mu tafi kinga yau na lura Hamma musharraf A dinne a goshinshi baki ga da yadda ya gaida momma ba kaman ana mishi dole" mikewa khairi tayi tana murmushi fitowa sukayi se suka ganshi a cikin motan momma da ya kasance light brown Mercedes benz, da sauri Amrah ta shige baya, tare da rufe kofan, d'an tsayawa khairi tayi kan ta bud'e bayan itama da niyyar shiga...................
Taji husky masculine voice d'inshi na cewa "uban waye driver d'inku?" Sake kofan tayi tare da bud'e gaba ta shiga, lumshe ido yayi yana mamakin kamshin turarenta a zuciyarshi yace "Ashe ba irin kazaman masu aikin nan bace" da oud 24hours take anfani oil d'inshi wadda be wuce 250 ba, duk kamshin jikinshi da kamshin motan be hana shi shakan sassayanyar kamshinta ba, ta'be baki yayi tare da yin reverse da motan ya fice...................
Gombe high school suka je, Amrah tayi hanyarta tana cewa khairi "se na dawo" tana kallon musharraf Tace "Hamma thanks" be ko kalle ta ba balle ta sa ran amsawa, bayanshi khairi tabi ganin ya fara tafiya tana tafiya tana kallon en matan school din yadda suke ta kallonshi kaman sun ga sabon hallitta musamman en ss3 masu zanawa...............
Ta'be baki tayi tana sake tsiririyar tsaki ganin yadda en matan gabansu suka wani chanza tafiya daga d'aura ido akanshi, a haka suka karasa office na principal a take yayi mata registration na waec da neco ya kuma biya kudin uniform kala biyu, a take aka je da ita aka bata yana nan zaune ta fito ya mike yana ma principal d'in godiya cikin harshen turanci kan ya fice tabi bayanshi.................
Seda sukayi nisa da tafiya kan tayi gyaran murya a hankali tace "Ina kwana?" Seda ta fidda ran amsawanshi kan taji yace "se yanzu kika ganni?" Waro ido tayi kan ta ta'be baki tace "Dada tace In maka godiya taga kayan da ka sayowa su nabeel mun gode" seda ya nisa tukun don kanshi yace "ce miki akayi don ke nayi" Shiru tayi bata kara magana ba har taga sun shiga wani wuri da alamun filin saida wayoyine ba tare da ya mata magana ba ya fice...................
Kusan 30mins tukun taga ya shigo nan ma be ce mata komai ba yaja motar suka wuce gida yana parking taga ya ajiye mata wani Leda karami da bata san me a ciki ba kallonshi tayi da alamun tambaya tace "wa zan kai wa?" Seda ya ajiye kafanshi d'aya a waje hannunshi rike da irin ledan hannunta guda biyu yace "ki yar" kan yayi wucewarshi zuwa site d'inshi................,,
Baki ta turo gaba kan ta fito ta rufe kofan tare da nufan cikin gida a d'akinta ta yada zango tana bud'e ledan hannunta kwalin waya ta gani na Samsung galaxy A10s budewa tayi tana juya wayan a hannunta golden