Advertisements
Chapter 17 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 38

48K to 51K   out of 113.1K words

kallonta a rayuwanshi be ta'ba tausayawa wata mace ba bayan kannenshi da mamanshi da ershi se wannan wani irin tausayinta yake ji..................

Yana ta kallon yadda take ta fad'an kwachewa har Amrah ta kawo ruwan, a hannunta ya dinga adu'a yana tofawa yana cikin yi momma ta fito da wani rober a hannunta burner ta nufa ta zuba garin tare da kunnawa ta kaishi karshe, a take hayakin ya fara tashi zuwa lokacin ya gama adu'ar da ze yi, yace "watsa mata" Amrah ta zuba a hannu ta watsa mata wani irin kara tayi da ya sashi lumshe ido sam be son hayaniya amma ya ya iya, ihu ta ci gaba da yi na fitan hankali sake ta yayi tayi ta birgima a wurin har suka tafi, hannunta ta sa ta dafe kanta tana mikewa zaune a hankali ta bud'e ido ganin kallon da suke mata da halin da take ciki yasa ta fashe da kuka sossai, karasawa Amrah tayi ta rungumo ta a jikinta hakan ya sa ta kara karfin kukanta tana boye fuskanta.....................

Mikewa yayi ya fice yana jin tausayinta sossai na yawa a zuciyarshi, part dinshi ya shiga ya ga nuri na kwance little kwance a jikinta har bacci ya d'auke ta, karasawa yayi ya d'agata ya kaita d'aki ya kwantar a kan gadonshi ya dawo parlorn yana adu'ar Allah yasa nata basu tashi ba don In hakan ya faru akwai matsala, a natse yace "nuriyyah" a hankali ta bud'e ido yace "me ya faru?" Kanta ta nuna mai, mikewa yayi ya nufi karamin table dake parlorn akwai jug da ruwa a ciki se cup ya d'auka ya tsiyaya.................

Tare da komawa kusa da ita ya zauna adu'o'i sossai yayi a ruwan tare da mika mata kar'ba tayi ta sha dayawa ta shafa sauran a jikinta, kallonshi tayi taga irin kallon da yake mata hakan yasa tayi murmushi tare da cewa "thanks hamma" mikewa yayi ya shige d'akinshi, ta sanadinta ya iya adu'o'i dayawa na ruqya, cire kayan jikinshi yayi tare da d'aura towel ya shige toilet....................,....













#vote
#share
#comment







'Yar mutan Adamawa



๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—







IGIYAR RAYUWA๐Ÿ˜ญ







๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo


'Yar mutan Adamawa

Pageโžก๏ธ4๏ธโƒฃ8๏ธโƒฃโ–ถ๏ธ4๏ธโƒฃ9๏ธโƒฃ
๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Ba irin rarrashin da Amrah bata mata ba amma ta kasa dena kuka gani take ta rasa aikin nan, aikin da dashi take taimakon kanta da en uwanta, aikin da ta sha wahala kan ta sameshi, rufin asirinsu kenan aikin nan, a hankali momma ta kira sunanta "ummulkhairi" d'agowa tayi tana kallonta ba tare da ta amsa ba tana jira taji ance ki tattara ya naki ya naki ki tafi kin gama aiki damu se ji tayi momma tace "Ashe baki yarda da kaddara ba?" Da sauri khairi tace "wallahi momma na yarda da kaddara me kyau ko marar kyau, ai bazan ta'ba zama cikakkiyar musulma ba se na kasance me yarda da kaddara"...................

Momma tace "good, toh me yasa kike kuka haka? Imani yana da hakika, hakikaninsa kuwa shine kaddara, Allah yana cewa a cikin suratul qamar "mun hallici komai da qaddara" ya kuma cewa a suratul A'ala "shine wadda yayi hallita, kuma shine ya daidaita ta, kuma shine wadda ya qaddara abubuwa, kuma ya shiryar dasu" ya kuma cewa a suratul Furqan "kuma ya hallici ko wani abu, kuma ya qaddara shi, qaddarawa" kiyi hakuri kiyi shiru da kukan nan dan Allah, ko basu ta'ba tashi bane se yau?"...............

Share hawayen fuskanta khairi tayi tace "na gode da tunatarwanki momma hakika na yarda da qaddara, da ban yarda dashi ba da ban kawo nan a rayuwata ba, na yarda qaddara ce ta sa na tankawa hauwa har idi yazo ya tadda mu ya d'auki hukunci, na yarda qaddarar abinda ke jikina yasa na murd'ewa Maman hauwa hannu har hakan ya fusatata ya kuma tunzurata ga ja mana sharri a idon duniya, qaddara shi ya d'auke min Abbana a sadda ban yi zato ba, ban ta'ba tsammanin zan iya rayuwa ba shi ba seda qaddara ya nuna min komai me yiwuwa ne...................

Qaddara shi ya rabani da d'an uwa na wadda muka rayu ciki d'aya mahaifa d'aya na watanni tara, muka fito duniya a tare muka kuma rayu a tare na shekaru 17, muka yi jimamin rashin mahaifinmu tare me makon ya barmu muyi wahalan rayuwa tare a wuri d'aya se ya d'auke mana shi, ya kaishi inda bamu sani ba" kuka ne yaci karfin ta, hannunta momma ta rike tana kallonta cike da tausayawa tabbas tun randa ta fara ganin khairi ta san tana cike da damuwa na wani abin...................

Wadda bata san ko menene ba, haka kawai take jin tsantsar tausayinta, za kuwa ta so jin wacece khairi, maganan khairin ne ya katse mata tunani inda take cewa "Ina kewarsu, Ina kewarsu sossai kuma Ina ganin ni ce sanadiyar komai da ya faru damu a rayuwa, na rasa yadda zanyi, na rasa wadda zan tunkara da damuwata, na rasa wadda zan kwanta a jikinshi inyi kuka iya yina be d'aga hankalinshi ba, Dada baza ta Jura ba, In har ta san ina cikin damuwa itama hankalinta baze ta'ba kwanciya ba, nayi iya kokarina don ganin na boye abinda ke ci na a rai amma abun na shirin fin karfina"...................

Momma tace "zaki iya ummulkhairi, dukda ban san wacece ke ba, na tabbatar bakiyi sanadiyar mahaifinki ba sbd yanayinki da tarbiyarki be nuna hakan ba, In ba zaki damu ba Ina so ki bani labarin rayuwanki, Ina son zama miki gini wadda zaki dafa ki tsaya har ki kai ga cimma nasara a rayuwanki" khairi tace "toh momma zan fad'a miki wacece ni, amma yanzu azahar yayi bari In munyi sallah" Da toh momma ta amsa kan ta mike ta haura, miemie ta zo ganganta ta dafa kafad'arta tare da bubbugawa kan ta wuce itama, Amrah ce ta taimaka mata ta mike sukayi d'akin khairin....................

Anan sukayi sallah tare, bayan sun idar sukayi adu'o'i suka shaafa Amrah tace "bari In debo miki abinci kici kan momma ta sauko" abincin taje ta d'ibo mata, bata wani ci mai yawa ba ta ture, da Amrah suka fito yayi daidai da saukowar momma, miemie, da nuriyyah, zama sukayi, momma a two seater, Miemie a kasa kan rug, don bata cika son zaman saman ba haka Allah yayi ta, se nuri da ta zauna a one seater..................

Amrah bata zauna ba tace "bari In d'aura mana abincin dare" sam bata son sake jin labarin khairi don kuka sossai yake saka ta, don a sadda taji na farko ta jima batayi bacci ba tayi kuka har idonta ya rine seda momma ta tambayeta me ya sameta amma ta boye da abu ne yafad'a ciki, "jollof rice kiyi da nama, se pepper soup din cow-tail" Cewar momma, kitchen din ta shige......................

Gyara zama khairi tayi akan rug din parlorn ta fara da "kamar yadda kuka sani sunana ummulkhairi sunan mahaifina Umar sanda sannan mahaifiyata sunanta safiyya Ali gamji........." sallamar musharraf ce ta katse ta, a hankali ta d'aga kai ta kalleshi shima cikin sa'a kanta idonshi ya fara fad'awa, sanye yake da kananan kaya da alamu be samu yaje sallar juma' a ba sbd ita, tun kafin sallamanshi kamshinshi ya sanar da ita kusantowarshi haka sauyawar bugun zuciyarta, sanye yake da black jeans da red polo shirt me guntun hannu, ba tare da ya tanka kowa ba ya samu doguwar kujera ya kwanta tare da lumshe ido.................

Ba yadda khairi ta iya haka ta ci gaba da bada labarinta daki daki, tun daga kan labarin iyayenta har nasu, har zuwansu gombe da abinda ya faru dasu 'batar d'an uwanta, neman aikinta zuwa ga fyaden da ya so afkawa cikin rayuwanta su musharraf suka ceceta kawo yau..................

Kuka nuri da miemie ke yi bilhakki yayinda silent tears ke bin fuskan momma, musharraf kam be bud'e idonshi ba ma balle In san wani hali yake ciki, khairi ma kukan take momma ce tayi karfin halin share hawayenta tace "kuyi shiru dan Allah kuna kara mata ciwon abinda ke ranta" se shiru su nuri sukayi amma hawaye yaki dena fita sossai tausayinsu khairi ya kamasu, momma ce ta dinga lalla'ba khairi da kalamai masu daadi har ta samu tayi shiru.................

Duk abunda sukeyinย  nan idon momma na kan musharraf tana son sanin halin da ya shiga jin labarin khairi amma yaki bata daman sanin hakan, don ko motsi be yi ba balle ya nuna alamun yaji komai, tun kan ta gama jin labarin khairi take kitsima abu a ranta kuma tana fatan tabbatuwarshi sede bata San ko khairi zata amince ba.....................

A hankali tace "ummulkhairi zaki iya auren d'ana musharraf???" Ba khairi da musharraf ba har miemie da nuri seda maganar ta dake su, da sauri ya mike ya zauna yana warowa momma idanunshin nan, harara ta sakar mishi tana kau da kai tace "ba zan tilasta ki ba, sbd banda wannan hurumin amma Ina mai tabbatar miki ba yabon kai ba d'ana ze iya zama miji na gari a gareki sbd kyawawar halayyanshi, duk da rayuwa ya chanza min shi, amma har yanzu shi dinne de daga ciki, I want my old son back, Ina kwad'ayin miki samun miji kaman shi, a lokaci d'aya Ina mishi kwad'ayin samun mace irinki me kyau, baiwa, ilimin addini da tarbiya...................

Zaki iya zuwa kiyi tunani kuma kiyi shawara, be wise and chose what will be best for yhu and ur family daughter, all the best dear" musharraf ze yi magana kenan suka ji hayaniya daga waje gashi an fara yayyafi duk da musharraf be son shiga ruwa haka ya mike ya fito su momma suka biyo bayanshi, daga kan varendern parlorn ya tsaya yana kallon mai gadi na kokuwa da wani da be sani ba ko don be lura da kyau bane oho................

D'aga hannu yayi ya yafito me gadin hakan yasa ya sake mutumin suka nufo wurinsu tare, yana matsowa kamanninshi na fitowa, wani irin tsawa da ya tsorata dukkansu musharraf yayi inda yace "me ya kawo ka!!!! Me ya kawoka inda muke??? Ka manta mu marasa anfani ne? Ka manta mu kashin tsiya ne? Ka manta ni marar tarbiya ne? Ka manta uwarmu ballagaza ce?"....................

Kuka mutumin da khairi bata san wanene ba ya fashe dashi yana durkusawa kasa ga ruwan se kara karfi yake, cikin sanyin murya yace "na tuba Abubakar ku yafemin, fatima ki taimakamin don Allah na kwanta da yardar 'ya'yana da kuma adu'arsu a kaina, wallahi na chanza ba senator Mahmoud Adam da kuka sani ba ne a da, I'm so sorry for all my mistakes, plz find place in your heart to forgive me ko ba don ni mijinki ba ko ba don ni cousin dinki ba, ko don ni musulmi d'an uwanku".....................

Momma da ta fara hawaye musharraf ya kalla tare da lumshe ido a hankali ya bud'e har sun sauya kala a zafafe yace "baza mu yafe ba, ka fice ka bar min gida wallahi na tsaneka, tsana mafi muni a duniya da Allah ya bamu daman kisa ko da na mutum d'aya ne da kai zan fara kashewa a rayuwata, tirrrr tirrr Ina ma ana chanza uba? Nayi Allah wade da ranar zuwanka du............" tasssssss tasssss momma ta d'auke musharraf da mari hagu da dama a zafafe tace "baka da hankali Abubakar mahaifin da ya tsuguna ya haifeka kake gayawa irin wannan magana? Irin tarbiyan da nayi maka kenan Musharraf??" Baya baya ya fara har ya sauka daga kan varender din ruwa ya soma dukan shi sossai don ruwan ya fara karfi.....................

Da tsantsar mamaki yake kallon momma ya manta when last ta d'aga hannu a kanshi a rayuwanshi gabad'aya amma yau yau sbd wannan mutumin mommanshi me ji dashi ta iya d'aga hannu ta mareshi har sau biyu, hawaye ne ya fara zuba a idonshi wadda In ba ka kula sossai ba baza ka gani ba sbd ruwan dake zuba a kanshi....................

Da sauri nuriyyah ta zo gaban momma tace "momma me yasa zaki d'aga mishi hannu bayan ya fad'i gaskiyar abinda ke ranshi? Ba hamma musharraf kad'ai ba ko ni bazan iya yafewa wannan mutumin ba ko kin manta halin da ya jefaki a ciki? In kin manta naki na san baza ki ta'ba manta nawa ba, In kuma shima kin manta na tabbatar ko za'ayi duniya sau nawa ne baza ki ta'ba manta na hamma musharraf ba, yanzu akan wanchan azzalumin kika mari hamma?" ..................


Juyawa tayi kan baban nasu tace "A rayuwana ban ta'ba ganin mutum me son kanshi irinka ba, duk abinda ka mana be ishe ka ba se ka dawo ka rabaย  kan mu? Hakan da kakeyin kana tunanin ze sa mu soka? To Albishirinka hakan sede ya kara mana tsananka, tsana kuma wadda tafi ta yanzu" momma tace "nuriyyah plz" nuriyyah da yanzu take kuka on top of her voice tace cikin tsawa "then he should leave and never come again".....................

Kallonshi tayi tace "leaveeeee!!!!!" Cikin muryan kuka kuma a tsawace, mikewa yayi yana kuka ya fice, musharraf dake tsaye kaman gunki ne ya fara layi basu ankara ba se fad'uwarashi suka ji, da gudu sukayi kanshi momma dake kuka sossai ne ta fara jijjigashi tana kiran "musharraf musharraf Dan Allah ka tashi, no plz kar ka min haka wallahi ba da niyya na mareka ba, musharraf! Musharraf!! Musharraf!!!"....................

Mai gadi ne yaje da gudu ya kira drivern momma da na musharraf din suka zo suka sashi a mota, Amrah da zuwan baban nasu ta fito itace taje da gudu ta d'auko musu hijabai, momma ta kalli khairi tace "plz khairi ki kula da zarah dake site din musharraf" bata jira amsanta ba ta bisu, da gudu suka fice zuwa asibiti, FMC suka je take family doctor d'insu ya kira wasu doctors din suka rufu kan musharraf da numfashi ke shirin barin kirjinshi.................









*ga na gobe๐Ÿ˜Š don gobe baza ku jini ba*









#vote
#share
#comment








'Yar mutan Adamawa



๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—







ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  IGIYAR RAYUWA๐Ÿ˜ญ







ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย ย  ๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย ย  'Yar mutan Adamawa

Pageโžก๏ธ5๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃโ–ถ๏ธ5๏ธโƒฃ3๏ธโƒฃ
๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—๐ŸŽ—

Musharraf ba shi ya farka ba se bayan magrib, a hankali ya bud'e ido yana kallon momma dake zaune kan sallaya tana karatun Qur'an a wayanta, mayar da idon yayi ya lumshe yana tunanin marin da momma ta mishi sbd mutumin Chan, duk tunaninshi yayi ya rasa me yasa momma ta mareshi don ya gayamishi abinda y dace dashi da rayuwanshi....................

A hankali ya mike ya zauna tare da gyara pillown da yake kai zuwa bayanshi ya jingina yana taune lips sbd kanshi da ke Sara mishi da jirin da yake ji, motsin shi ne ya sanar da momma farkawanshi tsayar da karatun tayi tana kallon gadon, ganin da gaske ya farka ne yasa ta mikewa tana cewa "sannu musharraf"....................

Kai ya gyad'a ba tare da ya kalleta ba, a hankali tace "wai kai se yaushe zaka girma ne ka san abinda yake daidai da wadda ba daidai ba?" Tura lips dinshi yayi ba tare da yace komai ba, seda ta kuma cewa "ba da kai nake ba musharraf?" Yace "Toh ni momma me kuma nayi bayan ba nine da lefi ba kika mare ni gaban kannena da masu aiki" murmushi momma tayi tana girgiza kai tace "Toh yanzu fushi kake da ni kenan?" Kara tura bakin yayi ita kuma ta saki murmushi tana cewa "Toh kayi hakuri, na san ba lefinka da be maka abinda ya maka ba da baka fad'amishi ko wacce kalma ta fito daga bakin ka ba"........................

Ajiyar zuciya ta sauke kan ta ci gaba "Ina kwa'bar ka ne don bana son Allah ya kama ka da laifi, sbd uba de uba ne ko min lalacewarshi adu'a ne kawai tsakaninku ba wai zagi ba, yanzu In ni ce nayi maka haka haka zaka dinga zagi na?" Had'e rai yace "subhanallah ki dena kwatanta kanki dashi plz momma, baza ki ta'ba ko da kwatanta abinda ya aikata ba" girgiza kai tayi tace "In yana cikin kaddara na dole hakan ya kasance ko da kuwa bana so, shi yasa nake so ka yarda kaddaranshi kenan, ku yafemishi tabbas ya tuba, don naga hakan" Shiru yayi be ce komai ba....................

Kanshi ta ta'ba jin jikinshi har yanzu da zafi yasa ta mikewa tace "bari na kira doctor zazza'bin nan be sauka ba" hannunta ya rike yace "a'a momma zanyi sallah tukuna ko la'asar banyi ba" duk maganganun da yake yin nan muryanshi ba wani fita yakeyi ba sbd mura da ciwon kai, bowl ta samo mishi a toilet da ruwan gora ta rike mishi yayi alwala don ba ze iya mikewa ba sbd jiri haka yake mishi In har jininshi ya hau...............

A zaunen yayi sallah yana idarwa ta sa mishi pepper soup da Amrah tayi, da kanta ta dinga bashi har ya ce ya koshi, magunguna ta 'balla mishi wadda bata jima da sayowa ba, yana 'bata fuska yana komai haka ta sashi sha dole, yana gama sha doctor na shigowa da fara'a ya mishi sannu da jiki amsawa musharraf yayi yana d'an murmushi....................

Dube dubenshi yayi kan yace "masha Allah, Dan Allah ka kwantar da hankalinka samun jinin da ya hauran nan ya sauka" murmushi kawai musharraf yayi ba tare da ya ce komai ba, fita doctor Aslam yayi don ba yau ya san halin musharraf ba, momma tace "ga jallabiya nan ko zaka chanza" kar'ba yayi ta fice daga d'akin bayan wasu mintuna ta dawo da waya sakale a kunnenta tana kallonshi ya chanza zuwa jallabiyan brown color sossai ya mishi kyau kaman ba shine mara lafiya ba........................

"Eh yaya, amma da sauki sossai a'a hawan jinin ne de, toh mun gode se da safe" tana kashe wayan ta kara danna wani layin bayan an d'auka suka gaisa tace "Rabi'ah ya kk ya su afreen?" Be ji me

17 / 38