Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
da ta kirasu dominshi, murmushi ta saki tace "muna hanya gobe idan Allah ya kaimu" wani irin ihu suka saka cikin jin daad'i maida idonsu da zasuyi kan wayan suka had'a da musharraf Ai da gudu suka watse suka bar fuskan wayan na kallon gini, murmushi ya saki yayinda khairi ke dariya harda rike ciki.
Kallonta yake tayi yana mamakin mutanen da suke cewa In ka auri mutum sonshi raguwa yakeyi a zuciyarka, shi kam be gani ba sema sonta da kaman kara mishi a keyi a kullu yaumin sossai ya shagala da kallonta har be san sadda ta gama dariyar ba se iska me kamshin strawberry da ta hura mishi a fuskanshi hakan ya sashi lumshe idon ya kuma ware a kanta a hankali yace "Ina sonki ummu Abdurrahman".
Juya ido tayi alamun tunani kan tace "waye ummu abdurrahman kuma?" Yace "ke mana duk kika haifi d'a namiji Abdurrahman Sudays zanyi naming d'inshi don Ina son sunan" shagwa'be fuska tayi tace "zan iya kuwa baby? Baka ji su Amrah na cewa Adda nuri na wahala ba?" Yace "I didn't believe them me yasa muna waya da nuriyyah bata ta'ba sanar da ni ba? And more over Ai kowa da yadda pregnancy dinshi ke zuwa so plz ki manta da maganansu" shafa cikinta yayi yace yana karya wuya "ni kam Ina mamaki duk irin jarumta na dinnan ace har yanzu banyi ajiya anan ba?".
Baki ta turo tare da ture hannunshi wayanta ta d'auko ta kira momma ta sanar dasu zuwansu, haka ma dada nan kam ya kar'ba suka gaisa da dadan da kuma twins, nan fah ta shiga group din family d'insu ta sanar da shigowarta gombe a goben don saura kwana uku a fara events d'in bikin su marwa duk ankon da za'ayi sun turo mata sample ta nema a nan abujan telan su Afreen ya kashesu da styles d'inshi masu tsananin kyau aka goge mata sune ma kasan akwatin tafiyansu.
Bayan ta gama wayoyinta ne ta dubi musharraf dake kwance rigingine ya zuba mata idanu tace "baby lafiya kuwa irin wannan kallon?" Yace "wallahi kyau kika min bana ta'ba gajiya da kallonki hasken idaniyata Ina sonki har ban san adadi ba, a tsakankanin da kika shigo rayuwata ban ta'ba zaton zan fad'a irin wannan komar son ba ko da ance zan fad'a to tabbas me rabani da wadda ya fad'a d'in se Allah.
Amma gashi yau Abubakar Assidiq (musharraf) ya zurma ciki yayi Nisan da baya jin kiran, idonshi yayi rufewar da inba tauraruwarshi ummulkhair ba baya ganin ko wacce mace a matsayin mace se ma maza 'yan uwanshi da ya maishe su" fuskanta ta matso setin nashi tana d'an hawa jikinshi tace "ummulkhair ma na tsananin son mijinta, hasken rayuwanta, me cetonta har yau Ina jinjina tsayuwa da kayi ka ceceni a lokacin da wasu suka so keta min haddi na tabbatar da kai ka so hakan ne sbd kaine me driving a lokacin kuma kai ka fara fitowa kan haidar, sannan ba'a mamaki da ikon Allah baby, Allah shi ke sawa bawanshi son wadda ya so a lokacin da ya so, zaka sha mamaki In na ce maka tun daga randa na fara d'aura idona a kanka a arabian estate na fad'a tarkon sonka me tsanani da azaba so me hana bacci..." katseta yayi ta hanyar maidata kasanshi yayi mata runpa da broad bare chest d'inshi.
Yana kallon tsakiyar idonta yace "ya isa haka qalbee In ba so kike zuciyata ta fashe da kalamanki ba, dukda kin riga fara sona amma kuma na fi sonki yanzu akan son da kike min, kece numfashi na, In har bakya tare dani to tabbas na dena numfashi kece hasken idaniya na a duk sadda kika barni to bana iya gani sbd kin tafi da hasken dake haska min hanya ta cikin idanu na, kece fitilar zuciyata a duk sadda kika dusashe toh fah zuciyata bazata kara wani anfani ba sbd ba jigonta kinyi kane kane a cikinta, bana iya kwararren minti guda ba tare da kwalkwalwana, zuciyana da kuma numfashina sun ambaci sunanki ba, wallahi ban san iya son da nake miki ba, Ina miki....." bakinta ta rufe da nashi duk tsikar jikinta na tashi kalamanshi na narkar mata da zuciya.
Amsa yayi ya fara aika mata da wasu irin darrusa da ita kad'ai ce me iya fahimta har tayi hadda ta kuma rubuta gwajin aji da jarabawa a kanshi ba tare da ta kuskure ko abu guda ba, ita kad'aice me fitowa da flying colors a wannan class na malamintan, zamewa nayi waje kan waennan malama da d'aliban su rutsani, sossai suka nunawa juna irin son da sukeyiwa juna bayan sunyi wanka ta saka mishi akwati biyu a gaba tana mika mishi kaya yana shiryawa nata ya fi girma komai ta d'auko ta miko.
Dariya da mamaki suka kamashi yana dariya yace "qalbee Ina zaki da waennan kayan? Ba de planning barina kikeyi ba don wannan yafi karfin sati biyu sede shekara biyu" turo baki gaba tayi tace "baby me abun dariya anan? Duk fah zanyi anfani dasu" yana ci gaba da murmushi ya girgixa kai ashe da gaske ne da aka ce duk inda mace take bata rabo da tarukucen kaya yanzu dan Allah ina zata kai duk waennan kayan, be kara cewa komai ba se dariyan da yakeyi jefi jefi yana kallon akwatintan, Ai kuwa ta turo bakin nan kaman ze ta'ba gini hakan kuwa kara bashi dariya yake.
"Kina da kyau" ya fad'a In a whisper kallonshi tayi ya d'aga mata gira tare da kashe ido, murgud'a mishi bakin tayi tare da ficewa daga d'akin yana murmushi ya ja musu zips d'in akwatunan tare da d'agawa ya jingina da jikin wardrobe jallabiya ya sanyo sbd su nasreen da suke nan ya sauko kasa d'akin da suke sauka ya kalla dayake dad da Abban gombe sun turomata da kayayyakin d'akin, kokonto yake na inda ta shiga daga karshe d'akin little ya bud'e se kuwa suka had'a ido tana tsaye tana shirya mata kayanta cikin akwati yayinda little ke zaune bakin gado tana zuba mata surutu.
Ciki ya karasa ya biyewa little sukayi ta surutu har sukayi nasarar sata dariya harda rike ciki cikin farin ciki da kaunar juna suka fito khairi na cewa "yau na bar baba A'i da aiki" me aikin da hajiya ruqayyah ta turo musu mijinta ya rasu kuma bata ta'ba haihuwa ba gashi ta manyanta don zatayi sa'a da momma hakan yasa suke girmamata kaman ba me aiki ba, bayan su musharraf sun zauna ta kawo musu natural lemo da take harhad'awa ta sa a fridge a gabansu ta ajiye da cup ta wuce kitchen don duba baaba A'i.
A daren su nasreen suka tafi don samun su had'a kayan da zasu tafi dashi washegari karfe goma cip suka had'u a airport ba wani 'bata lokaci suka sauka a gombe motoci biyu suka zo taryansu daga gidan momma Inda ba 'bata lokaci suka isa har parlor momma tayi musu iso Bayan gaisuwa da sannu da hanya ta gabatar musu da abinci dayake 'yan boko ne ba wani fulako suka zauna suka kwashi gara.
Momma kam farin ciki kaman ya kasheta don ganin yadda tilon d'anta ya koma gashi kulawar da khairi ke bashi a gida haka take bashi a gaban kowaye don shi ya koyarmata da hakan Bayan sun gama ci suka koma parlor inda khairi tace "momma banga su Amrah ba" bata rufe baki ba suka shigo parlorn ihu suka saka tare da nufarta suka rungume suna jin daad'in ganinta tsaki musharraf yaja yana girgiza kai bayan gama oyoyo d'insu musharraf ya dubi momma.
"In zaki lura da wanchan zaki ga irin kaman da sukeyi da qalbee ko momma?" Ta kalli Abul tace "kwarai kuwa" yace "toh shine twin brother d'inta" nan ya basu labarin yadda ya tsinci kanshi a hannun muggan mutane da yadda ya tsira momma salati ta dingayi tana mamakin halin mutanen duniya maganan musharraf ne ya katse mata mamakinta "yanzu na tara familyn Alhj Abba Umar suna jirana da surprise da nace zan musu" mikewa momma tayi tace "Toh ku tashi mu tafi" mikewa sukayi suka fito, ababban parlorn inna suka tarda mutanen gidan gabad'aya zaune, sallaman Abul ne yasa dada mikewa da karfi.
*Aslm kwana biyu kun jini shiru banji daad'i bane na lalla'ba na yi muku ba don na warke ba se don kar nayi ta ajiyeku jira zanyi briefing in shaa Allah 2-3 pages left*
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️9️⃣6️⃣▶️9️⃣7️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Da sassarfa ya karasa ya fad'a jikinta yana jin kewan mahaifiyarshi na dawo mishi sabo hawayen tausayin kansu ya ci gaba da sulala daga idanunshi, mutuwar tsaye dada tayi na mintuna abunda bata ta'ba mafarki ba, bata ta'ba sa rai ba, ko a kiyasce bata ta'ba kiyasta ganinshi yanzu ba sede ba'a mamaki da ikon Allah, Allah aka ce yafi gaban komai yau gashi bata mutu ba Allah ya had'a ta da d'anta da ta fidda ran ganinshi kuka ta fashe dashi tana tuna rayuwansu na baya.
Khairi da tayi narai narai da ido alamun itama kukan zatayi suka had'a idanu da musharraf harara ya sakar mata hakan yasa ta mayar da hawayen nata don dole inna ce ta katse shirun parlorn da cewa "Kai Habu menene wai ka wani tara mutane ba tare da wani jawabi ba kwatsam wani katon saurayi yazo ya fad'a jikin safiya yana ta kuka kaman wadda akayiwa mutuwa" murmushi musharraf yayi yace "Abulkhair kukan ya isa haka plz saketa ka samu wuri ka zauna, inna yanzu zamu miki bayani" sake dada yayi ta zauna shima ya zauna a gefenta tare da riko hannunta se a lokacin yaji kunyan abunda yayin ya kamashi ganin mutane dayawa a parlorn don duk familyn an had'u sbd bukin da suke dashi.
Cikin natsuwa Alhj Abdulrashid yayi musu bayanin kanshi da yadda ya samu Abul inda yana ajiye aya Abul ya d'auka ya musu bayanin bayan fitanshi gida da abunda ya faru dashi inna kuwa ta dinga zagin waenchan mutane yayinda Abba ya sha Adu'a dada ma sossai ta mishi godiya murmushi kawai yayi nan 'yan matan sukayi waje haka hajjiya ruqayya, dada da momma sukayi d'akin dadan inna ma ta tafi d'akinta yayinda haidar da su Jamal suka ja musharraf zuwa part d'in samarin gidan.
Drinks aka kawo wa iyaye mazan inda shafin hira ya bud'e anan Alhj Abdulrashid ya amayar da abunda ke ranshi don d'an boko ne tsantsa be iya rufa rufa ba, sunyi murna sossai inda suka ce zasu tuntu'bi dada, a bangaren musharraf kuwa suna de zaune da su jamal se hiransu sukeyi amma shi kam be sa musu baki ba sam sede abun dariya yayi murmushi, haka 'yan matan da suka kasance su goma sha d'aya chas a zaune a parlorn mommy suna shan hira amare da Adda fadeelah suna site d'in umma little ita kad'ai zaune a parlor tana kallo sbd su nabeel suna makaranta haka Ameer ma, a gaba suka saka khairi da su Amrah suna rokonsu su dawo gidan nan da zama har a gama buki, murmushi kawai khairi takeyi tana ayyana yadda zata iya rabuwa da musharraf na sati guda ta san shima ba yadda ze yi ba sun riga da sunyi shakuwar da ko kwana d'aya da kyar zasuyi In ba sa tare da juna.
Amrah ce ta dubi su Asiya tace "tab ku gama 'bata nyau bakinku kuyi shiru don wannan Juliet d'in baza ta iya rabuwa da romeo d'inta ko na awanni biyar ba bare kwana bakwai" harara khairi ta sakarwa Amrah yayinda 'yan matan suka kwashe da dariya tana murmushi tace "seriously baby baze yarda nayi kwanakin nan ba tare da shi ba amma ku gwada tambayarshi wala alla ya yarda".
Hafsat tace "kaji 'yar air kema kin san ba yarda zeyi ba shine zaki turamu ya dizga mu" Asma'u tace "bare ma yadda yake wani ciccin magani yake 'bata ran nan Ina muka ga fuskan tambaya" Afreen tace "bari zan gwada tambayarshi" murmushi kawai khairi tayi tana girgiza kai kan wayanta ta maida hankali ganin yana haske sakon musharraf ta gani inda ya turo "You are everything I think about. Yes, I am mad. I am madly in love with you." Murmushi me kyau ta saki tana girgiza kai ta fara replying.
"My very existence revolves around you. I am nothing without you my sweetheart. And I love yhu too baby" ajiyar zuciya ya sauke yana sake murmushi me sauti haidar yace "hmmm wannan irin unique dariya haka na tabbatar kanwarmu ce sila so pay for it" harara musharraf ya sakar mishi suka kwashe da dariya musharraf yace "Ai let me tell yhu something da baka sani ba no amount in this world that can buy this happiness neither gold nor diamonds, kai gaskiya ya kamata wadda be yi aure ba yayi aure don wollah duk wadda be da aure be san abunda ake kira happiness, natsuwa da enjoyment ba" waro ido su jamal sukayi don sun san da su yake tunda haidar na da aure.
In disbelief bashir yace "Lallai ma musharraf dama ka iya zolaya?" Faisal kam se dariya yake jamal yace "kwantar da hankalinka muma mun kusa angwancewa muji abinda kukeji" musharraf yace "yhu are not serious da kun shirya da munji a kasa" haidar yace "Ai ko gashi har sun fara zama tuzurai" dariya musharraf ya sake yana kallon faisal da ya fusata kaman ze naushi haidar kan shima ya fara 'bula shi nan fah suka fara tsokanansu suna musu dariya tun suna jin haushi har suka komar da abun wasa.
Se yamma lis su musharraf suka shirya tafiya zasu wuce da su nasreen yayinda Abba ze kama hotel ba yadda su daddy basuyi da shi ya kwana anan ba yaki Abul kam nan suka barshi 'yan matan gabad'ayansu suka rako su parking lot su nabeel na ta shagwa'ban zasu bi su sbd little da suka gani amma dada ta ki sun dawo suka samu hammansu ya dawo inda daad'i kaman ya kashesu ganinshi.
Kasa kasa hafsa tace "Afreen tambayar mana shi mana" kallon shi Afreen tayi zuciyarta na tsinkewa gaskiya baza ta iya ba yadda ya had'e rai kaman be ta'ba dariya ba yasa tsoron tunkararshi ya shigeta kaman ya san zasu so hakan dama seda ya raya a ranshi khairi zata so tambayarshi kwanaki anan abunda baze yarda dashi ba kenan.
Har suka ja motarsu suka fice daga gidan fuskan nan nashi ba a sake ba, a d'akin nuri momma ta sauke afreen da nasreen yayinda little ta sauka d'akinta, khairi kuma part d'in mijinta ta yada zango, kullum sede suje gidan buki su yini su dawo, ranar d'aurin aure da safe khairi suna zaune daga parlorn hajiya suna jin d'aurin auren da ake daga nan sbd a kofan gidan ake yi, kaman daga sama khairi taji d'aurin auren da akayi daga karshe inda maroka suka fara sanarwan 'an d'aura auren safiyya Ali gamji da mijinta Alhj Abdulrashid hameed' khairi is beyond shock abunda bata ta'ba zata ba bata ta'ba kawo hakan a ranta ba, sossai ranta ya sosu taji ba daad'i.
Bawai don auren da dadan tayi ba se don rashin fad'amusu Ai ya kamata ta fad'a musu amma suji abu daga sama haka sam ba daad'i bata gama tunaninta ba taji nabeela na cewa "Adda Khairi dada d'o nyaune"(dada na kira) kallon su nasreen dake ta murna tayi kan ta mike ta nufi sauka daga saman zuwa part d'in inna, "salamu alikum" ta furta a sadda ta sa kanta a d'akin na dada.
Dada da Abulkhairi ne suka amsa ta karasa ta zauna a sanyaye tace "dada gani" Shiru dada tayi na mintuna sama da biyar kan tace "na san ban kyauta ba, na san bazakuji daad'in auren da nayi ba tare da shawaranku ba, nima ban san da gaske zanyi auren ba seda aka fara zartar da d'aurin auren su Marwanatu, tun randa kuka zo gidan nan da dare inna ta kirani take fad'amin abunda Abdulrashid yazo dashi inda take sanar dani yace tun kan zuwanshi tun be ganni ba be san ya nake ba ya kudiri aure na, sbd labarina ya matukar bashi tausayi.
A lokacin na nunawa inna ban yarda ba, ba yadda batayi ba naki, su Hamma muddasir ma sun yi sun yi naki, inda suka bashi hakuri amma shi kullum se ya zo yayi magiya ban fad'a muku bane sbd ban da niyyan auren amma maganganun inna na yau sun karya min zuciya har na aminta da auren a kurarren lokacin da ban samu nayi shawara da ku ba, kuyi hakuri ni karan kaina ban ta'ba zaton auren wani namiji ba bayan mahaifinku ya soni son da ban ta'ba ganin irinshi ba ya zauna dani tun daga farkon zaman mu har karshe ba tare da ido ba amma be ta'ba nuna gajiyawarshi gareni ba bare yayi maganan auro wata, na soshi kaman numfashi na kuma har gobe Ina sonshi, ban so yin wani aure ba sbd Ina son zama shugaban matanshi na gidan aljannah amma Allah be yi ba, Allah yaji kanka Umar ya kai haske makwancinka, ban ta'ba kai kaina kasa da sunan sallah ban nemar mishi gafara ba, ban fata auren da nayin nan ya katse wanna........"
Kuka ne ya sarke ta dama tunda ta fara maganan hawaye ke tsiyaya a idonta, su Abul da khairi ma kuka suka sake suna jin mutuwan ya dawo musu sabo ta'bon na nan ashe be da ranan warkewa a cikin zukatansu, kuka suka dinga yi kaman yanzu ne akayi musu mutuwan inna ce ta shigo da sallama baki sake take Kallonsu d'aya bayan d'aya kan tace "wani irin shashanci ne wannan safiya? Me kukeyin nan? Yanzu fisabilillahi god'e god'e dake ki zauna kisa yara a gaba kina kuka sunayi auren dole aka yi miki?".
Girgiza kai dada tayi tana share hawaye hararan su khairi tayi tace "ko su waennan pakarun ne suka ce miki basa son auren naki?"