Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
tayi saving tare da danna call.
Bayan ta d'aga tace "Khairi ya kike ya gidan ki?" Khairi tace "lafiya kalau Adda, Adda kin ganeni?" Fadeelah tace "wani irin ganewa khairi mun ta'ba had'uwa ko?" khairi ta tuna mata, Take kuwa ta tunata nan ta dinga jimami da dana sanin kin bata aiki da tayi cikin dariya khairi tace "ba komai Adda haka Allah ya tsara kuma Ai ra'ayinki kika fad'amin am very sure har yanzu baki da mai aiki" Fadeelah tace "hakane".
"Adda wani magana nake son muyi dake akan matsala da muka samu da Hamma musharraf" Fadeelah tace "matsala da musharraf kuma? Toh Ina jinki khairi" nan khairi ta bata labarin komai ta karasa da fashewa da kuka, Shiru fadeela tayi na mintuna kan tace "kenan akwai matsala, amma Haka kawai musharraf baze yi miki haka ba sbd hankalinshi da hangen nesan shi why not in ya dawo aiki yau ki sameshi ki roke shi sossai fiye da yadda kikeyi da akan ya fad'a miki laifinki.
Ina kyautata zaton sharri aka yi miki wadda shi kuma ya kasa zama dake ya tambayeki gaskiya ne ko karya don ze ji tsoron amsan da zaki bashi" bayanai ta dinga mata akan yadda zatayi cikin damuwa khairi ke amsata har ta gama bata shawaran suka kashe waya tana mamakin me ta tarewa wani ko wata da zai so kin zaman lafiyanta a d'akin aurenta.
Bayan dawowar little tayi mata wanka tare da sa musu abinci suka ci tare sukayi sallahn kan suka zauna kallo a parlorn har karfe 3 kallon little dake bacci kan cinyanta tun awa d'aya daya wuce tayi tare da saukar da kanta a hankali ta d'aura mata akan trow pillow kitchen ta shiga ta fara harhad'a abubuwan da zatayi aiki dashi na abincin darenta, sossai ta dukufa aiki har seda taji ana kiran la'asar a masallacin dake cikin unguwansu kan ta fito Bayan ta sa zobon da ta gama cikin fridge.
Little ta tasar suka shige d'aki sukayi alwala sukayi sallahn kan khairi ta bata darduma da qur'aninta izu goma da kuma wasu kananan littatafai na usulul thalatha, da hakkul mubeen, fita tayi don ta tabbatar malaminta ya zo Ai ko de ta hangeshi daga bayan rumfar motoci tsaye karasawa tayi ya kar'bi katon sallayar ya shimfid'a musu suka zauna tare da fara d'aukar karatu.
A ciki kuma kitchen khairi ta koma ta ci gaba da aikinta kan magrib ta gama tuwonta na semo da miyan egusi da bitter-leaf wadda yaji stock fish, ta shirya tsab a dining tare da dawowa kitchen ta fara tattare abinda ta 'bata tana gamawa ta shige d'aki tayi wanka tare da alawala don magrib da ya gabato aiko tana fitowa ana kira a daidai lokacin kuma little ta shigo sukayi sallah tare kan taje ta sa mata abinci ita kuma ta dawo daki tare da bud'e alqur'ani ta fara karantawa.
Little na cin abinci musharraf ya shigo rike da briefcase dinshi da alamu ya sha aiki don duk a gajiye ya shigo yana hana kanshi hutu ne sbd be son tunani ya mishi yawa, little dake cin abincinta a tsakiyar parlorn tana kallon cartoon tace "welcome paapi" yace "thanks dear, what are yhu eating?" Yace "your favorite, mommy cooked it bakaji daadinshi ba" murmushi kawai yayi yace "enjoy dear" kan ya nufi haurawa little ta sake cewa "paapi me yasa yanzu baka cin abinci a gida and in kaje Gombe kuma tare muke ci ko da wani lokaci?" Dafe goshinshi yayi tare da cewa "Ina ci mana little" tayi saurin cewa "ni de ban ta'ba gani ba, plz come and eat paapi yayi daad'i sossai ga best drink d'inka ma".
Ajiye briefcase dinshi akan kujera yayi tare da nufan dining ya tsakuri kad'an a plate ya ci be san sadda ya cinye ba ya kuma karawa tun ranar d'aurin aurensu rabon da ya ci abinci yaji yayi irin wannan koshi da yayi a yau hamdala yayi kan ya mike ya d'auki briefcase dinshi ya haura yana cewa little "let me freshen up" da Ohk ta amsa yayi haurawanshi.
Seda isha yayi khairi ta fito tayi mamaki sossai da little tace mata paapinta yaci abinci shi da yace he hates all what will come from her hands, girgiza kai kawai tayi kan ta jata d'aki sukayi isha bag pack din little ta d'auko ta sata a gaba tayi assignment d'inta kan tayi alwala tazo ta kwanta don tana bacci da wuri ita, seda khairi ta tabbatar ta kwanta kan ta mike ta shirya cikin nylon night gown fari me tsantsi sossai wadda ya kai kasan gwiwanta tayiwa kanta feshin Arabs performs d'inta kan ta zura hijabin sallahnta da ya ke sharan kasa ta fice fuskanta fayau Ba komai duk taku d'aya da zatayi na steps din da take bi bugawar zuciyanta karuwa yake.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️8️⃣8️⃣▶️8️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Babban parlorn dake saman ta fara cin karo dashi had'adden parlorn da ya tafi da imaninta komai na ciki sky blue se ratsin fari fari a abubuwa dayawa wani katon wall sticker ne zagaye da parlorn da In baka sani ba zaka ce carpet ne aka manna tsabar had'uwanshi, bata tsaya kalle kalle ba ta bud'e d'akin farko dake parlorn babba ne sossai ba komai cikinshi se abubuwan gym dinshi dumbbell, treadmills da dai sauransu, janyo kofan tayi ta koma na karshe ta bud'e nan kuma ba komai se shimfid'add'an tiles fari da wani carb ward na littatafai kaman library sede litattafan basu dayawa har chan hakan yasa carb ward dinma ya zama daga jikin gini d'aya.
Jikin windown room din kuma study table ne me had'e da kujerunshi guda biyu se kofan toilet dake gefen kofa wurin ya mata kyau sossai musamman da ya kasance d'akin corner room ne, kallon white door din tsakiyan tayi kenan tabbas shine nashi zuciyarta dake ta tsalle ya kasa zama wuri d'aya ta dafe tsoro ne fal ranta amma ya ta iya hakan shine solution.
Seda tayi adu'o'inta kan ta tura kofan da sallama duhu dulum d'akin kaman ba wuta a gabad'aya gidan ko tafin hannunka baza ka iya gani ba sbd an kashe duk wani abu me supplying haske a d'akin, sake sallama tayi a hankali, jin ba'a amsa ba yasa ta juyawa don ficewa se taji an kunna wutan d'akin, a tsorace ta juyo se ta hangeshi zaune chan karshen gado a takure kaman ba gidanshi ba kallon seconds biyu yayi mata kan ya maida kanshi tsakanin cinyoyinshi.
A rud'e take kallonshi sbd hawayen da ta gani ke zuba a idonshi da kyar ta samu ta seta kanta kan ta karasa bakin gadon cikin natsuwa ta zauna a hankali tace "Hamma na zo mu yi maganar fahimta ne dakai, na gaji da irin wannan zama da mukeyi Ina rokon ka don alfarman annabi da alqur'ani ka fad'amin laifin da na aikata a gareka ko zan samu sa'idar azabtar danin da kakeyi".
Shiru yayi kaman baze ce komai ba kan ya d'ago kai yasa hannu ya share fuskanshi cikin dashewar murya alamun ya jima yana kukan yace "me yasa zaki min haka ummulkhairi? Me yasa kika dasa min bishiyar soyayyarki a zuciyata wadda har root din ya mamaye ko Ina bayan kin san you are not pure? Me yasa baki gayamin komai akan hakan ba se kawai inji daga wani wuri kuma a ranar d'aurin aurenmu? Khair me na miki da zafi haka? Am really heartbroken am hurting down there" ya sa hannu a kirjinshi yana mata alama.
Hawaye ta fara yi me tayi ne haka da bata sani ba? Kukanshi ba karamin d'aga mata hankali yayi ba ita kanta ta san abun ba karami bane tunda har yasa jaruminta kuka amma bata da masaniya akan abinda yake cewa hakan yasa tace "I think am confused, Sam ban fahimci inda zantukan ka suka dosa ba" wayanshi ya jawo tare da kunna hasken har hannunshi na 'bari wurin hawan WhatsApp din da kyar ya kai kan numbern ya lumshe ido kan ya mika mata wayan.
Kar'ba tayi tare da kallon fuskan wayan Ai bata san sadda tayi wani irin mikewa ba tana ambaton "innalillahi wainna ilaihi rajiun" jikinta ne ya d'auki rawa har tana kasa tsayuwa a rud'e ta fara scrolling din fuskan wayan Ai bata san sadda tayi wani irin kara ba tare da sulalewa kasa ta fad'i sumammiya da gudu ya sauka zuwa kanta ya d'ago kanta zuwa kan kafanshi tare da sa hannunshi a hancinta ya zata mutanenta ne suka zo se yaga akasin haka don suma tayi chak ya d'agata ya d'aura kan gado tare da zare mata hijab din jikinta da sauri ya shig bayangida ya d'ibo ruwa yazo ya fara shafa mata a fuska zuwa wuyanta.
A hankali yakeyi yana yi yana karewa jikinta kallo, ajiyar zuciya me karfi ta sauke kan ta bud'e ido Shiru tayi na seconds kan ta tuna abinda ta gani Ai a rud'e ta rungumeshi tare da cusa kanta a cikin kirjinshi ta fashe da wani azababben kuka tana girgiza kai a jikinshi muryanta a rarrabe take cewa "wal........llahi ba.... ni ba..... ce, bani bace..... wallahi ban san sadda akayi hakan ba, kar ka ce min ka yarda ban sani ba amma ba ni bace zan iya mata rantsuwa da alqur'ani wani namiji be ta'ba ta'ba jikina ba bayan muharramaina se masu taimako na In jikina ya tashi amma wanchan ba ni bane, wallahi ba ni bace...." magana kawai takeyi cikin fitan hankali da tsantsar rudewa ga kuka da takeyi kaman ana zare ranta ta rasa a wani irin duniya take.
Hawaye ne ya gangaro mishi tausayinta na kashe mishi zuciya dukda be tabbatar da ba itan ce ba ganin tana kakkafewa da alamun zata sake suman ne yasa shi saurin d'agota tare da had'e bakinsu wuri d'aya a hankali ya fara bata wani irin hot kissing da ya fara goge mata duk wani abu dake adane a cikin kwakwalwanta, a hankali a hankali yake tafiyar da ita kaman ze yi kaman baze yi ba kaman kwai haka yake lalla'ba jikinta tun yana iya controlling kanshi har yaji ya kasa a lokaci d'aya ya birkice mata abinda ta san taji daga karshe shine kawai adu'ar saduwa da iyali daya karanto cikin dashewar murya.
Da gudu na fice don kar su lalatawa mamana da mommyna ni, a bakin kofa na makale se after like 15mins na lalla'ba na koma cikin d'akin.
Rungume da ita na hangoshi idanunshi na zubar da hawayen tsantsar sonta da tausayinta na shigarshi wani zazzafar kaunarta yaji yana huda jini da jikinshi har cikin 'bargonshi, farin cikin babu wadda ya ta'ba sanin mishi mata na kara mamayeshi and kuma hakan ya kara tabbatar mishi ita d'in mallakinsa ce shi kad'ai, Toh amma waye ke son d'aura mata wannan sharrin? Waye yayi kokarin raba musu auren da suka gina cikin so da Amana har shiga cikin wannan ginin ya gagaresu?.
Da kyar ya samu hawayenshi ya tsaya a hankali ya mike yana kallon fuskanta a hankali take numfashi hawaye kuma na sauka a idanunta zuwa kan kunnuwanta rungumeta yayi a cikin kunnuwanta ya rad'a mata "am so sorry qalbee, am sorry na kasa tunkararki da maganan tun farko ne sbd tsoron irin amsar da zan samu daga gareki ki yafemin Dan Allah" mikewa yayi ya fad'a toilet d'inshi ya had'a mata ruwa me zafi a cikin jacuzzi dinshi bata ji dawowarshi ba se d'agata da taji yayi tare da zame blanket din, da sauri ta kuma shigewa jikinshi don ba komai jikinta ga kunya kaman ta nitse kasa ga takaici da damuwar tunanin wadda ya so 'bata mata aure, ga haushin musharraf da takeji na kin gayamata da wuri har seda ya wahalar mata da kanshi ya wahalar da ita.
Kara ta saki tana kankame shi jin zafin da ya ratsata yayinda ya ajiyeta cikin jacuzzin cike da tausayinta yace "sorry" nan ma bata tanka shi ba har yayi mata wankan da kanshi ya barta tayi wankan tsarki da kanta dukda yadda kunya ke cinta amma haka ta fuske tayi wankan a gabanshi ko kallonshi batayi ba, towel ya bata ta d'aura d'aga kafan da zatayi don takawa taji wani azababben zafi ya ratsa ta hakan yasata sakin ihu tare da dukawa ta fashe da kuka.
Murmushi ya sake marar sauti wallahi khairi raguwace shi ya tabbatar be yin abu biri biri ko da karfi karfi musamman ta wannan 'bangaren a natse ya bi da ita he's very sure bata ji ciwo ba sede ya san dole zata ji zafi ko kad'an ne sbd ba wadda ya ta'ba saninta kan shi, d'aukanta yayi ya fice da ita zuwa kan gado ya shimfid'e ta kan ya janyo riganta ya sanya mata gashinta daya sauko har kasan wuyanta ya sa towel din ya goge mata sossai kan ya koma toilet da towel din bayan ya ajiye ya fara had'a ruwan wankanshi.
A nan kuma bayan ya kyaleta har ta kwanta se kuma ta mike tare da janyo wayanshi da ta jefar daga kasan gadon ta kunna ta fara kallon hotunan, guda hud'u ne kuma duk ita kad'aice fuskanta ya fito namijin fuskanshi be fito ba, hoton farko zaune take a gaban dressing mirror daga ita se towel karami pink ta sheda towel d'inma nata ne iyakarshi cinyarta.
Gashinta zube a baje da alamu kuma a jike suke, wani ne da bata san ko waye ba tsaye daga bayanta ba'a kallon fuskanshi sbd ya binne cikin gashinta a tsakankanin wuyanta, hannunshi zagaye da cikinta ita kuma ta lumshe idanunta hannunta na d'aure akan nashi. Hoto na biyu kwance take akan kirjin wadda bata sani ba suna tsaye a tsakiyar shower ruwa na zuba akansu anan kam fuskanshi ya fito kad'an kurawa fuskan ido tayi hawaye na ta zarya a idanunta ita Allah ya gani bata ta'ba sanin me wannan fuskan ba amma gata kwance akan kirjin wani a cikin shower da alamu kuma jikinsu ba kaya don har tsakiyar bayanta ana gani.
Hoto na uku zaune take akan kafanshi tana facing dinshi tayi baya da kanta sossai daga ita se wani t-shirt iya cinya ya rike bayanta da hannu biyu tare da binne kanshi a tsakanin kirjinta, hoton karshe suna kwance akan gado tana rigingine shi yana samanta bakinshi cikin nata yana kissing, hannu ta d'aura a bakinta tana sake siririn kuka, wayan taji an zame daga hannunta d'ago kai tayi se ta ganshi tsaye sanye da black three quarter jikinshi ba riga.
Dukar da kanta tayi tana me ci gaba da kukanta zama yayi tare da janyota cikin faffad'ar kirjinshi ya rungume yana shafa bayanta cikin kasa da murya yace "it's Ohk plz kukan ya isa haka it's hurting me" cikin kuka tace "ka duba Dan Allah it looks real wallahi bayan ni ban san sadda akayi ba, ban san yaushe akayi hakan ba" ci gaba da shafa bayanta yayi a hankali yace "na miki alkawari bazan ta'ba hutawa ba har se na gano wadda yayi miki wannan sharrin tabbas ba ke bace amma fuskanki ne hakan ya tabbatar min da editing ne, karki kara sawa kanki damuwa akan abun nan".
A hankali tace "plz komai ya faru irin haka ka fad'amin ba wai ka sani a cikin tunani da damuwa ba, hankalina ya tashi na kashe darare dayawa ido biyu sbd tashin hankalin da na shiga." Kara rungumeta yayi yace "I promise to be by your side forever and for always. I love you. Nothing can do us apart, nayi miki alkawarin bazan kara boye miki magana irin haka ko na dakika d'aya ba" Kai ta gyad'a mishi ya kara sata a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya.
Bayan kaman seconds talatin yace "I am not the best husband in the world. But I promise you one thing, I will work hard every single second of my life to make you happy and make this relationship better each day. Please forgive me." Cikin whisper tace "Apology Accepted" kara rungume ta yayi yace "thanks love, naji daad'i kwarai da yadda na sameki na gode da wannan kyautar mafi daraja a duniya Allah ya miki albarka" a hankali ta amsa da Ameen Shiru suka ci gaba da kwanciya har bacci ya d'auketa, mikewa yayi ya kwantar da ita tare da rufe mata jiki da blanket toilet ya koma yayi alwala tare da d'auro alwala ya fito ya fara nafilfilin godiya ga Allah har seda bacci ya kusa cin karfinshi kan ya zo ya kwanta tare da janyota jikinshi ya lullu'besu seda yayi pecking goshinta kan ya gyara ta da kyau tare da lumshe ido cikin salama bacci ya d'aukeshi.
Asubar fari ya farka ya shiga toilet yayi alwala ya fito se ya kasa tashinta fita yayi zuwa kasa ya wuce masallaci bayan an Idar da sallah ya zauna yayi musu adu'a sossai, kan ya taso zuwa gida d'akinta ya shiga ya tada little ya kaita bayi tayi alwala yazo ya d'aurata kan sallaya kan ya fita zuwa kitchen Kwai ya fasa ya soya har da attarugu ya d'an saka a ciki bayan ya gama ya sa wani a plate sauran yasa a wani karamin beautiful warmer ya d'aura akan wani mini silver tray me kyau, ruwan zafi ya d'aura ya had'a tea na daidai su uku ya zuba a flask karami ya d'aura a gefen trayn tare da sawa little a cup ya ajiye gefen plate din kwanta, bread ya d'auko ya d'aura akan trayn tare da wasu beautiful cups kanana guda biyu ya d'aga warmer din ya sa kananan plate guda biyu kan ya mayar ya d'aura coolern.
Trayn ya d'auka ya haura dashi zuwa d'akinshi janyo center table dake gefen gadon ya d'aura mata trayn tare da komawa jikin wardrobe dinshi ya d'auko joter da pen ya dawo ya zauna tare da yage paper d'aya yayi rubutu akai ya d'an d'aga flask ya ajiye rabin papern na nunawa yadda zata gani da kyau. Kan ya mike ya fice zuwa d'akinta ya