Advertisements
Chapter 3 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 38

6K to 9K   out of 113.1K words

dake shirin fad'uwa da sauri ya saki khairi a guje yaje ya tare mahaifiyar tasu tare da d'aura kanta kan kafanshi yasa hannunshi kasan hancinta a firgice yace "er uwa dada.... dadaa bata numfashi" a guje khairi tayi wurin randa tare da d'ibo ruwa tazo ta zuba mata a fuska numfashi taja me karfi tare da sauke ajiyar zuciya se kuka tana maimaita "Allahuma Ajjirna fi musibatin, innalillahi wainna ilaihi rajiun" suma yaran kar'ba sukayi don su d'an samu natsuwa Ai kuwa maganan Allah se ga d'an natsuwa ya saukar musu khairi ta taya Abul suka d'aga Dada zuwa kan taburma suna ajiyeta Baban sulaimi na sallama a rude ya shigo yake tambayarsu wani labari ne yake ji a wajen nan khairi kam ta kasa magana se sabon kuka da ta 'barke dashi Abul ne ya samu ya mishi bayani, nan yace "Toh ai zama be kama mu ba, tashi maza Abulkhairi muje gidan sarkin muji wani chargi office aka kaishi" mikewa Abul yayi yana cewa "er uwa ki bar kukan nan haka ki kula da Dada" Kai ta gyad'a mishi suka fice inda Dada ke adu'ar Allah ya sa a samu nasara, bangaren Abba kuwa shock ya hana shi fahimtar me akeyi sam be san ya akayi tafiyar ba har suka iso Jalingo devision aka jefa shi cikin cell cikin hantara da bakar magana had'e da zagi, sam hankalinshi yaki dawowa jikinshi balle har yayi analyzing abunda yaji sunce, shi 'umar sanda' yayiwa wata fyad'e? Da sauri ya furta Auzubillahi minnashaid'anir rajeem wani irin dariya polisawa da masu laifi da suke cikin cell d'in suka fashe dashi na tsantsar shakiyanci wani yace "Da kake jin daadi a kan 'yar mutane baka San shed'an ba se da akayi ram dakai toh waye shed'an din anan In ba kai ba?" Suka kara shekewa da dariya hawaye ne ya silalowa malam Umar yana karanta duk adu'ar da tazo bakinshi don samun sauki daga mahaliccinshi.

Gidan sarki su Abul suka fara zuwa inda suka ga tsantasr wulakanci kafin aka fad'a musu police station din da aka kaishi ba 'bata lokaci suka fara tafiya tunda Nisan dake tsakani ba har chan bane, sun isa inda suka nemi ganawa da wadda case d'in ke hannunshi inda aka had'a su da police d'in bayan dogon wulakanci kai tsaye yace ya riga yayi filling case d'in za'a shiga court dashi on Monday su nemi lawyer kawai shine, sun nemi ganinshi ma an hana haka suka taho damuwa fal fuskan Abul tunani yakeyi ta inda ze fara tunda shine namiji babba a gidan shi ze d'auki duk wani nauyi yanzu a shekaranshi ta 17 ta Ina ze fara? Ya san 'yan uwan iyayenshi ba taimakonsu zasuyi ba sema dariya da karin wulakanci da tunanin nan suka isa gida a inda suka bar su khairi anan suka dawo suka samesu zaman akallah awa biyu zama suma sukayi inda khairi ke tambayar "ya akayi D'an uwa? Ba shi bane ko?" Hannu Abul yasa ya share hawayen fuskanshi yace "se adu'a kawai za'a shiga court ran Monday sunce mu nemi lawyer kawai" kuka Dada ta sa dama khairi kam hawayenta tun tuni basu tsaya ba, d'an nasiha baban sulaimi ya musu akan jarabawarshi kenan su ta mishi adu'a ze fito ne in shaa Allahu se da yaga sun d'an natsu tukun yace "yanzu ya kukega za'ayi da batun lauyan ni ba karfi gareni ba balle ince zan taimaka da wani abin" khairi tace "ba komai baba yanzu ma kayi mana abunda baza mu ta'ba mantawa da kai ba, ka riqe mu kaman en uwanka wadda 'yan uwanmun na jini suka kasa" hawaye ta share ta ci gaba da yake khairi nada zurfin tunani se ta kawo wani shawara "me ze hana mu sayar da gonan Abba muyi hayan lawyer?" Abul yace "baze yiwu ba er uwa gonan fa kenan da muke da se gidan nan muka sayar Ina zamu samu kudin abubuwan bukata?" Dada tace "sayarwan shine kawai mafita Allah ze dube mu, kai kana nan kana tunanin abubuwan bukata ina muka samu kwanciyar hankalin anfani da abubuwan bukatan bayan mahaifinka na tsare" Baban sulaimi yace "tabbas shawaran khairi shine abun anfani da, bari zanje In nemo mai saya Allah yasa kar su mana sayen wulakanci don sunga muna kan kafa" Ameen suka amsa gabad'ayansu ya mike har ya kai kofa ya juyo yace "Abulkhairi zo muje ayi komai a gabanka" mikewa Abul yayi ya bi shi daidai lokacin nabeel ya fito yana hamma da kaikaya ido yazo ya fad'i kan kafan khairi yana cewa "Adda khairi velo mi nanata(yunwa nakeji)" se lokacin ta tuna bata d'aura abun karyawa ba mikewa tayi tana cewa "wad'u munyal ha mi defa jotta d'o(yi hakuri bari inyi girki yanzun nan)" kitchen ta shige tana jin fitowan nabeela tana tambayar Dada me yasa yau ba'a tashe su sunje makaranta ba Dada ta ce mata, Abba ne baida lafiya karsu damu zasuje gobe, suka ci gaba da ma Dada tambayoyin 'yan jarida tun tana amsa musu har ta gaji ta kyale su. Farin shinkafa kawai khairi ta dafa ta soya musu mai ta had'awa nabeel da nabeelah se ta sawa Dada tare da d'aukawa ta fito musu dashi nabeelah ce ta kar'bi nasu suka zauna suka fara ci inda Khairi tayiwa Dada bismillah hannu Dada ta sa ta fara ci duk jiki a sanyaye jin bata ji khairi naci ba yasa tace "ummulkhairi me yasa bakya cin abinci?" Khairi da ta buga tagumi damuwa ya nuna sossai a fuskanta bata ma san dada nayi ba, seda Dada ta kara cewa "khairi! Khairi!!" A firgice tace "na'am dada kina bukatar wani abu ne?" Dada tace "ki sa hannu muci abinci, zamanki da yunwa bashine ze sa a sake mahaifinku ba adu'a shine kawai magani" Kai khairi ta gyad'a tare da sa hannu asanyaye ta fara ci bata wani ci sossai ba ta mike tare da d'age kwanon don dada ta dad'e da cire hannu ita dinma karfin hali ne kawai sbd kar yaranta su karasa karaya amma ita kad'ai ta san abunda takeji, su nabeel tayiwa wanka suna ta mata surutu ta kasa amsa musu har ta shirya su, nabeel ya fice wasa yayinda nabeelah ta zauna tana taya khairin lallice kwanonin da suka 'bata, suna gamawa khairi takai kitchen daga kitchen d'in ta fara jiyo kukan nabeel da sauri ta fita tana tambayrshi me ke faruwa yace "Adda ba kinga su Aisha ba naje muyi wasa wai uhm uhm mamanta ta hanata wasa damu wai Abbanmu yayiwa hauwa fyad'e kar wtkl nima halinshi nayi, Adda khairi me fyad'e?" Dafe gini khairi tayi jin wani irin hajijiya da ya d'auke ta juya ido ta fara don hana hawayen idonta zuba amma inaa kaman an bud'e fanfo maimaita innalillahi kawai takeyi don maganganun yaron sun girgizata yanzu har 'yan unguwan nan sun yarda Abbansu zai aikata fyad'e kuma da hauwa? Wait hauwa fah? Zamewa tayi ta zauna dirshan tare da sake kuka mai sauti........








#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa



🎗🎗🎗🎗🎗







                 IGIYAR RAYUWA😭







                                            🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad gurin

          'Yar mutan Adamawa

Page➡️9️⃣▶️🔟
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Wata kyakyawar yarinyace da baza ta wuce shekara hud'u ba an mata d'inkin atampha doguwar riga me kyau kaman ba yarinya ba, gashinta ya zubo har kumatunta ta gaba kasancewar kitson chuku da na gaba da aka mata an kawata shi da beets masu kyau, se tsalle take tana cewa "yes yes Anty Amrah, Anty Amrah" Kallon inda take kallo nayi se naga kyawawan 'yan mata na kokuwa a tsakiyar parlorn akan wani pink t-shirt dake hannun marar tsawon kuma tsiririyar wadda bazata wuce 17yrs ba wacce naji yarinyar tana kira da Anty Amrah se kokarin boyewa take yi a bayanta inda d'ayar da ta kasance doguwa kuma tafi Amrahn ki'ba bazata wuce 18 and half ba, ta samu nasarar fisgewa ihu yarinyar ta saka "yeeeeeeeeeaaahhh Anty miemie!!! Anty Miemie!!" Ci gaba sukayi da kokawarsu akan rigan yayinda yarinyar take ta tsalle tana kiran duk wadda rigan yazo hannunshi, kaman daga sama sukaji ance "Amrah, miemie wai wani irin banzan hali ne wannan? Wai se yaushe zaku girma ne?" Kanta na maida idanuna wow wata kyakyawar mata na gani da baza ta wuce shekaru 49 ba daga kallo d'aya na gane fulanin gombe ce sbd farinsu da ya nuna sossai a jikinta sanye take da atamphar holland riga da zani ta yafa gyale akan d'ankwalin dake kanta kafanta sanye da flat shoe, shagwa'be fuska yarinyar chan tayi tace "ohh no granny you spoiled the fun" zaro ido momma tayi tace "kaniyarki ne zarah, ku kuma sakarkaru daku a gaban 'yarku kuke wannan iskancin dama?" Shagwa'be fuska Amrah tayi wadda itace karama tace "momma ai Miemie ce da neman fad'a sabuwar rigar da Adda nuri ta sayo jiya na d'auka zan saka yau shine fah wai ta rigani se na bata" miemie tayi saurin cewa "karya takeyi momma na fa riga ta d'auka kuma anjima kad'an nake son sawa sbd Ina da lectures don taga na d'auka shine wai se na bata" momma tace "rufemin baki miemie ba kece babba ba? To maza bar mata rigan ita kuma nuriyyahn zata zo ta sameni zata saya muku abu guda d'aya baza ta ce na waye ba kuma baza ta ce ga wadda taba kyauta ba ta barni da raba fad'a" turo baki Miemie tayi tana kallon Amrah inda Amrah tayi mata gwalo a harzuke tace "momma ba kin ganta ba!!!" Momma tace "Auta kika sake mata gwalo se na kwace rigan na bata" sum sum sum Amrah ta haura stairs inda miemie tabi bayanta don zuwa shiryawa ten take da lectures, kasancewarta d'alibar jami'a na gombe state university inda Amrah ke gombe high school sss3, nurriyah kuma tana service d'inta a nan cikin gomben, zarah kuma tana nursery  two itama Gombe high school take, kallon zarah momma tayi tace "Hey little zo kiji" ganin yadda zarahn ke tura baki yasa ta kirata, tana bubbuga kafa ta karaso ta kwanta akan cinyar momman, momma tayi murmushi kan tace "I have some good news" zarah tace "what is it?" Momma tace "your paapi is coming 2morrow" wani irin tsalle zarah ta daka tana ihun murna da gudu ta haura stairs don sanar da Aunties d'inta murmushi kawai momma tayi tare da maida hankalinta kan katon plasman dake aiki a parlorn ganin Bollywood ke aiki yasa ta d'auki remote don mayarwa sunnah tv..

parlor ne madaidaici a saman anyi furnishing dinshi da royals cushion masu tsananin kyau da tsada komai milk da gold ne a parlorn gefe karamin kitchen ne da basu anfani dashi amma akwai komai na bukata Chan gefen kitchen d'in kuma toilet ne babba me kyau, se wani corridor da a ciki d'akunan baccinsu yake, seda zarah ta isa kofar d'akinsu Amrah taja birki don tunowa da yadda suke nuna rashin jin daad'insu In aka ce Paapi d'inta ze zo, fasa shiga tayi ta juya zuwa room d'inta dake facing na su miemie yayinda na momma ke gefenta na nuriyyah kuma na gangan nasu miemie karshen corridor din kuma console ne had'add'e purple an jera wasu turarukan wuta masu kyau daga kasanshi socket ne wadda burner ke jone a jikinshi a kuma kunne yana fitar da hayaki me kamshi kad'an kad'an kasancewar a low aka saka ta, tana shiga ta fad'a kan gadonta tare da jawo wayanta iphone 6plus ta fara game (baki na rike tare da cewa shagali 'ya'yan masu akwai) ........

***
Ta bangarensu Abul kuwa da kyar suka samu mai sayan gonan inda ya tura wani ya gane mishi gonan kaman yadda suka ce ne? Sunje yaga gonan ya kira maigidanshi ya fad'a mishi sallamansu saurayin yayi su kuma suka damka mishi takardun dama sun riga sun gama ciniki akan naira dubu d'ari uku, Ajiyar zuciya Abul ya sauke saura neman lawyer nan suka bazama da kyar suka samu ganin wani lawyer 'Barr Aliyu karofi' inda yace kud'in aikinshi dubu d'ari bayan ya gama sauraronsu da kyar suka samu ya bar musu a 70thousand inda yace suje abinsu ze je ya gana da Malam Umar d'in kan ya shigo unguwar nasu exchanging contact sukayi da Abul godiya sossai suka mishi kan suka fice lokacin karfe 1 na rana dukkansu ba wadda ya karya a galabaice Abul ya shigo gidan tare da samun kan taburma ya zube da sauri khairi taje randa ta d'ibo mishi ruwa ta kawo mishi ba musu ya kar'ba yasha tana ajiye abinci a gabanshi take mishi sannu Dada ma sannu tayi mishi, da kai ya amsa yana kallon nabeel da nabeelah da suke kwance gefen dada suna barci, maida hankalinshi kan khairi yayi wacce ke tambayarshi "An kuwa dace?" Murmushi ya mata tukun yace "eh twiny mun samu mun sayar da gonan akan kud'i dubu d'ari uku, kuma mun samu lawyer wadda ya nemi a bashi 70thousand matsayin kud'in aikinshi" a take fara'a kad'an ya bayyanah a fuskan khairi da Dada sun d'an ji dama dama se faatan Allah ya basu nasara a shari'ahn, bayan Abul ya gama cin abinci ne yake tambayar khairi "er uwa ya akayi waennan sarakan wasan suke bacci yanzu? Ko basu da lafiya ne?" Runtse ido khairi tayi tana Jin zafin abinda zata furta a zuciyanta, a sanyaye tace "mutanen unguwa sun hana yaransu wasa dasu suna tsoron kar su lalata su" zaro ido Abul yayi a hankali yace "what??" Bayanin abunda ya faru d'azu da nabeel ya fita ta bashi inda ta d'aura da "yanzu d'an uwa abinda mutanen unguwan nan zasu saka mana dashi kenan? Koma da gaske hakan ya faru ya kamata su nuna mana kyama da kyara? Har su nabeel yara kanana da basu san me duniya take ciki ba?" Mikewa Abul yayi ba tare da yace komai ba ya wuce d'akinshi jin hawaye na shirin zubo mishi kenan mutane basu yarda da kaddara ba? Ko ma da gaske Abbansu ya aikata abunda ake zarginshi dashi be ci su tausaya mishi ba? Zaman shekaru 19 wasa ne? Katifanshi ya fad'a yana ji komai na duniyan ya fice mishi a rai.........

***
Tsaye yake gaban wardrobe d'inshi yana ta Jan tsaki kaman wani tsaka idonshi na yawo kan kayayyakin gaskiya shi baxe iya saka wani manyan kaya ba ya san kuma In yaje gombe a haka yau juma'a ba tare da manyan kaya ba se momma tayi fad'a maida idonshi yayi kan suits d'inshi kasancewarshi ma'aikacin banki suit sun ninka kowani irin kaya yawa a wardrobe d'inshi se kuma kananan kaya jumpopinshi kam tsab zaka iya kirge su da yatsun hannu janyo wani black suit yayi dake had'e da red long sleeve shirt tare da red neck tie, seda ya saka vest da boxers tukun ya d'auko well ironed trouser na suit d'in ya saka yabi da red long sleeve shirt d'in kan ya d'aura necktie dinshi wurin takalmanshi ya nufa ya za'bo wata cover black se sheki takeyi ya saka ya koma gaban dressing mirror ya feshe jikinshi da mahaukatan turarukanshi dake kashe en mata, brief case dinshi da ya zuba mahimman abubuwanshi ya d'auka tare da komawa bakin gadonshi ya d'auki bakin rigan suit d'inshi ya makala a hannunshi d'ayan hannun riqe da wayanshi ya fice a parlor ya samu me kula mishi da gida me mishi share share da goge goge daniel a tsaye yana jiran fitowanshi ba tare da ya kalli inda yake ba yace "ka kula" yayi ficewarshi Daniel na mishi Allah ya kiyaye a waje ya samu driver d'inshi isa na jiranshi shiga kawai yayi bakinshi d'auke da adu'ar matafiya, ba 'bata lokaci sukayi sallama da garin Abuja zuwa Gombe...

**
Tsaye tayi akan momma dake kitchen tana aikin yiwa d'anta namiji kwaya d'aya tal girki se tura baki take momma tace "Auta wai nikam lafiyanki bance ki gyara min kifin Chan tun d'azu ba?" Amrah tace "momma dan Allah mana laraba tayi wallahi ban son aikin kifin nan ga wancan boss d'in ya wani ce be cin abincin masu aiki ni wlh....." tsawan da momma ta daka mata ne yasata rufe bakin ta da hannu tare da saurin cewa "Afwan momma" kifin ta nufa ta fara aikinshi tabbas basa son ace hamma Musharraf ze zo amma suna sonshi har cikin ransu shine gatansu da ba don shi ba da basu kasance a wannan gida dasuke ciki ba da basu zama cikin d'alibai 'ya'yan masu kudi ba, da basa cikin farin ciki kaman yadda suke yanzu, dukda bata da wayo sossai abubuwa sukayi ta faruwa dasu hakan be sa ta manta waye Musharraf a rayuwansu ba shine katangarsu hagu da dama in ya zube toh suma sun zube yana iya kokarinshi wurin yi musu abunda suke so amma sam basa jin daadin zama dashi Inuwa d'aya kasancewarshi mafad'aci ko motsi me kyau kayi kan iya 'bata mishi rai ya maka tatas fad'ansu na sako da sakon nan ma da sukeyi da miemie duk sbd ba ya nan ne amma In yana nan ko tarin d'ayansu baza kaji da sunan fad'a ba, Allah ya sa ma be yin fiye da kwana biyu, dukan da miemie ta sake mata a baya ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula a masifance tace "kut Lallai Miemie wallahi kinci bashi" miemie na dariya tace "oho de, yau su Anty Amratu ne a kitchen? Me ake dafa mana?" Hararanta Amrah tayi jin ta kirata da sunan da bata so wai Amratu, ganin yadda Amrah ke hararanta ne yasa tace cikin dariya "yi hakuri Autanmu" Da gudu Miemie ta fice ganin Amrah tayi kanta da shirin duka momma bata tanka su ba se murmushi da take tana mamakin irin fad'an sako da sako da sukeyi da junansu wadda baza ka ta'ba gani Musharraf yayi da nuri ba ko don shekaru dayawa ya bata ba kaman waennan ba? Bata sani ba, A parlor Miemie taga zarah se jin daadi take tana ta aikin waya daga jin yadda take wayan ta gane da Ya Musharraf take waya bata jira gama wayansu ba ta

3 / 38